Showing 207001 words to 210000 words out of 262509 words

Chapter 70 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21379

shi saboda labarin su da ya sanar mana." Aunty Sadiya ta yi ɗan murmushi a ranta ta ce. 'Ashe har yanzu tsohuwar zumar tana nan." Ameen bai yi musu ba ya ɗauki wayarsa ya kira abokin nasa kamar yadda Mama ta ce amma bai d'aga ba. Ya dube ta ya ce. "Daga nan can zan je, duk halin da ake ciki zan sanar muku." Mama ta ce. "Allah yasa mu ji Alkhairi." Suka amsa da Amin, sai dai shi Ameen ko kaɗan ba ya ji a ransa Daddy zai fita daga cikin wannan case ɗin. Har ya tashi zai tafi Mama ta tsayar da shi, ya koma ya zauna dan jin mai zata faɗa masa. Mama ta ce. "Ameen dama kana son Neehal tuntuni mai yasa baka taɓa sanar mun ba?" Ya yi shiru na wasu sakanni kansa a ƙasa sannan ya ce. "Na yi zaton baza ki amince mun ba, shi yasa na fara faɗawa Dad domin ya shawo mun kanki, shi kuma ya ce mun in bar maganar ba zai bani ita ba,ban kuma san dalilinsa na yi hakan ba, shi yasa kawai na haqura." Mama ta ce. "Me zai saka in ƙi amince maka Son? Komai kake so a duniyar nan idan ina da shi zan baka, da ka faɗa mun da abu ɗaya zai saka bazan baka ita ba, idan ita ta ce baka so." Ya yi shiru bai ce komai ba. Mama ta ce. "Tashi ka je, Allah ya yi maka albarka, ya jib'anci al'amuranka ya shirya ka." Ya yi murmushi cikin jin daɗin addu'arta ya ce. "Amin Mum, Allah ya ƙara sauƙi." Mama ta yi murmushi ta ce. "Ameen, ka biya ka duba Neehal ɗin kafin ka wuce." Ya amsa mata sannan suka yi sallama da Aunty Sadiya ta yi masa kwatancen inda aka kwantar da Neehal ya tafi, yana jin zuciyarsa na masa sanyi kasancewa da ya yi da Mama, sai ya ji wani kaso na cikin damuwarsa na yayewa. Har lokacin da ya je dakin Neehal bata tashi ba baccinta take. Suka gaisa da Hajiya ta shiga tambayar sa ko shi ma cutar yake ne duk ya yi wani iri. Bai bi takan ta ba ya ƙarasa bakin gadon da Neehal take ya tsaya yana kallon ta, zuciyarsa na k'issima masa abubuwa da yawa a kanta. Ya yi kusan 10 minutes sannan ya yiwa Hajiya sallama ya tafi.












Sai da sha ɗaya ta wuce sannan Neehal ta tashi daga baccin. Toilet kawai take je ta yi uzurinta ta kuskure baki ta fito ta cewa Aunty A'isha ta kai ta gurin Mama. Aunty A'isha ta ce ta bari a basu sallama mana, amma ta ƙi yarda harda kukanta, ganin haka yasa Aunty A'ishan ta raka ta. Suna shiga ɗakin ta tafi da gudu ta rungume Mama dake kwance idanunta a lumshe. Mama ta buɗe ido ta ce. "Daughter, Ya jikin naki?" Cikin sanyin murya tana duban yanda Maman ta zabge lokaci ɗaya ta ce. "Da sauqi Mama, ya naki?" Mama ta ce. "Alhamdulillah." Sai kuma ta fara kuka. Aunty Sadiya ta ce mata. "Kukan na mene ne kuma Neehal?" Bata yi magana ta cigaba da kukanta. Mama ta ce. "Me ya faru?" Cikin kuka ta ce. "Ki yi haquri Mama, na san ni ce sanadin wannan ciwon naki, saboda......." Cikin sauri Mama ta katse ta da faɗin. "Wanne irin shirme ne wannan Neehal, bana hana ki irin waɗannan maganganun ba, ciwo Ubangiji ne ke ɗora shi kuma shi ya ɗora mun. Ki bar kukan hakan kin ji ƴar albarka, ke ba lafiya karki ƙarawa kanki wani ciwon." Ta gyaɗa mata kai tana share hawayenta. A ranar aka sallami Neehal duk da dama already ta sallami kanta, sai magungunanta da zata cigaba da sha. Ranar haka aka dinga zuwa duba Mama, ƴan'uwa da abokan arzik'i ko ta ina, ana kuma yi musu murnar bayyanar Neehal. Da yawan mutane sun ɗauka damuwar ɓatan Neehal ce ta sakawa Mama ciwo har ta kwanta a asibiti. Kwanan Mama huɗu aka sallame ta daga asibitin, Alhamdulillahi jikin nata ya yi sauƙi, amma cikin zuciyarta cike take fal da damuwar abun da mijinta ya aikata da zullumin makomar rayuwarsa, duk da dai har yanzu abun da ya faɗa na sharad'in ƙungiyarsu akan kisan duk wanda ya fallasa sirrinsu har yanzu bai tabbata a kansa ba. Su Uncle Ahmad da Abba da Uncle Mahmud suna ta cuku_cuku akan case ɗin Daddy, amma abun ya ci tura ko damar ganin sa basu taɓa samun yi ba. Ameen kuwa ya yi busy suna ta aikin ganin sun kamo sauran ƴan ƙungiyarsu Daddy. Duk inda Daddy yake tunanin za'a ga wani daga cikin ƴan ƙungiyar an je duk ba'a same su ba, gaba-d'aya sun ɓace bat tamkar aljanu, da alama su ma suna can suna shirin ko ta kwana akan farautar su da suka fahimci ana yi. Babu wanda yasan halin da Daddy yake ciki sai ƴan'uwa na jiki_jiki da ya zama dole, ko ƴan dubiya sun tambaye shi idan an zo su Mama sukan san abun da zasu faɗa na rashin ganin shi da ba'a yi ba, wanda zai saka baza a yi tunanin ko da akwai wata matsalar ba.........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*7️⃣1️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*














*Barkanmu da Sallah, fatan an yi Sallah lafiya? Allah ya maimaita mana, Amin.*
















.........Aunty Sadiya ta yi kanta tana kiran sunanta tare da jijjigata. Neehal ta faɗa jikinta ta rungume ta tana faɗin. "Please Mama wake up, karki mutu ki bar ni, dan Allah Mama ki tashi karki tafi ki bar ni., Mama! Mama!..." Aunty A'isha ta zo ta janye ta tare da rungume ta, ta shiga rarrashinta cikin dauriya. Dan itama hankalinta ba a ƙaramin tashe yake ba na ganin halin da Maman take ciki, ta umarci Zulai dake tsaye ta ɗauko ruwa mai sanyi a shafawa Maman ko Allah zai sa ta farfaɗo. Hajiya kuwa bata motsa ba, dan bata jin idan ta tashi ƙafafunta zasu iya ɗaukar gangar jikinta balle har su yi tafiya, sai salati take yi tare da duk addu'ar da ta zo bakinta cikin matuƙar gigita na wannan mummunan al'amarin. Aunty Sadiya ta bar jikin Mama ta ɗauko wayarta ta shiga kiran Numbern Ameen, tana shiga amma ba ya ɗauka. Aunty Sadiya ta karɓi ruwan da Zulai ta kawo ta fara shafawa Mama a fuska, amma ko alamar zata motsa ba su gani ba. Hankali a tashe suka ɗauke ta sukay Mota dan kai ta asibiti. Ganin yanda aka ɗauki Mama kamar gawa ya ƙara tayar da hankalin Neehal, stress ɗin sun mata yawa, ga tashin hankalin tafiyar da aka yi da Daddy ga halin da Mama take ciki ga kuma dunbin damuwar dake cunkushe a cikin zuciyarta, hakan yasa ta sume itama. Sai daukar ta aka yi aka haɗa da Mama aka kai su asibitin.








*AFTER TWO HOURS*














*HOSPITAL*


A hankali Neehal ta buɗe idonta tana kallon saman ɗakin da take na wasu sakanni, sannan ta juyo da kanta gefen damanta domin fahimtar gurin take. Aunty A'isha dake zaune a kujerar gaban gadon marasa lafiya ta rafka tagumi ta sauke ajiyar zuciya tare da tashi tsaye cikin sauri ta ƙarasa kusa da Neehal ta kama hannunta ta ce. "Sannu Neehal, kin tashi? Bari a kira Doctor." Neehal ta d'aga mata kanta dak'yar, tana so ta tambaye ta ina Mama amma kuma ta kasa motsa bakinta da niyyar magana, ga wani irin ciwon kai da kanta ke yi mata. Aunty A'isha ta fice daga ɗakin, Hajiya dake zaune akan sallaya ta taso ta shiga yiwa Neehal sannu, Neehal ta gyaɗa mata kai kawai tare da mayar da idanunta ta lumshe. Har lokacin tana jin nauyin da ƙirjinta da yay mata gami da zafin zuciya. Bayan mintuna kaɗan Aunty A'isha suka dawo tare da wani likita, ya dudduba Neehal ɗin tare da yi mata ƴan tambayoyi, ta amsa masa da kai kawai ta nuna masa kanta da ƙirjinta a matsayin inda yake yi mata ciwo. Ya cire mata drip ɗin hannunta sannan ya cewa Aunty A'isha ta bata magungunan da suka siyo mata, amma su bata ko da tea ne ta fara sha. Zai je ya haɗo allura ya dawo yay mata. Sukay masa godiya shi kuma yay mata addu'ar samun sauƙi. Aunty A'isha ta taimaka mata ta tashi zaune ta kuskure mata baki, sannan ta haɗa mata tea ɗin ta bata ta sha. Da ƙyar Neehal take had'iye tea ɗin saboda ɗacin da take jin yay mata a bakinta, kaɗan ta sha ta ɗauke kanta. Aunty A'isha ta bata magungunanta ta sha sannan ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Ta dubi Aunty A'isha cikin muryar marasa lafiya ta ce. "Ina Mama?" Aunty A'isha ta ce. "Tana Emergency na asibitin nan sun bata gado, amma jikin nata da sauƙi yanzu." K'walla ta taru a idon Neehal, kamar zata yi kuka ta ce. "Ina son na gan ta." Aunty A'isha ta ce. "Gurin da take ba'a bari a shiga, kin ga Hajiya ma tun d'azu take naci sun hana ta shiga, sun ce sai ta farfaɗo za'a samu ganin ta, amma Sadiya tana gurin, da zarar ta farfaɗo zata kira mu ta sanar mana." Neehal ta fara hawaye amma bata ce komai ba. Aunty A'isha ta ce. "Mene abun kuka kuma ke da baki da lafiya? Ki kwantar da hankalinki zata samu lafiya Insha Allah, karki saka damuwa a ranki ki ƙarawa kanki ciwo." Neehal ta gyaɗa mata kai sannan a hankali ta ce. "Ƙarfe nawa? Ina son na yi Sallah Aunty." Aunty ta ce. "Ƙarfe tara na dare, mu je in kaiki toilet ki yi alwala ko in kawo miki ruwan nan ki yi idan baza ki iya tafiya ba?" Ta taune lip ɗinta sannan ta ce. "Zan iya zuwa toilet ɗin." Aunty A'isha ta taimaka mata ta tashi da ƙyar ta kai ta toilet ɗin ta yi tsarki sannan ta ɗauro alwala suka dawo ɗakin ta yi Sallar Magriba da isha'in dake kanta a zaune.














**************






Ameen tun bayan da ya kawo Neehal gida ya koma gidansa ya kulle kansa a ɗaki ya cigaba da binkicen da yake hankalinsa a matuƙar tashe. Gabansa na faɗuwa ƙirjinsa na dokawa a million saboda fargaba. Baya son abun da yake zargi ya tabbata. Yana jin Hafsah tana ta yi masa knocking amma bai bi ta kanta ba, Sallar la'asar ce kawai ta fitar da shi daga gidan zuwa masallaci, yana dawowa ya koma ɗakin ya ƙara rufe kansa. Wannan karon sai da ya yi wanka saboda uwar zufar da yake haɗawa. Bayan ya fito ya ɗauki wayarsa ya kira wani suna magana yana lallatsa laptop ɗinsa, da alama tare suke aikin da wanda yake wayar da shi.








Bayan wasu mintuna yana cikin aikin lokaci ɗaya ya yarda wayar hannunsa da system ɗin gabansa a matuƙar gigice. Ya shiga bubbuga hannunsa akan goshinsa yana maimaita kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un a fili. Ya miƙe tsaye idanunsa a lumshe, wani irin jiri ya ji ya kwashe shi hakan yasa ya yi saurin dafe hannayensa a jikin bango, ƙirjinsa na d'agawa saboda yanda zuciyarsa take bugawa. Ya daɗe a haka kafin ya zame ya zauna a ƙasa hannunsa dafe da ƙirjinsa, idanunsa sun yi ja jajur. Cikin wata irin murya dake nuni da tsantsar tashin hankali yake faɗin. "Ya Allah...! Dad why? Why?" Yana jin wayarsa tana ringing amma ko kallon inda take bai yi ba. Sai da ya ga Magriba tana ƙoƙarin yi sannan ya lallaɓa ya tashi da ƙyar ya ɗauki wayarsa ya kira wani abokinsa jami'in SS, ba tare da tunanin komai ba ya sanar masa da buƙatarsa tare da ƙudirinsa akan Daddy. Sannan ya koma ya kwanta akan gado ruf da ciki, yana son ya ɗauki system ɗinsa ya cigaba da duba abu amma ya san ko ya ɗauka babu abun da zai gane a cikinta, balle har ya fahimci wani abu. Duk wani bincike da zai yi akan al'amarin Neehal ya yi kuma ya gano komai duk abun da yake son gani, sai dai ya yi da na sanin yin binciken, da ya san abun da zai binciko kenan da tun farko bai fara binciken ba. Duk yanda mutum yake tunanin tashin hankalin da Ameen yake ciki ya wuce nan, mahaifi fa! Mahaifinsa wanda yake matsayin uban Neehal a yanzu amma shine da aikata mata wannan abubuwan? A matsayinsa na babban jami'in tsaron ƙasa mai ƙoƙarin ganin ƙasar sa ta gyaru tare da kama duk wani ɓata gari amma shine da kansa a cikin ɓata garin. Shine dalilin da ya saka kenan ya hana shi Auran Neehal ashe yana da wata manufar ne a kanta? Tambayar da yake ta yiwa kansa wanda ba shi da mai ba shi amsa me yasa Daddy ya shiga wannan ƙungiyar? Wanne irin rud'in shaid'an ɗin ne da huɗubar mummunar zuciya suka ɗebe shi ya faɗa cikin halaka ta duniya da lahira? Babban tashin hankalinsa ɗaya halin da Mama zata shiga idan ta ji Daddy ne ke aikata duk waɗannan abubuwan. Ya zata ji? Ya duniya zata ɗauki maganar? Wata zuciyar tasa kuma ta kasa yarda cewa Mahaifinsa ne da wannan ɗanyen aikin, tana ta faɗa masa ya sake bincike may be gaskiya ta bayyana, wataƙila wani ne ya shiryawa Dad ɗin haka, ko kuma wasu abokan nasa suke wannan harkar yake bin su amma shi ba ya yi? Ko ko ko.......Babu abun da bai kissima a ransa ba dangane da wannan harkar da Daddy yake yi. Ya fara bibiyar al'amarin Neehal ne tun lokacin da aka biyo ta har cikin gidansa, ada baya ɗaukar abubuwan da suke faruwa da wata manufar, ya yi zaton daga Allah ne kawai, sai lokacin zuciyarsa ta fara yi masa kokwanton tabbas da wata a ƙasa. A yau ya ji duniyar tay masa zafin da bata taɓa yi masa irinsa ba a rayuwarsa, ya ji ya tsani kansa da Daddy, bai san da idon da zai kalli Mama da Neehal ba, a ce Mahaifinsa wanda Neehal takewa kallon Uba a gare ta shi yake aikata mata haka? Tsananin tashin hankali da damuwar da Ameen ya shiga a yau baza ta faɗu ba. Har bayan Sallar isha'i yana kwance a inda yake cikin mawuyacin halin damuwa, zuciyarsa na k'issima masa abubuwa mara sa kyau a kansa, harda wacce ta bashi shawarar ya kashe kansa saboda damuwa da tsananin takaici da kunyar duniya. A hankali ya fara dawowa cikin nutsuwarsa da taimakon Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un da yay ta maimaita a cikin ransa. Hakan yasa ya iya tashi dariyar cikin k'unar zuci, bai bi takan wayarsa da ake ta kira ba da bugun ƙofar da Hafsat take masa ya shiga toilet ya ƙara watsawa jikinsa da ya ɗauki zafi ruwa tare da dauro alwala. Ya fito ya xora jallabiya ya tayar da Sallar Magriba da isha'i dake kanshi. A kowacce sujjada yana roƙon Allah yasa mafarki yake ba gaske ba ne abin da binciken sa ya nuna masa, tare da roƙon ya farkar da shi cikin gaggawa, ko kuma idan ma gaske ne Allah yasa ba Daddy ba ne, wani ne daban gaskiya zata bayyana a gaba.......










Aunty Sadiya tana tsaye a bakin window'n ɗakin da Mama take tana lek'enta cikin tsananin tausayawa, Maman na kwance akan gadon ƙaramin ɗakin da take ita kaɗai an saka mata robar numfashi (Oxygen) a hancinta. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe idonta ta buɗe sannan ta yi baya ta zauna akan kujera tana sauke numfashi cikin yanayin tsantsar damuwa. Wayarta dake hannunta ta latsa, hakan ya yi dai-dai da shigowar kiran mijinta cikin wayar Barrister Ahmad. Ta d'aga tare da karawa a kunne gami da sallama, bayan ya amsa mata cikin taushin murya ya ce. "Haleemah ya jikin Yaya Fateemah da Neehal?" Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. "Da sauqi Habibi, naga Ya A'isha ta mun text ta ce Neehal ta farfaɗo, Yaya Fateemah kuma gata nan a kwance har yanzu dai shiru." Uncle Ahmad ya ce. "Masha Allah, itama Yayan Insha Allahu zata farko cikin k'oshin lafiya, damuwar data riske ta lokaci ɗaya ne yasa ta cikin wannan halin." Aunty Sadiya ta ce. "Allah yasa." Uncle Ahmad ya nisa ya ce. "Komai zai wuce Insha Allah, gobe da sassafe nima zan taho Kanon sai mu je can inda Yaya Tafida yake mu san ya za'a yi da case ɗin." Aunty Sadiya ta ce. "Ɗazun nan Yaya Hamza (Abba) ya bar asibitin nan, kuma daga can inda aka tafi da Daddy yake, ya ce sun ƙi bari ma ya gan shi, sun ma ƙi saurarar shi balle a yi magana." Uncle Ahmad ya ce. "Kin san case ɗin nan ba ƙaramin case ba ne, musamman ma da bamu san evidence ɗin da Ameen ya ba su ba, amma Insha Allahu zamu yi iya yin mu wajen ganin Yaya Tafida ya fito, su kuma sauran ƴan ƙungiyar an kama su." Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. "Barrister kana ganin Yaya Tafida zai iya fita daga cikin case ɗin nan kuwa? Su kuma sauran ƴan ƙungiyar a iya kama su?" Uncle Ahmad ya ce. "Insha Allah Habibty, babu abun da ya fi ƙarfin Ubangiji, bincike kuma shi zai bayyana gaskiya." Aunty Sadiya ta ce. "Haka ne." Uncle Ahmad ya ce. "Ameen ɗin ya zo asibitin kuwa?" Ta ce. "Ina ta kiran wayarsa ba ya pick." Ya ce. "Allah yasa dai lafiya yake, ki cigaba da kiran sa, Insha Allahu za'a yi sa'a ya ɗauka." Aunty Sadiya ta ce. "Toh." Daga haka suka yi sallama ta katse wayar. Layin Ameen ta kira. Har lokacin yana zaune akan sallaya hannunsa dafe da kansa. Yana jin kira ya shigo cikin wayarsa, kamar ya share sai kuma ya yi wani tunani, ya san definitely cikin kiran da ake ta yi masa baza a rasa na Mama ba, rashin ɗaukar mata waya kuma zai ƙara saka ta a cikin damuwa, hakan yasa ya miƙe da sauri ya ɗauko wayar a inda ya yasar da ita cikin tsananin dauriya saboda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login