Showing 42001 words to 45000 words out of 262509 words
Chapter 15 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
zuciyarta cike da tunanika kala_kala. Jin hayaniyar mutane sun fara dawowa ta sauke ajiyar zuciya tare da tashi zaune, addu'a ta tofa musu sannan ta tashi ta ɗauko blanket ta lullub'e musu dukkan jiki da shi kansu ne kawai a waje. Toilet ta shiga, rigunan yaran ta fara wanke wa sannan ta goge make up ɗin fuskarta da tissue, tana cikin wanke fuskarta da sabulu Haneefan ta shigo ɗakin tana kiran sunanta. Turus Haneefan ta tsaya bayan ta ƙaraso tsakiyar ɗakin tana kallon yaran dake bacci akan gadon cikin mamaki, a hankali ta ƙarasa gadon ta zauna tana duban yara cike da sha'awa, a rayuwar Haneefan tana bala'in son twins, kan yaran ta shafa tana addu'ar Allah ya bata twins itama. Neehal ta fito daga toilet tana faɗin "Kiran me kike mun haka kamar sabuwar makauniya?" Haneefan ta harare ta tace "Makauniyar ce, ashe kina nan hankalinki kwance mu muna can namu a tashe." "Akan me?" Neehal ta tambaya tana shimfida Darduma domin yin Sallah. Shigowar Mama dakin ya hanata tada Sallar, Mama ta tsaya kawai tana bin ta da kallo. Neehal ta ce "Sannu da zuwa Mama." Rai a ɓace Mama ta ce mata "Kin kyauta Neehal Na gode." Neehal data san kwanan zancen ta ce "Ki yi haquri Mama, wallahi kaina ne ke ciwo kamar zan mutu shi yasa na dawo gida dan na huta." Mama ta ce "Shine ba za ki faɗa a dawo dake gidan ba sai kin yi ƙarya." Neehal ta yi ƙasa da kanta ta ce "I'm sorry ban san na wahalar da kowa ne." Mama ta tab'e baki ba ta ce komai ba, ta juya zata fita idanta ya sauka akan *twins* dake bacci akan gado. Ta dubi Haneefan wadda ta kasa ɗauke idanunta daga kansu ta ce "Haneefan Waɗannan Yaran fa ?" Haneefan ta ce "Nima anan na zo na same su Mama." Mama ta maida dubanta ga Neehal wadda gabanta ke fad'uwa dan bata san ya Mama zata karb'i zancen yara ba, ta ce "Ƴaƴan waye?" Neehal ta sauke numfashi ta ce "Mama long story ne." "Long story kuma?" Mama ta tambaya cikin rashin fahimta, Neehal ta gyaɗa mata kai tare da bata labarin yanda ta samu yaran. Ta ƙara da faɗin, "Na ji tsoro sosai a time ɗin da na gan su, har da zan wuce na barsu sai kuma na yi tunanin kar na barsu wani abun ya cutar da su, gashi sai kuka suke suna kiran Daddy." Mama ta yi shiru kawai tana kallon Neehal, tana son gano gaskiyar abun da Neehal ɗin ta faɗa, ta san Neehal bata mata ƙarya dan ko ta yi ma sai ta gano ta. Mama ta ce "Neehal kin san bana son ƙarya ki faɗa mun gaskiya yaran waye?" Neehal ta ce "Wallahi Mama abun da na faɗa miki shine gaskiya ki yarda mana." Mama ta ce "A ina kika gan su?" Neehal ta ce "Titin Ahmadu Bello ta cikin layika amma." Mama ta yi shiru tana tunani tare da kallon yaran cike da tausayawa, Haneefan ta ce "Allah sarki ko dai sato su aka yi Allah ya yi nufin kub'utar da su shine aka yarda da su a gurin." Mama ta sauke numfashi ta ce komai ma zai iya faruwa, ɗauko ɗaya Haneefan bari na ɗauki ɗaya mu kai su part ɗin Daddy, tunda nan akwai baƙin da za su kwana, kafin safiya mu san abun yi akan su." Haneefan ta ce "Toh." tare da lallaɓawa ta ɗauki ɗaya, yarinyar ta ɗan firgita cikin bacci ta ce "Daddy." Haneefan ta rungume ta ajikinta tana shafa bayanta. Mama ta ce "Babu kaya ajikinsu dama?" Neehal ta ce "Akwai, ya ɓaci da amai ne shine na wanke suna toilet." Mama ta ɗauki ɗayar itama suka fice daga ɗakin. Neehal ta bisu da kallo kafin ta tada Sallah, tana hamdala a ranta da Mama ta fuskanci lamarin Yaran cikin sauƙi.
*▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️*
*ABUJA*
*▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️*
Wata matashiyar budurwa ce ke kai kawo a cikin wani madaidaicin bedroom hannunta riƙe da waya ƙirar iPhone, yanayinta ya nuna tana cikin wani tashin hankali, wayar hannunta ce ta ɗau ruri wanda hakan yasa ta ɗan firgita tare duba wayar da sauri, jikinta har rawa yake ta d'aga wayar ta kara a kunne. A ɗan zafafe ta ce "Haba Gaye ya zan yi ta kiran ku amma ku ƙi d'aga mun waya, kun sa hankalina gaba-d'aya ya tashi ina tunanin ko an samu matsala ne a aikin." Gayen ya ƙyalƙyale da dariya cikin wata ƙatuwar muryarsa ta ƴan shaye_shaye ya ce "Haba haba, ki yi hanzarin tofar da yawunki domin ni bana taɓa yin aiki a samu matsala kuma bana son ana ambata mun ita a cikin aikina, yanzu nan yarana suka kira ni akan aiki ya kammala yanda ake so, yanzu ke kawai nake jira da cikon kuɗina." Wata doguwar ajiyar zuciya budurwa ta sauke ta sharce gumin dake goshinta ta ce "Baka da matsala Gaye indai kuɗi ne yanzu nan zaka ji alert har da ƙari ma akan wanda na ce zan baka." Gaye ya yi murmushi ya ce "Sai na jiki." Tare da kashe wayar. Wani tsalle budurwar ta yi ta faɗa kan gado tana ƙyalƙyala dariyar farin ciki da samun nasara. A fili ta fara faɗin "Ahmad dole yanzu hankalinka ya dawo gare ni tunda na rabaka da abun da yake hanaka kallon mata da sunan soyayya." Ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya tare latsa wayarta domin turawa Gaye kuɗinsa.
Had'ad'd'en asibiti ne wanda daga gani babu tambaya na masu hannu da shuni ne, wata mata ce tsaye a Emergency ward tana kaiwa da komo wa tare da karanto duk addu'ar da ta zo bakinta cikin kuka, kallo ɗaya za kai mata ka fuskanci tana cikin tashin hankali ba kaɗan ba. A gefe guda kuma wata yarinya ce zaune akan kujerun dake gurin wadda ba za ta wuce shekara 15 ba, tana rufzar kuka da dukkan ƙarfinta. Wani Babban Mutum ne ya ƙaraso gurin tare da wasu mutane biye a bayansa, matar na ganinsa ta ƙara fashewa da kuka tana faɗin, "Alhaji ba a gansu ba ko? Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, ya ALLAH ka bayyana mana yaran nan a raye ko a mace, Allah ka kare su da kariyarka a duk inda suke, Allah kasa suna hannu na gari, Allah ka dubi maraicinsu." Sai kuma ta fashe da kuka abun gwanin ban tausayi. Ta ƙarasa inda mutumin yake ta riƙe hannunsa tana faɗin "Alhaji dan Allah ka taimake ni kasa a nemo yaran nan, ko dan mummunan halin da mahaifinsu yake ciki sanadiyyar ɓatansu, dan Allah Alhaji karna rasa ɗanaa." Mutumin wanda ga dukkan alamu mijinta ne cikin lallami ya ce, "Police suna can suna iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun nemo yaran, kuma insha Allahu muna saran za a gansu, ki kwantar hankalinki kin ji." D'ago da jajayen idanunta da suka ci kuka suka koshi ta yi tana duban sa ta ce "Ta yaya hankalina zai kwanta Abbansu, alhalin ga yarona can kwance rai a hannun Allah, jikokina kuma an neme su an rasa ka faɗa mun ta yaya hankalina zai kwanta!" Ta ƙarashe maganar cikin tsananin kuka. Mutumin ya sauke numfashi cikin ƙoƙarin ɓoye tasa damuwar ya ce "Allah yana sane da mu Fatima, kuma insha Allahu shi zai kawo mana mafita, ke dai kawai ki dage da addu'a." Ta gyaɗa masa kai tare da sakin hannunsa ta zauna saboda jirin dake neman yar da ita, mutumin ya nufi gurin da yarinyar dake ta kuka take ya zauna tare da janyo ta jikinsa ya fara rarrashinta. Mutanen da suka zo tare da mutumin suka jinjina kai zuciyoyinsu cike da tausayin wannan ahali. Matar ta d'aga hannunta sama a fili take faɗin, "Ya Ubangiji na roƙe ka ka tashi kafaɗun *AHMAD* ɗina, ka bayyana masa yaransa da gaggawa a duk inda suke, Allah duk wanda yake da hannu a ɓatan yaran nan Allah ka tona asirinsa." Gaba-d'aya mutanen wurin suka amsa da "Amin ya Allah.".........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:40] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*2️⃣0️⃣*
..........Bayan wasu mintuna wani likita ya fito daga ɗakin da Ahmad yake yana goge fuskarsa da handkerchief, Matar ta riga kowa mik'ewa tana faɗin "Doctor, ya ya jikin nasa?" Likitan ya sauke numfashi yana dubanta ya ce "I'm sorry to say Hajiya, just pray." Bai jira amsarta ba ya juya ga Alhajin ya ce "Ka biyo ni office Alhaji." Matar tana sheshshek'a ta ce "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, likita me kake nufi? Har yanzu kenan Ahmad be farfaɗo ba?" Alhaji ya dube ta ya ce "Ki zauna ki yi addu'a kamar yadda Doctor ya ce, zan je inji bayaninsa." Matar ta gyaɗa kai tana salati ta koma ta zauna jagwab, yarinyarta ta matso kusa da ita tana sauke numfashi ta ce "Ummi, tunda har yanzu ba'a gansu ba ki kira gidan su Ammi ki sanar musu, ya kamata zuwa yanzu su ma su san halin da ake ciki." Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Tun d'azu naso kiran su Zahra, Abbanku ne ya hana ya ce kar a tayar musu da hankali a bari aga abun da hali zai yi, amma yanzu tunda ba a gansu bari na kira Yaseer na faɗa masa, kin san Ammin tana da hawan jini yanzu in ta ji sai ya tashi, amma shi Yaseer ɗin ya san ta yanda zai faɗa mata hankalinta ba zai tashi ba sosai." Zahra ta gyaɗa mata kai kawai cikin sanyin jiki.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
*KANO*
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Jiki a sanyaye su Mama suka kwantar da yaran a wani ɗaki dake part ɗin Daddy, sosai al'amarin yaran ya girgiza kwanyar Mama, tafi 5 minutes tana kallon yaran kafin ta sauke numfashi ta juya ta fita bayan ta lullub'a musu bargo, Haneefah dama suna kwantar da yaran ta fice. A falo suka ci karo da Aunty Sadiya da Aunty A'isha. Aunty Sadiya ta dubi Mama ta ce "Ya Fatima kin ga Neehal ɗin?" Mama ta ce "Eh, ashe gida ta dawo wai kanta na ciwo." Aunty A'isha ta ce "Ayya, hayaniya ce Allah ya sauwaaqe." Aunty Sadiya dake kallon Mama ta ce "Lafiya kuwa na ganki wani iri?" Mama ta sauke numfashi ta ce "Ina fa lafiya Sadiya." A rude Aunty Sadiya ta ce "Me ya faru?" Mama ta ce "Ku zauna maganar ba ta tsaye ba ce." Sosai Aunty A'isha da Aunty Sadiya suka jimanta al'amarin, zargika kala_kala suka yi akan yarda yaran da akay, Mama ta ce "Sanin gaibu sai Allah." Ɗakin da yaran suke suka shiga suka gan su, Amma Mama ta roƙe su a kan kar su sanar da kowa hatta da Hajiya kuwa. Bayan Neehal ta idar da Sallah ta ɗauko wayarta ta kira Sadik, rejected yay kamar ko da yaushe sannan ya kira ta. Tana d'agawa ta ce "I'm sorry Ya Sadik Please." Sadik ya kwaikwayi yanda take magana ya ce "Um um, ba zan yi sorry'n ba." Neehal ta yi murmushi me sauti jin yanda ya yi ta ce "Haba Yayanah na kaina, idan baka hakura ba kuka fa zan yi." Ta ƙarashe maganar cikin shagwab'a. Sadik ya sauke numfashi ya ce "Shikenan komai ya wuce dear, amma ina kika shiga?" Neehal ta ce "Kaina ke ciwo shi yasa." Cikin tausayawa Sadik ya ce "Subhallah, sannu Allah ya sauqaqe, amma dai kin sha magani ko?" Neehal ta ce "Yanzu dai zan sha." Sun taɓa hira kaɗan suka yi sallama, saboda ta samu ta sha magani ta kwanta ta huta.
Hameedah ce zaune ta ɗora kanta akan cinyar mahaifiyarta tana kuka ƙasa_ƙasa, ganin tabbas ta rasa Ameen tunda gobe zai angonce da wata. Mumy wadda ta gaji da rarrashi tun a gurin bikin ta ce "Wai Hameedah meke damunki ne? so kike har sai mutane sun fuskanci halin da kike ciki, masu dariya su yi miki suna Allah ya ƙara, na ce miki daure zuciyarki za ki yi ki nuna kamar baki damu ba, a yi bikin nan a gama." Hameedah ta d'ago kanta cikin sheshshek'a ta ce "Mumy na yi iya yina nayi ƙoƙarin hakan amma na kasa, wallahi Mumy ba ki ji yanda nake ji a cikin zuciyata ba kamar ana rura mun garwashin wuta." Mumy ta ce "Na san abun da ciwo, kuma nima ina jin yanda kike ji, amma ki daure dai, na faɗa miki ko mai daren daɗe wa sai kin auri Ameen in dai da bokaye a cikin duniyar nan, yanzu dai ki share hawayenki in faɗa miki wani abu kin ji My daughter." Hameedah ta gayd'a mata kai ta fara share hawayen nata.
Misalin ƙarfe 12:30 na dare Ameen ne zaune a falon Daddy shi da Mama da ta kira shi, ya tattara duka hankalinsa yana sauraren abun da zata faɗa masa. Mama ta ce "Dama d'azu kai ka tsayar da Neehal?" Ya ce "Eh." Mama ta ce "Akan wanne dalili?" Ya yi shiru, Mama ta ce "Ka yi shiru ina maka mgn." Ya ce "Babu komai Mama." Mama ta girgiza kai ta ce "To me ne dalilin da yasa ka bata kayan data saka? bayan ga wanda suka ɗinka za su saka ita ƴan'uwanta." Ameen ya ce "Mama wai dama wannan shine kiran da kika mun? wallahi na ɗauka wani babban abunne ya faru." Mama ta harare shi ta ce "Ban sani ba." Shigowar Neehal falon ya hana Ameen faɗar abun da zai faɗa. "Ke kuma daga ina?" Mama ta tambayi Neehal tana kallonta, Neehal ta turo baki gaba ta ce "Bacci zan yi a nan saboda ina son na kwana tare da yaran." Mama ta nuna mata dakin da suke da hannu tana faɗin "Suna nan, zaki wani kwaso jiki a daren nan ki taho kamar da tare da su kike kwana." Neehal ba ta ce komai ba ta shige, Ameen da ya bita da kallo har ta shige dakin sannan ya dubi Mama ya ce "Wanne Yara ne kuke magana akansu." Mama kamar ta share ta ƙi faɗa masa sai kuma dai ta sanar masa, don abokin kuka shi ake fadawa mutuwa. Shima ya girgiza da lamarin, amma dai ya ce wa Mama da safe sai akai yaran gidan Radios da Televisions a bada cikiyarsu ko za a dace a samu iyayensu. Mama ta yi na'am da shawarar shi. Neehal ta daɗe kafin bacci ya ɗauke ta, tana ta aikin kallon yaran, tana jin ƙaunar su na mamaye mata zuciya.
Washegari da safe Neehal tana tattare ɗaki Yarinya ɗaya ta tashi tana kiran sunan Daddy, Neehal ta ajiye tsintsiyar hannunta ta ƙarasa gadon ta d'ago ta tana faɗin "Kin tashi, mu je ki yi fitsari to." Yarinyar dake binta da kallo ta gyaɗa mata kai. Bayan ta yi fitsarin Neehal ta wanke mata baki da fuska suka fito, suna fitowa ta ga itama ɗayar ta tashi zaune tana ta mutsitsika ido, Neehal ta kama ta itama ta kaita toilet, Bayan sun fito ta kalle su ta ce "What is your names?" Wadda tafi surutu ta ce "Afrah, amma Daddy yana ce mun Princess, a lesson da islamiyya kuma *FATIMA AHMAD*." Neehal ta jinjina kai ta ce "Nice name Darling." Sannan ta juya ta kalli Ɗayar ta ce "Ke fa." Yarinyar ta ce "Amrah, amma Daddy yana ce mun Jewel a lesson da islamiyya kuma *AISHA AHMAD*." Neehal ta Jinjina kai tana murmushi ta ce "Nice name sweetheart." Afrah ta ce "Aunty safiyar ta yi zaki kai mu gurin Daddy ko?" Neehal ta gyaɗa mata kai zuciyarta cike da k'aunar yaran. Mama ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da tea flaks da ƙananun cups, yaran suka bita da kallo kafin su haɗa baki a tare su ce "Ina kwana." Mama ta ajiye kayan hannunta tare da amsa musu, ta ƙaraso ta shafa kansu da cike da kaunarsu, dan yaran sun matuƙar burge ta ba kaɗan ba, musamman da suka gaishe ta, ga dukkan alamu daga gidan tarbiyya suke. Mama ta dubi Neehal ta ce "Ɗauko musu kayansu a saka musu, bari na haɗa musu breakfast su yi." Neehal ta amsa mata tare da ficewa daga ɗakin, yaran suka bita da kallo kamar za su bita. Bayan sun yi breakfast Neehal ta musu wanka ta shirya su cikin rigunansu na jiya. Kasancewar yau ne d'aurin Aure yasa gidan ya ƙara cika da baƙi mata da maza, duk inda Neehal ta ɗora k'afarta su Afrah na biye da ita a baya, duk wanda ya tambaye ta yaran waye sai ta ce na wata Friend ɗinta ne. Ɗaya daga cikin sojojin gidan ta bawa kuɗi ya siyo wa musu kayan sakawa da takalma da panties, kafin Azhar ya kawo mata ta shirya su tsaf suka yi kyau sosai. kowa so yake ya ɗauke su ko ya musu hoto, amma yaran sun ƙi yarda da kowa sai Neehal, saboda ganin taron jama'a, ita kuwa ta cika su da kayan zaƙi dangin su chocolate da sweet suna ta sha. Mama kanta ya ɗau caji tana da hidima da mutane, hakan ya sa ba ta bi takan zancen yaran ba, dama kuma da taywa Daddy maganar su ya ce a bari bayan biki sai a san abun yi. Ƙarfe biyu na rana aka ɗaura Auren AL'AMIN MUHAMMAD TAFIDA da amaryarsa HAFSAT AHMAD ƊAN GASKE. Anan babban masallacin Juma'a dake cikin Narasawa G.R.A. Yau ma Neehal ta yi kyau sosai, shadda ta saka da safe Wadda aka mata akai mai kyawun gaske, ta kafa ɗaurinta. Su Afrah sai faɗin "Kin yi kyau Aunty." suke, Murmushi Neehal take idan suka faɗi haka. Ta ce musu "Thank you Dearies." Wajen ƙarfe uku Sadik ya ƙaraso gidan. Neehal ta fito tare da twins ɗinta, tunda ta fito ya ƙura mata ganin irin kyawun da ta yi. Neehal ta gaishe shi ya amsa yana kallon yaran, Neehal ta ce "Ya su Maamah da Abba?" Sadik ya ce "Suna Lafiya, Ya taro?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Allah ya sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya, saura naki kuma." Neehal ta yi murmushi ta ce "Yau har na gaji da jin wannan furucin, kowa muka haɗu sai ya