Showing 3001 words to 6000 words out of 262509 words
Chapter 2 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
da sunkuyar da kansa ƙasa, Dad ya nisa ya ce "Muhammad cuta ka yi a can barrak ɗinne ba mu sani ba?" Ameen ya ce "A'a Daddy" Dad ya ce "To wannan ramar fa ta menene?" Shafa lallausar sumar kansa ya yi tare da lasar lips d'insa na ƙasa, cikin girmamawa ya ce "Dad yanayin aiki ne kawai" Dad yay shiru ya na kallonsa ba tare da yarda da abin da ya ce ɗin ba, sanin halinsa koda zai kwana yana tambayarsa ba faɗa masa abin da ke damunsa zai yi sai ya kyale shi kawai, amma tabbas ya san akwai abin da ke damun ɗan nasa. Sauke numfashi Dad ya yi ya ce "Shikenan Captain, Allah ya taimaka ya ba da sa'a" Ameen ya amsa da "Amin" Dad ya gyara zama ya ce "Ɗazu kafin na fita mun yi magana da Doctor akan shirye_shiryen bikin Daughter, tunda bikin ya matso, ya kamata mu san abin yi mu fara shiri" Ameen ya ce "Hakane, Allah ya kai mu Lokacin da rai da lafiya, ya kuma sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya" Dad ya ce "Amin ya Allah, ta mun Magana kuma a kanka kaima, ya kamata a ce zuwa yanzun kaima ka fitar da matar Aure, dan mu da son samu ne ma a haɗa bikinka da na Daughter" Ameen ya d'ago kansa da sauri ya na duban mahaifinnasa amma bai ce komai ba, Dad ya ce "Kayi shiru Captain" Ameen ya sauke Numfashi ya ce "Dad a dan ƙara mini time, zuwa bayan bikinnata insha Allahu zan fitar da mata nima" Dad ya ce "To shikenan, Allah ya kai mu da rai da lafiya, ya kuma haɗa ku da abokan zama na gari, Allah ya muku Albarka" Ameen ya ce "Amin ya Allah" Wata hirar suka shiga daban akan aikinsu na sojoji.
Neehal tun tana sallah take jin wayarta na ringing, sai da ta idar ta yi shafa'i da wutri sannan ta ɗakko wayoyinnata dake cikin jakarta.
Wayarta da personnal sim ɗinta yake ciki ake kira, missed call ɗin Mama ta gani da na masoyinta, Layin Mama ta fara kira, ringing daya Mama ta d'aga, Neehal ta ce "Hello Mama" Mama ta ce "Wato Neehal har yanzu ba ki koyi sallama a waya ba ko?" Neehal ta ce "Sorry Mamanah" Mama ta ce "Sorry for your self, kin dawo gida ne?" Neehal ta ce "Eh tun ɗazu" Mama ta ce "Dad fa?" Neehal ta ce "Shima na ga car ɗinsa a parking space, amma ban je part d'in shi ba, na tsaya Sallah ne" Mama ta ce "Ok, kin ci abinci dai ko? Dannasan halinki da zama da yunwa" Neehal ta ce "Na ci snaks" Mama ta ce "Haka dai ki ka iya, Ina Hajiya?" Neehal ta ce "Ta na ɗakinta, Yaushe za ki dawo Mama?" Mama ta ce "Sai 10, dama kira na yi in ji ko kin dawo, zan yi abu yanzu ki kula" Neehal ta ce "Toh Mama sai kin dawo" daga haka ta katse wayar. Number'n Anwar ta dannawa kira, sai da ta kusan katsewa ya ɗauka, Neehal ta ce "Amincin Allah ya tabbata ga farin cikin zuciyata, dafatan ka wuni lafiya, kaina bisa wuya na, yau nasan Queen ta yi lefi" Anwar ya lumshe idansa cikin jin daɗin kalamanta da tsananin farin cikin jin muryarta ya ce "Tare da ke tauraruwar da ke haskaka birnin zuciyata, amma tabbas yau kam Queen ta mini laifi babba ma" Neehal ta waro kyawawan idanunta waje tana murmushin jin daɗin kasancewarta da masoyinnata ta ce "Haba my Habibi, a yi haƙuri mana insha Allahu Queen ba za ta kuma ba" Yanda ta yi maganar cike da shagwab'a ya sa sai da tsigar jikin Anwar ta tashi, ya ɗan sauke numfashi ya ce "Shikenan ai Queen ɗita ta wuce gaban komai a gurina, amma dai yau ta mini k'wauron jin muryarta wanda hakan ya sa na rasa nutsuwata gabad'aya" Neehal ta ce "Am so sorry mijin, missed call ɗin farko da ka mun ina bacci ne, da na tashi kuma na kira ka ba kai picking ba, har na je gurin aiki na dawo ba ka kira ba, sai yanzu" Anwar ya ce "Sarkin bacci, to ya kike?" Neehal ta ce "Alhamdulillah sai kewarka da ta cikamun zuciya da gangar jikina" Anwar ya ce "Missd You too my love, ya Mamana da Yayanah da Dad ɗinmu?" Neehal ta ce "Duk sunanan lafiya k'alau, ya Amminah?" Anwar ya ce "Masha Allah, Ammi tananan klu" Neehal ta ce "Ka gaidata Please da sauran 'yan gidan" Anwar ya ce "Za su ji Insha Allah, yaushe zan zo in ganki ne na yi missing kyakkyawar fuskarnan taki" Neehal ta ce "Gobe mana" Anwar ya ce "Allah ya kai mu amaryata" Hira suka ci gaba da yi irin ta masoya mai cike da nishad'i da farin ciki, ba su wani jima ba su ka yi sallama Neehal ta ce za ta part d'in Dad ne.
Da sallama ta shiga falon Dad, Dad na zaune akan kujera ya na karatun jarida time ɗin Ameen ya fita, Dad ya d'ago tare da amsa sallamar Neehal ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi, Neehal ma murmushin ta ke yi ta ƙaraso cikin falon tana faɗin, "My Dad yau na yi missing ɗinka over" Dad ya ce "Nima haka my daughter, ya aikin" Neehal ta ce "Alhamdulillah" tare da zama a gefen Dad d'in, Dad ya ce "Ɗazu bayan mun fito daga meeting na kunna TV na ce bari in ga daughter nah, time ɗin ki na labaran yamma" Neehal ta yi murmushi "Dad ya ce, yanzu nake shirin kiranki na ce ki had'o mini fruits" Neehal ta Mik'e tana faɗin "Bari na had'o maka to" Dad ya ce "Yawwa ɗiyar albarka" Neehal ba ta wani jima ba, ta dawo ɗauke da vowl wanda ta yayyanka fruits d'in a ciki, ta ajiye akan Centre table ɗin dake gaban Dad, Dad yana dubanta da murmushi a kan fuskarsa ya ce "Thank you Amarya" Neehal ta rufe fuskarta cikin jin kunya. Tare su ka sha fruits d'in da Dad, ya na ta zolayarta da yake Dad mutum ne mai barkwanci, hirar su suke irin ta ɗa da mahaifin da ya ja ƴaƴansa a jiki, har sai da Mama ta dawo sannan Neehal ta koma part ɗinsu. Sau da ta biya ɗakin Hajiya ta mata sai da safe sannan ta wuce nata ɗakin, wanka ta fara yi sannan ta ɗauki wayoyinta ta kwanta akan lumtsumeman gadonta bayan ta kashe light d'in ɗakin, data ta kunna ta shiga yanar gizo, sai wajen 1pm ta kashe datar bayan ta gama shan hira da masoyinta Anwar da besty'nta Haneefah da sauran freinds ɗinta da 'yan'uwa da abokan aiki. Misalin ƙarfe uku da ƴan mintuna na daren Mama ta kirata, ɗagawa ta yi muryarta cike da bacci ta yi sallama, Mama ta amsa mata tare da faɗin "Ki tashi ki yi Sallah toh" Neehal kamar za ta yi kuka ta ce "Mama dan Allah ki bar ni na yi bacci na, gobe fa da safe za ni aiki, kuma ban daɗe da kwanciya ba" Mama ta ce "Ni na hanaki kwanciya da wuri, ai kin san da sallar ki ka tsaya chat" Neehal ta ce "Ba fa chat na yi ba, karatu na yi, kin san 2 weeks ya rage mu fara exam" Mama ta ce "Na ji, ki tashi ki yi Sallar dai, ko raka'a biyu ce, kin ga auren ki ya kusa, ki roƙi Allah ya kawar muku da fitintunu a zama auranku, yanda auren yanzu ya zama na zamani, dole sai mun dage da addu'a" Neehal ta ce "To Mama" Mama ta ce "Yawwa my daughter, ki yi addu'a sosai, sharrin mutum da Aljan Allah ya kare mu" Neehal ta ce "Ameen, bye" Mama ta katse wayar, Neehal ta yunk'ura ta tashi ta shiga toilet dan d'auro alwala.
Washegari, bayan ta idar da sallar asuba ta yi karatun Alkur'ani mai girma izifi biyu, sannan ta ɗauko materials ɗinta na school ta ɗan dudduba, gari na fara haske ta tashi ta gyara ɗakinta, sannan ta faɗa toilet ta yi wanka. 7:30 ta sakko ƙasa cikin shirinta na zuwa gurin aiki, ta na sanye da hijabinta wanda ya zo mata har ƙasa, Mama ta na kitchen ta na haɗa break fast, ƙarasawa kitchen d'in ta yi ta ce "Morning Mum" Mama ta ce "Morning dear, har kin fito" Neehal ta ce "Ehh, kin san yau Sunday za mu haɗa labaran week d'in gabad'aya dole sai na je da wuri" Mama ta ce "Amma dai ki tsaya ki yi break" Neehal ta ce "Idan na je can zan ci, bari na ɗiba cake" Mama ta ce "A'a ki dai tsaya ki ci abincin ko kaɗanne nasan halinki ba ci za ki yi ba" Neehal ba ta musa ba, ta haɗa tea a ƙaramin cup ta d'ebi soyayyayen phatatoe d'in da Mama ta soya kaɗan, ta koma falo ta ci. Kayan ta dawo kitchen ta ajiye bayan ta gama ci, ta yi wa Mama sallama, Maman ta mata addu'a ta fice. Sai da ta biya part d'in Dad sharp_sharp ta gaishesa sannan ta fito ta tafi........✍️
*Ku cigaba da haƙuri, ina yin garau za ku na samun Read more da yawa insha Allah.*
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL ⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*0️⃣2️⃣*
.............A hankali ta tura ƙofar falonsa, ta yi sa'a kuwa ƙofar a buɗe ya barta, shiga ta yi gabanta na ɗan fad'uwa saboda sanin halin Yayannata da kuma tsoronsa da take masifar ji. Ya na zaune a kan kujera 2 seater ya jingina bayansa a jikin kujera idanunshi a lumshe hannunshi dafe da kanshi, Neehal ta ƙaraso kusa da shi a hankali idanunta k'ur a kansa, gabantane ya fadi ganin irin ramar da ya yi, dan ɗazu kwata_kwata bata lura ba, a ɗan ruɗe ta ce "Yaya!" Bai motsa ba balle ya nuna ya ji ta. Ba ta damu ba ta zauna a kusa dashi kamar za ta yi kuka ta kuma faɗin "Yayah ba ka da lafiya ne?" Shiru yay mata kamar ba zai amsa ba, sai kuma can ya d'ago da kansa ya na ɗan sauke numfashi ya dubeta, kallon ta ya yi na 3 seconds kafin ya daukey idonshi daga kanta tare da girgiza mata kai alamar a'a. Idanunta na kawo ruwa ta ce "Gashinan ka rame, Please yaya mai ke damunka?" Haɗe rai ya yi sosai har sai da gabanta ya fadi amma bai ce komai ba, hawaye ne ya fara zuba daga idanunta wanda ta kasa tantance na banzan da ya yi da ita ne ko kuma na ganin shi cikin damuwa da ta yi?" Ta na hawayen ta ce "Yay......" cikin tsawa ya dubeta ya ce "Kin san bana son takura ko? tashi ki fita" turo ɗan karamin bakinta ta yi gaba ta na share hawayen fuskarta ta tashi ta fita, Bin ta ya yi da kallo ta ƙasan ido har ta fice, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya maida idanunshi ya lumshe zuciyarsa na masa ɗaci.
Haneefah ta dubi Neehal da ta tsaya jiki a sanyaye tun da ta dawo kitchen d'in ta ce "Besty me ya faru na ganki haka?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya idanunta na cikowa da k'walla ta ce "Yaya ne" Haneefah ta ci gaba da juya miyar da take dan in da sabo ya ci ace ta saba da rashin shirin Neehal da Yayannata, kamar ba za ta kula da zancen ba sai kuma dai ta ce "Me yay miki kuma yau" Neehal cikin raunananniyar murya ta ce "Besty ba ki ga yanda Yaya ya rame ba, amma na tambayeshi meke damunshi shine ya ce mun bakomai, na roƙe shi ya faɗamun shine ya koro ni" Ta ƙarashe zancen hawaye na zubo mata akan kuncinta, Haneefah ta juyo ta fuskance ta, ta ce "Ni fa daɗina dake saurin kuka, yanzu mene abun kuka anan?" Neehal ta ce "Ba za ki gane ba ne Besty, amma ba ki ji yanda nake ji araina ba, ganin shi cikin damuwa da na yi" Haneefah ta ce "Tom shikenan ki yi masa addu'a, koma me ya ke damunsa Allah ya yaye masa ya kuma bashi lafiya" Neehal ta ce "Ameen" Haneefah ta ce "Yawwa ko ke fa, to share hawayennaki 'yar Mama, kin san fa ke amarya ce ba na son na ga kina damuwa, kar mu kaiwa ya Anwar ke a rame" Neehal ta yi Murmushin yaƙe, saboda fad'uwar da gabanta ya yi, ta rasa me ya sa a duk lokacin da a ka yi zancen bikinta sai ta ji fad'uwar gaba, daurewa kawai ta ke yi, fita ta yi daga kitchen d'in domin ta je ta shirya, ɗakin Mama ta shiga ta tarar da Mama zaune ta na karatun Alkur'ani mai girma, zama ta yi har Maman ta kai ƙarshen aya, Mama ta d'ago ta dube ta, ta ce "Kin gama girkinne?" Girgiza mata kai Neehal ta yi, Mama ta ce "Toh menene kuma na ganki haka?" Cikin damuwa Neehal ta ce "Mama Yaya ne na ga kamar bashi da Lafiya, kuma na tambayesa me ke damunsa ya ƙi faɗamun sai ma koroni ya yi" Mama ta ce "To ke halin Ameen ɗinne ba ki sani ba ko me? Kin san ba faɗa miki zai yi ba, wa ya aike ki?" Neehal ta b'ata fuska ta ce "To ba Yayana ba ne?" Mama ta ce "Kin ga Yayanki ai, Ni tashi ki je ki ƙarasa mun girki kar time ya k'ure ki bar Ni da shi" Neehal ta tashi tana turo baki gaba ta fita. Bedroom ɗinta ta shiga, rage kayan jikinta ta yi ta shiga toilet dan yin wanka.
K'arfe uku dan wasu mintuna Neehal ta gama shirinta cikin wata rantsatstsiyar doguwar rigar abaya maroon colour, wadda ta ji kwalliyar stones milk colour, rolling mayafin abayar ta yi, ta yi kyau sosai duk da ba wata kwalliya ta yi ba, daddad'an turarenta mai daɗin ƙamshi ta feshe jikinta da shi, zoben gold ta zira a ɗanyatsanta na tsakiyar hannun damanta, na kusa da shi kuma ta zira zoben azurfa mai kyan gaske, yatsun hannun hagunta suma fashion ɗin zobuna masu kyau ta sa musu guda biyu, tsadadden agogon hannu milk colour ta zira tare da abun hannu mai kyau, flate shoe mai kyau milk colour ta zira, wayoyinta dake kan mudubi ta kwasa ta zuba a cikin handbag ɗinta mai kyau itama milk colour. Light din ɗakin ta kashe ta janyo ƙofar ta fito ta sauko ƙasa. Haneefah ta kammala girkin cus_cus ɗin da Neehal ta ɗora, ta na zaune a falo Neehal ta sakko, Haneefah ta bita da ido tana murmushi ta ce "Kaga amaryar ya Anwar, kin yi kyau sosai" Neehal ta yi murmushi ta ce "Har na kai ki yin kyan?" Haneefah ta ce "Wane Ni, ke fa harkin fara irin shining ɗinnan na amare" Neehal ba ta kulata ba, ta nufi kitchen, Haneefah ta tashi ta koma kusa da Hajiya ta fara tashinta.
Hajiya ta buɗe ido a hankali tana salati, tashi zaune ta yi tana mutsitstsike ido, duban Haneefah da take dariya ƙasa_ƙasa ta yi ta ce "Ai dama nasan sai ke, dan Neehal dai ba za ta yi mun wannan muguntar ba, To ke da Allah, ina cikin baccina mai daɗi kin katsemun ko uban me zan miki idanna tashin Oho?" Haneefah ta tsuke fuska ta ce "Hajiya dan na tashe ki ki ci abinci ki yi Sallah, shine za ki ce mugunta, gani na yi ke bakya wasa da Sallah kuma lokacinta ya kusa" Hajiya ta ce "To yi haƙuri ai ban sa ni ba, yaushe ki ka zo gidan? ya kuma Maryam ɗin?" Haneefah ta ce ɗazu na zo ai, na tarar ki na ta sharar baccinki, Mommy kuma tananan Lafiya k'lu" sakkowar Mama ƙasa ya katse musu maganar da suke, Haneefah ta mik'e ta je ta yi hugging Mama. Mama na murmushi ta ce "Welcome, yaushe ki ka zo?" Haneefah ta ce "Na ɗan jima" Mama ta ce " sannunki Ya Barrister?" Haneefah ta ce "Tananan klu" Mama ta kalli kofar kitchen ta ce "Neehal ba ta gama girkin ba ne, ta yi ta fito ku shirya ku tafi kar ku yi late" kafin haneefah ta ce wani abu Neehal ta fito daga kitchen d'in, Mama ta bita da kallo fuskarta ɗauke da mamakin ganin ta a shirye, Neehal ta ƙaraso kusa da su ta ce "Mama na gama abincin" Mama ta mata wani kallo ta ce "To sannu" Sannan ta juya ta kalli Haneefah ta ce "Kin taya ta girki ko?" Haneefah ta sunkuyar da kanta ƙasa ba ta ce komai ba, Mama ta ce "Ba magana nake miki ba Haneefah?" Haneefah ta ce "Mama ƙarasa mata miya kawai na yi, na ce ta je ta shirya dan mu yi sauri mu tafi" Mama ta ce "Ba na ce ko sauke abu ki dena taya ta da shi ba, ki barta ta dinga yin komai da kanta" Haneefah ta gyad'awa Mama kai. Neehal ta ɗan turo baki gaba ta wuce za ta ɗauki jakarta, Mama ta ce "Kun ci abincinne?" Haneefah ta ce "Na k'oshi Mama, ina gama cin abinci na fito, sai dai idan mun dawo" Mama ta dubi Neehal ta ce "Ke fa?" Neehal ta ce "Ni ma haka" Mama ta ce tunda kin cika cikinki da kayan zak'i ba, ki wuce kitchen ki d'ebo abinci ki ci kar na ɓata miki rai" Neehal ta ɓata fuska, amma ba ta da zaɓi sai bin umarnin Maman, kitchen d'in ta koma ta d'ebo abinci kaɗan a plate ta dawo falon ta zauna a ƙasa ta fara ci kamar ba ta so, ta na ci ta na yamutsa fuska, kaɗan ta ci Mama ta ce ta tashi su tafi, tun da ɓata musu lokaci kawai take ba cin abincin za tay ba. Neehal na duban Mama da Hajiya ta ce "Sai mun dawo" "Mama ta ce ƙarfe nawa za ku dawo?" Neehal ta ce "8" Mama ta ce "8 ina Hospital" Neehal ta ce "Mama yau fa Saturday me za ki yi a Hospital kuma?" Mama