Showing 210001 words to 213000 words out of 262509 words
Chapter 71 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
wani irin juyawa da kansa yake masa. Ganin Aunty Sadiya ce yasa ya ɗaga wayar ya saka ta a handsfree amma bai ce komai ba. Cikin sauri Aunty Sadiya ta ce. "Ameen ina ka shiga ne yau?" Shiru ya yi bai bata amsa ba. Ta kuma cewa. "Kana lafiya Ameen? Ka yi magana mana." Ya runtse idonsa numfashinsa na fita da sauri da sauri cikin matuƙar sanyin murya ya ce. "I'm fine." Aunty Sadiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Masha Allah." Cikin matuƙar damuwa ya ce. "Ina Mum?" Ta ce. "Muna tare da ita, tun d'azu take kiran ka tana son magana da kai amma baka pick call ɗin." Ajiyar zuciyar shi ma ya sauke ya ce. "Zan zo yanzu in gan ta." Aunty Sadiya ta ce. "Ba ma gida, muna Hospital." A ruɗe ya ce. "What? Kuna me? Waye ba shi da lafiya?" Aunty Sadiya ta ce. "Neehal ce bata jin daɗi." Ya taune lip ɗinsa da ƙarfi sannan ya ce. "Wanne asibitin kuke?" Ta ce. "Nasarawa." Ya ce. "Okay gani nan zuwa." Bai jira amsarta ba ya katse kiran. Mukullin Mota kawai ya laluba ya buɗe ɗakin ya fita. A falo ya tarar da Hafsat zaune idanunta sun yi jajur alamun ta ci kuka ta k'oshi, ta bi shi da kallo zuciyarta fal kishi. Ya ɗan tsaya yana kallon ta. Miƙewa ta yi ta tako gabansa tana kallon sa cikin firgicin ganin yanda ya fice daga hayyacinsa a yini ɗaya. Ta fashe da kuka a hankali cikin kukan ta ce. "Meke damun ka Al'ameen da ka yi wannan ramar lokaci ɗaya? Tun d'azu ka rufe kanka a ɗaki ka bar ni cikin zullumi da damuwa, ka san kuma dole hankalina zai tashi." Lumshe idonsa ya yi cikin k'unar zuci, ya san bai kyauta mata ba tunda bata da masaniyar abun da yake faruwa balle tay masa uzuri akan halin da yake ciki. Bai ce komai ba ya kama hannunta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma ya shiga share mata hawayen fuskarta. Ta kwace hannunta tare da faɗawa jikinsa ta rungume shi. A hankali ya kai hannunsa ya ɗan bubbuga bayanta alamun rarrashi, kafin ya zare ta daga jikinsa ya zaunar da ita akan kujera ya fice daga falon ba tare ya yi magana ba. Ta bi shi da kallo cikin tsananin takaici, a tunaninta duk wannan halin da yake ciki saboda Neehal ne, wutar kishi da tsanar Neehal ne ke ƙara ruruwa a cikin ranta. Ita kam wannan shegiyar yarinyar ta zame mata ƙarfen ƙafa a tsakaninta da mijinta, amma zata yi maganin abun, dole ne ta yiwa tufkar hanci tun kafin dare yay mata ta zo tana kuka da idanunta.
Ikon Allah ne kawai ya kai Ameen asibitin dan baya cikin nutsuwarsa ko kaɗan. Aunty Sadiya ya kira ta faɗa masa section ɗin da suke. Ya buɗe Mota da ƙyar ya fito yana jin jikinsa kamar ba nasa ba saboda damuwa. Cikin kulawa da tausayawa Aunty Sadiya ta tarb'e shi, kama hannunsa ta yi ta zaunar da shi sannan ita ma ta zauna. A hankali ta ce. "Ameen! Ka ga yanda ka koma kuwa? Kamar wanda ya yi jinyar shekara guda, ga jikinka na ji shi ya yi wani irin zafi." Lumshe idonsa ya yi bai ce komai ba. Cikin tausayawa Aunty Sadiya ta ce. "Ka yi haquri Ameen, haka rayuwa take cike da kalubale da jarrabawa, damuwa baza ta taɓa maka maganin abun da ke damun ka ba sai dai addu'a." Gyaɗa mata kai ya yi a hankali sannan ya motsa labbansa da ƙyar ya ce. "Ina Mum da Miemerh?" Aunty Sadiya ta ce. "Neehal tana cikin asibitin nan amma ba'a nan wajen ba, Ya A'isha da Hajiya suna tare da ita, Yaya Fateemah kuma tana cikin ɗakin nan." Ta ƙarashe zancen da nuna masa ɗakin da Mama take. Cikin mamaki ya buɗe idonsa yana kallon ɗakin bugun zuciyarsa ƙaruwa. Aunty Sadiya ta ce. "Damuwar data same ta lokacin ɗaya ce yasa har ta suma, amma zuwa yanzu Doctors sun shawo kan matsalar har ta samu bacci, bana son ka ƙara tayar da hankalinka akan tashin hankalin da kake ciki already, shi yasa da muka yi waya ban sanar maka ba." Bai jira jin ƙarashen zancen Aunty Sadiyan ba ya miƙe ya nufi ɗakin cikin sauri. Ya ƙarasa gaban gadon da take ya ƙura mata ido, cikin zuciyarsa yana jera mata addu'ar samun lafiya. Yayin da tashin hankali da damuwar da yake ciki ya ninku ganin halin da Mama take ciki. Ya san ya rasa Daddy a rayuwarsa dan hukuma baza ta taɓa barin shi ba, koda ba'a kashe shi ba zai ƙare rayuwarsa a prison ne, amma ba zai so ya rasa Mama ba Mace mafi soyuwa a gare sa, Mahaifiyarsa mai tarin alkhairi ga duk wanda ya rabe ta. Ya ɗora hannunsa akan nata a hankali tare da lumshe idonsa da suka yi jajur yana kukan zuci. Daddy bai musu adalci ba, me yasa ya faɗa wannan mummunar harkar da har su koma ga mahaliccinsu tabon abun da ya aikata ba zai bar rayuwarsu ba? Haka ya zauna a gaban Mama yana ta tunane_tunane wanda yake ƙara masa radad'i da k'uncin zuciya. Da wanne ido zai kalli Neehal da ƴan'uwanta? Da wanne ido zai kalli Mama da nata ƴan'uwan? Da wanne ido zai kalli mutanen duniya da dangin Daddy akan abun da Dad ɗin ya aikata? Kunyar kowa yake ji har shi karan kansa, ji yake tamkar shi ya aikata wannan abun kunyar. Wani Doctor ne ya shigo ɗakin yasa shi dole ya fita, dan farko ma faɗa ya kama akan shiga ɗakin da ya yi, Aunty Sadiya ta bashi haquri ta ce ɗanta ne ya zo ganin ta. Ganin yanayin Ameen Aunty Sadiya ta shiga kwantar masa da hankali cikin kalamai masu taushi, da ƙyar ta lallaɓa shi ya koma gida wajen ɗaya saura na dare, dan da cewa ya yi a nan zai kwana, Aunty Sadiya ta ce ya baro Hafsat ita kaɗai ya koma gobe da safe sai ya dawo. Bai je yaga jikin Neehal ba saboda dare da ya yi, idan ya dawo da safen ya je ya duba ta.
Bayan Neehal ta idar da sallolin ta, ta koma kan gado ta kwanta, ba jimawa likitan ya dawo yay mata allurar bacci. Sai dai tashin hankali da damuwar da take ciki ya hana baccin zuwar mata, ko alamun shi bata ji. Ta lumshe idonta dai kawai ta fara tunane_tunane. Rayuwarta ta fara tunowa tun tana ƙarama lokacin iyayenta suna raye, bata iya tuno komai a lokacin sai fuskokinsu da wasu moment ɗinta tare da su kaɗan. Ta tuna yanda Aunty A'isha take bata labarin irin tarin k'aunar da mahaifinta yake mata, ta tuna farkon dawowarta hannunsu Mama da irin riqon gaskiya da amana da sukay mata, gami da tarin k'aunar da suke nuna mata. Mama ta nuna mata son da ko ɗan data haifa albarka, lokuta da dama tana danne farincikinta dana ɗanta domin nata farincikin. Ta tuna wasu lokutan baya lokacin tana ƙarama hankali bai gama isar ta ba, yanda take ɓatawa Ameen abubuwan amfaninsa tana sane, shi kuma babu haquri zuciya a kusa, yana ɗan maketa ta kwanta tay ta birgima tana ihu a ƙasa, Mama ta zo ta ɗauke ta, ta rarrashe ta, shi kuma tay masa faɗa ta ce ya daina dukar mata yarinya ƙarama, yay mata faɗa ko nasiha mana idan ta yi masa abu ba wai duka ba. Sai sun koma ɗaki sannan ita kuma Maman tay mata faɗan ta daina taɓa masa abubuwa. Ta tuna wata rana lokacin tana Jss Mama ta aike ta ta kira shi, ta tarar yana toilet yana wanka, ga laptop ɗinsa a ajiye akan bedside drower a kunne. Ta zauna ta dinga lallatsa masa tay masa barna ba kaɗan ba ta tay masa delete ɗin some important documents ɗinsa. Ranar ta gane Allah ɗaya ne a gurinsa dan tsallen ƙwado ya saka ta, wuni ta yi ranar kuka ƙafa ta ƙi takuwa. Yayin da Mama ta kusa cinye shi ɗanye da masifa. Hakan da Mama take yi ba wai tana yi dan ta saka ta raina Ameen ɗin ba ne, hasali ma bata yi masa faɗa koda wasa a gabanta sai dai wanda Allah ya yi ta ji ko ta gani, kuma kodayaushe cikin nuna mata ta girmama shi take, ita Maman tana yi masa haka ne dan tsoron kar su cutar da marainiyar Allah. Mama ta yi mata tarbiyya irin wacce ake fatan kowacce uwa ta yiwa ƴaƴanta, ta nuna mata respect ɗin na gaba da ita ko waye ne. Hakan yasa ko yaya mutum ya girme mata take girmama shi. Ta tuna Daddy da tarin k'aunar da ya nuna mata a duniyar nan, Daddy ko faɗa baya mata sai dai nasiha, a duk lokacin da zai mata magana cikin fara'a da zolaya yake mata, ko me take so a duniyar nan yana yi mata shi idan bai fi ƙarfin shi ba kuma abun ba mara kyau ba ne. Ko laifi ta yiwa Mama ta san inta kamata zata yabawa aya zaƙinta gurin Daddy take gudawa ta buya, shi kuma ya bawa Mama haquri ita kuma yay mata faɗan har ta kuma. Tun tana ƙaramarta Mama ta koyar da ita yawaita karatun Alkur'ani da azkar da yin nafilfili wanda zuwa yanzu sun zamar mata jiki, uwa uba ibadah da nusar da ita son lahira fiye da duniya. Ita kuma me zata ce da waɗannan bayin Allah a rayuwarta? Sun zame mata garkuwa, bango, jigo da duk wani abun tunk'aho a rayuwa. Komai za su yi baza ta taɓa ganin baƙin su ba a idonta. Wannan abun da ya faru ta san ƙaddara ce Allah ya ɗora musu su duka. Ta tuna yanda dangin mahaifinta dana mahaifiyarta suka banzartar da ita, k'anin mahaifiyarta uwa ɗaya ya kasa yi mata riqon tsakani da Allah, saboda a ganinsa wahala zata zamar masa. Yanzu gashi da bata hannun nasa ya zama abun tausayi, dan ganin da tay masa lokacin bikinsu da Sadik ya zama kamar wani almajiri, duk ya fita hayyacinsa duniya ta fara koya masa hankali. Ta tuna ƙaddarar rayuwarta da yanda al'amura suka dinga tafiyar mata, ashe ƙaddarar ba ta_ta ba ce ita kaɗai, ta shafi mutane masu girma da daraja mafi soyuwa a gare ta, wadda duk matsayin da ta kai a rayuwar nan su ne sanadi. 'Ya Allah ka fitar da Daddy daga cikin wannan al'amarin, Allah ka yafe masa dukkan abun da ya aikata maka ka shirya shi ya bar wannan mummunar hanyar, Allah ka saka masa akan sanya shi cikin wannan harka ba tare da yardarsa ba da bara_gurbin abokinsa ya yi sanadin shigar sa. Allah ka tashi kafaɗun Mama ka bata lafiya da ikon cinye wannan jarabawar daka ɗora mana.' Ta faɗi haka a zuci tana zubar da hawaye. "Yaya..." Ta faɗa can ƙasan mak'oshi, ko yana ina ko a wanne halin yake ciki yanzu sai Allah. Da tunanin Ameen da halin da yake ciki allurar da akay mata ta yi aiki a jikinta bacci ya ɗauke ta wajen ƙarfe uku na dare.........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*7️⃣3️⃣*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
...........Washegarin da aka sallamo Mama ya kama Ranar Lahadi. Da safe su Maman suka hallara a part ɗin Mama a Falon sama dan tattaunawa akan al'amarin Daddy. Uncle Mahmud, uncle Ahmad, Kawu Musa, Abba da Mama. Kawu Musa da bai san abun da ya faru da Daddy ba sai a yanzu Abba ya sanar masa da komai. Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un kawai yake maimaitawa cikin tsananin d'imuwa. A ruɗe ya ce. "Subhallahi, wanne irin mugun aboki Alhaji yake tarayya da shi? gaskiya ya cika cikakken mara imani, matsiyaci ne na ƙarshe amma." Abba ya ce. "Ai Ginyau ba ƙaramar cuta ya yi mana ba, dan ya yi sanadiyar ɓacin sunan zuri'armu." Mama ta ce. "Hmm, idan bera da sata daddawa ma da wari, da a ce Yaya Tafidan bai bi shi ba ai bai isa ya ɗauke shi ya kai shi ba, ko kuma yana zaune a gida ya saka shi a cikin ƙungiyar ba." Kawu Musa ya ce. "Kar ki ce haka Hajiya, babu ta yanda za'a yi dan mutum ya ce maka ka zo ku je wani guri ka yi tunanin a wannan mummunar hanyar zai saka ka, ko da zai kaika gurin irin waɗannan mutanen baza ka taɓa kawowa a ranka saka a cikinsu za'a yi ba, kuma idan har gaskiya ne abun da Alhaji Tafida ya faɗa to duk abun da ya aikata a cikin wannan ƙungiya ba'a hayyacinsa ya yi ba, tunda tsaface shi suka yi. Duk abun da ya aikata na saɓon Allah alhakin yana kan waɗanda suka saka shi a ciki ko a gurin Ubangiji, domin ba shi da yanda zai yi ne a dole yake aikatawa, kuma shi ma ya ce abun yana damun sa. Dan haka yanzu dole mu san yanda za'a yi ya fito daga hannun hukuma sannan kuma ya bar cikin wannan ƙungiyar. Ita kuma Neehal wannan abubuwan da suka dinga samun ta sanadiyyar shi Alhaji Tafidan ba laifin kowa ba ne sai mu danginta, domin da mun riƙe ta a hannunmu babu ta yanda za'a yi wannan al'amarin yakasance a gare ta. Watsi da ZUMUNCI da gudun wahala na ƴan'uwan mahaifinta da mahaifiyarta duk shi ya janyo mata, banda haka ta yaya har za'a ce yayar kishiyar mahaifiyarka ce zata riƙe ka banda ma da mutunci sosai a tsakani, alhalin da danginka a raye. Su suna can sun saki baki tunda yarinya ba'a hannunsu take ba babu ruwansu da wahalarta koma me zai faru da ita ya faru basu da asara. Bacin su kuma wahalar da mahaifinta ya yi da su." Uncle Mahmud ya ce. "Malam Musa da zancenka gaskiya, amma duk da haka Ubangiji ne ya ƙaddara mata hakan zata faru da ita." Kawu Musa ya ce. "Haka ne, amma komai yana da sanadi a rayuwa, rashin ZUMUNCI ba ƙaramin abu ba ne, wanda bai yi shi a duniya ba fa aka ce zai yi shi a wuta. Yanzu da ace tana hannunmu mu danginta da Alhaji Tafida ya faɗa wannan harkar ai baza su ce ya je har inda take ya cutar da ita ba, tunda kamar yadda suka faɗa ba shi yake ciyar da ita ba da sauransu." Abba ya ce. "Haka ne Malam Musa zancenka dutse, na fahimci abun da kake nufi da maganar ka da kuma abun da kake son faɗa. Mutane ne yanzu sun mayar da zumunci na ganin ido da kuɗi, zumuncin Allah amma ba'a son yin sa, kuma an mayar da hakan kamar ba komai ba." Kawu Musa ya ce. "Ƴar guda ɗaya tal a duniya amma su kasa riƙe ta, bacin tarin Alkhairin da mahaifinta yay musu da yana raye. Amma kuma da yake Allah mai ƙudura ne ba ka ga yanda su Salisun suka koma ba yanzu gaba-d'ayansu. (Ƴaƴan Baffa, wanda ya riƙe Umma da Abba.) Sun zama abun tausayi, abun da zasu ci ma gagarar su yake yi, ita ɗin da suka so ta tagayyara gashi Ubangiji sai d'aga ta yake, wannan ƙaddarar data same ta ma Insha Allahu komai ya zo ƙarshe, kuma da ma rayuwar mumuni dole sai da jarrabawa. Wallahi idan kuka ga halin matsin rayuwar da Umar yake ciki sai kun tausaya masa, kuma shi ma duk alhakin marainiyar Allah da ya zalunta ne ya fara kama shi." Mama ta jinjina kai ta ce. "Na gani tabbas, lokacin bikin Neehal da Sadik kamar ba shi ba, har wani tsufan dole ya yi." Kawu Musa ya ce. "Ba dole ba, zaluntar Maraya ai ba wasa ba ne, ga kuma watsi da ZUMUNCIN Allah." Uncle Ahmad ya ce. "Mutanen duniyar nan sai addu'a, ita dai wannan yarinya Allah yasa iya wahalarta kenan duniya da lahira, Allah ya bata miji na gari da zai riƙe ta da amana." Gaba-ɗaya suka amsa da "Amin ya Allah." Sannan suka koma hirar Daddy da yanda za'a yi ya fito, inda suka k'ark'are akan matsayar za su nemi abokin Ameen waɗanda suka tafi da Daddy dan su san ya za'a ɓullo wa abun.
Neehal tana kwance a ɗakinta tana tunanin rayuwa da bata rabo da shi Mama ta shigo ɗakin. Ta tashi zaune tana amsa sallamar da ta yi. Mama ta zauna a gefenta ta ce. "Neehal ban ga kin fito kin ci abinci ba." Kamar zata yi kuka ta ce. "Mama bana jin yunwa ne, wai yaushe Daddy zai dawo?" Mama ta ce. "Ban sani ba Neehal." Ta fara hawaye ta ce. "Mama dan Allah ki cewa su Abba kar su bari a kashe shi, ko kuma su cewa Yaya yasa waɗanda suka kama shi su sake shi." Mama ta ce. "Al'amarin ba ƙarami ba ne Neehal, ke dai ki tay masa addu'a kin ji." Neehal ta d'aga mata kai. Mama ta ce. "To share hawayen mu je ki ci abinci, ai ba zai yiyu ki zauna da yunwa ba."
Bayan Azhar sai ga Mommy'n Hameedah fakal_fakal ta zo gidan, duk zaman da Mama ta yi a asibiti bata zo ba sai yau, yauma dan ta ji labarin abun da ya faru da Daddy ne a wajen Kawunsu k'anin mahaifinsu. Ta zo tay ta ƴan koke_kokenta akan abun da ya samu Daddy tare da borin kunyar abun da suka yiwa Neehal na mutuwa da samarinta suke yi. Daga Mama har Neehal babu wanda ya kula ta, sai da ta gaji dan kanta ta yi shiru. Da yamma Ahmad ya zo gidan. Lokacin Neehal bacci ma take Mama ta tashe ta. Tunda ta sakko ya ƙura mata ido ganin yanda ta rame ta ƙara haske, idanunta duk sun jeme alamun suna shan kuka. Ta zauna a ƙasa nesa da shi a hankali ta ce. "Ina yini?" Ya ce. "Lafiya k'alau Princess ya jiki? Ashe Mama ma bata da lafiya?" Ta ce. "Da sauqi, ita ma Maman