Showing 18001 words to 21000 words out of 262509 words
Chapter 7 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
ta na da madaidaicin jiki, ta na sanye da wata doguwar riga 'yar kanti, ta yafa mayafi kalar rigar kanta babu ɗankwali sai fuskarta da ta sha uban make up. Neehal ta bita da kallo fuskarta ba yabo babu fallasa, ita kuwa wani matsiyacin kallo take bin Neehal da shi. Neehal ta yi ɗan murmushi ta ce "Sannunku da zuwa Aunty Hamida" kamar ba ta ji ba, ta yi banza da ita, Neehal dama ta san za'a rina, duk da kasancewar Hamida 'yar gidan k'anwar Dad ce amma ba sa shiri ko kaɗan, ko dan hakan ya samo asali ne daga rashin shirin Mahaifiyar Hamidan da Mama ne?. Neehal ranta ya ɓaci a kan abin da Hamida ta mata, dama shi ya sa bata son shiga sabgarta, Mama ce ke tursa sata dole, ta rasa me ta yi wa Hamidan ta tsane ta over. Hamida ta zauna ta na kar kaɗa ƙafa, Mahaifiyarta wadda suke k'ira da Mumy ta ƙaraso cikin falon ta zauna ita ma ta na huhhura hanci, Neehal ta dube ta ta ce "Sannu da zuwa Mumy ina yini?" Ta mata wani kallo ta ce "Lafiya k'alau, ya hak'uri kuma?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Daga haka suka yi shiru, Neehal ta maida hankalinta a kan kallon da take, bayan wasu mintuna Mama suka sakko ita da Hajiya da Dije da ta je kiranta. Mama ba yabo ba fallasa ta ce "Sannunku da zuwa" Mumy ta ce "Yawwa" Mama ta ce "Ya gida Suwaiba?" Mumy ta ce "Lafiya k'alau" Mama ta ce "Masha Allah" tare da zama a kan kujera, Hajiya ma ta zauna. Hamida kamar ba ta so ta ce "Ina yini Mama?" Mama tace "lafiya k'alau, Hamida ya aiki" tace "Fine Mama" Hajiya yadda ba su mata magana ba, itama ba ta musu ba, TV kawai take kallo hankalinta kwance. Su Dije suka dawo falon da ruwa da lemo gami da drinks, Zulai ta gaishe su kamar yadda Mumy ta amsa wa Dije haka ta amsa wa Zulai a wulak'ance. Can dai Mumy ko me tuna sai ta dubi Hajiya ta ce "Ina yini Hajiya?" Hajiya ta ce "Lafiya" tana keb'e fuska, Hamida da ke ta latsa wayarta ita ma ta gaishe ta a yangance. Mumy ta gyara zama ta dubi Mama ta ce "Sai muka ji kuma an kashe saurayin Neehal" Mama ta ce "Eh ƙaddara ta riga fata." Mumy ta ce "To Allah ya ji k'an shi, amma ni fa ina ganin wannan abun kamar da sa hannu, a ce yarinya duk wanda maganar aure ta shiga tsakaninsu sai an kashe shi, sai ka ce firlm ko labaran tatsuniya?" Mama ta yi shiru ba ta ce komai ba, domin da rainin hankali Mumy ta yi maganar. Hamida ta tab'e baki ta ce "Hmmmm gaskiya dai Mumy, dan Ni na ma fi tunanin ko wani baƙin Aljanin ne ya aure ta.........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:31] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
0️⃣9️⃣
...........Hajiya ta dubi Hamidah ta na mitsi_mitsi da ido ta ce "Ke! Ki iya bakinki, mugun nufinki Insha Allahu ba dai a kan Neehal ba, ato, bakinki ya sari ɗanyen kashi" Hamida za ta kuma magana Mommy ta girgiza mata kai, tab'e baki ta yi ta ci gaba da latsa wayarta a gadarance, Mama kuwa kamar ba ta ji su ba, ta musu banza. Neehal ma ko d'aga kanta ba ta yi ba, balle ta nuna ta san me su ke cewa. Hakan kuwa ba ƙaramin k'ona ran Mommy ya yi ba, domin kuwa ta so Mama ta kula ta su yi ta yi, ko kuma Neehal ta tankawa Hameedah Dad ya dawo ta haɗa mata sharri, sai kuma ba ta samun haɗin kai ba. Mama tashi ma ta yi ta wuce sama abin ta, Neehal ma bin bayanta ta yi dan zaman falon ya ishe ta. Hakan kuwa ya ƙara kona ran Mommy. Ɗakin da suke sauka idan sun zo Mama ta sa su Dije suka gyara musu, da yake daga Abuja suke a can suke da zama, su Dije suka kwasar musu kayansu zuwa d'akin. A gadarance su Mommy da Hameedah suke yin komai a gidan, Mama kuwa ba ta tanka musu haka ma Neehal, Hajiya ce ma sarkin magana, amma Mama ta roƙe ta a kan ko me za su yi kar ta kula su. Ko da Dad ya dawo part d'insa suka je su na hira, har sai da dare ya yi sosai sannan ya ce ya kamata su je su kwanta, Mama kuwa dama ta san hali shi ya sa ba ta je ba, sai da ya kira ta da kansa a waya. Washegari Neehal tun safe ta wuce gurin aiki, dama tun ranar mutuwar Anwar ba ta koma ba sai yau.
Misalin ƙarfe 11 na safe Ameen ya shigo gidan, kamar yadda ya saba part d'in Mama ya nufa direct, da key d'in hannunsa ya yi amfani ya buɗe kofar, da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga. Hameedah ce kwance a kan kujera ta na latsa waya, Mahaifiyarta kuwa ta fice gidan k'awayenta. Da sauri ta tashi zaune jin sallamarsa tare da faɗaɗa fara'arta wadda tun da ta zo gidan ba ta yi kamarta ba. Ameen ya kalle ta sau ɗaya ya kau da kansa, har ya ƙaraso cikin falon kallon sa take kamar za ta lashe shi bakin ta ya ƙi rufuwa dan farin ciki. Cikin kaud'i da iyayi ta ce "Sannu da zuwa Ya Ameen." Ta ƙarashe zancen tare da mik'ewa ta koma kusa da shi. Ya kalle ta ba yabo ba fallasa ya d'aga mata kai. Hameedah ba ta damu ba ta ce "Yayanah I missed you so much, na manta when last da na ganka, last zuwan da na yi ba mu haɗu ba, gashi kai kuma ba ka zuwa gidanmu." Ameen ya banzatar da zancen nata ya ce "Yaushe ki ka zo?" Cike da jin daɗin ya biye mata suna hira ta ce "Yesterday, ni da Mommy mun zo gaisuwa ne?" Ameen ya ce "Tun yaushe aka yi rasuwar amma sai yanzu za ku zo?" Hameedah ta ɗan shagwab'e ta ce "To ai Yaya ka ga ina zuwa aiki, sai weekend nake da time." Ameen ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma can ya ce "Neehal as she is your cousin sis, amma a mata rasuwa ki ce sai kin samu time za ki zo mata gaisuwa?" Hameedah ta tab'e baki tare da ɓata fuska ba ta ce komai ba, sai kuma can ta ce "Kasan Mommy ma ba ta ji dad'i ba time ɗin shi ya sa ba mu zo ba, kuma na ga ita gaisuwa ai ba ta tsufa, tun da mun masa addu'a ai is ok." Ameen bai kuma ce mata komai ba ya mik'e ya nufi sama gurin Mahaifiyarsa. Mama ta na operating system ya yi knocking k'ofar ɗakin, Mama ta ba da umarnin a shigo. A hankali ya buɗe k'ofar bakin sa ɗauke da sallama. Mama ta d'ago ta na duban sa ta amsa masa, ya ƙaraso ya zauna a gefen ta ya ce "Gud Morning Mum, how are you?." Mama ta ce "Lafiya, ka zo lafiya? Ya aiki?" Ya ce "Alhamdulillah, ina Neehal fa?" Mama ta ce "Ta je aiki." Ya gyad'a kai kawai tare da ƙoƙarin mik'ewa. "Koma ka zauna ina son magana da kai." Muryar Mama ta katse masa hanzarinsa. Ya gyara zama tare da bata duka hankalinsa. Mama ta ture laptop d'in gabanta ta na dubansa da kyau ta ce "Ameen me kake tunani a kan al'amarin Neehal? Ba ka ganin kamar wasu ne suke bibiyar rayuwarta? Duba da a baya an kashe Jameel ma" Shiru ya yi alamun nazari kafin ya sauke Numfashi ya ce "Mum, babu irin tunanin da ban yi ba a kan wannan al'amarin, tun lokacin na ci karo da labarin mutuwar Anwar dake ta yawo a media, amma kuma da na yi wani nazari da lissafi sai na ga kamar kisan Anwar da Jameel ba shi da alaƙa da Neehal." "Saboda me ka ce haka?" Cewar Mama ta na kallon sa. Ameen ya ce "Idan ba ki manta ba Mum, shi Jameel dama can ya na da 'yan adawa a rayuwarsa duba da yanayin aikinsa." Mama ta ce "Hakane, domin kuwa tun a wancan lokacin da aka kashe Jameel ko kaɗan ban yi tunanin kisan ya na da alaƙa da Neehal ba, dan some times Idan ya zo gaishe ni ya na yawan cewa a taya su da addu'a saboda magauta da mahassada, amma kuma kashe Anwar da aka yi ya birgita mun duk wani lissafi na Ameen." Ameen ya ce "Duk da an kashe Anwar amma ba na tunanin kisan Anwar ya na da alaƙa da na Jameel" Mama ta yi shiru ta na jin dama furucin Ameen zai tabbata da sai tafi kowa farinciki, za ta so a ce ba dan Neehal ake kisan ba, amma kuma abun da kamar wuya musamman idan ta yi duba da....... "Kar ki sa wa ranki damuwa Please Mom, kuma ki cire tunanin wai ko dan Neehal aka kashe Anwar" Ameen ya katsewa Mama tunaninta da faɗin haka. Mama cikin damuwa ta ce "Ameen! Ka na so ka kwantar mini da hankali ne kawai kamar yadda ka saba a kodayaushe idan ka ga ina cikin damuwa, amma ba ni kaɗai ba ma, ko A'isha da Sadiya mun yi maganar da su kuma suma duk tunanin su haka ne." "To ai dama tunanin ku duk ɗaya ne ku mata." Cewar Ameen ya na murmushi. Mama ta ɗan harara shi ta ce "Su kuma sauran mazan da muka yi maganar da su fa?" Kamar a ɗan rud'e ya ce "Su wa kenan?" Mama ta masa wani kallo ta ce "To mene na yin hakan kuma, kamar wanda aka zabura?" Ameen ya ɗan lumshe idonsa ya ce "Nothing, kawai ban so ki ka yi maganar da wasu ba" Mama ta ce "Ahmad ɗin Sadiya ne fa sai Mahmud, su kuma ka ga ai duk na gida ne." Ameen ya ce "Hakane, Insha Allahu ko ma yaya ne Allah zai warware mana, kuma Insha Allahu problem ɗin ba daga wurin Neehal ta ke ba." Mama ta ce "Ameen ya Allah." Ameen ya mik'e ya na faɗin "Ina Hajiya fa?" Mama ta ce "Tun safe driver ya kaita gidan Sadiya yau can za ta wuni." Ya ce "Ok" har ya juya Mama ta ce "Ka ga Hameedah kuwa" ya gyad'a mata kai alamar Eh ba tare daya juyo ba, Mama ta yi murmushi kawai dan tasan tun da ya yi haka ba ya son zancen Hameedan ne.
Neehal ta na zaune a office d'inta ta na duba wasu takardu Haneefah ta shigo office d'in bakinta ɗauke da sallama. Neehal ta amsa mata tare da dire da takardun a kan table ɗin gabanta. "Har kun gama editing ɗin?" Neehal ta tambayi Haneefah dake ƙoƙarin zama. Haneefah ta ce "Eh, ai time ɗin labaran ya kusa" Neehal ta ce "Hakane" sannan ta gyara zama ta na duban Haneefah ta ce "Haneefah!" Haneefah ta dube ta da mamaki domin tasan tunda Neehal ta kira ta da sunanta abu mai mahimmanci za ta faɗa mata. Neehal ba ta jira amsar Haneefah ba ta cigaba da magana. "Haneefah zuciyata ta na cikin fargaba gami da zullumi da tsoro a kan kisan Anwar, Ina tsoron a ce ta dalilina aka kashe Anwar" Haneefah ta ce "Me ya sa ki ke cewa haka ne wai Neehal, ta yaya kisan Anwal zai zama saboda ke?" "Saboda an kashe Jameel ma a baya." Haneefah ta ce "Ki dena tunanin saboda ke aka kashe su, na faɗa miki wannan maganar tun kafin yau amma kin k'i ki daina ta, akan me za'a na kashe miki samari?" Neehal ta ce "Shine ban sani ba Haneefah." Haneefah ta mik'e ta koma kusa da Neehal ta dafa kafad'arta, cikin son kwantar mata da hankali ta ce "Kin ga Neehal kar ki saka wannan abun a ranki har ya yi tasiri a cikin zuciyarki, Jameel da Anwar lokacin mutuwar su ne ya yi, da lokacin su bai yi ba babu wanda ya isa ya kashe su. Kawai Allah ya yi ajalinsu ya na hannun waɗanda suka kashe sun ne, amma wlh Neehal ni har yanzu zuciyata ba ta yarda saboda ke a ka kashe su Anwar ba." Neehal ta sauke numfashi ta ce "Amma kuma Haneefah yanayin yanda ake kashe sun ɗaya ne, duk harbe su ake fa." Haneefah ta ce "Kar ki yi la'akari da wannan, duba da yanda zamani ya sauya, yanzu ai ko barayi ne za su yi sata zai yi wahala ki gansu da wuk'a ko wani makamin, sai dai yara, amma waɗanda suka shahara da bindigu suke zuwa, Dan haka idan an harbe Anwar da Jameel ba hakan ya na nufin mai kisan ɗaya ba ne." Neehal ta yi shiru kawai ta na kallon Haneefah tare da auna maganganunta a mizanin nazari. Bayan kamar minti uku ta ce "To Haneefah ko dai aljanu ne?" "Haba Neehal, wanne aljanu kuma? Kar ki ɗauki alhakin bayin Allah, idan aljanu ne kuma sai su dinga harbe mutum, su da suke da hanyoyin cutar da mutane kala_kala." Haneefah ta katse Neehal da faɗin haka cikin tarar numfashi. Neehal ta runtse idonta kawai tare da dafe kanta cikin kullewar kwanyarta. Haneefah ta saki kafadunta ta koma kujerar da ta taso sannan ta ce "Da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, idan da rabon shan numfashin mutum a duniya ko a na yanka naman jikinsa sai ya rayu, idan kuma kwanan mutum ya ƙare ko da lafiyar sa k'alau dole sai ya amsa kiran mahaliccin sa, ki sa wannan a ranki Allah shine mai yin komai a kuma sanda ya so." Neehal ta ja wani gwauron numfashi ta ce "Tabbas maganganunki gaskiya ne Haneefah, kuma Insha Allahu zan cire wannan tunanin daga raina, amma zan dage da addu'a a kan Allah ya bayyana gaskiyar al'amari." Haneefah ta ce "Ko ke fah, su kuma sai ki ta musu addu'ar neman gafara da dacewa a gurin Ubangiji" Neehal ta ce "Insha Allah, Ni kuma tawa ƙaddarar kenan duk wanda na so ba ma kasancewa tare sai mun rabu." Yanda Neehal ta yi maganar sai da Haneefah ta murmusa ba tare da ta sani ba, Neehal ma murmushin ta yi domin kalaman Haneefah sun fara sanyaya mata zuciya. Ta na murmushin ta ce "Dariya ma na baki ko?" Haneefah ta ce "Ai yanda ki ka yi maganar ne kamar wata sabuwar marainiya." Neehal ta ce "Me ne marabata da sabuwar marainiyar?" "Marabar ku ki na da iyaye samari kawai ki ka rasa, kuma suma za ki samu wasu nan gaba wanda har za ki manta da na baya." Neehal ta mata wani kallo ta ce "Hmmmm, ki na tunanin zan iya ƙara son wani ɗa namiji a duniyar nan ne? ai ni da soyayya kuma sai dai na ga a na yi" Haneefah ta yi wani ɗan murmushi ta ce "Zance ma kenan, za ki yi ta zama ne ba ki yi aure ba? Ko kuma za ki yi Aure ba tare da soyayya ba? Ni na faɗa miki ki rubuta ki ajiye sai kin so wani fiye da son da ki ka yi wa Jameel da Anwar." Neehal ta tab'e baki ba ta ce komai ba, dan ita ba ta ɗauki maganganun Neehal da mahimmanci ba, ban da haka ta yaya za ta so wani fiye da son da ta yi wa Anwar d'inta? Ai tun ranar da Anwar ya rasu ta yi wa kanta alƙawarin ta bar soyayya har abada.
Yau ma gidan Mama Haneefah suka wuce bayan sun tashi daga aiki, suna shiga ta ga Hameedah ita ba ma tasan ta zo ba, dan Neehal ta ma manta da zuwanta ba ta faɗa mata, ita kuma rabonta da gidan tun ranar Alhamis. Suka yi sallama, Hameedah ta d'ago ta musu wani kallo kamar ta ga kashi ta ƙi amsa musu sallamar. Haneefah da ta fi Neehal saurin ɗaukar zafi ta ce "Sai ka ce mutum ba musulmi ba a yi sallama ya na ji ya ƙi amsa wa." Aiko Hameedah dama kaɗan take jira, dan ta je part d'in Ameen za ta masa shirme ya korota, gashi dama ta tsani Haneefah kamar yadda ta tsani Neehal. Mik'ewa tsaye ta yi kamar wata sabowar kamu ta fara ɗura_ɗuran ashar ta na zagin Haneefah har ma da Neehal da ta bata kula ta ba. Haneefah za ta biye mata Neehal ta ja ta su ka hau sama. Bayan sun shiga daki Neehal ta dube ta ta ce "Mai ya sa ki ka kula ta dan Allah? Kin san halin ta fa." Haneefah ta na ware rolling d'in kanta ta ce "Amma dai ai gaskiya na faɗa mata, ita say ta yi ta yi wa mutane kallon banza ta na musu masifa, ni kuma zan mata shiru ne, ai ba tsoron ta nake ba." Neehal ta ce "Na san bakya tsoron ta dama, amma dan Allah ki dai na kula ta, kome za ta yi." Haneefah ta ce "Shikenan Insha Allahu haka ba za ta kuma faruwa ba." Washegari tun safe su Hameedah suka shirya suka wuce Abuja. Mama ta haɗa musu tsaraba kamar yadda take wa kowa idan ya zo gidanta. Hameedah kuwa kamar karta tafi saboda ganin Ameen da take, shi kuwa ko kallo ba ta ishe sa ba. Hameedah ta na bala'in mutuwar son Ameen, shekarun ta kusan 30 amma ta ƙi aure wai jiran shi take, Family kowa ya ɗauka soyayya suke nan kuwa ita kaɗai take haukan ta. Mahaifiyarta kullum ta zo sai ta ce wa Dad ya kamata a saka ranar bikin su, a duk lokacin da ta fadi haka sai Dad ya yi murmushi ya ce "Suwaiba Na fi so Ameen ya yi maganar Hameedah da kansa, ko kuma so ki ke ya raina mini 'yar tawa ya ga kamar neman kai muke da ita." Ita kuwa Suwaiba (Momy) sai ta kada baki ta ce "Yoo tunda shi ya ƙi magana ai mu sai mu yi, abu duk na gida ai duk ɗaya