Showing 195001 words to 198000 words out of 262509 words

Chapter 66 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21484

farko dana fara zargin sa na taɓa tambayar ki cikin hikima ina yake zuwa yanzu shi da ya yi retired? Kika ce mun gurin kasuwancinsa yake zuwa dubawa sai kuma Mall ɗinsa da yake lek'awa time to time. Kuma ɗan wannan abun ba zai saka mutum ya wuni a waje ba, tunda daga kasuwancin har Mall ɗin nasa akwai masu kula da su, babu abun da zai yi idan ya je, ko kina tunanin zai je ya zauna a cikin yaransa ne? Abu na uku kuma Yaushe rabon da ki ga wani abokinsa ya zo gidan nan alhalin kuma kafin ya shiga wannan ƙungiyar suna zuwa sosai? Duk da ba a gidan nan nake kwana ba amma na san wannan kuma na sa an bincika mun. Tun daga lokacin dana fara zargin sa na saka ido sosai akan duk wani motsinsa, amma da yake shi ma da shirinsa yake tafe na sha bak'ar wahala kafin na gano wasu abubuwan, su ma ba sukai cikakkiyar hujjar da zan iya cewa direct shi ba ne, shi yasa ban bayyana ba. Sannan sai labarin abun da ya faru da Neehal a gidan Ameen, shi ma ya ƙara tabbatar mun da zargi na. Na girgiza ba kaɗan ba a lokacin dana gane da saka hannu Yaya Tafida a duk abubuwan da suke faruwa da Neehal, domin ban taɓa zaton haka daga gare shi ba, Yaya Tafida mutumin kirki ne kowa ya san da haka, na yi mamaki matuƙa da yakasance dan cikin ƙungiyar matsafa duk da ban san ta yanda aka yi ya shiga ba amma na san tabbas ba'a san ran shi ba ne ƙaddarar sa ce ta zo a haka. Lokuta da dama ina kulle kaina a ɗaki in yi kukan takaici da baƙin cikin wannan al'amari, gami da tausayin ku ke da Ameen da Neehal da shi kan shi Yaya Tafidan, idan zaki lura har gidan nan na rage zuwa, saboda watarana kar na yi subutar baki na faɗa miki wannan mummunan labarin, ko kuma mu haɗu da Yaya Tafida in kasa jurewa in masa wata maganar da zai gane na san abun da yake. Dalilin da yasa kullum al'amarin Neehal yake ƙara tab'arb'arewa tare da ƙara yin gaba saboda wanda yake aikata abun da shi a ake zama a tattauna akan matsalar da kuma hanyoyin da za'a magance abun yana cikin mu, the way da zamu kawo mafita duk ya sani, shi kuma sai ya canza salo yanda zai ƙara kawar da tunanin mu daga kan abun. Shi yasa muka kasa samun mafita al'amarin ya ƙi ci ya ƙi ƙarewa, sai yanzu da ita kanta Neehal ɗin Allah ya nuna mata shi da idonta. Kuma muna fata Insha Allahu ƙarshen abun ne ya zo."












Mama ta runtse ido ta buɗe numfashinta na kaiwa da komowa da sauri da sauri ta ce. "Tabbas biri ya yi kama da mutum Sadiya, sai yanzu da kikai waɗannan maganganun sannan wasu abubuwan suke dawo mun kwanyata. Ku san shekaru goma sha biyu kenan da nake lura Tafida kamar baya cikin nutsuwarsa, sai yay ta yin wasu irin abubuwa amma ban taɓa kawo komai a raina ba. Sannan kuma lokuta da dama ana kiransa a waya sai ya dinga ƙin d'agawa a gabana, ko kuma ya d'aga ya ce yana zuwa zai kira daga baya. Na raba shi da *Kabir Ginyau* saboda ba mutumin k'warai ba ne, amma na lura bai rabu da shi ba, duk da ya ce mun ba mu'amala suke yi kamar ta da ba, gaisawa kawai suke. Sannan kuma lokacin da aka sace Sadik tun a wurin d'aurin Aure Usman ya ce a ɗaurawa Neehal Aure da wani amma ya ce a'a, bayan iyayen Sadik sun ce ba zai auri Neehal ba na same shi a ɗaki ni da shi na ce masa zan aurawa Ameen Neehal mu huta da wannan tashin hankalin, amma ya dinga kawo mun wasu hujjoji da suka akan hakan har na haqura na bar al'amarin, ashe duk kansa yakewa tanadi, ashe da Mushirinki miji nake zaune, me yasa ka aikata haka Tafida? Why? Why? Ko ɗan ɗanka guda ɗaya tilo a duniya bai kamata ka aikata wannan mummunan laifin ba, bai kamata ka ɓata masa suna a Duniya ba. Ka cuce ni ka cuci Ameen, am sorry Ameen ban maka zaɓin Uba na gari ba." Mama ta ƙarashe zancen cikin sark'ewar numfashi. Aunty Sadiya ta shiga bubbuga bayan ta a hankali tana maimaita mata sunan Allah. Kuka sosai Aunty A'isha da Hajiya suke yi, dan wannan abun ba ƙaramin girgiza zuciyoyinsu ya yi ba. Neehal ta kama hannun Mama tana kuka amma bata ce komai ba, so take tay mata magana amma ta kasa. Mama ta damk'e hannunta cikin dashashshiyar murya ta ce. "Ki yi haquri Neehal, duk wannan abun da ya faru nina jawo miki, da na barki a hannun A'isha ta riƙe ki da ƙila haka baza ta faru da ke ba." Neehal ta girgiza mata kai tare da rungume ta ta ƙara fashewa da kuka.












A hargitse Daddy ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi cikin matuƙar tashin hankalin da Mama zata iya cewa tunda suka yi aure bata taɓa ganin shi a cikin irinsa ba, Abba na biye da shi a baya shi ma cikin tashin hankali yana tambayar shi abun da yake faruwa ya gan shi duk a birkice. Mama ta janye jikinta daga jikin na Neehal ta miƙe tsaye cikin sauri, ta nuna shi da hannunta cikin muryarta dake fita da ƙyar saboda tsantsar damuwa ta ce. "Me ya kawo ka inda muke, ko ka zo ka ƙara mana wani ciwon zuciyar ne akan wanda ka saka mana ni da marainiyar Allah da bata ji ba bata gani ba? Ko kuma ka zo ne ka aiwatar da mummunan nufinka a kanta a gaban mu?" Daddy ya ƙaraso kusa da ita ya kama hannunta kamar zai yi kuka ya ce. "Dan Allah Fateemah ki tsaya ki saurare ni in miki bayani, na san a yanzu ji kike kamar ki kashe ni saboda tsana, amma dan Allah ki tsaya ki ji mai zan faɗa miki, wallahi ba laifina ba ne nima babu yadda zan yi ne." Mama ta fizge hannunta ta ce. "Muhammad ko ganin ka bana k'aunar yi balle na ji wannan muryar taka mai ƙara mun k'una da baƙin ciki a cikin raina, dan Allah ka fice daga ɗakin nan ko kuma ni in fita in bar maka gidanka. Ka ba ni mamaki kuma ka bani kunya, ashe dama ba dan Allah kake riƙon Neehal ba? Yanzu duk abubuwan da suke faruwa da ita kai ne sanadi?" Daddy ya ƙara riƙe hannunta ya ce. "Please Doctor, ki mun wannan alfamar ki tsaya ki saurare ni in miki bayani, ko da wannan zata kasance alfarma ta ƙarshe da zaki mun a rayuwata. Please and please, ni kaina a yau na ji tsani kaina da rayuwata." Mama ta kuma k'wace hannunta ta ce. "Bayanin me zaka mun Tafiya? Bayanin kai ka kashe Jameel da Anwar ko kuma bayanin kana riƙon Neehal ne saboda ka lalata rayuwarta? Ko kuma bayanin da zai ƙara tabbatar mana kana cikin ƙungiyar matsafa kai ɗan shan jini ne?" Abba dake bakin ƙofa yana kallon su cikin tsananin mamaki ya ce. "Subhallahi, Fateemah me kike faɗa haka? Kin san kuwa mai kike cewa? Mijinki ne fa General Muhammad Tafida a gabanki ba wani ba." Mama tana hawaye ta ce. "Na sani Yaya, Na sani." Sai ta mayar da duban ta ga Daddy ta ce. "Ka cuce ni, ka cuce ni Muhammad, ka ɓata wayonka, ka ɓata rawarka da tsalle, yanzu duk damuwa da k'aunar da kake nunawa Neehal duk na Ƙarya ne? pretended kawai kake yi saboda kar mu gano mummunan nufinka a kanta? Muhammad why? Me yasa? Mai Ubangiji ya rage ka da shi a rayuwar nan da ka zaɓi saɓa masa da laifin da ba ya yafewa? *Shirka* fa muham......" Kasa ƙarasa abun da take son faɗa ta yi saboda numfashinta da ba ya fita sosai, sai haki take jikinta na wani irin ƙyarma. Daddy ya yi ƙoƙarin riƙe ta ta yi baya da sauri kamar zata faɗi, da sauri Aunty Sadiya ta tashi ta riƙe ta, ta zaunar da ita a bakin gado. Cikin kuka Hajiya ta ce. "Na shiga uku ni Zainabu, wannan wacce irin masifa ce, Allah ka farkar da ni idan mafarki nake." Aunty A'isha ta dubi Mama cikin sanyin murya ta ce. "Ki yi haquri mu saurari Yaya Tafida mu ji me yake tafe da shi, ki bi komai a sannu dan Allah, kar wani mummunan ciwon ya kama ki." Mama zata yi magana amma ta kasa, sai jujjuya kanta kawai take. Abba ya ce. "Ni fa ƙara saka ni a cikin duhu kuke, dan Allah ku fahimtar da ni abun da yake faruwa." Aunty A'isha ta ce masa. "Ka zauna yanzu zamu ji komai daga bakin Yaya Tafida." Abba ya ƙaraso ya zauna akan carpet cikin tsananin al'ajabin wannan murdadden al'amarin. Aunty A'isha ta mayar da duban ta ga Daddy dake ta yiwa Mama sannu cikin tsananin tashin hankali, ta ce masa. "Ka zauna ka yi mana bayanin muna sauraren ka." Daddy ya sauke nannuyar ajiyar zuciya ya goge gumin da ke ta tsalala a fuskarsa sannan ya zauna shi ma ya fara magana kamar haka.












Shekaru goma sha uku da suka wuce baya Abokaina Alhaji Karbir Ginyau da Alhaji Idris suka dame ni akan na shiga harkar siyasa, tunda ina da kuɗi kuma na san manyan mutanen ƙasar nan gani General na sojoji mulki ba zai mun wahala ba. Na nuna musu ni bana son harkar siyasa ko kaɗan kuma ba zan yi ba. Alhaji Kabir abokina ne tun samartaka, zan iya kiran shi ma da aminina. Sai dai halayyar mu k'wata_k'wata ba iri ɗaya ba ce, shi mutum ne mai matuƙar son abun duniya dan zai iya yin komai akan kuɗi, sannan yana harkar bin matan banza. Ina faɗa masa gaskiya a kodayaushe a matsayinsa na abokina amma ko kaɗan ba ya ɗauka. Yakan ce mun idan mutum bai shana ba a gidan duniya mai zai yi? Da na ga ba zai taɓa dena halinsa ba sai na koma bin shi da addu'ar fatan shiriya idan mai shiryuwar ne. Kabir ya dinga mun naci da magiya akan in shiga siyasa harkar akwai samu sosai a cikinta. Na nuna masa ni fa ba zan yi ba, amma ya ishe ni da naci da magiya, har na amince masa zan yi amma na ce sai na yi shawara da iyalina. Na tuntubi Fateemah da maganar, da farko ƙin amincewa ta yi sai daga baya na lallaɓa ta ta yarda da ƙyar ta amince in yi siyasar, bayan ta kafa mun sharad'an yin komai cikin gaskiya da tsoron Allah. Zuwa lokacin nima ina son yin siyasar sosai, Kabir ya ƙwadaita mun yanda ake samun Alkhairi a cikin ta. Ban fara siyasa daga matakin ƙasa ba sai na fito takarar shugaban ƙasa. Na saka kuɗi na mai yawa na siyi Form ɗin takara. A hankali na fara tara mabiya da magoya baya, na samu waɗanda suka daɗe a cikin siyasar ake damawa da su suka d'aga hannuna. Tunda na fara harkar sai na fara shiga busy, yau mu ne nan garin gobe mu ne can. Wannan dalilin yasa Fateemah ta ƙara tsanar harkar, har ta fara mun zancen ko zan haqura in daina. A lokacin ni kuma abun ya shiga raina sosai gaskiya, sai na lallaɓa ta na ce mata da zarar komai ya dai-dai ta zan koma normal kamar da. Ana haka Kabir ya ce mun harkar siyasa fa dole sai an haɗa da taimakon malamai. Ban kawo komai a raina ba nake ba shi kuɗi a matsayin wanda za'a kaiwa malamai suke yin addu'a. A lokacin ni akaran kaina na san idan aka yi Elections ba zan taɓa winning ba, amma sai na saka a raina komai dan dagiya ne wani lokacin zan iya cin zaɓen. Sai na dage da taimakawa jama'a da takalawa, ta hanyar samar da maguda nan ruwa a wuraren da ba su da ruwa, da kuma gina masallatai a ƙauyuka. A hankali sunana ya fara baza ƙasar nan, mutane suka san ni sosai. Watarana ranar da ba zan taɓa iya mantawa da ita ba a rayuwata, ranar baƙin ciki ranar da tsautsayi yasa na faɗa cikin k'azamar ƙungiyar da babu komai a cikinta sai shirka da tsantsar rashin imani. Alhaji Kabir ya zo ya same ni har office ɗina ya ce mun, yanzu na fara yin masoya sosai a ƙasar nan, zata iya yiyuwa in ci zaɓe, dan haka in zo mu je zai kai ni wani guri da za'ai mun aikin da zai saka in ci zaɓen, dan siyasar yanzu dole sai da haka. Na ce masa in dai gurin kaucewa hanya ne baza ni ba, ni babu wanda zan kaiwa kukana sai Allah shi zan roƙa da shi na dogara. Kabir ya dinga nuna mun ba wani abu ba ne ai wannan is common thing, in ma ban yi yanzu ba sai na yi watarana, dan indai na ce kwanciya zan yi a siyasa zan ga kwanciya, za ai komai babu ni. Nan dai ya dinga saka mun san abun a raina yana mun huɗubar banza har kalamansa suka yi tasiri a kaina, sheɗan ya dinga zuga ni tare da ƙawata mun daɗin mulki da cigaban rayuwa da zan samu in har na haye kujerar mulkin shugabancin ƙasar nan. Ni har ga Allah na bi Kabir da niyyar zai kai ni wurin wani malamin, irin malaman soron nan ko masu duba, amma ko kaɗan boka da masu tsibbu ba su zo raina a matsayin wanda Kabir zai kai ni gurin su ba. Amma me? Mun yi tafiya ta kai ta awa uku kafin mu tsaya a wani tangamemen gida dake can wajen gari, babu gida gabansa babu gida bayansa, shi kaɗai a gurin. Muna zuwa ƙofar gidan na ji gabana ya faɗi, na dubi Kabir da ya gaji da mitata da nake ta yi masa tunda na ga muna ta tafiya ta ƙi ƙarewa na ce masa. "Ina ka kawo ni Kabir?" Ba tare da ya kalle ni ba ya ce. "Inda na ce zan kawo ka mana." Daga haka ya buɗe Motar ya fita, nima ban da zaɓi sai bin bayan nasa.














Ya k'wank'wasa ƙofar gate ɗin gidan, mintuna kaɗan wani ɗan tsoho ya zo ya buɗe mana, suka yi maganar da ni ban ji me suke cewa ba sannan Kabir ya shige gidan. Na tsaya na ƙi shiga saboda yanda gabana yake ta faɗuwa sosai, sai hasbunallahu'wani'imal'wakil nake maimaita a cikin raina. Kabir ya juyo ganin ban bi shi ba ya ce in shigo mana. Na ƙara tambayar sa Kabir wai inane nan ka kawo Ni? Ni fa hankalina ya ƙi kwanciya da gurin nan, gaskiya gida zan koma. Ya ce, ka zo mu je ka gani mana, haba ka cika garaje matsalata da kai, mu ci wannan uwar tafiyar sannan ta tashi a banza, wannan abun da taimakon ka zan yi ba kaina zan yiwa ba. Na yi tsaki sannan na bi bayan shi. Wani dogon lungu ne a cikin gidan, nan muka bi mu kaita tafiya sannan na ga mun shiga wani ƙaton Parlour, wanda babu komai a cikin sa sai wasu irin abubuwa marasa kyan gani a rarrataye, na shiga bin Parlour'n da kallo tsigar jikina na tashi. Kabir ya buɗe wata ƙofa dake falon ya shiga tare da yi mun alamar in biyo bayan shi. Ban musa ba na bi shi na shiga nima, abun da na tarar a ɗakin ba ƙaramin daga mun hankali ya yi ba ya kuma girgiza tunanina, har na yi tunanin ko mafarki nake. Wata mace hakimce akan kujera ta mulki tsirara haihuwar uwarta, kanta babu gashi a aske yake tal kamar Namiji. Ta ɗaura wani jan k'yalle a hannunta da ƙafarta. Sai zazzare idanu take yi. Gabanta kuma wani tulu ne na zinare wasu k'artan maza guda biyu suma ba kayan kirki a jikinsu suna tsiyayo mata wani jan abu mai kauri a cup tana ƙarba ta sha. A fili na ce A'uzubill...... Amma kafin na ƙarasa na ji an buge mun bakina, na juya dan ganin waye amma ban ga kowa ba. Kabir ya tsugunna yay sujjada ga matar nan wanda hakan ya ƙara tayar mun da hankali. Na sunkuya na d'ago shi cikin fusata na sharara masa mari na ce. Kabir gurin matsafa masu shan jini ka kawo ni gurin mushirikai? To rashin imanina bai kai haka ba, neman duniya ta ba zai saka in ɓata har haka ba. Na juya na fice daga ɗakin cikin tsananin fusata da baƙin ciki ina Allah wadaran halin Kabir. Tafiya nake kamar zan tashi sama ina haɗa hanya har na kai bakin gate ɗin gidan, na dubi mai gadin gidan a fusace na ce masa ya buɗen ƙofa. Amma kafin ya yi wani yunƙiri sai gani na na yi a ɗakin dana bar Kabir da wannan matar yanda na bar su. Na shiga rarraba ido cikin tsananin al'ajabi ina bin ɗakin da kallo tare da tunanin da yanda aka yi na iya dawowa ɗakin cikin kiftawar ido ni da nake a bakin gate. Na bi su da kallo kamar yadda suka tsaya cak suna kallo na su ma, na buɗe baki da niyyar magana ko addu'a amma na ji na kasa. Sai na juya da sauri na ƙara ficewa daga ɗakin, wannan karon da gudu na ƙarasa gate ɗin gidan. Amma nan ma kafin kiftawar ido na ƙara ganin an mayar da ni wannan ɗakin. Sai da muka yi haka har sau uku, ni na ƙi haqura in tsaya a ɗakin kamar yadda suke so, su kuma sun ƙi bari na in fita daga gidan, sai na kai bakin gate sannan su ƙara dawo da ni cikin ɗakin. A na ukun ne matar nan ta shek'e da wata mahaukaciyar dariya tana duba na, ni kuma inata aikin zazzare idanu da numfarfashi. Sai da ta yi dariyarta mai isarta ta gama sannan ta murtuke fuska kamar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login