Showing 111001 words to 114000 words out of 262509 words
Chapter 38 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
Magriba ta ƙarasa gida, zuciyarta cike da zumud'in ta je ta bawa Mama labarin canzawar da Uncle Umar yay mata. A falon ƙasa ta tarar da Mama da Ameen har da Hafsah a zaune sune hira. Ta ƙaraso cikin falon da sallama. Suka amsa mata, Hafsat ta bi ta da kallo cikin tsananin tsanar ta, Ameen kuwa bai ko d'ago ba hankalinsa yana kan wayarsa da yake ta aikin latsawa. Mama ta ce "Sai yanzu." Ta ce "Eh Mama, sai da na jira Uncle ɗin ya dawo muka gaisa." Mama ta ce "Kin kyauta kuwa, suna nan k'alau dai?" Ta ce "Lafiya k'alau suna gaishe ki." Ta mai da dubanta ga Ameen ta ce "Yaya Ina yini." Ciki_ciki ya amsa da faɗin "Lafiya." Ta mayar da duban ta ga Hafsat itama ta gaishe ta. Hafsah ta amsa da fara'ar munafurci akan fuskarta, har da tambayarta ya aiki. Ko zama bata yi ba ta wuce upstairs dan yin sallar dake kanta. Ameen ya bi ta da kallo ta ƙasan ido. Bayan 10 minutes ya miƙe ba tare da ya kalli inda Mama da Hafsah suke ba, ya bi bayan ta upstairs ɗin.........✍️
_*A yi haquri da typing error, ban yi edit ba ne.*_
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*4️⃣7️⃣*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
.........Idar da Sallar ta kenan ta ji an turo ƙofar ɗakin an shigo. Ta juyo da sauri dai_dai lokacin da ya yi Sallama a can ƙasan mak'oshinsa. Ta amsa masa cikin nazartar yanayin sa. A hankali ta ce "Yaya!" Ya amsa mata da ido ba tare ya yi magana ba. A hankali kuma ya fara takowa ya ƙaraso inda take ya tsugunna a gabanta tare da zuba mata narkakkun idanunsa da suke a lumshe. Ta yi ƙasa da kanta gabanta na fad'uwa saboda fargaba, a tunaninta wani laifin ta yi ya zo ya yi mata masifa kamar yadda ya saba. Ji ta yi Gaba-d'aya ta takura da kallon da yake bin ta da shi, sai cukuikuye hannuwanta take a cikin hijabin dake jikinta. Ta d'ago kanta ma ta dube shi ta kasa, ga k'amshinsa kamar ƙara buɗe mata kofofin hancinta a kai saboda yanda take jin sa. "From where are you?" Ta ji muryarsa a ɗan zafafe yana tambayar ta. Ba tare data yi wani k'wakwk'waran motsi ba ta ce "Gidan Uncle Umar." Ya yi shiru na wasu sakanni kamar ba zai tanka ba sai kuma ya ce "Mene haɗin ki da wannan guy ɗin?" Ta d'ago ta kalli fuskarsa cikin rashin fahimta ta ce "Wanne guy ɗin Yaya?" Ya ɗan taune lip ɗinsa ya ce "Baban twins kika ce ko wanene ma oho? Ya yi maganar irin i don't care ɗin nan. Ta ɗan yi murmushi ta ce "Oh Yaya wai Uncle Ahmad kake nufi?" Ya kalle ta kallon mamakin Uncle data kira Ahmad da shi. Ya ce "Eh shi." Ta girgiza kai tana kifkifta idanuwa ta ce "No.. nothing." Ya wurga mata wani kallo ya ce "Tarbiyyar da Mama ta yi miki kenan ki dinga tsayawa wani k'ato yana riƙe miki hannu ko?" Ya ƙarashe maganar a ɗan tsawace. Ta tsorata sosai dan bata taɓa tunanin ya ga lokacin da Ahmad ya riƙe mata hannu ba. Ya sassauta murya ya ce "Why Miemerh? Idan da Mama ta fito a time ɗin fa Me zaki ce mata?" Jikinta ne ya yi sanyi ta rasa me zata ce, tabbas da ace tsautsayi ya sakko da Mama ta ga sanda Ahmad ya riƙe mata hannu da kashinta ya bushe a gurin Maman, tunda ta sha nusar da ita akan illar hakan ga ƴa mace. Sai ta ji haushin kanta dana Ahmad ɗin ya cika mata zuciya. Zata yi magana kenan suka ji an buɗe ƙofar ɗakin. Mama ce ta shigo, ta dubi Ameen ta ce "Me kake yi anan?" Ya miƙe ba tare da ya yi magana ya nufi ƙofa, Mama ta matsa masa ya fice tana bin sa da kallon tuhuma. Ta mayar da duban ta ga Neehal bayan ya fice ta ce "What happened?" Cikin rashin gaskiya ta ce "Nothing." Mama ta tab'e baki ta ce "Ku kuka sani." Sannan ta juya ta fice. Neehal ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idonta, haka kawai ta ji wata irin kunyar Ameen ta rufe ta, yanzu bata san irin kallon da yake mata ba a cikin ransa na ganin Ahmad ya riƙe mata hannu. Ta yiwa kanta alƙawari ba zata ƙara bari haka ta faru ba. Tunda dama hakan bai taɓa faruwa a gare ta da wani ɗa namiji ba sai Ahmad ɗin, shi ma dan tana masa kallon kamar jininta ne, kuma ta san ba da wata mummunar manufa yake riƙe mata hannun ba.
Hafsah ta cika ta yi fam kamar zata yi bunduga saboda baƙin cikin bin bayan Neehal da Ameen ya yi, a haka ya sakko ya same ta. Ta yi saurin ɓoye ɓacin ranta ta k'ak'alo murmushi ta ce "Baby har ka sakko." Ya zauna a kusa da ita cikin kulawa ya ce "Eh, bari na je na yi sallah, idan na dawo sai mu wuce gida ko? Ta ce "Ai na ɗauka a nan zamu kwana." Ya yi mata wani kallo bai ce komai ba. Ta yi murmushi cikin ranta tana jin wata irin k'aunarsa na ƙara cika mata zuciya. Ita kanta ta san ta yi dace da mijin kere sa'a, dabi'un Ameen suna bala'in burge ta, more especially muskilancinsa yana bala'in tafiya da imaninta. Yana ɗaya daga cikin abun da ya ja hankalinta a kansa, gashi ya iya kula da mace, ta tabbatar za a bashi lamba ɗaya a wannan fannin, ta san sai a tara maza ɗari kafin a samu wanda iya tarairayar mace da nuna mata tsantsar k'auna kamar Ameen ɗinta. Ya miƙe ya fice daga falon, ta bi shi da kallo. Komai nasa kyau yake mata, tafiyarsa ma kaɗai abun burgewa ce. Tana son Ameen over shi yasa bata son ɓacin ransa ko kaɗan, duk abun da ta san zai ɓata masa rai ko yaya ne gudun shi take. Shi yasa take danne duk abun da take ji a ranta a duk lokacin data gan su tare da Neehal, dan ta san bata isa ta nuna masa ɓacin ranta ba akan haka. Ta tsani Neehal over, tsanar da ita kanta bata san adadinta ba, tun lokacin data samu labarin ba su Mama ne suka haife ta ba ta ji yarinyar gaba-d'aya ta fice mata a rai.. Maganar Mama data dawo falon ne ya katse mata tunanin da take. Mama ta ce "Au Ameen ɗin fita ya yi?" Hafsah ta ce "Eh ya je masallaci." Mama ta ce "To mu je sama kema ki yi Sallar, na ji an fara kira." Hafsah ta miƙe ta bi bayan Mama. Bayan ta idar da Sallah Mama ta kawo mata abinci, tana cikin ci Ameen ya dawo gidan. Neehal kuwa tana ɗakinta ta ƙi fitowa, har sai da ta tabbatar sun bar gidan sannan ta fito falo. Anan ta tarar da Mama, ta zauna a kusa da ita ta shiga bata labarin zuwan ta gidan Uncle Umar. Cikin farin ciki Mama ta ce "Masha Allah, na ji daɗin wannan labarin, dama kullum fata na da addu'a ta Allah ya waiwayo da hankalin danginki gare ki, ku dinga zumunci kamar kowan ne ahali." Neehal ta ce "Nima Mama na ji daɗi sosai, ba ki ga yanda Uncle Umar yake mun magana ba, cikin kulawa kamar ma kunya ta yake ji akan abubuwan da yay mun a baya." Mama ta ce "Haka muke so dama, Allah ya ƙara shirya mu ya nuna mana gaskiya da sani akan abubuwan da muke aikatawa ba dai_dai ba." Neehal ta ce "Ameen." Mama ta ce "Ki je ki ci abinci, bari na je part ɗin Daddy." Neehal ta ce "Toh." Tare da miƙewa, ɗakinta ta koma ta ɗauko wayarta ta kira Uncle Usman ta sanar masa sauyawar da Uncle Umar yay mata. Daren yau ba su yi waya da Ahmad ba, tana ganin yana kiran ta ƙi pick. Washegari da safe ma tana ganin kiran sa lokacin tana gurin aiki shima ta ƙi ɗauka. Bayan Magriba Sadik ya zo gidan kamar yadda ya saba zuwa, sun jima suna hira a gurin da suka saba zama. Har yake mata zancen shi kam zai turo iyayensa a yi maganar aurensu ya matsu ya ganta a cikin gidansa a matsayin matarsa ta sunna. Cikin jin kunya ta ce masa babu matsala zata yiwa Mama maganar idan ta koma ciki.
Zuciyar Sadik Cike da farinciki ya koma gida, a main Parlour ya tarar da iyayensa da k'annensa kamar kodayaushe. Ya yiwa iyayen nasa sannu da gida ƙannansa kuma suka yi masa sannu da zuwa ya shige ɗakinsa. Bayan shigar sa ɗakin ba jimawa Batul ta zo ta ce ya je Abbansu yana kiran sa a part ɗinsa. Ya amsa tare da tashi ya biyo bayanta suka fito. Abba yana zaune shi da Umma da Maamah, kamar yadda tsarinsa yake idan zai yi magana da ƴaƴansa a gaban su Maamah yake yi. Sadik ya samu guri ya zauna a ƙasa bayan ya ƙarasa falon Abban. Abba ya dube shi cikin kulawa ya ce "Abubakar na kira ka ne akan maganar yarinyar da kake zuwa gurinta, kamar yadda na ce zan yi bincike akanta da iyayenta na yi, kuma Alhamdulillahi na samu kyakkyawan sakamako kamar yadda ake fata dama. An tabbatar mun yarinyar tana da tarbiyya, mahaifinta kuma mutumin kirki ne. Dan haka na yarje maka ka cigaba da zuwa gurin ta." Murmushi ne ya bayyana akan fuskar Maamah na farinciki. Sadik kuwa ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin bayanan Abba, daman ya san babu wata matsala da za'a samu a gurin Neehal. Maamah ta ce "Masha Allah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Abba ya ce "Ameen." Tare da mayar da duban sa ga Sadik wanda kansa ke ƙasa ya ce "Ashe ma yarinyar nan ce mai aiki a gidan TV na ASTV?" Sadik ya shafa kansa ya ce "Eh ita ce Abba." Abba ya ce "Masha Allah, Allah ya yi mana jagoranci." Umma da baƙin cikinta ya kasa b'oyuwa akan fuskarta ta tari numfashin Abba ta ce "Alhaji wacce yarinya na ji kana magana a kanta? Ba dai Neehal ɗin nan ba ta gidan Alh. Tafida?" Abba ya ce "Ita mana, ai yarinyar da mahaifinta sanannun mutane ne a ƙasar nan." Umma ta jinjina kai irin ta ga mugun abun nan ta ce "To gaskiya Alhaji baka yi bincike yanda ya kamata ba, indai akan yarinyar nan ne?" Abba ya ɗan canza fuska ya ce "Kamar yaya kenan?" Umma ta tab'e baki ta ce "Ita yarinyar fa su Alhaji Tafidan ba su ne asalin iyayenta ba." Sadik ya d'ago da sauri ya kalle ta, Maamah zata yi magana Abba ya riga ta da faɗin "Kamar ya ba su ne iyayenta ba Ruqayyah? Ban gane me kike son faɗa ba." Umma ta ce "Ina nufin riqon ta suke Alhaji ba ƴarsu ce ta cikinsu ba, riqonta kawai suke amma ko dangi ba su haɗa ba." Abba ya ce "Wannan ai ba wata matsala ba ce, indai tana da asalinta ai shikenan." Umma ta ce "Hmm, hakane. Amma kuma akwai wata matsalar bayan wannan." A harzuk'e Maamah ta ce "Wai ni Rukayya dan Allah me Yaron nan ya tsare miki a gidan nan ne, duk abun da zai yi sai kin san yanda kikai kika kawo masa cikas, akan wane dalili zaki takurawa ɗana? Me ya tsare miki?" Abba ya d'aga mata ya ce "Ya isa haka Kaltum, barta ta ƙarasa maganarta." Umma ta harari Maamah sannan ta cigaba da magana. "Abu na biyu Alhaji, wanda na same sa daga majiya mai ƙarfi akan yarinyar, na so in ɓoye maka kar in faɗa a mun wata fassarar daban, amma na kasa saboda yanda ba zan bari a cutar da ɗan cikina ba, haka ba zan bari a cutar da naka ba. Ita yarinyar ce duk wanda zata aura sai an kashe shi..." A zabure Sadik ya miƙe tsaye yana duban Umman, zuciyarsa na wani irin bugu ba tare da ya ji ƙarshen zancen nata ba." Abba ya haɗe rai sosai ya ce "Kin ga Rukayya, bana son shirme wannan wacce irin magana ce mara ma'ana?" Umma ta ce "Wlh Alhaji ba ƙarya ba ne, nima na girgiza da na ji zancen dan da farko ma ban yadda ba sai da aka tabbatar mun, samari har biyu sai an saka ranar Aurensu sai a wayi gari a tarar an kashe su idan....." A fusace Abba ya katse ta da faɗin, "Wannan duk ba hujja ba ce Rukayya, Babu mai kashewa da rayawa face Ubangiji, suma waɗanda suka rasun kwanansu ne ya ƙare. Dan samarin yarinya guda biyu sun rasu baza a ce daga ita ba ne, Ubangiji ne ya karb'i abinsa. Dan haka kar na ƙara jin wannan maganar mara kai da tushe, kuma wannan dalilin ba zai sa na hana Sadik cigaba da neman Auren yarinyar ba." Yana gama faɗar haka ya tashi ya shige ɗakin baccinsa. Maamah ta sauke ajiyar zuciya cikin jin daɗin yanda mai gidan nasu bai goyi bayan abokiyar zamantata ba a wannan karon. Miƙewa ta yi ta kama hannun Sadik dake tsaye kamar an dasa shi suka bar falon, ba tare da ta kuma kallon inda Umman take ba. Umma ta yi ƙwafa tare da raka su da harara, a fili ta furta "In kun san wata baku san wata ba ai, wallahi indai ina raye Sadik ba zai auri wannan yarinyar da Ubanta yake da arzik'i ba, mu zuba mu gani, shege ka fasa."
Har ɗakin Sadike Maamah ta kai shi ta zaunar da shi a bakin gadonsa. Cikin tausasawa ta ce "Kar abun da Rukayya ta faɗa ya d'aga maka hankali Sadik, ka dai san halinta ba sai na faɗa maka, zata iya yin ko wanne irin sharrin dan ganin auran ka da yarinyar nan bai yiyu ba. Ka dogara da Allah, ka kuma dage da addu'ar neman zab'insa ka ji." Sadik ya d'aga mata kai yana sakin ajiyar zuciya. Sai da kwantar masa da hankali sannan ta bar ɗakin. Kwanciya ya yi bayan fitar Maamah zuciyarsa na tariyo masa abun da Umma ta faɗa akan Neehal, tabbas ya san Sauratinta ya rasu kafin su haɗu, har Haneefah ma ta tabbatar masa da an kusa bikinsu lokacin da ya rasun. Amma bai san da wani ba bayan shi ba. Wani b'arin na zuciyarsa kuwa cike yake da mamakin cewa wai ba su Mama ne suka haifi Neehal ba, shi ko kaɗan ma bai yarda da wannan batun ba. A yanda yake jin Neehal a cikin ransa koma me za'a faɗa a kanta ba zai iya rabuwa da ita ba, ko yaya take yana son abarsa kuma a haka zai aure ta. Balle ma ya san bata da wani aibu. Tashi zaune ya yi a ransa yana faɗin 'Dole ma ya yiwa Maamah magana ta faɗawa Abba ayi_ayi a saka ranar bikinsu kowa ma ya huta.' Ko da suka yi waya da Neehal yau sai da ta gane kamar yana cikin damuwa har ta kasa shiru ta tambaye shi. Amma ya ce mata babu komai, dan Maamah ta gargad'e shi akan kar ya sake ya yiwa Neehal zancen. Umma kuwa bayan ta koma ɗaki Yayan Abban su Sadik wanda suke kira da Kawu ta kira ta sanar masa ƙarya da gaskiya akan yarinyar da Sadik yake nema. Kawu ya dinga masifa a waya kamar zai ari baki yana faɗin "Shi Surajon (Abba) ba shi da hankali ne yana ji yana gani zai salwantar da rayuwar ɗansa har zai da ce wannan abun ba wata matsala ba ce? To ina nan zuwa a cikin satin nan in same shi, domin kuwa wannan yarinyar dole Sadik ya rabu da ita." Cikin jin daɗi Umma ta masa sallama, zuciyarta fari k'al kamar takarda.
Bayan kwana biyu Ranar Laraba Neehal ta dawo daga gurin aiki da Yamma, tana zaune a ɗakinta tana operating system Mama ta shigo ɗakin, bayan ta yi Sallama Neehal ɗin ta amsa mata ta ce "Neehal Ahmad ya zo, yana ƙasa." Ta d'ago kanta da sauri ta ce "Uncle Ahmad kuma?" Mama ta ce "Ki yi sauri ki je kar ki bar shi yay ta jiran ki, na san ki da shiririta." Neehal ta ce "Toh." Sannan ta miƙe ta ɗauki Hijabi ta zira ta fito. Haka kawai ta ji zuciyarta na d'okin ganin sa, ko dan ta kwana biyu rabon ta da shi ko a waya ne. Yana zaune hannunsa tallafe da fuskarsa idanunsa akan steps, wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke jin takun tafiyarta. Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon. Ya miƙe tsaye da sauri kamar wanda aka tsikara ya ƙarasa gabanta ya tsaya daf da ita kamar zai rungume ta, cikin wata irin murya ya ce "Princess!" A hankali ta ce "Na'am Uncle." Ya kamo hannunta tay saurin k'wacewa tare da yin baya ta zauna akan kujera. Ya ƙarasa ya tsugunna a gabanta ya ce "Princesss mai ya faru idan na kira wayarki bakya ɗauka, ko wani laifin na miki?" Ganin yanda yake magana cikin damuwa sai ta ji tausayinsa mai tsanani ya cika mata zuciya, har ta fara da na sanin abun da ta yi masa. Cikin raunin murya ta ce "I'm sorry Uncle, ka koma ka zauna akan kujera." Ya girgiza mata kai tare da faɗin "No Princess, please tell me me ya faru." Ta ce "Seriously babu komai Uncle ɗina." Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa jin yanayin da ta yi magana ya tabbatar masa babu komai ɗin. Ya koma ya zauna sosai tare da zuba mata idanunsa. Cikin marairaicewa ya ce "But Princess why? Na shiga damuwa sosai da ƙin d'aga kira na da kike, har na fara tunanin ko ba lafiya ba. Na karb'i Numbern