Showing 39001 words to 42000 words out of 262509 words

Chapter 14 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21420

ne Neehal? Tun d'azu nake ta baza ido ko zan ga kin shigo amma shiru, kuma na kikkira ki baki ɗauka ba." Neehal ta sauke numfashi ta ce "I'm sorry sai yanzu na ƙaraso ne." "Kina ina?" Haneefah ta tambaye ta cikin zak'uwa, Neehal ta ce "Ina harabar gurin tare da Yaya." Haneefah ta ɗan kalli gabanta inda take hango mutane ta ce "Gurin da nake hango mutane?" Neehal ta ce "Eh." Haneefah ta ƙaraso gurin tana duba Neehal, Neehal ta hango ta ta je kusa da ita tare da dafata tana faɗin "Ga ni nan fa." Haneefah ta juyo amma ta gaza cewa komai sai bin Neehal da ido kawai take ganin kayan dake jikinta da kuma irin kyawun da ta yi. Neehal ta ce "Ya dai, wannan kallon fa?" Haneefah ta ce "Na mamaki ne sai kuma kyawun da kika yi kamar ke ce amaryar, amma yana ga kin saka wasu kayan ba irin namu ba." Neehal ta shagwab'e fuska ta ce "Rigimar Yaya mana." Ta kwashe duk yadda suka yi da shi ta faɗa wa Haneefah a tak'aice. Haneefah ta yi murmushi ta ce "Kuma wallahi kin yi kyau sosai, make up ɗin naki ma ya fi namu kyau." Neehal ta ce "Kuma takun ta yi kyau, ina su Ameera fa?" Haneefah ta ce "Suna ciki suna cashewa, nikam tunda na zo ko rawar ban yi ba, hankalina yana kan ki, musamman da kayan ki suke wurina, har fa Mama sai da na kira na faɗa mata, shima Yayan na kira shi bai ɗauka ba." Neehal ta ce "Shi yasa na ga missed call ɗin Mama." Haneefah ta ja hannun Neehal tana faɗin "Zo mu shiga ciki, kafin su amarya su shigo." Neehal ta kalli inda su Ameen suke ta ga anyi arranged ƙawayen Amarya da Abokanan Ango, domin shiga wurin. Ameen duk abun da ake hankalinsa na gun Neehal da ya tsaida ta, domin so yake su shiga gurin tare, amma suna zuwa inda ya barta ya neme ta ya rasa. A cikin halla kowa ya zazzauna filin rawa ma babu kowa, sai Mc dake ta karaɗin isowar ango da Amarya. Neehal kuwa gurin cousins ɗinta suka nufa, tana zuwa kowa ya fara yaba kyawun da ta yi, hotuna suka shiga ɗauka kowa yana so ya yi da ita. A nutse ƙawayen Amarya suka fara shigowa suna ɗan rausayawa abun gwanin sha'awa, nan fa mutane suka mik'ewa suna video a wayoyinsu, ga masu Camara ma nata fama ko ta ina, shigowar Ango da Amarya aka sauya sauti zuwa wak'ar masoya, a hankali suke tafiya har suka ƙarasa mazauninsu. Nan fa wurin ya fara cika da jama'a kowa yana so ya ɗauke su a hoto, da ƙyar Mc ya samu mutane suka ragu. Amarya da ango sun yi kyau sosai, abu ɗaya ne ya musu cikas rashin dacewar kalar kayansu, dan ita Hafsat gown ɗin jikinta purple colour ce. Hafsat har ta gaji da ciwon bakin da ƙawayenta suke mata akan me yasa ba su saka kaya kala ɗaya ba ita da Ameen? Itama ba ta ji daɗin hakan ba ko kaɗan, kuma ta tambayi Ameen ɗin tun kafin yau amma bai faɗa mata kalar kayan da zai saka ba. Neehal tana zaune dan su ba su tashi ba saboda cikowar mutane, ji ta yi kamar wayarta tana vibrate tana dubawa ta ga Ameen ne ke kiranta. Da mamaki ta ce "Yaya kuma, yana high table amma yana kira na, to me zan masa?" Haneefah dake gefen ta ta kama hannunta ta ce "Taso mu je, sai a mana hotuna ma da su." Neehal ba dan ta so ba ta mike tana faman riƙe riga suka je. Ta zauna a gefen Ameen Haneefah kuma ta zauna a gefen Hafsat aka ɗauke su a hoto, Neehal ta dubi Ameen ta ce "Yaya na ga ka kira ni." Ameen ya harare ta ya ce "Me na ce miki?" Neehal ta ɗan turo baki gaba ta ce "To ai na ga shigowa za ku yi shiyasa kawai na taho." Duk maganganun da suke masu ɗaukar hoto nata musu ba tare da sun sani ba, domin sai suka zama tamkar suke Ango da Amaryar. Neehal ta tashi ta zagaya bayan kujerar da suke ta ɗan sunkuya tsakanin Hafsat da Ameen ta ce "Aunty ina yini." Hafsat ta saci kallon Ameen ta ga ita yake kallo hakan yasa ta ɗan saki fuska ta ce "Lafiya k'alau." Neehal ta ce "Ya taro." ta ce "Alhamdulillah." Kusa da ita Neehal ta je ta zauna ta ɗan rungumo ta aka musu hoto, Hafsat kuwa ji ta yi tamkar Neehal wuta ta sa mata a jikinta da ta taɓa ta.






An cigaba da gudanar da shagalin biki yanda ya kamata, Amarya da Ango sun fito tsakiyar fili anata zuba musu lik'i. Neehal ma ta yi liƙi da kuɗin da Ameen yasa wani abokinsa ya bata bandir ɗin 200. Neehal tana gurin bikin ne amma hankalinta gaba-d'aya yana gurin Sadik, sai kiran shi take amma ba ya picking. Mama ma ta zo gurin ita da tawagarta ta yi kyau sosai cikin wani haddadden less kalar orange and black, Maman Hafsat ma ta zo. Neehal da taje yiwa Mama lik'i Maman tai ta kallonta cike da mamakin kayan da ta gani a jikinta, amma bata mata magana ba, kuma ko shakka ba ta yi tasan duk shirin Ameen ne wannan.






Ƙarfe 9:30pm Neehal ta ja Haneefah gefe cikin damuwa ta ce "Besty Ina ta kiran Ya Sadik ba ya picking, Allah ya sa lafiya." Haneefah ta ce "Nima tun d'azu nake son na ce miki banga Ya Sadik ba, amma bari na kira shi na ji." Neehal ta ce "Ya kikkira ni fa, time ɗin ko gurin kwalliyar ba mu tafi ba, ina tunanin fa ya zo da ya kira ni ban ɗauka ba shine ya tafi." Haneefah da hankalinta ke kan wayarta ta ce "To ke me yasa kika ƙi d'agawar?" Neehal ta ce "I think in ya ji ban d'aga ba zai kira ki shi yasa." Haneefah ba ta kuma cewa komai ba jin wayar Sadik ta shiga, har ta yi zaton ba zai d'aga ba sai kuma ta ji ya d'aga tare yin sallama. Ta kalli Neehal tare da amsa masa, ta ƙara da faɗin "Ya Sadik ina yini." Ya ce "Lafiya k'alau, Ya taro?" Haneefah ta ce "Alhamdulillah, ya na ga ban ganka a wurin bikin ba?" Sadik ya ce "Na zo ai na kira Neehal ba ta ɗauka ba, kawai na wuce." Haneefah ta ce "Ayya da ka kira ni ai, dan get pass ɗinka ma yana wurina." Sadik ya ce "Don't worry, Allah ya sanya Alkhairi." Haneefah ta ce "Ameen." Tana shirin ce masa ga Neehal ta ji ya katse wayar, Neehal dake kallon Haneefah ta ce "Me ya ce?" Haneefan ta ce "Ya zo ya tafi." Neehal cike da damuwa ta ce "Fushi ya yi da ni kenan? Shi yasa ma naita kiran shi ya ƙi pick." Ta ƙarashe zancen kamar zata yi kuka." Haneefan ta ce "Ki kuma kiran shi yanzu nasan zai d'aga, d'azun ma may be ba ya kusa da wayar ne." Neehal ta ce "Toh." Sai da ta fice daga hall ɗin saboda hayaniya sannan ta kira shi amma still bai ɗauka ba. Text ta tura masa kamar haka. _I'm sorry Ya Sadik, Please ka d'aga wayata_ Sadik ya yi murmushi lokacin da ya ga text ɗin Neehal, kafin ya kirata har wani kiran nata ya kuma shigowa, rejected ya yi sannan ya kira ta. Ta d'aga da sauri cikin shagwab'a Ta ce "Ya Sadik I'm sorry please, time ɗin da ka ki......" "Kar ki damu ba komai, ya taron?" Sadik ya katse ta da faɗin haka. Neehal ta turo baki gaba ta ce "Ai na yi fushi tunda baka dawo ba." Sadik ya ce "Haba 'yar ƙanwata a yi mun afuwa mana." Neehal ta ce "Um, um nidai sai ka zo zan haqura." Sadik ya ce "Shikenan ki ba ni 15 minutes gani nan zuwa." Neehal ta ce "Yawwa Yayanah sai ka zo." Sadik ya katse wayar yana murmushi, yana jin farin ciki a cikin zuciyarsa. Neehal tana yin taku kaɗan ta ga wasu maza biyu a gabanta a tsaye, ta canza hanya da sauri ta ga sun ƙara shan gabanta, ɓata fuska ta yi sosai tare da tsayawa ta ce "Lafiya?" Suka yi murmushi sannan wani a cikinsu ya ce "Lafiyar kenan ƴan'mata." Neehal ta ja ɗan ƙaramin tsaki ta wuce da sauri ta bar su a gurin. Tunda ta koma cikin hall ɗin ta ji kanta na mata ciwo, ta yi tunanin ko yunwa ce dan rabon ta da abinci tun safe hakan yasa ta nemo abinci ta ɗan ci, amma a banza kamar ma ƙara mata ciwon kan aka yi har wani jiri_jiri take ji, gaba-d'aya gurin bikin ya gundure ta, so take kawai ta ganta a gida. Gurin Aunty Sadiya ta je ta ce mata "Aunty dan Allah ara mun key ɗin Motarki idan da ita kika zo." Aunty Sadiya ta ce "Me za ki yi da shi?" Neehal ta ce "Wata Friend ɗina zan kai gida yanzu zan dawo." Aunty Sadiya ta ce "Ina?" Neehal ta ce "Anan cikin Narasawan suke." Aunty Sadiya ta ce "Ta bari a tashi mana, ai an kusa tashi sai a kaita." Neehal da take magana cikin dauriya saboda ciwon kai ta ce "Ana ta kiran a gida ana cewa ta dawo, a hakan ma sai an mata faɗa." Aunty Sadiya ta buɗe Pos ɗinta ta ɗauko key ɗin Motar ta bawa Neehal tana faɗin "Take it, amma ki yi sauri, ki kuma kula da hanya sosai kin ga dare ne." Neehal ta ce "Insha Allahu Aunty, thank you." Aunty Sadiya ta faɗa mata inda ta yi parking Motar ta fito ta nufi gurin.








A hankali take driving saboda ciwon kai gashi kuma dare ne, ta cikin layika take bi saboda ta yi saurin zuwa gida, abunka da G.R.A ko ina tsit babu mutane, amma akwai wadatuwar haske, tana shiga wani layi ta taka wani wawan burki da ƙarfin gaske cikin tsananin razana saboda abun da ta gani, ƙara dallare gabanta ta yi da hasken filitar Motar dan ta ƙara tabbatar da abun da idanunta suke gane mata..........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:40] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*








_By_
_Zeey Kumurya_










*1️⃣9️⃣*












...........Dafe kanta dake barazanar tarwatsewa ta yi saboda yanda yake sara mata, tattaro dukkan dauriyarta ta yi ta buɗe Motar ta fito ba tare data kashe ba, da fitilar wayarta ta haske Yaran mata guda biyu wanda suke ta kuka manne da juna, ga haushin da wasu karnuka suke yi wanda ga dukkan alamu shike ƙara firgita Yaran. Neehal addu'a take acikin ranta zuciyarta cike da tsoro, domin ba tasan yaran mutane ba ne ko aljanu, ƙura musu ido ta yi cike da tausayawa a ranta tana faɗin "Idan har Yaran nan mutane ne to duk wanda ya ajiye su anan bai da imani ko kaɗan, yanda duniyar nan ta lalace ace yara ƙanana a daren nan amma su kaɗai a bakin layi, layin ma irin wannan da babu mutane, ga su ƴaƴa mata, yanda duniyar nan ta lalace idan wani mugun ya ƙyalla ido ya gansu ai sai ya ɓata musu rayuwa.' Lokaci ɗaya Neehal ta nemi ciwon kan dake damunta ta rasa tunanika kala_kala ta shiga yi akan yaran, cike da faragaba ta kama ƙafar ɗaya daga cikin yaran ta duba, jin kamar ƙarar tahowar Mota cikin layin yasa ta yi addu'a ta kamo hannun yaran wanda ganin tana haska su yasa suka ƙara rukunkume junansu. Babu musu yaran suka biyo ta still suna cigaba da kuka, Neehal ta buɗe bayan Motar ta saka su sannan ta shiga gaba ta tada Motar ta nufi gida, har suka je gida yaran ba su dena kuka ba tare da kiran sunan *Daddy* a kofar part ɗin Mama ta yi parking Motar, ta fito da sauri ta fito da yaran suma da har yanzu ta gaza ce musu ko ƙala, ɗaukar ɗaya ta yi ta ja hannun ɗaya suka shige ciki, babu mutane sosai a gidan duk suna gurin dinner, sai tsoffi kawai da waɗanda ba a rasa ba. Neehal ta gaida mutanen data tarar a falo sannan ta wuce sama, babu wanda ya tambaye ta game da yaran tunda biki ake za su yi tunanin ko ƴaƴan wata ne.






Direct Neehal ɗakinta ta nufa ta sauke yarinyar dake hannunta wadda ta yi shiru tare da yin luf a jikinta, Neehal ta zauna a gefen gado tasa yaran duka a gabanta tana kallo, koda ba'a faɗa mata ba tasan yaran twins ne, saboda komai nasu da ya kasance iri ɗaya. Kyawawa ne kuma farare ga gashi an musu two babies, babu alamar talauci a jikin yaran, fatarsu luwai_luwai ga dukkan alamu daga gidan kuɗi suke, sai k'amshin turaren yara mai daɗi suke. Neehal ta fara tambayar kanta da faɗin "To wa ya ajiye su a waje a wannan daren? Ko dai fitowa suka yi suka kasa gane gida, ko kuma sato su aka yi? Gashi yaran da shigarsu tsaf cikin doguwar riga ƴan kanti masu kyau da tsada, ƙafafuwansu ne kawai babu takalmi ga....." "Aunty ki kai mu gurin Daddy." wadda da Neehal ta ɗauka da za su shigo ta katse ta da faɗin haka cikin maganarta ta yara. Neehal ta sauke numfashi tare da shafa kan yarinyar ta ce "Ina Daddy'n yake?" Ɗayar da hanyar yanzu bata daina kuka ba tace "Yana gida." Neehal ta janyo ta jikinta ta ce "Wa ya ajiye ku a waje?" Yarinyar ta ce "Wasu ne." Neehal ta ce "Ina mom ɗinku." Suka haɗa baki gurin faɗin "Daddy ya ce ta tafi ba zata dawo ba." Neehal ta yi shiru kawai tana kallon yaran, lokaci ɗaya suka cigaba da kuka suna kiran "Daddy Daddy, su dai akai su gurin Daddy'nsu." Neehal ta rungume su a jikinta tausayin yaran na ratsa dukkan jikinta, domin ta fahimci ba su da uwa saboda yanda suke kiran sunan Daddy kawai da kuma abun da suka ce mata. A hankali kuma ta d'ago su daga jikinta ta shiga goge musu hawayen fuskokinsu, tsabar kuka idanunsa sun yi jajir fuskarsu ma haka. Neehal cikin lallashi ta ce "Ku yi hakuri da safe zan kai ku gurin Daddy kun ji." Yaran suka d'aga mata kai suna sakin ajiyar zuciya. Neehal ta ce "Kun ci abinci?" Suka girgiza mata kai alamar a'a, Neehal ta shafi fuskokinsu ta ce "Bari na dafa muku indomie da tea, kuna ci ko?" Wadda tafi magana ta ce "Eh, Daddy Yana dafa mana every Morning." Neehal ta ce "Bari in dafa muku to." Ta mik'e ta cire ɗan kwallin dake kanta, tana cire ɗan kunne yarinyar ta ce "Aunty amarya ce ke.?" Neehal ta yi murmushi tare da d'aga mata kai, Ta lura yarinyar na da wayo da surutu saɓanin ɗayar data fahimci miskila ce. Neehal ta cire gown ɗin jikinta ta ɗauko wata riga mara nauyi ta nufi kitchen yaran na biye da ita a baya, ta lura duk a tsoro ce suke.






A can gurin biki kuwa Sadik ya ƙaraso ya kira wayar Neehal ba ta ɗauka ba, sai ya kira Haneefah ta zo ta shigar da shi, Haneefah ta kai shi suka gaisa da Mama da Ya Ameen ya musu Allah ya sanya Alkhairi. Haneefan tana ta neman Neehal amma bata ganta ba, ta kira wayarta kuma bata ɗauka ba, ta bawa Sadik hakuri ya ce babu komai. Sai wajen 11 aka tashi daga dinner, Aunty Sadiya tana ta neman Neehal itama dan ta bata car key ɗinta. Mama ta kira Haneefan ta ce mata "Ina Neehal ne? Ta zo mu wuce gida." Haneefan ta ce "Mama tun d'azu ban ganta ba, da Ya Sadik ma ya zo nay ta neman ta za su gaisa amma ban ganta ba." Mama ta ce "Kin kira wayarta kuma?" Haneefan ta ce "Eh, bata ɗauka ba." Mama ta yi shiru kawai tana sauke numfashi. Sai da za su shiga Mota Aunty Sadiya take faɗa mata yanda suka yi da Neehal, Mama tay ta faɗa tana cewa Aunty Sadiya "Me yasa zata bawa Neehal Motar a daren nan ta yi driving?" Aunty Sadiya ta ce "Mu yi fatan Allah yasa tana lafiya kawai." Ameen ma yana ta baza ido ko zai ga Neehal su tafi tare amma bai ganta ba.










Kallon yanda yaran suke cin abinci kawai Neehal cike da tausawa, a nutse suke ci amma kana gani ka san suna tattare da yunwa, sun ci sosai ɗaya ta fara kakarin amai, Neehal ta yunk'ura ta dauke ta da sauri ta yi toilet da ita, aikwa suna shiga ta fara kela amai, kafin ta gama itama ɗayar ta shigo tana yi, Neehal sai sannu take musu cike da tausayawa. Ta wanke musu baki bayan sun gama, ta cire musu rigunan jikinsu saboda sun ɓaci, ta dawo da su ɗaki suna ta sauke numfashi, Neehal ta lallaɓa su da ƙyar suka sha tea kaɗan, sannan ta kai su toilet ta musu wanka, dan duk sun yi kashi a cikin pampers ɗin jikinsu. Neehal tay ta mamakin yanda yara sun girma kamar waɗannan amma ake sa musu pampers, kuma da bakinsu za su iya cewa za su yi kashi. Komai na yaran iri ɗaya ne, babu wani abu daya bambanta a jikin su, harta da fingers ɗinsu iri ɗaya ne. Neehal ta naɗo su da ƙananun towels ɗinta, ta shafe su musu jiki da lotion sannan ta karkaɗe gado ta kwantar da su, har sun kwanta wadda tafi magana ta tashi kamar za ta yi kuka ta ce "Aunty ki kai mu gurin Daddy." Neehal ta matso ta janyo su jikinta sannan ta ce "Zan kai ku insha Allah, amma yanzu dare ya yi ku kwanta ku yi bacci da safe sai na kai ku." Yaran suka yi lamo a jikin Neehal ba su ƙara cewa komai ba, cikin 5 minutes ta ji saukar Numfashinsu alamun bacci ya ɗauke su, sai sakin ajiyar zuciya suke. Neehal ta raba su da jikinta a hankali tare da gyara musu kwanciya, ƙura musu ido ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login