Showing 243001 words to 246000 words out of 262509 words
Chapter 82 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
"Kai fa ba doctor ba ne Yaya." Ya kalle ta yana murmushi ya ce. "Amma ai ɗan Doctor ne ko?" Ta turo baki ta ce. "Nima ai ƴarta ce." Ya janyo ta jikinsa ya ce. "Dama waya ce ba ke ƴarta ba ce? Wa ma ya isa ya faɗa." Shi ya bata maganin tana bab'b'ata fuska kamar zata yi kuka ta haɗiye. Ya kwantar da ita cikin mintuna kaɗan ta yi bacci, saboda harda maganin da yake saka a bacci a cikin wanda ya bata. Bayan ya kwashe kayan ya kai kitchen ya dawo ya yi karatun Alqur'anin da bai samu ya yi ba bayan Sallar Asuba kamar yadda ya saba kullum. Ƙarfe goma da mintuna Mama ta turo aka kawo musu breakfast, ya ɗiba ya ci sannan ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya. Falo ya koma ya kira abokansa da suke ta yi masa missed call tun jiya, abun da ya guda shi suka dinga yi masa wato shak'iyanci, wai saboda ya yi amarya ya b'uya kwana biyu ko d'uriyarsa ba'a ji. Sai da 12 na rana ta wuce sannan Neehal ta tashi, Alhamdulillah jikin nata ya yi mata sauƙi sosai, ciwon jikin da zugin da take ji duk sun tafi sai kaɗan. Jikinta ne kawai take jin shi fayau babu k'wari. Abincin da Mama ta kawo ya haɗa mata ta ci sannan ya fita Masallaci dan yin Sallar Azhar. Ita kuma ta shiga gyaran gidan, bayan ta gama ta yi Sallah sannan ta dawo falo ta kunna kallo dan ta gaji da kwanciya, shi kuma bai dawo ba dama ya ce mata zai biya ta wani guri kafin ya dawo. A tunaninta gidansa zai je gurin Hafsat dan ita har yanzu bata san Hafsan ta yi yaji tana gidansu ba, tunda babu wanda ya sanar mata.........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*
_*By*_
_*Zeey Kumurya*_
*8️⃣5️⃣*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
.........Misalin ƙarfe biyu Ameen ya je gidan Mama, kamar ba gidan ne kwana biyu da suka wuce a cike fal da jama'a ba duk an fashe. Zulai da Dije ya tarar suna aiki ƙasa, sai wasu cousin's sister ɗin Dad su uku a zaune suna hira, da yake su sai jibi za su wuce dan ba'a ƙasar nan suke zaune ba. Yana shiga suka fara tsokanar shi, ya zauna suka gaisa yana murmushi sannan ya tashi ya nufi sama. Aunty A'isha da Amira da Ammi matar Uncle Mahmud ya tarar suna gyara a parlour'n. Bayan sun gaisa Aunty ta ce. "Yanzu muke shirin zuwa gidan naka ni da Amirah da Maryam." Ya ce. "To ya naga ko shiryawa baku yi ba?" Aunty ta ce. "Muna ƙarasa aikin nan zamu shirya mu tafi." Ya gyaɗa kai kawai sannan ya nufi ɗakin Mama. Mama tana haɗa kayan da ta yi fitar biki da su Aunty Sadiya tana taya ta ya shigo ɗakin da sallama. Suka amsa masa tare da kallon sa. Aunty Sadiya ta ce. "Ango ka sha ƙamshi, shine ka baro mun d'iyar tawa ita kaɗai a gida." Murmushi kawai ya yi bai ce komai ba ya zauna tare da gaishe su. Yana kallon Mama ya ce. "Mum gajiyar bikin ce naga ko murnar gani na bakya yi?" Mama ta harare shi ta ce. "Ka san abun da ka yi mun ai." Ya langwabe kai ya ce. "Yau kuma me na yi?" Aunty Sadiya ta yi murmushi ta ce. "Zai wuce akan maganar Hafsah ne." Da ɗan mamaki ya ce. "Hafsah kuma?" Mama ta ce. "Ka yi mamaki da muka sani ko? Tunda kai baka sanar mana ba, yanzu Ameen abun da ka yi ka kyauta kenan?" Ya sunkuyar da kansa bai ce komai ba. Mama ta cigaba da yi masa faɗa, bata san me ya faru ba amma gaba-d'aya ta ɗora masa laifi." Ganin yanda ta ɗauki zafi sai ya sanar musu da abun da ya faru ranar da ya kaiwa Hafsat kayan faɗar kishiya. Aunty Sadiya ta yi salati ta ce. "Gaskiya Hafsah bata kyauta ba, amma ta ɓata wayonta da wauta, tun yaushe aka daina irin wannan kishin, ina ganin ta wayayyiya ashe sakarya ce." Mama ta ce. "Duk da haka da ka bita gidan nasu, ko kuma ka zo ka faɗa mana sai a sasanta ba sai maganar ta yi nisa ba, yanzu iyayenta baza su ji daɗi ba a ce tafi wata a gida amma ka ƙi zuwa, za su ga kamar wulaqanci ne." Ya sauke numfashi ya ce. "Ita fa ta tafi da kanta Mum ba da iznini na ba." Mama ta ce. "Duk dai da haka, haquri zaka yi, abun da haquri bai bayar ba rashin sa ma bazai bayar ba." Ya ce. "Shikenan Mum insha Allahu zan je gidan nasu." Mama ta ce. "Yaushe?" Ya ce. "I will select the day." Mama ta ce. "Shikenan, Allah ya yi muku albarka ya kau da fitina a tsakaninku, Allah ya haɗa maka kansu, kai kuma ka zamto mai adalci a tsakaninsu, Allah ya baka ikon hakan kai ma." Ya ce. "Amin, insha Allah." Mama ta ce. "Tun ɗazu na yi girki gashi har rana ta yi ba'a kai muku ba, zaka tafi da shi ko su A'isha su tafi da shi?" Ya ce. "Daga nan ba gidan zan koma ba direct, zan biya can gidan Hafsah na ɗauko abu." Mama ta ce. "Yanzu gidan babu kowa kenan a cikinsa?" Ya ce. "Daa da masu aikinta, last week na je su je gida kawai idan ta dawo sa dawo, mai gadi ne kawai a gidan." Aunty Sadiya ta ce. "Allah ya kyauta." Mama ta ce. "Ya Neehal ɗin? I'm trying her number bata shiga." Ameen ya ce. "May be network ne, idan na koma zan kira ki sai na haɗa ku." Mama ta ce. "Toh, ta ce ma tabar ɗayar wayarta a nan gidan, in zaka tafi sai ka tafin mata da ita." Ya ce. "Okay, Ina tsohuwar gidan nan ne?" Mama ta nuna Aunty Sadiya ta ce. "Sai dai in wannan uwar taka ce tsohuwa amma ba tawa ba." Aunty Sadiya ta yi murmushi ta ce. "Hajiya tana ɗakin Neehal na da tana bacci." Ameen ya ce. "Aikin kenan." Harararsa Mama ta yi, ya yi murmushi.
Ƙarfe Uku da ƴan mintuna Neehal tana ɗaki tana drying gashinta data manta tun safe bata yi ba su Aunty A'isha suka zo. Ta yi packing gashin ta d'aura ɗankwali ta fita parlour. Murna kamar ta kashe ta da ta ga su ne. Suka zauna suka ci abincin da suka zo da shi tare suna ta hira. Ana yin Sallar la'asar Aunty ta ce za su tafi. Neehal ta dinga roƙon ta kar su tafi su ƙara zama, harda hawayenta su Amira na yi mata dariya. Daƙyar Aunty ta yarda suka kai ƙarfe biyar a gidan.
Kwana biyun nan Hafsat ta yi su ne cikin k'unci tamkar tana cikin k'abari, idan ka gan ta sai ka ɗauka cuta ta yi duk ta lalace ta yi duhu. Yau tun safe ta je ta tasa mahaifiyarta a gaba da kuka, wai ta bar ta ta koma gidanta ita ta gaji da zaman nan, ta san halin Ameen bazai taɓa zuwa ba. Mom ta yi shiru bata ce komai ba, ita kanta al'amarin ya fara isarta, abun kunya ne a gurinta k'awayenta su san ƴarta ta yi yaji, kuma indai aka cigaba da tafiya a haka dole wataran su sani, gashi Ameen ya wuce duk inda take tunani, bata taɓa zaton za'a kawo har i yanzu bai zo ba, ta tabbatar da maganar Hafsah na cewa Ameen ya wuce duk inda suke tunani kuma ba ya ɗaukar raini da wulaqanci. Ta dubi Hafsat cikin tausayawa ta ce. "Ki yi haquri Daughter mu jira babanki ya dawo, ya ce wani aiki ne ya tsayar da shi amma insha Allahu next week zai dawo, idan ya dawo sai ya je ya samu mahaifin shi Ameen ɗin su yi maganar." Hafsat ta gyaɗa mata kai ta ce. "To Mom ina son na je gidan Aunty Safiyya na yi kwana biyu, na gaji da zaman nan haka." Mom ta ce. "Indai hakan zai saka ki ji daɗi to ki shirya anjima driver ya kai ki, kuma ki saki jikinki dan Allah kina cin abinci ko kya yi kyan gani ki ɗan ciko, idan shi Ameen ɗin ma ya gan ki a haka ai sai ya raina ki, ya ce saboda shi kika damu kanki haka." Ita dai Hafsah bata ce komai ba, koma a yaya Ameen zai gan ta bata damu ba, ita dai fatanta Allah ya dai-daita su ta koma gidanta, babban abun da yake bak'anta mata rai idan ta tuna yana can tare da wannan shegiyar yarinyar data tsana, sai ta ji wani baƙin ciki ya cika mata zuciya, kamar zata haɗi zuciyar ta mutu. Bayan ta je gidan Aunty Safiyya ta ɗauki wayarta a b'oye ta kira Ameen tunda ita Mom ta ƙara k'wace wayartata, sai dai har wayar ta yi ringing ta gama bai ɗauka ba, dama ta yi tunanin hakan. Ta ji daɗin zuwanta gidan Aunty Safiyya, saboda yanda ta daɗa kwantar mata da hankali, ta ce tana nan tana shiri na musamman wanda zai saka dole Ameen ya zo da kukansa yana roqonta ta koma gidansa, lokaci kawai take jira a gama aikin.
Kafin Magriba Ameen ya dawo gida, lokacin Neehal tana zaune a falo tana karatun Alkur'ani kaɗaici ya ishe ta. Ya tsaya yana kallon ta bayan ya yi sallama yana shaƙar daddaɗan ƙamshin dake tashi a cikin parlour'n. Sai da ta kai aya sannan ta rufe Alkur'anin ta ajiye ta ɗago tare da amsa masa sallamar. Ya sakar mata murmushi sannan ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta yana kallon ta kamar zai lashe ta. Ƙasa ta yi da kanta cikin sanyin murya ta ce. "Sannu da zuwa." Ya ɓata fuska ya ce. "Haka aka welcoming ɗin miji dama?" Ta ɗan kalle shi ta ce. "To ya ake yi?" Ya ce. "Special hug and kiss to him." Ta waro ido sai kuma ta yi saurin rufe fuskarta da hannunta. Ya yi murmushi a ransa yana ƙara hasko wani bambancin na Hafsat da Neehal wato kunya, Hafsat ko a ranar da aka kawo ta gidansa bata nuna kunya ba sam, hasalima da ya je ko irin kukan nan na amare bata yi, babu alamun ma ta yi dan idonta ragal da shi. Ya rungume ta a hankali cikin kulawa da k'auna ya ce. "I missed you so much baby love." Ta yi shiru tana shaƙar ƙamshinsa tare da sakin ajiyar zuciya a hankali, tana jin wani abu yana yawo a cikin zuciyarta game da shi, kenan ita ma she missed him? Ya kama hannunta yana ɗan murzawa ya ce. "Have you eaten food?" Ta gyaɗa masa kai ta ce. "Kai fa?" Ya ce. "Na ci a gidan Mum." Ɗago kanta ta yi daga ƙirjinsa tare da ɓata fuska ta ce. "Shine ka je gidan Mama baka tafi da ni ba?" Ya shafa kanta ya ce. "Kin taɓa ganin amarya ta fita kwana biyu da kaita inba wata lalurar ba?" Ta girgiza masa kai. Ya ce. "To kin gani, idan an kwana biyu sai na kaiki ko?" Ta gyaɗa masa kai sannan ta ce. "Ina wayata? Ko baka gama checking ɗin ba ne?" Ya gyaɗa mata kai yana shafa kuncinta. Ta ce. "To ka bani, ina son na kira Family and Friends na yi musu ban gajiya." Ya ce. "Alright, Mum ma ta bani ɗayar wayarki da kika manta a gida." Ya zaro ta a aljihunsa ya miƙa mata. Ta karɓa ta ce. "Contacts ɗina duk suna cikin ɗayar ai." Ya ce, "To bari na ɗauko miki." Ya sake ta ya miƙe ya shiga ɗakinsa ya d'auko mata wayar ya kawo mata. Ya zauna ya ce. "Ki bari a yi Sallah sai ki kikkira su." Ta ce. "Toh." Ya janyo ta jikinsa ya shiga aika mata da saqonninsa masu rikitarwa, sai da aka kira Sallar Magriba sannan ta samu ya k'yale ta. Bayan an yi Sallah ta shiga kiran wayar, Daddy ta fara kira sannan Mama sannan Haneefah. Da suka gama waya da Haneefah sai ta kira Ummin su Ahmad, suka gaisa ta yi mata ya suka je gida da bangajiyar biki gami da godiya sannan ta ce ta bawa Zahra wayar. Bayan ta bata sun gaisa ta ce. "Shine kuka tafi ba ku zo ba, aida ko twins kun kawo mun, amma sai tafiyar ku na ji kawai ko sallama babu." Zahra ta ce. "Ki yi haquri, wallahi sai da na ce zamu zo washegarin da aka kaiki Ummi ta hana, na ce a kawo miki twins to shi ma Yaya ya hana ya ce sa zo miki wani lokacin." Neehal ta ce. "Shikenan ina twins ɗin nawa?" Zahra ta ce. "Suna gidan Yaya." Neehal ta ce. "Ki gaishe mun da su sosai, ko kuma ki turo mun ma numbern Aunty Khadijan sai na kira ta mu gaisa da su." Zahra ta ce. "Toh shikenan zan tura miki." Daga haka suka yi sallama ta katse kiran. Ta cigaba da kiran friends ɗinta da abokanan aikinta tana yi musu ban gajiya, har Batul k'anwar Sadik ma sai da ta kira. Ta yi mamakin yanda katin wayarta ya ishe ta wannan kiraye_kirayen, sai bayan ta gama ta duba ta ga ashe Ameen ne ya tura mata credit daga account ɗinsa.
Har bayan isha'i Ameen bai dawo ba. Ta yi wankanta ta shirya cikin wasu riga da wando masu kyau, wandon irin mai buɗewan nan ne ta ƙasa, ta saka hula pink colour a kanta da yake kwalliyar jikin kayan pink colour ce, ta yi kyau sosai. Ta zauna a falo tana kallo sai baza ƙamshi take. Tara saura Ameen ya shigo gidan bakinsa ɗauke da sallama. Ta kalle shi cikin wani irin salo ta juya masa ido tare da amsa masa sallamarsa cikin karyar da murya. Sandarewa ya yi yana kallon ta dan salon nata ya shige shi ba kaɗan ba. Bata motsa ba sai ido data zuba masa tana murmushi. Ya ƙaraso a hankali ya ajiye ledodin hannunsa ya rungume ta tare da sakin ajiyar zuciya. Ita ma ajiyar zuciyar ta sauke ta ɗan shafa kansa ta ce. "Welcome Yayana." Ya lumshe idonsa yana ƙara shigar da ita jikinsa tare da shaƙar ƙamshinta da ya fara saukar masa da kasala. Ta ɗan ture shi ta ce. "Daga zuwanka zakai mun syqueising ɗin kaya." Ya buɗe idonsa yana sauke numfashi ya ce. "Kin yi kyau sosai baby, ina son wannan ƙamshin naki." Ya ƙarashe zancen yana shafa kwantaccen gashin gaban goshinta. Ta ɗan murmusa ta ce. "Thank you." Sannan ta bar jikinsa ta tashi ta nufi fridge. Ya bi ta da kallo. Ruwa ta tsiyayo masa mai sanyi a cikin glass cup ta kawo masa, ya karɓa tare da yi mata godiya ya shanye. Ya janyo ta ya ɗora ta akan cinyarsa sannan ya buɗe ledodin da ya shigo da su, ice-cream ne da choculates da wafer da popcorn a ciki, abubuwan da ya san tana matuƙar son su sosai. A baki ya bata komai ta ci, shi kuma ya sha ice-cream kawai. Ta tattare sauran ta ajiye a fridge bayan sun gama. Ya Ɗauke ta cak ya kai ta ɗakinsa ya dire akan gado shi kuma ya shige toilet. Murmushi ta yi ta tashi ta fice ta koma ɗakinta ta kwanta. After 20 minutes ya biyo bayanta, ya shirya cikin wasu white ɗin kayan bacci. Ya hau kan gadon ya yaye bargon data lullub'a ya ce. "Da kika gudo nan ɗin bazan iya zuwa ba ne."Cikin marairaicewa ta ce. "Ni fa Yaya bacci nake ji, ka koma ɗakinka." Ya ɗora hannunsa a kan cikinta ya ce. "I can't." Ɓata fuska ta yi bata kuma magana ba, Ƙasa ya yi da hannun nasa a jikinta ya ce. "Ya jikin naki? I hope kin warke?" Kamar zata yi kuka tsoro ƙarara akan fuskarta ta ce. "Ni ban warke ba." Ya kwanta tare da janyo ta jikinsa ya ce. "Kar ki mun kuka, babu abun da zan miki, I just want to sleep with you." Ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido ta saka hannayenta ta zagaye bayansa da su kamar yadda ta ji ya yi mata..........✍️
```Ban yi edit ba.```
*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*
_*By*_
_*Zeey Kumurya*_
*8️⃣6️⃣*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️*
Jameey