Showing 186001 words to 189000 words out of 262509 words

Chapter 63 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21405

tana cikin damuwa ko zata ji abun da ya tokare mata ƙirji ya yi ƙasa, amma sai hawayen suka ƙi zuwa wannan karon. Ta buɗe idonta tare yin murmushi mai ciwo wanda ya matuƙar bawa su Mama mamaki ta ce. "Shikenan Mama, Allah yasa haka shi Alkhairi, dama na san haka zata iya faruwa." Bata jira amsa ba ta miƙe dak'yar ta nufi upstairs, ko ganin gaban ta bata yi sosai saboda tsananin damuwa. Suka bi ta da kallo gaba-d'ayan su cike da tsantsar tausayawa Aunty A'isha har da k'walla. Hajiya ta fashe da kuka ta ce. "Gaskiya duk mai aikatawa yarinyar nan wannan abun Allah ka wulaqanta rayuwarsa ta duniya da lahira, Allah ka saukar masa bala'in da ya fi ƙarfin sa." Mama ta lumshe idonta wani tunani na d'arsuwa a cikin ranta wanda take ganin Insha Allahu shine ƙarshen matsalar Neehal. Aunty Sadiya ta ce. "Komai ya kusa zuwa ƙarshe da yardar Allah." Aunty A'isha ta ce. "Allah yasa." Suka cigaba da jimanta al'amarin, suna jinjina wulaqanci irin na Hajiyarsu Sadik. Aunty A'isha ta ce. "Ni ban ji daɗin maganganun da kika faɗa mata ba Sadiya, tunda babbar mace ce ta haife ki." Aunty Sadiya ta ce. "Ai bata da wani girma sai na jikinta, dan abun da ta yi halin ƙananun mutane ne." Hajiya ta ce. "Gwara da kikai mata hakan ai, da za ji zancen Shari'ah ai shiru ta yi ta kama kukan munafurci, yanzu sai a tattara musu kayansu da kuɗaɗen su a mayar musu." Daddy ya ce. "Insha Allahu gobe zan kira Alh. Musa da su Usman sai su zo mu mayar musu." Suka amsa da Allah ya kai mu. Su Aunty's ba su wani jima a gidan ba suka tafi, saboda yanda zuciyoyinsu gaba-d'aya babu daɗi, Hajiya ma ta ce gobe zata wuce Gombe.












Dak'yar Neehal ta iya ƙarasawa ɗakinta saboda juyawar da kanta yake mata. Ta faɗa kan gado tana maimaita Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un cikin sark'ewar harshe. Jikinta gaba-ɗaya rawa yake kamar yadda take jin zuciyarta na bugawa da ƙarfi, ba rabuwa da Sadik ne yafi damun ta ba, *Baƙin tabon* da aka yiwa rayuwarta ne ya fi komai damun ta, ta san shikenan an fara kenan, duk wanda ya ƙara fitowa da niyyar Aurenta mutanen gari zasu hana shi ko kuma idan ya ƙi jin maganar mutane iyayensa wanda ya zama dole yay musu biyayya su hana shi, shikenan kuma wataƙila ita da Aure sai a lahira. Ta tuno gawar Jameel data gani lokacin da za'a kai shi makwancinsa na gaskiya, sannan ta tuno Anwar ma, ta tuno Ahmad ranar da suka rabu a soyayya sannan ta tuno moment ɗinsu da Sadik na d'azu, ta tuna yanda yake kallon ta da yanda ta ga jikinsa a sanyaye da damuwar data hango ƙarara akan fuskarsa, ashe duk na rabuwa da ita ne, hirar ƙarshe suka yi, kallon ƙarshe yake mata ashe. Sai a lokacin ta ji wasu hawaye masu d'umi suna bin kuncinta, wanda take jin kamar a zuciyarta suke sauka suna ƙara mata zafin da take ji a cikin zuciyarta_ta. Ta daɗe a cikin wannan halin mai wuyar fassaruwa, wanda ta kasa bambance a sume take ko a normal rayuwa saboda tsananin damuwa. Bata san mintunan data ɗauka ba ko awanni ba sai ji ta yi Mama tana mata magana. Ta d'ago kanta da yay mata nauyi ta dubi Maman, Mama ta taɓa jikinta ta ji ya yi zafi. Ta shafa fuskarta ta ce. "Ki tashi ki yi Sallah, ko baza ki iya ba?" Ta yunƙura ta tashi zaune dak'yar, a zaunen ma sai ta ji kamar jiri yana ɗibar ta, amma saboda kar tayar da hankalin Mama ta ce. "Zan iya." Mama ta ce. "Sannu kin ji, ki yi Sallar sai ki ci abinci ki sha magani, ki yi ta maimaita sunan Allah da Hasbunallahu'wani'imal'wakil, Insha Allahu zaki ji sauƙin zafin zuciyarki." Ta gyaɗa mata kai kawai. Mama ta bi ta da kallon tausayawa sannan ta tashi ta fice. Bayan ta yi Sallar a zaune Mama ta kawo mata abinci, favourite ɗinta Mama ta yi hoping zata iya ci, amma lauma ɗaya ta yi ta ji abincin ya kasa wucewa ta mak'oshinta, sai ta ji kamar ƙasa ta watsa a bakin nata, ba shiri ta furzar da abincin. Sai tea Mama ta haɗa mata ta sha shi ma da ƙyar ta iya shan kaɗan. Mama tay mata allura ta kwanta ta samu bacci ya ɗauke ta. Tana cikin baccin ta ji muryar Haneefah a kanta. Ta buɗe ido sai ta gan ta zaune a gefen ta. Haneefah ta ce. "Yau kuma bacci ake, na ɗauka zan zo in tarar kuna hira da Habibin naki." Neehal ta tashi zaune bata ce mata komai ba ta sauka ta shiga toilet saboda fitsarin data ji ya ɗaure mata mara. Bayan ta fito ta cewa Haneefah. "Yaushe kika zo?" Haneefah ta ce. "Na kai 30 minutes, na gaji da jiran ki har sai kin tashi da kanki shi yasa na tashe ki." Neehal ta ce. "Kin kyauta ai, gashi nan kin ja mun ciwon kai." Haneefah ta ce. "Sharri kayan k'walba." Sai kuma ta yi murmushi ta ce. "Ashe an ga Ya Sadik, dan iskanci shine baki kira ni kin faɗa mun ba." Neehal ta ce. "Sorry ƙawata, wallahi babu wanda na faɗawa, farinciki ya mantar da ni." Haneefah ta ce. "Sai fa Mommy ce da muka yi waya d'azu take mun zancen, ta ɗauka ma na sani. Na ce mata ban sani ba wallahi, ta ce mun Mama ce ta kira ta, ta faɗa mata." Neehal ta ce. "Ya dawo, cikin k'oshin lafiya ma." Haneefah ta ce. "Masha Allah, haka muke fata dama, yanzu sai k'unci da damuwa su ƙare Tunda Ango ya dawo." Haneefah ta ƙarashe zancen cikin sigar tsokana. Neehal ta yi murmushi mai ciwo ta ce. "Mu fara yin Sallah Haneefah, na ji an shiga a masallaci sai in baki labari." Haneefah ta ce. "Toh."












Duk yanda Neehal take tunanin Haneefah zata ruɗe idan ta ji an fasa Auren su da Sadik sai ta ruɗe fiye da haka, ta miƙe tsaye kamar wata zautacciya tana ambaton Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Idanunta a waje. Neehal ta kama hannunta ta zaunar da ita ta ce. "Karki tada hankalin ki Haneefah nina barwa Allah komai, domin shi yake tsara mun rayuwa kuma ya fi ni sanin dai-dai a cikin ta, ki taya ni da addu'a Allah ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar tawa." Ta ƙarashe maganar cikin matuƙar raunin murya. Haneefah ta girgiza kanta idanunta fal da hawaye ta ce. "Abun ya yi yawa Neehal, daga wannan sai wannan, amma ba komai, komai na Allah ne kuma aure lokaci ne da shi idan lokacin yinki ya yi dole ki yi, babu wani mahaluƙi da ya isa ya hana yiyuwar sa." Neehal ta ce. "Hmmm, Haneefah ni ƴar jarida ce cikakkiya, a kullum cikin jin labarin halin da duniya take ciki nake, haka kuma ina jin labarin ƙaddarar mutane da dama, kowa da irin tasa, wasu matsalar talauci, wasu ciwo, wasu matsalar gidan aure ga suna nan dai matsalolin da yawa barkatai. Amma ban taɓa jin irin nawa ba, Ni kam Haneefah na fitar da rai da Aure har abada, zan cigaba da rayuwata ni kaɗai, in dage da bautawa Ubangiji nah domin samun rabauta a k'iyama. Amma Haneefah na gaji da wannan tashin hankalin, ƴan'uwa da abokan arziki kowa babu kwanciyar hankali. Ki kalli Mama fa, matar da ba ita ta haife ni ba, amma na tabbata damuwata ta kusa saka mata wani ciwon, haka ma Daddy jibi yadda gaba-d'aya ya rame duk saboda ni, ga su Aunty su ma cikin damuwa suke saboda ni, ga ki kema da sauran mutane. A kwanakin nan sai na ji gaba-ɗaya na tsani kaina da rayuwata, amma da nai wani tunani d'azu sai na yi istigfari, na tuna Ubangiji ya bar ni cikin k'oshin lafiya, ga wasu can kwance a gadon asibiti cikin jinya, wanda da zasu ganni na san zasu ce ina ma sune ni yanda nake da lafiyar nan. Rayuwa cike take da k'alubale kala-kala, kuma kowa da irin tasa ƙaddarar, ni kam na karb'i tawa hannu bibbiyu, yanzu addu'a kawai nake Allah ya cire mun son Sadik da tunanin sa daga cikin raina, na san hakan zai rage mun damuwar da nake ciki." Haneefah ta ja gwauron numfashi ta zare hannunta daga cikin na Neehal ta ɗora su akan ƙafarta, cikin confidence ta ce. "Insha Allahu Neehal zaki yi aure da mijin kere sa'a nan ba da jimawa ba, duk wannan k'uncin da kike ciki zai wuce ya zamto tamkar firlm a gare ki." Neehal ta lumshe ido tana jin kamar abun da Haneefah ta faɗa ba zai taɓa tabbata a gare ta ba...........


















******************************








Sabuwar rayuwa Neehal ta buɗe a shafin rayuwarta, a ƙoƙarin ta na ganin ta manta da dukkan abubuwan da suka faru da ita a baya a rayuwarta. Ta yi ƙoƙari sosai wajen cire Sadik daga cikin zuciyarta tare da dagewa da addu'a. Ta koma shiru_shiru a rana bai fi ta furta kalmomin daza a iya irgawa ba. Kafin ka ga murmushi a fuskarta kam za'a daɗe. Alkur'ani da azkar su suka zamto abokan hirar ta, wani lokacin kuma takan taɓa karatun Hausa novels wanda Aunty Sadiya ta tuttura mata dan su ɗebe mata kewa. Tana kuwa jin daɗin karatun littafan sosai. Bata fita ko'ina, saboda a ganin ta tana fita za'a fara nuna ta ana gata nan ita ce duk wanda zata aura sai an kashe shi. Mama da Daddy sun yi sun yi ta koma gurin aikinta amma ta ƙi, da suka takura mata sai ta saka musu kuka, dole suka haqura suka ƙyale ta. Duk wani abu da Mama ta san zai sata farinciki shi take yi, haka zata fita da kanta ta jido mata su sweets wanda ada ita take hanata shan su, amma yanzu duk dan ta yi farinciki take siyo mata. Tun ranar da aka mayar wa da Sadik kayansa gidansu ya turo mata text ɗin ban haquri da nuna mata ba laifinsa ba ne ba su ƙara magana ba. Ahmad ya zo tun cikin week ɗin da ya samu labarin bayyanar Sadik, yay mata murna ya sanar mata bikinsa watan malaudi. Bata sanar masa an fasa bikinsu da Sadik ba dan ta san tsaf zai iya dawowa cikin rayuwarta a matsayin masoyi, ita kuma bata son hakan, ta riga ta cire babin soyayya a rayuwarta. Kuma baza ta so yabar yarinyar da zai aura saboda ita ba, dan ko ita akaywa haka baza ta ji daɗi ba. Ameen kuwa sai ya zo gidan ya tafi ma ba su haɗu ba saboda wunin ɗaki take, babban dalili ne yake fito da ita falo ko ya saukar da ita ƙasa.










Yau ta kama Monday, wanda ya yi dai-dai da wata ɗaya da fasa Auren su da Sadik. A jiya ne kuma ƙawarta Zee ta Bayero ta sanar mata result ɗinsu na last semester is on the corner. Hakan yasa ta shirya yau zata je gurin aikin su, saboda ta ciccike wasu takardu na promotion ɗin da za'ai mata, tunda yanzu zata bar aiki da k'walin Deplomer ne ta koma da na Degree, kafin result ɗin ya fito komai ya yi ready sai ta haɗa ta yi linking ɗinsu. Dama zaman gidan ya fara isar ta, kuma wannan aikin shine gatan ta a duniyar nan, baza ta so ta rasa shi ba.Ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa, ta yi kwalliya sama_sama a ƙoƙarin ta na ganin kar mutane su gane halin damuwar da take ciki. Sai dai a fuska ne kawai ta iya pretended amma damuwar na nan kwance a cikin zuciyarta. Ta tsaya tana kallon kanta a mudubi, sai ta ga ta rame musamman ta wuya da saman ƙirjinta. Hakan yasa ta cire mayafin jikinta ta ɗauko hijabin da zai shiga da kayan jikinta ta saka. Ta ɗauki jakarta wadda wayoyinta ke ciki ta nufi ƙofa, har ta buɗe ƙofar zata fita ta dawo ta ɗauki wata ƙaramar wayarta keypad wanda bata fiya amfani da ita sosai ba, ta saka ta a cikin aljihun rigar jikinta sannan ta fita. A falo suka ci karo da Mama, Mama ta yi murmushin jin daɗin yanda ta gan ta. Ta kama hannunta ta ce. "Kin tashi lafiya Daughter." Neehal ta ce. "Lafiya k'alau Mamana, ina kwana." Mama ta ce. "Lafiya k'alau, ko kefa Neehal har na ji daɗi da zaki koma aikin nan, zai ɗebe miki kewa ba kaɗan ba, jiya da Ameen ya zo kin yi bacci yay ta faɗa wai iskancin me ya hana ki komawa aiki." Neehal ta yi murmushi ta ce. "Mama ɗan nan naki halinsa sai shi, Yaushe ya daina masifar zuwa na aikin, amma yanzu dan bana zuwa zai ce in koma." Mama ta ce. "Nima na yi mamakinsa, wai zama guri ɗaya babu fita gara kina fita kina ganin jama'a hakan zai rage miki damuwa." Neehal ta ce. "Haka ne, shi yasa yau na shirya komawa, Daddy ya fita ne?" Mama ta ce. "Yana nan yanzu dai zai fitan." Neehal ta ce. "Bari na je na gaishe shi." Mama ta ce. "Okay." A falo ta tarar da Daddy zaune yana waya, ta zauna a ƙasan kujerar da yake a zaune, sai ya katse wayar ya dube ta da murmushi ya ce. "Daughter an fito? Ta ce "Eh Daddy ina kwana?" Ya ce. "Lafiya k'alau ƴar albarka, dafatan kin yi breakfast?" Ta ce. "Na yi Daddy." Ya ce. "To Masha Allah, sai yaushe zaki dawo?" Ta ce. "Zan kai yamma saboda cike_ciken da zan yi." Daddy ya ce. "To Allah ya taimaka, ki kula fa sosai kin ji." Ta ce. "Insha Allah Daddy." Sannan ta miƙe tay masa sallma ta fita, ta koma ta yiwa Mama Sallama ta tafi.








Ta ji daɗin fitar da ta yi yau sosai, sai ta ji duk rabin damuwarta ta kau, tana ta hada_hada cikin jama'a ko time ɗin tunani bata samu ba, balle ta tunano abun da zai dame ta. Duk inda ta gilma ma'aikata na yi mata magana, wasu na tsokanarta da wata sabon gani wasu kuma suna yi mata ya jiki, saboda abun da ta cewa Manager ɗinsu kenan da bata zuwa bata da lafiya ne. Sai yanzu ta ƙara tabbatar da abun da Mama take faɗa mata kullum akan ta dinga fita zata ji sauƙin damuwar dake ranta. Sai yamma ta baro gurin aikin tana jin zuciyarta wasai. Ta shigo farkon layin su ta ga wata Mota tana tahowa daga cikin layin, ta yi b'arin left inda masu shiga suke bi, masu fita kuma right side suke bi, amma sai ta ga Motar saitin da take bi nan ita ma take bi, kuma layin nasu yana da faɗi sosai, three motors zasu iya wucewa a lokaci ɗaya ba tare da sun takura ba, kuma babu kowa a layin balle ta ce an tsare masa hanya ne. Ta cigaba da tafiya slowly tana kallon ikon Allah, sai ta koma right side ta bar masa left side ɗin, sai ta ga shi ma ya canza ya koma inda ta koma. Ta yi tsaki ta cigaba da tafiyar ta, a ranta tana faɗin baza ta kuma matsawa ba, sai dai shi in ya ga zasu yi karo ya matsa. Amma me, sai kawai ganin Motar ta yi ta sha gaban ta kamar zata buge ta. Ta taka burki cikin sauri gabanta na fad'uwa. Kafin ta yi wani yunkurin ta ga maza guda biyu sun fito daga cikin Motar cikin sauri, ta yi looked Motar ta_ta da sauri cikin mamakin dalilin da yasa waɗan nan mutanen zasu tare mata hanya, ta shiga ambaton Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un a cikin zuciyarta. Suka ƙaraso inda take suka yi mata knocking glass ɗin Motar. Da farko ta tsorata sai ta ƙi buɗe musu, amma daga baya kuma da ta ga suna bata mata time sai ta zuge glass ɗin Motar ƙasa ta dube su cikin dakiya da son ɓoye tsoron da take ciki ta ce. "Me kuke buƙata a gurina, da zaku taren hanya and then ku zo kuna mun knocking?" Ɗaya daga cikin su ya juya yana kallon layin da babu kowa sai su kaɗai, ɗayan kuma ya bata amsar tambayar ta da watsa mata wani abu a fuska. Ta rufe idanunta tare kare fuskarta_ta da hannunta tana jujjuya kanta saboda juyawar da ta ji ya fara mata, cikin wasu sakanni kanta ya langwab'e a jikin kujerar da take. Da sauri wanda ya watsa mata abun ya zira hannunsa ta saman glass ɗin ya yi unlocked ɗin Motar, sannan ya ja murfin ya buɗe ya shiga, ya mayar da Neehal kujerar mai zaman banza sannan ya zauna a driver seat ya rufe Motar ya tayar da ita ya yi reverse ya fice daga layin da mugun gudu. Ɗayan wanda ya kasance kamar mai yi masa gadi ya juya cikin gudu ya shiga Motar da suka fito daga ciki ya kunna ta ya bi bayan ɗan'uwansa a guje.........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*6️⃣8️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*












........."Ya...ya... Al...lah kasa mafarki nake ba gaske ba ne abun da yake faruwa." Ta sauke hannunta tare da runtse idonta tana girgiza kai, cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ta buɗe ido ta ga babu shi a gurin, Allah yasa idan ta buɗe idon ba shi zata gani ba wani daban zata gani idanunta ne ke mata gizo. Ta buɗe idonta a hankali kamar mai tsoron buɗewa bugun zuciyarta na ƙaruwa. Shi ɗin ne dai tsaye a gaban ta yana kallon ta. Ta sake nuna shi tana ƙoƙarin yin magana amma ta kasa sarrafa harshenta ta yi maganar, sai rawar baki kawai take. Ta juya cikin fitar hayyaci ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice da gudu, ƙofar dake kusa da dakin ta murd'a ta buɗe ta shiga, cikin ikon Allah kuma ƙofar a buɗe take. A cikin wani ɗan ƙaramin ɗaki da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login