Showing 135001 words to 138000 words out of 262509 words
Chapter 46 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
kawai wayar ce baza ta karɓa ba. Sai yay wa yaran sallama ya katse wayar ya tura mata text. Sai bayan sun gama surutunsu sun fita falo sannan ta tashi ta ɗauki wayar, a lokacin ta ga text da Numbern sa. Cikin sauri ta shiga karanta abun da ya turo. _Princess, ya jikin naki, da fatan kin samu lafiya. I MISSED YOU ALOT._ Ta ji wani murmushi ya subce mata, ko ba komai ya nuna care a kanta, duk da bata san me yasa 2 days ya daina kula ta ba, ita kuma tsananin kunyarsa ce tasa in ya kira take kasa pick. Tay masa reply da, _Ina lafiya Uncle, dafatan kai ma haka?_ Ta rungume wayar a ƙirjinta zuciyarta na azalzalarta akan ta kira shi, ta ji muryarsa. Duk da ta ji yanzu da suna waya da su Afrah, amma ta yi missed ɗin yanda yake mata magana da ita a cikin kunnenta cikin salo mai narkar da zuciya, tana ta tunanin nasa bata san bacci ya ɗauke ta ba. Sai ƙarfe ɗaya saura Mama ta tashe ta. "Ki tashi, ki shirya ki shirya su Amrah, ko kin manta zaku fita ne?" Ta tashi zaune cikin muryar bacci ta ce "Ban ma san sanda baccin ya ɗauke ni ba." Mama ta ce "Sai ki tashi yanzu, kafin Salma ta ƙaraso, gidan A'isha zaku fara zuwa sai ya je ya ɗauke ku a can." Tana sakkowa daga kan gadon ta ce "Toh."
Kafin ƙarfe biyu Neehal ta gama shiryawa cikin wani plan cotton material mai kyau, milk colour an masa ado da coffee colour, ɗinkin Baby gown ta yi das a jikinta. Ta yi simple d'auri da d'ankwalin material ɗin, sannan ta yafa mayafi coffee colour. Ta yi kyau sosai, hannunta ya ci zobuna da abun hannu, sai tashin sassayan k'amshinta take. Ta zira plate shoe coffee colour a farar ƙafarta, sannan ta ɗauki ƙaramar handbag itama coffee colour ta zira wayoyinta a ciki. Ta kalli kanta a mirror tana tambayar kanta 'Shigar jikinta ta dace data zuwa gidan surukai? Tun kafin tay wanka take ta tunanin kayan da zata saka a jikinta, da a niyyar ta Hijabi zata zumbula ta tafi, amma kuma data zo saka kayan sai ta fasa ta ɗauko na jikinta wanda bata taɓa saka su ba ta sa. Ta sauke numfashi tana jin zuciyarta wani iri akan zuwa gidansu Sadik ba tare data san dalili ba, ba yau ne first time ɗinta zuwa gidan surukai ba, ta je gidan su Anwar da Jameel, amma wannan sai ta ji kamar ta ce ta fasa zuwan. A hankali ta juya ta fice jikinta a sanyaye, a falon ƙasa ta tarar da Mama da Twins data shirya su tun d'azu, ta kora su gurin Mama dan ta samu damar shiryawa a tsanake. Afrah ce ta fara ganin ta, cikin kaud'inta ta ce "Aunty You look so beautiful." Neehal ta yi murmushi, Amrah ta juyo itama ta ce "Kin yi kyau Aunty." Tay mata murmushi ta ce "Thank you dears." Ta ƙarasa ta zauna a kusa da Mama dake kallon ta, ta ce. "Mama shiga ta bata yi komai ba?" Mama ta ce "Babu abun da ta yi, Daughter sai ma kyau da tay miki." Ta yi murmushi kawai, Mama ta ce "Na ga jikinki duk a sanyaye, ki saki jikinki Daughter babu abun da zai faru sai Alkhairi, Insha Allahu, wannan shine last zuwan ki another in-laws Family." Ta ce "Allah yasa." Ba jimawa da zamanta Salma ta iso gidan, cikin shiga ta mutunci. Mai kyau ce, Black beauty da ita. Ta gaishe da Mama sannan suka gaisa da Neehal, Neehal ta kawo mata drinks ta sha kaɗan bisa takurawar Mama. Kafin ƙarfe uku sun isa gidan Aunty A'isha, Salma da yake she is so friendly tay ta tsokanar Neehal da suna tafiya, dan Mama ta mata bayanin inda za su je, Neehal kam sai dai tay mata murmushi kawai.
Sai bayan la'asar Sadik ya zo ya ɗauke su dan kai su gidansu, har da Maryam ɗin Aunty A'isha suka tafi. Ta so barin su Afrah a gidan Aunty A'isha, amma suka saka ihun sai sun bita, Aunty A'isha ta ce ta je da su kawai. Duk uban warning da ta ja musu akan kar su yi surutun su in je gidan, amma tun a Mota suka fara yiwa Sadik zuba, shi kuma yana biye musu cikin fara'a. Parking ɗin Sadik a compound ɗin gidan su, ya yi dai_dai da fad'uwar gaban Neehal. Ta lumshe ido a ranta tana fatan wannan gidan ya zama na ƙarshe a zuwa gaisuwar surukai a rayuwarta.
Salma ce ta fara fita daga cikin Motar su Afrah suka bi bayan ta cikin zumud'in sun zo unguwa sai kuma Maryam. Sadik ya dubi Neehal ya ce "What happened Wifey?" Ta ce "Nothing, me ka gani?" Ya girgiza kai tare da faɗin. "Babu komai." Ya buɗe Motar ya fita sannan ya zagaya ya buɗe mata. Ta ɗan ɓata rai tana masa kallon bata so hakan ba. Ya yi murmushi ya ce "To naga sai jan aji kike, Maamah kuma na san zuciyarta ta cika taf da d'okin ganin ki." Ta fito tana faɗin, "Like me." Ya ce "Sure?" Ta ce "Sosai ma, waye ba zai so ganin Mamansa ba?" Ya yi murmushi, suka jera suka nufi cikin gidan, Salma na bin bayan su tare da tsokanar su tana faɗin. "Gaban dai Mama za'a je, a rage rashin ta ido." Neehal ta harare ta. Sadik ya ce "A'a gwara dai ta gani da idonta irin son da sirikar ta takewa ɗanta, ko Baby?" Neehal ta ɓata fuska ta ce "Kar ka sa in kasa shiga, ni ka yi gaba ma." Ya yi murmushi tare da yin gaban kamar yadda ta ce.
Sadik ne ya buɗe musu ƙofar part ɗin suka shiga bakunan su ɗauke da Sallama, kan Neehal a ƙasa, da ƙyar take iya d'aga ƙafarta, sosai take jin wata irin kunya tun ba ta yi tozali da surukan nata ba. A ƙasan carpet suka zauna dukan su. Afrah tana kallon falon ta ce "Uncle Sadik gidanka ne nan?" Ya kamo hannunta yana murmushi ya ce "Gidanmu ni da my Family ne." Neehal ta janyo ta tana hararar ta, ta zaunar da ita a gabanta. Sadik ya zauna a kusa da ita ya ce "Me tay miki kuma?" Kamar zata yi kuka ta ce "Ni dai ka tashi daga kusa da ni dan Allah kar Maamah ta fito." Ya tashi yana mata dariyar tsokana, sannan ya nufi ɗakin Maamah. Tare suka fito shi da Batul da Maaman, cikin fara'a Batul ta tarb'e su, suka gaisa. Maamah ma da fara'a ta zauna a Falon, suka gaishe ta cikin girmamawa. Daga yanda kan Neehal yake ƙasa Maamah ta gane ita ce sirikar ta_ta, and 100 💯 ta yaba da Neehal a matsayin surukarta. Batul ta cika musu gaban su da kayan ciye_ciye da na sha, wanda aka tanada domin su. Maamah ta ja su Afrah ɗakinta dan yaran sun burge ta ba kaɗan ba, gashi ba su da wahalar sabo. Maryam da Salma ne kawai suka ci abubuwan da aka kawo musu, amma Neehal ƙin ci ta yi, duk da Maamah ta bar falon, Batul ma korar ta Sadik ya yi duk dan Neehal ta sake amma ta ƙi sakin jikinta. Sadik ya dawo kusa da ita ya zauna ya ce. "Ki ci abincin mana Wifey, Maamah fa da kanta ta yi girkin nan musamman dan ke, ko in baki a baki?" Ya ƙarashe zancen da kashe mata ido. Ta harare shi dama ciki take da shi, ya nuna wa Maamah ita sai ka ce haka aka ce masa ana yi. Da ƙyar ta kurb'i juice ɗin da ya zuba mata a cup, ganin yanda ya wani marairaice mata. Kafin su tafi Abban Sadik da yake yana gari ya zo sun gaisa cikin fara'a da nuna jin daɗin ganin su. Umma ma ta zo sun gaisa ita ƴaƴanta ƴan'mata guda biyu, su kay ta satar kallon Neehal kuwa, amma duk kallon nasu ba su ga makusa a jikinta ba. Sai kusan Magriba suka tafi, Maamah ta sa Batul ta juye musu Gaba-ɗaya sauran kayan ciye_ciyen da suka bari, Abba kuma ya bawa su Afrah kuɗi wanda da farko ƙin karɓa su kay, sai Sadik ne ya karɓar musu. Sosai Abba ya yaba hankali da tarbiyya gami da kunyar Neehal. Suna fita Batul ta ce, "Gaskiya Yaya ya iya zaɓen mata, mai kyau da kunya." Maamah ta yi murmushi cikin jin daɗi, Umma kuwa tab'e baki ta yi. Gidan Aunty A'isha Sadik ya mayar da su, bayan ya shigar musu da kayan ciki, Neehal ta rako shi bakin Mota tana ɓaɓɓata fuska. Ya shiga cikin motar, amma ya bar murfin a buɗe ya ce mata, "To ba mun baro gidan Maaman ai, ki saki jikinki mana." Ta turo baki ta ce "Ina ruwanka da ni, ai mun ɓata." Ya marairaice ya ce "Ni ɗin Wifey, Please ki yi haquri na tuba." Ya ƙarashe zancen yana haɗa hannunsa biyu guri ɗaya. Ta kalli fuskarsa wadda take bayyana farincikin da zuciyarsa take ciki a yau. Ta ce "Sanda ka bani kunya a gaban su Maamah ai baka san da haqurin ba." Da ƙyar dai ya lallaɓa ta, ta haqura suka yi sallama. Bayan ya mata godiyar zuwa gaishe da su Maamah. Ana yin Sallar Magriba suka bar gidan Aunty A'isha, saboda Salma da zata wuce gida. Suna zuwa gida Salma ta fara bawa Mama labarin irin kyakkyawar tarb'ar da suka samu a gidan su Sadik, Mama ta ji daɗin hakan sosai. Salma bata jima ba ta tafi bayan Mama ta cika ta da Alkhairi, Neehal ma ta bata turaruka da sabbin undies.
Ranar Sunday kamar yadda Ahmad ya faɗa da hantsi ya sauka a Kano a gidan Mama. Neehal tana bacci su Afrah suka tashe ta cikin murna. Ta tashi da ƙyar dan bata jima da kwanciya ba, suka sanar mata Daddy ya zo. Sai ta ji gabanta ya faɗi, dan har yau ba su kuma magana da shi ba, tun ɗan chat ɗin nan da sukay ta message. Ta tashi ta shiga toilet ta wanke baki da fuska, sannan ta fito ta ɗauki Hijabi ta fice. A falon sama ta gan shi yaransa a jikinsa suna masa surutu. Ta zauna akan carpet kanta a ƙasa ta ce "Sannu da zuwa Uncle." Ya d'ago ya dube ta cike da d'okin ganin ta, ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani sanyi na ratsa zuciyarsa. Sauke su Afrah ya yi daga jikinsa ya ce su tafi gurin Mama, sannan ya sauko daga kan kujerar da yake ya zauna a kusa da ita. "Princesss!" Ya kira sunanta a hankali. Ba tare da d'ago kanta ba ta ce "Na'am." Ya lumshe ido ya buɗe ya sauke su akan fuskarta ya ce "I missed you so much." Ta d'ago ta kalli fuskarsa itama saboda azalzalar da zuciyarta take mata akan hakan, ta yi murmushi ba ta ce komai ba. Ya tallafi fuskarsa da hannunsa ɗaya ya ce, "Wow, Princess kin ƙara kyau, Please karki daina mun wannan murmushin." Kamar zuga ta ya yi sai ta ɓata rai tare da ɗauke kanta daga gare sa. Cikin damuwa ya ce "Why Princess?" Ta turo baki ta ce "Babu komai." Ya ce "No, akwai Princess, tell me what happened? Bana son na gan ki cikin damuwar nan." Ta yi shiru, ya kamo hannunta ya ce "Please." Ta k'wace hannunta ta ce "Ba kai ne ka daina kula ni ba, yanzu ma na san dan su Afrah ka zo ba dan ni ba." Ya yi shiru yana kallonta, yana tunanin abun da yasa yay mata hakan ko kuma ya ce sukai wa juna." A hankali ya ce "Ke kika fara daina kula ni Princess, idan baki manta ba ranar dana tafi na kira ki da daddare Twins suka ɗauka, nay ta jiran kiran ki idan kin dawo tunda sun ce mun ba kya nan, amma baki kira ni ba, dana kira da safe kuma sai na ji Twins ne suka ɗauka again. That is why na ƙyale ki, may be haka kike buƙata, i thought ina takura miki ne. But I'm sorry." Sai ta ji bata kyauta masa ba, amma ita kunyarsa ce tasa ta yi haka, yanzu ma kawai daurewa ta yi har ta iya kallon sa bisa tilastawar zuciyarta. Ta marairaice ta ce "Ka yi haquri Uncle." Ya yi murmushi ya ce "Babu komai Princess, Princess bata taɓa laifi a wajen Uncle ɗinta." Cikin shagwab'a ta ce "Kuma ni baka takura mun ba." Ya ce "To me yasa kika daina kula ni?" Ta juyar da kai gefe ta ce "Kunyar ka nake ji, ban san ta yaya zan maka magana a time ɗin ba." Ya matso ya juyo da fuskarta ya ce "Let me hug you, sai ki daina jin kunya ta." Ta ja baya da sauri kamar zata yi kuka ta ce "Ai na daina since." Ya yi murmushi yadda duk ta tsorata ya ce "Shikenan, amma idan kika ƙara mun haka, i know what I did." Ta kawar da zancen da faɗin, "Ya su Ummi?" Ya ce "Suna nan k'alau, Mamy ta ce "Kun je gidanta jiya." Ta ce "Uhm." Sai kuma ta shagwab'e fuska ta ce "Wai dagaske tafiya zaka yi da Twins yau?" Ya ce "Eh mana, Gobe za su yi resuming School, hutun nasu babu yawa 2 weeks ne kawai." Ta ce "Shikenan, but i will miss them." Ya ce "Ki bi mu, mu tafi tare." Ta ce "Soon, Insha Allah zaku ganni, Relatives ɗin Dad ma suna ta complain bana zuwa." Ya ce "I was so surprised fa, ace kin zauna a Abuja for some years amma Allah bai taɓa haɗa mu ba." Ta ce "To ai bana fita, daga gida sai School, in kuma zan fita tare da Mama ne." Ya ce "Haka ne, Mummy's girl." Sai ta yi murmushi, ta tuno Ameen saboda shi yake yawan faɗa mata haka. Sai bayan Azhar suka tafi suka bar Neehal cikin kewar su, su ma yaran kuka suka saka da za su tafi, wai sai da ita za su tafi. Da ƙyar Ahmad ya lallashe su ya ce zata biyo su itama soon.
*A WEEK AFTER*
Ranar Friday da safe Mama tana gyaran part ɗin Daddy Ameen ya kira ta a waya, ta ɗauka suka gaisa, daga yanda ta ji muryarsa ta san ba k'alau ba. Ta ce "Ya jikin Hafsan?" Cikin damuwa ya ce "Muna asibiti Mum, ta yi Miscarriage." Mama ta ce "Subahanallahi, yaushe?" Ya ce "Cikin daren jiya." Cikin jimantawa da damuwa Mama ta ce "Allah ya bata lafiya, yanzu tana ina?" Ya ce "Hospital." Mama ta ce "Wanne?" Ya faɗa mata wani private Hospital ne dake kusa da su." Mama ta ce "Bari ta shirya ta zo." Daga haka su kay sallama. Ta kira Daddy ta faɗa masa, sannan ta ƙarasa aikin da take cikin sauri ta shirya ta tafi ita kaɗai, tunda Neehal tana wurin aiki.
Jikin Hafsan da sauƙi ta tarar da ita, tunda tun daren jiyan akay mata ƙarin jini da wankin ciki. Tana kwance akan gadon marasa lafiya, sai mahaifiyarta da mahaifinta a ɗakin. Mama tay mata ya jiki, suka gaisa da parent ɗin nata cikin fara'a da mutunta juna. Kusan wuni Mama ta yi a Hospital ɗin tare da mahaifiyar Hafsah, Daddy ma ya zo ya duba ta da rana, da yamma kuma su Aunty A'isha da Aunty Sadiya suka sun zo. Mama ta kira Driver ya kawo su Dije tare da abincin data saka su, su girka. Ƴan'uwan su Hafsat ma suna ta zuwa duba ta. Tun zuwan Mama ta fuskanci Ameen yana cikin damuwa da b'arewar cikin Hafsat, ko tantama bata yi ya k'walla fa ransa akan cikin ne Allah kuma ya yi ba mai fitowa doron ƙasa ba ne. Tay masa addu'ar Allah ba su wani. Sai can yamma Mama ta dawo gida, lokacin Neehal itama bata jima da dawowa ba. Mama ta sanar mata abun da ya faru, ta ji ba daɗi sosai akan barewar cikin itama, dan duk sun san Hafsan na da ciki, har tana ta murna a ranta sun kusa samun new Baby. A daren ranar aka sallame su Hafsah, mahaifiyarta ta so tafiya da ita gida amma Ameen ya nuna bai so hakan ba, Mahaifin Hafsah kuma ya goya masa baya, ya ce tunda jikin nata da sauk'i ta wuce gidanta kawai. Dole mahaifiyar ta_ta, ta haqura, ta ce zata samo mata dattijuwar da zata na kula da ita har ta samu sauƙi, kamar wata wadda ta haihu, bayan kuma already tana da masu aiki ƴan'mata har guda biyu.
A daren Mama tana part ɗin Daddy suna hira ya ce mata. "Son fa ya kira ni d'azu in nemar masa alfarma a gurin ki." Mama ta ce "Alfarmar me?" Ya ce "Wai Daughter yake son ki ba su ta je ta musu ɗan kwana biyu, kafin Hafsah ta gama warwarewa." Mama ta ce "Ba tana da masu aiki ba, me kuma Neehal zata je tay musu?" Daddy ya ce "Kin san ɗan naki, ba ya cin abinci masu aiki." Mama ta ce "Ohh girki zata je tana yi masa kenan? To ban yarda ba, idan dan abinci ne zan na badawa akai musu." Daddy ya ce "Dama sai da ya ce mun baza ki bari ba, shi yasa ma ya kira ni, in lallame ki, ki barta ta je Doctor, kin ga akwai abubuwan da dole masu aiki baza su iya yi masa ba tunda matarsa bata da lafiya, amma ita Neehal ɗin zata iya masa." Mama tay shiru, Daddy ya ce "A taimaka mana ƴar Amaryata." Ya ƙarashe zancen da dariya. Mama ta ce "Ka ce mun amarya mana tunda zaku yaudare ni kai da ɗanka." Ya yi dariya sosai ya ce, "Yanzu dai kin bari ya zo ya ɗauke ta da safe? Just 1 week za ta yi ta dawo." Mama ta ce "Ka san ba zan iya har 1 week babu ƴata a gabana ba." Ya ce "Idan kuma da Allah yasa an yi auranta fa?" Ta ce "Aure