Showing 183001 words to 186000 words out of 262509 words

Chapter 62 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21448

yanda duk ta fita hayyacinta lokaci ɗaya. Ƙarfe bakwai na safe Daddy ya bar gidan dan zuwa Hospital's da kansa duba Neehal, gani yake kamar yaran da ya saka aikin basa dubawa da kyau shi yasa tun jiya har yau ba'a gan ta ba..........














Neehal tana rakub'e a gurin da ta yi Sallar Asuba har gari ya waye, ta rafka tagumi tana jiran ganin ikon Allah, bata taɓa riskar ranar data tsinci kanta a cikin tsoro da fargaba irin na yau ba, ta sadaqar ta karaya yau sai yanda Allah ya yi da ita tunda ya nufa ta wayi garin yau da ranta, ita kaɗai a cikin wannan gida tare da waɗannan azzaluman mutanen ai sai yanda suka yi da ita, amma bata daina addu'ar neman ɗauki a gurin Ubangijin ta ba. Wajen ƙarfe takwas aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, ta runtse idanta cikin matsananciyar fad'uwar gaba da murd'awar ciki, a hankali ta ce. "Shikenan, sun zo ida mummunan baƙin nufinsu a kaina, shikenan rayuwata ta zo ƙarshe." Jin an ajiye abu a gabanta yasa ta buɗe ido tare da d'ago kanta zuciyarta fal tsoro, wani farin saurayi ta gani tsaye yana kallon ta, gabanta kuma tire ne mai ɗauke da abinci, da alamun shi ya ajiye mata. Hawaye ya taru a cikin idonta ta fara kuka ta ce masa. "Fuskarka bata yi kala data masu cutarwa ba, ta yi kala data masu imani, dan Allah bawan Allah ka fitar da ni daga gidan nan kafin su gurɓata mun rayuwata, ni marainiya ce bani da kowa sai Allah, ka taimake ni dan Allah, na san baza ka so a wayi gari ka ga an ɓata rayuwar ƙanwarka ba, to ka ɗauke ni kamar haka ka fitar da ni daga gidan nan." Saurayin ya lumshe ido a hankali ya buɗe, kamar zai yi magana sai ya tuna ba'a ba su umarnin hakan ba, kuma akwai CCTV camera a ɗakin, sai ya juya cikin wani irin yanayi ya fice daga ɗakin. Neehal ta fashe kuka tare da saka ƙafa ta yi ball da abincin gabanta. Cikin kukan take faɗin. "Yaya where are you? Ka zo ka fitar da ni daga gidan nan kar su cutar da ni, kar su yi abun da zai sa zuciyar Mama ta buga, Daddy......." Haka ta dinga kiran sunan duk wani makusancinta tare da neman taimakon su, abun tausayi ta zama kamar wata zararriya. Ƙarfe goma saura wasu maza majiya ƙarfi guda biyu suka shigo ɗakin, Neehal ta tashi da gudu ta haye kan gado ta koma can ƙarshen gadon ta takure jikinta dake karkarwa kamar ana kad'a mata mazari. Gifd'a_gifd'an mutanen nan guda biyu suka bi ta gadon suka kamo ta tana ihun su sake ta har su kai ta inda za'a *keta mata haddi* amma kamar da dutse take magana abun da aka saka su kawai sukay. Fitar da ita suka yi daga ɗakin, wata ƙofa dake ƙarshen corridor ɗin gidan suka buɗe suka shiga, steps ɗin bene ne ya bayyana suka fara hawa da ita. K'ofofi uku ne a upstairs ɗin da suka hau, ta farko suka buɗe suka tura ta tana tirjewa sannan suka ja ƙofar suka fice. Ta d'ago kanta ta kalli mutumin dake tsaye a gaban gado yana saka face maks ta bogi a fuskarsa, sai dai kafin ya gama zirawa ta ga ainihin fuskar tasa, kuma ta gane shi. Ta miƙe cikin matuƙar dimaucewa daga fad'uwar da ta yi lokacin da mutanen nan suka yarda da ita. Dai-dai lokacin mutumin ya gama saka fake face maks ɗin, suka haɗa ido da shi ta cikin face maks ɗin da ya saka. Ko a cikin magagin bacci take ta ga mutumin nan sai ta gane shi, ko makancewa ta yi ta shafa fuskarsa sai ta gane shi, tsayuwarsa da siffar jikinsa kaɗai idan ta gani sai ta gane shi ko da ya juya mata baya ne, ko a cikin duhu ne, balle yanzu da yake tsaye a gabanta cikin haske suna pacing ɗin juna, ba fuskar bogi ba ko jikinsa duka ya ɓoye a cikin kayan ƙarfe sai ta gane shi, balle kuma ta riga ta ga fuskarsa ba tare da ya sani ba, ga kuma k'amshinsa da ba baƙo ba ne a gurin ta da ya mamaye ɗakin. Amma ita duk ba wannan ne damuwarta ba, damuwarta me ya kawo shi gidan? Me yake yi a cikin gidan da ake ƙoƙarin keta mata haddi? Me yasa k'artan mazan can suka kawo ta inda yake? Ko shine wanda mutumin da suka yi waya jiya ya ce zai aiwatar da mummunan ƙudirinsu a kanta? Ta d'aga hannunta dake karkarwa kamar an jona masa shock da ƙyar kamar yadda zuciyarta take fat fat fat kamar zata faso ƙirjinta ta fito ta nuna shi, cikin rawar murya numfashinta na fita da ƙyar kamar ana zarar ranta ta ce. "Ya..........✍️




(😭🙄 *Neehal wa kika gani ne!?* )


















*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*6️⃣6️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*














...........Sai kusan ƙarfe goma na dare Daddy ya dawo gidan, Yana cikin cire kaya Mama ta shigo ɗakinsa. Ta zauna akan stoll tana duban shi ta ce. "Daddy yau ina ka je ka daɗe haka? Gashi ina ta kiran wayarka bata shiga?" Daddy ya ce. "Au har kin manta inda na ce miki zan je da safe kenan?" Mama ta ce. "Sorry na sha'afa, sannu da zuwa da fatan kun dawo lafiya kuma an dace da abun da aka je nema?" Daddy ya ce. "An dace kam, bari na ci abinci nay wanka sai nay miki bayani." Mama ta yi murmushi ta ce. "Ga dukkan alamu dai baka da labarin an ga Sadik." Daddy ya ce. "What? Yaushe? Wallahi ban sani ba." Mama ta ce. "Tun yamma aka gan shi ko in ce ya dawo, dan Mamansa ta ce mun da kansa ya shigo gida cikin k'oshin lafiya." Daddy ya ce. "Alhamdulillah, kai Masha Allah for this nice story, to ya akai ya dawo?" Mama ta ce. "Bata faɗa mun ba, da zamu je gidan kuma rashin dawowar ka da wuri yasa bamu je ba, su Sadiya ma duk sun zo d'azun, amma gobe da safe Insha Allah zamu je gaba-d'ayan mu." Daddy ya zauna yana murmushin farinciki. Mama ta ce. "Kwanan masallaci ana sauka ya ƙare, yau sai ka more bacci ko zaka ciko, dan ba ƙaramar rama ka yi ba a Ƴan kwanakin nan." Daddy ya yi murmushin dake bayyanar da farin cikinsa ya ce. "Dole ai, bari na kira baban yaron na fara yi masa murna." Mama ta ce. "Toh, bari na kawo maka abincin ka nan ka ci." Daddy ya ce. "Ina Daughter ɗin ne da Hajiya?" Mama ta ce. "Sun kwanta tuntuni, Neehal ta sha kuka kanta sai ciwo yake mata." Daddy ya ce. "Sarkin kuka kenan, ta cancanci award ta wannan fannin." Mama ta ce. "Rashin duka ne da iskancin banza, abun kuka da bana kuka ba ita duk kuka take musu." Daddy ya yi dariya ya ce. "Duka kuma Doctor? Tab' ai ba me taɓa mun ƴa ya kwana lafiya, saurin kukanta kuma ai halitta ce, da yawan mutane haka suke musamman ku mata." Mama ta ce. "To Allah ya yaye mata."








Tun bayan isha'i Neehal take saka ran ganin kiran Sadik a wayarta amma ta ji shiru, tun tana jira har bacci ya ɗauke ta. Data tashi da asuba ta ɗauka zata ga text ɗinsa ko missed call ɗin sa, amma ko ɗaya bata gani ba. Bata yi tunanin komai ba sai ta yi tunanin ko yana cikin dangi ne anata murnar ganin sa, ko kuma a gajiye ya dawo ya yi bacci da wuri. Kafin ƙarfe goma na safe sun gama shirin su na zuwa gidansu Sadik dukan su, Aunty Sadiya ma ta zo, Aunty A'isha ce dai tunda a unguwar take sai dai su biya gidanta su ɗauke ta.










Mama da Daddy da driver a Mota ɗaya, Neehal da Hajiya kuma suna Motar Aunty Sadiya. Sun fara tafiya Mama ta dubi Daddy ya ce. "Jiya Ameen bai zo gida ba, yanzu kuma na kira shi ya zo mu je gidansu Sadik da shi wai ba zai samu damar zuwa ba, sun fita operating tun safe wani ƙauye." Daddy ya ce. "Allah sarki Son ba dai jajircewa a aiki ba." Mama ta tab'e baki ta ce. "Ni ban ma yarda da sun fita wani aiki ba, yau fa Saturday." Daddy ya ce. "Ina ruwan aikin tsaro da weekend Doctor, ko kin manta yanda na yi da ne, sai kina kira na kina Hamma Tafida wai baza ka dawo gida ba, idan ma kin same ni a wayar kenan." Mama ta yi murmushi tana tuna lokacin farkon Auren su ita da Daddy, lokacin suna faman yawon gari_gari a Nigeria idan an yi posted ɗinsa, wani gurin ma ba zai yiwu ya tafi da ita ba sai dai ya bar ta a gida. Cikin mintuna ashirin suka ƙarasa gidansu Sadik. A compound ɗin gidan suka tarar da Abban Sadik shi da Kawu. Suka gaisa cikin mutuntawa tare da yi musu murnar bayyanar Sadik da addu'ar Allah ya tsare gaba, Sannan su Neehal suka shige cikin gidan suka bar Daddy a gurin su Abba. Da fara'a sosai Maamah da ƴan'uwanta suka tarb'e su, suka gaisa cikin mutunta juna tare da ƙara jajanta abun da ya faru, su Mama sukay musu murnar bayyanar Sadik. Neehal dai tana ƙasa zaune akan carpet kanta a ƙasa, Hajja tana ta tsokanar ta, sai dai ta yi murmushi kawai, wata ƙanwar Maamah na tare mata. Ƴan'uwan Maamah suna da kirki sosai, kuma suna son Neehal da ɗansu, kawai babu yadda zasu yi dan su kansu al'amarin na ba su tsoro. Batul ƙanwar Sadik ce ta shigo falon, ta gaishe da su Mama sannan ta zauna a kusa da Neehal ta gaishe ta. Murya ƙasa_ƙasa yadda Neehal ɗin ce kaɗai zata ji ta, ta ce. "Aunty Neehal Yaya ya ce ki zo." Cikin d'oki Neehal ta ce. "Yana ina?" Batul ta ce. "Yana bayan gida nan." Neehal ta yi shiru dan bata san ta yanda zata iya tashi ta tsallake su Maamah da Mama ta tafi gurin Sadik ba. Maamah data fahimci abun da ke faruwa sai ta cewa Neehal. "Ƴata ku je da Batul ki ga jikin Sadik ɗin." Cikin jin kunya ta ce. "Toh." Sannan ta miƙe a hankali ba tare da ta kalli kowa ba ta bi bayan Batul wadda ta riga ta tashi. A wata rumfa dake bayan part ɗin Maamah suka same shi zaune akan ɗaya daga cikin kujerun robar dake gurin. Ta ƙura masa ido kamar yadda shi ma ya zuba mata nasa, sai ta ga ya rame ya ƙara haske. Ta zauna a kujerar dake fuskantar wadda yake kai, Batul kuma ta juya ta koma cikin gida. Sadik ya yi murmushi ya ce. "Neehal!" Ta mayar masa da matarnin murmushin ta ce. "Sadik!" Ya ce. "Na'am da fatan kina lafiya?" Ta ce. "Lafiya k'alau, Alhamdulillah Yaya Sadik, na gan ka cikin k'oshin lafiya ba kamar yadda muka yi zato ba, na ji daɗin hakan sosai sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba." Sadik ya ce. "Amin ya Allah, Are you sick?" Ta ce. "Lafiya ta k'alau, me ka gani?" Ya ce. "Duk kin rame Neehal." Ta ce. "Tashin hankalin ɓatan ka ne kawai amma yanzu ai komai ya wuce, tunda Allah ya dawo mana da kai lafiya." Sadik ya danne duk wata damuwa dake cikin ransa suka cigaba da hira da Neehal, har yake bata labarin yanda aka sace shi da inda aka kai shi.








A Parlour'n Maamah kuwa bayan fitar su Neehal ba jimawa Hajiyarsu Sadik ta shigo Parlour'n. Bacci take a part ɗin Umma aka taso ta aka ce mata iyayen Neehal sun zo. Su Mama suka gaishe ta cikin girmamawa. Ta amsa ba yabo ba fallasa sannan ta ce. "To Alhamdulillah, yaron mu ya dawo lafiya, mun gode da zuwar mana murna da kuka yi, amma ku sani babu batun Aure yanzu a tsakanin sa da ƴarku." Cikin mamaki Hajiya ta ce. "Saboda da me kuma?" Ta ce. "Saboda mu tsiratar da rayuwarsa daga faɗawa halaka mana, dan wannan yar taku ba matar aure ba ce, yawwa, dan haka baza mu ɗauki ɗanmu mu aura masa ita watarana kawai mu wayi gari mu ga an kashe mana shi ba." Mama ta kalli Aunty A'isha dake gefen ta da sauri suka haɗa ido. Cikin rashin jin daɗin abun da Hajiyarsu Sadik ta faɗa, Hajja ta ce. "Haba Hajiya, wannan wacce irin magana ce?" Hajiya data saki baki tana kallon ta, ta ce. "Ko mutuwa tana kunyar idon iyaye, amma ke matar nan ki dubi tsabar idon mu ki faɗa mana haka? Saboda mun zo inda kike." Maamah ko kaɗan bata ji daɗin abun da Hajiyar ta ce ba, ta dubi su Mama ta ce. "Dan Allah ku yi haquri." Hajiyarsu Sadik ta ce. "Haqurin me zaki ba su, kar ma su yi haqurin gaskiya ce dole a faɗe ta, ƴarsu annoba ce wadda zaman ta ma a cikin al'aumma bala'i ne, wa ya sani ma ko mayya ce take lashe kurwar samarin nata." Wannan kalmar ta maita da Hajiya ta danganta Neehal da ita ta bala'in k'ona ran su Mama ta yi ba. Hajiya ta ce. "Insha Allahu sai dai ki ga maita a zuri'arki ba dai a tamu ba, kuma Allah sai ya sakawa yarinyar nan k'azafin maita da kikai mata, ɗanku kuma ku kwad'anta shi ku cinye ko ɗan gold ne Neehal baza ta aure shi ba." Ganin abun yana neman ya zama babban faɗa Maamah ta yiwa Abba text akan ya zo, dan duk haqurin da Hajja take ba su akan ɗan Allah su bar maganar haka amma sun ƙi saurarar ta. Aunty Sadiya da baza ta iya jure cigaba da sauraren munanan kalaman Hajiyarsu Sadik akan Neehal ba ta miƙe tana duban Hajiyar ta ce. "Yarinyar nan ƙaddara ce Allah ya ɗora mata wadda babu wanda ya fi ƙarfin ya ɗora masa ita, ita ma ba yin kanta ba ne. Dan haka karki sake danganta ta da maita, idan kin manta bari in tuna miki shari'ar maita ba ƙaramin abu ba ne, wallahi idan kika sake alaƙanta Neehal da maita zaki sha mamaki." Tana gama faɗar haka ta ɗauki jakarta a fusace, ta cewa su Mama su tashi su tafi. Kafin su kai ga tashin Abban Sadik ya shigo falon a ruɗe, bai tambayi ba'asi ba dan ya san halin mahaifiyarsa ya shiga ba su haquri. Hajiyarsu Sadik kuma sai ta saka kuka wai ƴar cikinta wadda ta yi jika da ita ta zage ta amma ya zo yana ba su haquri.










Su Neehal suna can suna hira ba su san me yake faruwa ba, ita Neehal kanta gaba-d'aya ya kulle da labarin da Sadik ya bata, a yanda ta fuskanta waɗanda suke kawo masa abinci a inda aka ajiye shi su suka fito da shi suka dawo da shi gida. Kenan wanda yasa aka ɗauke sa shi ya saka aka dawo da shi, sai ta shiga tambayar kanta ta yaya Ameen ya fito da Sadik? Ko kuɗi ya bawa masu tsaron nasa fiye da yadda wanda ya saka su aikin ya ba su suka fito da Sadik ɗin? Ko kuma ƙarfi ya nuna musu ya tsoratar da su? Ko da hukuma ya haɗa su? Amma idan da hukuma ya haɗa su ai hukumar ce zata fito da shi su kuma a kama su. To ko dai ya san wanda ya sace Sadik ɗin ne? Sai ta girgiza kai a ranta tana cewa hakan ma ba zai taɓa faruwa ba, ta bar yiwa kanta tambayoyin tun kafin ta fara rubbish ɗin tunani akan Yayan nata wanda ta san ba za'a taɓa haɗa baki da shi a satar Sadik ba, ta k'udurce a ranta zata tambaye shi ya warware mata yanda abun ya kasance, duk da ta san halinsa da ƙyar ya bata amsa. Sadik yana ƙoƙarin faɗa mata abun da yake ransa na raba sun da aka yi dan kar ta ga lefin sa ta ga kamar ya zalunce ta ya yaudare ta, amma zuwan Batul kiran Neehal ɗin ya hana shi yi mata zancen, Batul ta ce ta zo su Mama suna jiran ta za su tafi. Neehal ta miƙe suka yi sallama da Sadik, ta lura da yanda jikinsa ya yi sanyi k'alau da kuma yanda yake bin ta da wani irin kallo. Ta tafi tana jin ba daɗi a zuciyarta kamar kar su rabu, sai ta tarar su Mama har sun shishshiga Mota zuciyoyinsu babu daɗi. Ta buɗe Motar Aunty Sadiya ta shiga, bata lura da yanayin da suke ciki ba saboda bata bari sun haɗa ido da kowa ba, har suka je gida babu wanda ya ce k'ala, sun yi shiru kowa da tunanin da yake a cikin ransa.










A Parlour'n Mama suka zauna gaba-ɗayan su, sai a lokacin Neehal ta lura kamar duk suna cikin ɓacin rai. Daddy ya sauke wani gwauron numfashi yana duban Neehal cike da tausayawa. dan shi ma Abba ya faɗa masa komai akan fasa Auren ta da Sadik. Mama ta janyo ta jikinta cikin damuwa ta ce. "Ya kika ga jikin Sadik ɗin?" A hankali ta ce. "Lafiyar sa k'alau." Mama ta sauke numfashi ta ce. "Ki yi haquri Neehal da rayuwa a duk yanda ta zo miki, duk abun da kika ga kin rasa ba Alkhairi ba ne a gare ki, idan kika yi haquri da tawakkali sai ki ga Ubangiji ya sauya miki da wanda ya fi wanda kika rasa ɗin, komai lokaci ne da shi kuma komai mai wucewa ne, na daɗi ko na wahala. Neehal iyayen Sadik sun ce ba zai aure ki ba." Ai Neehal ji ta yi kamar Mama ta soka mata mashi a ƙirjinta, ta runtse idanta a ƙoƙarin ta na ganin hawaye sun zubo mata kamar kodayaushe idan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login