Showing 54001 words to 57000 words out of 262509 words
Chapter 19 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
nuna mun Mutum ɗaya ne yake kisan Jamil da Anwar!" Dammmm! Gaban Mama ya yanke ya faɗi, a razane ta ce "Ke ko Sadiya wacce shaida kika gani data tabbatar miki da haka? Kuma waye yake kisan?" Aunty Sadiya ta ce "Alamomi da yawa ne suka nuna hakan Yaya, sai dai kuma har yanzu ba mu gano wanda yake kisan ba, amma muna nan muna binkice a kan hakan kuma insha Allahu sai mun gano ko waye." Mama ta ce "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, wannan wanne irin abu ne? wanene yake bin yarinyar nan da irin wannan sharrin? Me tai masa yake ɗaukar wa rayuwarta wannan mummunan matakin?" Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce "Shine abun da muke son sani muma." Ƙarshen tashin hankali Mama ta shiga da jin wannan batun, da har hankalinta ya kwanta ta fara tunanin ko ba dan Neehal ake kisan ba, amma kuma jin wanda ya kashe Jamil shi ya kashe Anwar ya tabbatar mata da sanadin Neehal ake kisan. Duk yanda Aunty Sadiya ta so kwantar wa da Mama hankali amma hakan ya gagara, dan sosai hankalinta ya tashi da jin wannan K'ADDARAR da ta shigo cikin rayuwar Neehal, abun da yake ƙara tadawa Mama hankali shine idan ta tuna ta yanda MAHAIFAN Neehal suka bar gidan duniya, ta matsu Daddy ya dawo ta labarta masa wannan mummunan labarin dan su san ta inda za su ɓullo wa al'amarin.
Misalin ƙarfe goma sha ɗaya da mintuna na dare, Neehal ce kwance akan makeken gadonta Amrah kwance a kirjinta tana bacci, Afrah kuma ta rungume ta ta baya itama tana baccin. Hotuna take kallo a wayarta idanunta na zubar da hawaye tamkar an kunna famfo, a fili ta fara magana kamar haka, "UMMANAH, ABBANA, JAMIL ƊINA, ANWAR ƊINA, Allah ya ji k'anku ya gafarta muku, ya sa kuna cikin aljannatur firdausi, Allah ya toni asirin duk wanda yake da hannu a kisanku." Kuka ta shiga rerawa ƙasa_ƙasa cikin tausayin kanta, rayuwarta ta baya na dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, kewar mahaifanta na ƙara mamaye dukkan zuciyarta, ta rasa me yasa yau suke ta faɗo mata a rai tun da ta tashi, ta daɗe tana kukan kafin bacci barawo ya yi gaba da ita.
*ASALIN LABARI..........✍️*
_*Ku yi haquri da wannan, yau na yi busy ne.*_
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:44] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*2️⃣5️⃣*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
............Alhaji *Muhammad Gabasawa*, Haifaffen garin Kano ne a wani ƙauye dake ƙaramar hukumar Gabasawa, mahaifiyarsa da mahaifinsa duk na can ne. Neman kuɗi ne ya kawo shi cikin birnin Kano tun yana saurayi gurin wani cousin ɗin mahaifinsa wanda suke kira da Baffa. Su biyu rak iyayensu suka haifa a duniya, daga shi sai Yayarsa mace, itama tana zaune a Gabasawan anan take aure. Gidansu babban gida ne a garinsu kuma sananne, kasancewar gidan yawa ne kuma kakansu na da arzik'i. Kayan masarufi suke siyarwa a ƙofar Nasarawa shi da k'anin Babansa wanda yake zaune a gurinsa, kuma Alhamdulillahi suna samu sosai. K'anin baban nasa (Baffa) wanda yake gurinsa yana riƙon yarinya sunanta *FATIMA* ƴar wansa ce uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, Fatima marainiya ce mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama, da a gurin kakarta wadda ta haifi su Baffa take a Gabasawa, daga baya kuma Baffa ya ɗauko ta ya ci-gaba da riƙon ta. Soyyayyace ta shiga tsakanin Fatima da Muhammad har ta kai su ga yin aure suka tare a nan qofar Nasarawa, Muhammad ya kama musu hayar gida ɗaki ɗaya. Fatima ita kaɗai ce Ƴa a gurin mahaifinta, amma a gurin mahaifiyarta su uku ne, kasancewr mahaifinta ya rasu da dadewa har mahaifiyarta ta ƙara aure a wani gidan ta haifi maza guda biyu. Shekar Fateemah biyu da aure ta haifi ɗanta Namiji, sai dai bayan suna ba jimawa ya dinga wani irin ciwo har ya ce ga garinku nan. A lokacin ne kuma Muhammad ya samu aiki a Company'n wani hamshaqin Alhaji, kasancewar ya yi karatun boko amma iya secondary ya tsaya saboda halin rayuwa. Bayan shekara Fatima ta ƙara haihuwar ƴarta mace, sai dai itama watanni ta yi ta ce ga garinku nan. Hankalin Fateemah ya fara tashi garin tana haihuwa yaran na mutuwa, Muhammad ne ma ke tausar ta yana bata baki. A ƙauye kuwa mahaifiyarta da Kakarta suna ta aiko mata magungunan Hausa, a cewarsu jeji ne ke kashe yaran nata. A wannan lokacin suka tashi daga ƙofar Nasarawa suka koma Gadon k'aya inda Muhammad ya gina gidansa madaidaici mai kyau. Lokacin ne kuma arzik'i ya fara bunƙaso masa, saboda mutumin da yake aiki a wajensa mutumin kirki ne ga kyauta ga jama'a, kuma yana jin dad'i aiki da Muhammad kasancewar sa mai gaskiya da riƙon amana, hakan yasa ya ƙara masa matsayi a Company'nsa da suke sayar da takin zamani. A wannan shekarar ne kuma Muhammad ya ziyarci ƙasa mai tsarki ya sauke farali. Sai da aka kusa shekara biyu sannan Fateemah ta ƙara samun wanin cikin, addu'a suka duk'ufa ita da Alhaji Muhammad akan Allah ya yara mata abun da zata haifa, wannan karan ma mace ta haifa, cikin ikon Allah yarinya ta fara girma ba kamar sauran ƴan'uwanta ba, farin ciki a gurin Fateemah da Muhammad da ba zai faɗuba, sai dai watannin yarinyar bakwai ta ce ga garinku nan. Ko kaɗan Fateemah bata nuna damuwarta sosai ba, zuwa lokacin ta sare ta karbi ƙaddarar da Ubangiji ya dora mata, k'annenta Umar da Usman su ta karb'o daga gurin mahaifiyarta ta ci-gaba riƙe su a gurinta, dan gidan da mahaifiyartata take aure ba wani jin daɗin shi take ba, ana dai zaman haquri ne kawai. Umar da Usman suka ci-gaba da zama a gurin yayarsu cikin jin daɗi, lokacin ma sun fara zama samari. Alhaji Muhammad shi yake musu komai babu abun da ya rage su da shi. Fateemah ba ta yi boko ba amma ta yi ilimin Addini dai_dai gwargwado, dan da auranta ma ta yi saukar Alqur'ani mai girma a makarantar matan auren da take zuwa. Fateemah macece mai haquri ga kawaici babu ruwanta, shiyasa mijinta yake jin daɗi zama da ita. Watarana cikin dare Fateemah ta tashi da wani irin murd'awar ciki, tayta nurququsu ba tare da Alhaji Muhammad ya sani ba, har ta samu cikin ya lafa mata, sai dai kuma tana koma wa ta kwanta ta ji wani irin amai ya taso mata, da gudu ta tashi ta yi toilet ta shiga kelaya aman, kakarin amanne ya tashi Alhaji Muhammad daga bacci, sosai ya tausaya mata yay mata sannu. A wannan daren ta yi aman ya kai sau uku, ga zazzaɓi mai zafi daya rufe ta. Da safe kuma cikin ikon Allah sai ta tashi jikin da sauk'i sosai. Haka tai ta yi har kwana uku tana zazzaɓin dare, ranar na huɗu Alhaji ya ɗauke ta suka je asibiti aka dubata, gwajin farko likita ya tabbatar musu tana ɗauke da juna biyu. Murna a gurin Alhaji Muhammad ba a magana, Fateemah kam yak'e kawai take duk da ba ta san abun da Allah ze yi ba. Sosai Fateemah take shan wahala a wannan cikin kamar ba za ta kai ba, laulayi take mai wahala, ba ta iya bacci cikin dare sai kusan asuba yake ɗauke ta, kakarta ita ta zo daga Gabasawa take zaune da ita, dan ko aiki ba ta iya wa. Haka suka cigaba da rainon cikinsu har ya shiga watan haihuwa, tun cikin yana wata bakwai idan ka ga Fateemah sai ka zata ta kusa haihuwa saboda girman cikin. Ranar wata Juma'a ta tashi da nak'uda, cikin ikon Allah kuma ba ta wani sha wahala ba ta santalu ƴaƴanta guda biyu duk mata. Zo ku ga murna gurin Alhaji Muhammad da Fateemah dama sauran ahalinsu baki ɗaya, yaran kyawawa kamar Fateemah sak suka yo, sai dai ɗaya fara ce ɗayar kuma chocolate color kamar Fateemah. Wadda ta fi farin ita aka haifa sannan mai duhun. A ranar aka sallame su suka dawo gida. Kusan ɗaki guda Alhaji Muhammad ya cika da kayan babies saboda tsananin farin ciki, kodayaushe cikin addu'ar Allah ya bar masa rayan yake. Bayan kwana uku da haihuwarsu da daddare ɗaya daga cikin yaran Allah ya amshi abarsa, Hussainar ce ta rasu mai duhun kenan. Kuka sosai Fateemah ta yi akan rasuwar yarinyar, domin ba ta taɓa jin k'aunar ƴaƴan da take haifa ba kamar waɗannan Twins ɗin, ga fargabar itama ɗayar kar ta mutu. Alhaji Muhammad ya ji mutuwar yarinyar sosai shima, haka dai aka yi sunan ɗayar, Ranar suna ta ci Sunan mahaifiyarta *Fateemah Zahra* amma *NEEHAL* za'ana kiranta da shi. An sha Suna sosai wanda duk haihuwar Fateemah ba'a taɓa yin kamarsa ba. A wannan lokacin ne kuma Umar k'anin Fateemah ya gama karatun Secondary ɗinsa, bayan Result ya fito kuma an samu Alhaji Muhammad ya sama masa gurbin karatu a Bayero University Kano. Fateemah kullum cikin godewa Alhaji Muhammad take ita da mahaifiyarta na yanda baya gajiya da dawainiyar k'annenta, kama daga cinsu,shansu,surarsu,iliminsu na boko dana addini duk baya gajiya da yi musu. Dama Alhaji Muhammad mutum ne shi mai kyautatawa ƴan'uwansa na birni dana ƙauye, hakan yasa kullum yake ganin cigaba a al'amuransa. Kowa ya tashi da buƙatarsa sai ya zo gurinsa, shi kuma indai ba ta fi ƙarfinsa ba zai maka. Neehal irin yaran nanne masu shegen Kuka, musamman cikin dare ba ta barin iyayenta su rintsa, Fateemah idan ta gaji da rarrashi takance "Allah ya nuna mun ranar da zaki bar ni na huta nikam, tun daga cikin ki har yau bana samun isasshen bacci." A duk lokacin da ta faɗi haka Alhaji Muhammad sai dai ya yi murmushi kawai. Watan Neehal bakwai kacal a duniya amma sai wayon tsiya, a lokacin rarrafe take ɗan yi amma akwai son yawo, Abbanta kullum da wayo yake fita daga gidan dan idan zai fita ta dinga ihu Kenan. Uncle Usman shine mai d'aukar ta idan ya dawo daga makaranta ya fita da ita, shi yasa tafi sabawa da shi akan Uncle Umar. Shekarta ɗaya da wata biyu Umma ta yaye ta, dan zuwa lokacin ta yi ƙafa ta fara tattakawa ga surutu duk da gwaranci take yi maganar ba ta fita sosai, ga kuma masifa, dan Yaro ɗan shekara uku ma dan tsaurin ido sai ta dinga dukansa, musamman idan aka zo gidansu, ga ta'adi komai aka ajiye sai taɓa. Neehal yarinya ce mai farin jini dan kowa sonta yake, kullum zaka ganta fess Ummanta bata barinta da k'azanta, Abbanta kuwa ba ya gajiya da yi mata siyayyar kayan sawa masu kyau da tsada. Tun tana ƙarama ba ta son hula, ana sa mata zata cire ta yar, gata da gashi mai yawa da tsayi kuma baƙi sidik. Shekararta biyu bakinta ya buɗe cui_cui sai ɗan banzan surutu kamar ta ci aku, ga tsokana kamar me. Umma kullum sai dai ta kalle ta mata addu'ar shiriyar Ubangiji. Sosai mahaifinta yake nuna mata gata kasancewar ta yarsa guda ɗaya tilo a duniya, sai dai ba irin gatan da zai ɓata ba, kuma suna mata tarbiyya dai_dai gwargwado. Shekarar Neehal uku a duniya lokacin ta fara zuwa islamiyya da boko, mahaifinta ya sai filin kusa da gidansu ya haɗe da nasa ya gina wani part ɗin, nan ma da suke ciki ya ƙara gyarashi. Dan zai ƙara aure ne ba dan ya dena don Matarsa ba, sai dan yana da halin yi kamar yadda Allah ya ce. Umma ko kaɗan ba ta damu ba akan za a mata kishiya, addu'a take kawai Allah ya kawo mata ta gari,kuma ta toshe kunnuwanta daga duk wata zuga ta k'awaye da ƴan'uwa. Neehal kam sai murna take Abbanta ya ce ya kusa kawo mata Aunty.
A'isha Sunan Matar da Abba zai aura, Ƴar asalin garin Gombe ce, mahaifanta duka na can ne kuma Fulani ne. Ƴan'boko ne na bugawa a jarida, amma bokon bata hana su yin ilimin Addini ba, ga su ƴan'gayu kyawawa. Bautar ƙasa ce ta kawo ta Kano har Allah ya haɗa ta da Abba suka fara soyayya. Su A'isha su Huɗu ne a gurin iyayensu, Fateemah (Mama) ita ce babba sai Mahmud (Uncle Mahmud) sai A'isha (Aunty A'isha) sannan auta Halimatus Sadiya ( Aunty Sadiya.) An yi bikin Abba da Aunty A'isha lafiya an gama Lafiya, a garin Gombe a ka yi komai, sai kuma ranar D'aurin Aure da Ƴan Gabasawa suka zo aka yi wuni a gidan Umma, Neehal daɗi kamar ya kashe ta ana taro a gidansu, tana ta b'arna Umma ba ta hana ta ba, balle ta faɗa ko ta dake ta. Ƴan kawo Amarya sun zo sosai daga Gombe, kwanan su ɗaya suka koma, suma ƴan Gabasawan ranar suka tattafi. Tun a washegari Aunty A'isha ta fara hidima da Neehal, duk da Umma ta hanata amma ta ƙi. Bayan kwana biyu shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Neehal da Aunty A'isha, dan Aunty A'isha ba ruwanta ita take mata komai, Neehal kam abun da yasa take son Aunty A'isha idan ta yi ta'adi bata faɗa kamar na Umma, Umma kuwa idan ta gaji da magana har make ta take. Da tafiya ta yi tafiya ma Neehal gurin Aunty'n ta koma da zama gaba-d'aya, Umma ta ce "Ala raka taki gona, ta huta da ciwon bakin bari_bari." Zaman lafiya ake tsakanin Umma da Aunty A'isha, Abba kuma yana yin adalci a zamansu, hakan yasa ba'ajin kansu kwata_kwata. Duk inda Aunty A'isha zata da Neehal take zuwa ko da kuwa tafiyar kwanaki za ta yi, hakan yasa danginta duk sun saba da Neehal tamkar jininsu haka suke kallonta.
*Bayan shekara biyu*
An yi bikin Uncle Umar k'anin Umma, inda ya tare da amaryarsa a unguwar Sabuwar gandu, bayan ya gama degree ɗinsa ya yi service Abba ya samar masa teaching a wata secondary school. Gidan da zai zauna ma Abban ne ya siya masa, Umma ta ce gaskiya ba zai karb'a ba abun ya yi yawa, dawainiyar ta yi yawa. Abba ya ce mata "Idan ba zai musu ba wa zai yi wa? Ko tana so ta nuna masa k'annenta ba nasa ba ne." Umma da ta ji ya faɗi haka sai ta haqura, amma fa ranar ya sha godiya da addu'oi a gurinta. Har yanzu da Neehal ta yi shekara biyar Umma ba ta kuma samun ciki ba, Aunty A'isha ma haka. Neehal kullum cikin mitar ita a haifa mata k'ani take, wataran har da kukanta, saboda Freinds ɗinta na makaranta duk yawanci suna da k'anne. A duk lokacin data faɗi haka Abba kan rarrashe ta ya ce ta yi addu'a Allah ya kawo. Neehal ta ƙara girma iyayi da surutu sun ƙaru.
Ranar wata Saturday da yamma ta dawo daga islamiyya, part ɗin Aunty'nta ta nufa direct tana k'wala mata kira, tana shiga falo ta yarda jakarta wadda Exercise book ne kawai a ciki sai pencil, ta cire ɗan mutsin hijabin jikinta shima ta yar, kanta babu d'ankwali saboda bata k'aunarshi ko kaɗan, fakakken gashin kanta da Aunty A'isha ta tsefa mata da safe ya bayyana, wanda ya sauka har ƙasan wuyanta. Har ta nufi bedroom ɗin Aunty ta tsaya turus saboda ganin wani matashi wanda ba zai wuce 17_18 years ba a zaune akan kujera yana latsa system ɗin Aunty A'isha. Neehal ta waro Ido dan bata taɓa ganinshi ba ta ce "Kaii! Waye kai, wa ya kawo ka gidanmu?" *AMEEN* Da bai masan da shigowar ta ba sai muryarta kawai ya ji ya mata banza, kasancewar sa muskili na bugawa a jarida. Neehal ta matso kusa da shi da ɗan ƙarfi ta ce "Kai baka ji ina maka magana." Ko d'agowa bai yi ba balle ya kulata, Neehal ta hau kan kujerar da yake ta kai bakinta dai_dai kunnansa da iya ƙarfinta ta ce "Kai ba ka ji ne, ko kai kurma ne!" Ameen ya d'ago a mugun fusace jin zata kashe masa dodon kunne ya wurga mata wani mugun kallo tare da hankad'e ta daga kusa da shi, Allah ya so kujerar da yake kai doguwa ce ta faɗa a kanta. Da sauri ta tashi zaune tana keɓe fuska tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Sauka ta yi daga kan kujerar ta yi bedroom ɗin Aunty da gudu tana kukan shagwab'ar da babu hawaye, Aunty A'isha ta tare ta da sauri tana faɗin "Me kuma ya faru Daughter?" Neehal ta keɓe baki ta ce "Wani ne a falo ya dake n......" Hango Mama da ta yi zaune a gefen gado yasa bata ƙarasa maganar ba ta nufe ta tare da d'ane mata cinya tana faɗin "Maman Abuja, yaushe kika zo?" Mama ta shafa kanta tana murmushi ta ce "D'azu na zo Daughter, wane ya kika ce ya dake ki?" Neehal ta turo baki ta ce "Ni ban san shi ba, wani yaro ne a falo." Aunty A'isha ta ce "Ba yaro ba ne Neehal Yayanki ne." Neehal ta ce "Aini ban da Yaya, kuma su Annur da Aslam duk suna da Yaya." Ta ƙarashe maganar kamar za ta yi kuka, Mama ta shafa kanta tana murmushi ta ce "Ke ma Daughter ga Yayanki nan na kawo miki kin ji? Daga yau kema kina da Yaya." Neehal ta gyaɗa mata kai tana murmushin jin daɗi an ce ga Yayanta. Mama ta dubi Aunty A'isha ta ce "Nikam A'isha da zaku bar mun Neehal ai da naji daɗi sosai wlh, ina son yarinya mace amma Allah bai bani ba." Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Tab' Wannan kam Ubanta ba zai iya bayar da ita ba, dan tsoka ɗaya ce a miya." Mama ta ce "Ni shaidace kam akan k'aunar da Alhaji Muhammad yake mata." Aunty A'isha ta kama Neehal ta cire mata uniform ɗin jikinta ta saka mata best da dogon wando. Neehal ta ce "Aunty kin dafa mun macaroni na?" Aunty A'isha ta ce "Yana kitchen na dafa miki, bari na zubo miki." Bayan Aunty ta zubo mata macaronin da miya ta fice falo da shi a hannu, gurin Ameen