Showing 87001 words to 90000 words out of 262509 words

Chapter 30 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21438

ce "Allah sarki, Ni kam tana burgeni, yarinyar a nutse take bata da rawar kai." Fadeelah ta ce "Ga ta da kirki wallahi so friendly babu ruwanta."










Neehal ta tura ƙofar ɗakin Ameen a hankali bakinta ɗauke da Sallama, k'amshinsa ne ya fara mata Welcome. Yana kwance akan gado jikinsa sanye da jallabiya brown colour idanunsa a lumshe. Neehal ta ƙarasa ta zauna akan bedside locker tana kallonsa cikin tausayawa, ya ƙara haske kuma ya ɗan faɗa. Hannunta ta kai a hankali ta taɓa wuyansa ta ji jikin nasa da zafi, a tunaninta bacci yake. Ta zare hannunta a hankali daga jikinsa ta ce "Allah ya baka lafiya Yayana." A hankali ya buɗe lumshashshun idonsa ya sauke su a kanta. Ta ce "Yaya! Sannu, ya jikin?" Bai amsa mata sai tashi zaune da ya yi yana taune lips ɗinsa. Cikin murya mara sa lafiya ya ce "Yaushe kika zo?" Neehal ta ce "Yanzu na zo, ya jikin naka?" Ya ce "Da sauƙi, ina Mum?" Ta ce "Tana gida daga school na biyo ta nan." Ya jinjina kansa tare da lumshe idonsa, daga gani babu tambaya ka san yana jin jiki. Neehal ta ji duk hankalinta ya tashi dan baza ta iya tuna sanda ya kwanta ciwo irin haka ba, hannun damansa ta kalla ta ga abun ƙarin ruwa alamun ya sha drips. Kamar zata yi kuka ta ce "Yaya me yake damunka? Mama ta ce mun zazzaɓi kake, kuma na ga kamar ba iya zazzaɓin ba ne kawai." Kafin Ameen ya bata amsa wayarta dake cikin jakarta ta fara vibrate, ta zuge jakar ta ɗauko wayar tare da d'agawa ganin Sadik ne. "Hello Yaya Sadik." Jin haka yasa Ameen ya juyo da sauri ya kalle ta, ta ce "Eh na dawo, ina gidan Yaya na je duba shi." Ta ɗan yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce "Tom sai ka zo." Tare da kashe wayar. Ameen ya mayar da idansa ya lumshe a hankali ya ce mata "Bani ruwa." Da sauri ta ɗauko ruwan dake gaban gadon ta buɗe sannan ta tashi ta miƙa masa tare da faɗin "Sannu Yaya Allah ya sauwaqe." Ya d'aga mata kai tare da karɓar ruwan ya sha. Ganin yanda ta damu sai ya kamo hannunta a cikin nasa yana kallon fuskarta ya ce "Menene?" Ta yi ƙasa da idonta ba ta ce komai ba, ya d'ago hab'arta da ɗayan hannunsa ya ce "Don't cry." Dan ya san halinta, ai ko kamar zugata ya yi sai ta fara hawaye, ita haka Allah ya halicce ta idan ta ga mutum ba shi da lafiya duk sai ta ji ta damu sosai, musamman ma Yayan nata da take jin kamar ta mayar da ciwon nasa jikinta. Ya ɗan tauna lips ɗinsa murya ƙasa_ƙasa ya ce "Kukan na mene?" Ta ce "Yaya baka da lafiya, na ga duk ka rame." Ya ce "Ai na ji sauƙi, kuma soon zan warke Insha Allah." Ta gyaɗa masa kanta. Ya yi ɗan murmushi sannan ya shiga goge mata hawayen fuskarta da tattausan tafin hannunsa ɗaya, ɗayan kuma yana riƙe da hannunta har lokacin. Dai_dai time ɗin Hafsah ta turo ƙofar ɗakin ta shigo.........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:52] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*3️⃣8️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*












..........Turus ta tsaya a bakin ƙofar cikin shock, wani abu mai tsananin ɗaci ya tsaya mata a mak'oshi, dama a fusace ta taho saboda Fadeelah ta sanar mata Neehal ta zo tana cikin ɗakin, sai da ta mata masifar me yasa zata bar wata ta shigar mata ɗakin miji sannan ta taho ɗakin. Neehal ta yi ƙoƙarin zame hannunta daga cikin na Ameen jin ƙarar buɗe ƙofar ɗakin, kuma ko tantama ba ta yi Hafsat ce, amma ya ƙi bata damar hakan, sai ma ƙara matse hannunta yake a cikin nasa duk da shim ya ji shigowar Hafsan. Sai da ya goge mata hawayen fuskarta tass sannan ya saki hannunta yana murmushi ya ce "Mommy's girl, rigimammiya kawai." Neehal ta koma kan bedside locker ta zauna ta turo ɗan bakinta gaba. Duk yanda Hafsah taso daurewa kasawa ta yi, sosai fuskarta ta nuna ɓacin ranta. Ta janyo ƙafarta data ji ta mata wani iri tana bankawa Neehal harara ta ƙaraso cikin ɗakin, ji take kamar ta janyo ta ta shak'e ta dan tsananin ƙiyayyarta da take ji a ranta. Neehal ta dube ta da murmushi akan fuskarta ta ce "Ina yini Aunty Hafsah." Kamar an mata dole ta amsa da faɗin "Lafiya." Neehal ta ce "Ya mai jiki?" A ranta ta ce ''Gashi nan a gabanki ai, kin ga jikin nasa munafuka' Amma a fili sai ta ce "Da sauqi." Daga haka Neehal ta ja bakinta ta tsuke sai ma ƙoƙarin tashi da ta yi dan ta ba su guri. Hafsah ta ɗan saki fuska ta zauna a kan gadon ta kai hannunta jikin Ameen wanda idanunsa ke lumshe ta ce "Baby ya jikin naka?" Ameen ya buɗe idanunsa ya kalli Neehal ba tare da ya amsa mata ba, ya ce "Ki bata abinci, daga school take." Neehal ta miƙe ta ce "No Yaya am full." Wani kallo ya wurga mata wanda yasa ta yin ƙasa da kanta. Hafsah ta had'iye wani malolon baƙin cikin da ya tsaya mata a mak'oshi, 'wato ba ma zai amsa mata magana ba, sai ma bata umarnin da bawa wata banzar yarinya abinci. Amma da yake makira ce sai ta dake kamar ba ta ji komai ba. Cikin kissarta ta ce "Ayya, ai ban sani ba sisina, mu je na baki abinci ki ci" Neehal zata yi magana wayarta dake hannunta ta hau vibrate, ta duba tare da d'agawa ganin Mama ce. Mama ta ce "Kin je gidan Ameen ɗin." Neehal ta ce "Ehh." Mama ta ce "Ya jikin nasa." Ta ce "Da sauqi." Mama ta ce "Is he sleeping?" Neehal ta ce "A'a, idonsa biyu yana ma zaune." Mama ta ce "Okay, bashi wayar." Neehal ta miƙa masa ba tare da ta yi magana ba, ya karb'a tare da kara wayar a kunnensa, ko da ba'a faɗa masa ba ya san Mama ce. Gaisawa suka yi, Mama ya masa ya jiki? Sannan ya bawa Neehal wayar. Ameen ya dubi Hafsah wadda ke kallonsa ya ce "Ina kika ajiye mun my phone's? Mum said ta kira ni ban yi picking ba." Hafsah ta ce ,"Suna Bedroom dina, bari na ɗauko maka." Sai kuma ta marairaice fuska ta dafa kafaɗunsa tare da faɗin "Babyna duk ka rame, ciwon nan yana wahalar mun da kai, nice mai cikin amma kai ne da laulayin." Neehal ta ɗan tab'e baki tare da fita daga ɗakin. Ameen bai cewa Hafsah komai ba, sai idanunsa da ya mayar ya lumshe. Neehal ta fito falo ta zauna ta ɗauko wayarta ta shiga latsawa, su Fadeelah kuwa sai hirarsu suke. Hafsah ta fito ta shiga bedroom ɗinta ta ɗauko wayoyin Ameen ta kai masa, sannan ta fito ta zauna kusa da k'awayenta ba ta ko kalli inda Neehal take ba. Fadeelah ce ma take ɗan sako ta a cikin hirar tasu, ita kuma sai dai ta yi murmushi kawai. Ganin Magriba ta kusa ta miƙe ta dube su ta ce "Aunty Hafsah zan wuce Allah ya ƙara sauƙi." Bata jira amsarta ba ta mai da dubanta ga su Fadeelah tana murmushi ta ce "Sai anjimanku." Fadeelah ta ce "Har zaki tafi Neehal? To ki gai da gida da Mama." Neehal ta ce "Mama zata ji." Sannan ta juya ta fice daga falon. Hafsah ta bita da harara tare da jan dogon tsaki bayan ta fita. Fadeelah ta kalle ta ba ta ce komai ba, a ranta tana mamakin wannan hali na ƙawartata. Neehal tana koma wa gida Mama ta kalle ta, ta ce "Kuka kika yi ko Neehal?" Neehal ta yi shiru, Mama ta ce "Allah ya shirye ki, ya jikin nasa?" Kamar zata kuma wani kukan ta ce "Da sauqi, amma Mama daga gani Yaya yana jin jiki sosai, duk ya rame." Mama ta ce "Ki masa addu'a, ba kuka ba." Ganin idanunta har sun fara ƙyallin k'walla. Da daddare Sadik ya zo suka sha zancensu, sun daɗe suna hira wanda kusan gaba-ɗaya hirar a kan bikin Haneefah suka yi ta. Lokacin da Sadik ya koma gida kamar kodayaushe idan mahaifinsu yana gari, iyayensa duka suna zaune a main Parlour, sai dai yau babu k'annensa. Ya shigo da sallama kan sa a ƙasa, suka amsa masa baki ɗaya. Umma ta ce "Um su Sadik yanzu kullum sai an je zancen ne?" Ran Maamah ya ɓaci amma ba ta ce komai ba. Abbansa ya ce "Idan ya je zance laifi ne?" Cikin kissarta da son ɓata Sadik ɗin a idon mahaifinsa ta ce "Ba laifi ba ne Abbansu, kawai dai na ga ya kamata a san inda yake zuwa zancen ne, domin a tabbatar da tarbiyyar yarinyar." Abba ya kalli Sadik dake tsugunne ya ce "A ina gidansu yarinyar da kake zuwa yake?" Cikin ladabi Sadik ya ce "A Nasarawa gidansu yake, sunan mahaifinta Alh. Muhammad Tafida." Abba ya maimaita sunan kamar mai son tuno wani abu "Alh. Muhammad TAFIDA? kamar na san sunan nan, amma dai zan bincika, dan kamar Yadda Ummanku ta faɗa ya kamata mu san inda kake zuwa ɗin, idan gidansu yarinyar gidan tarbiyya ne sai ka cigaba da zuwa, idan kuma akasin haka ne kasan sauran." Ya ƙarashe zancen yana kallon Sadik. Sadik ya gyaɗa masa kai zuciyarsa babu fargabar komai, dan yasan babu wani abu bad da za a samu a gurin Neehal ko iyayenta Insha Allahu.










Washegari da safe sai ga Hajiya ta zo wai ta zo duba Ameen ne. Neehal tana bacci ta ji Maganar Hajiya a kanta. A hankali ta buɗe idanunta dake cike da bacci, cikin muryar bacci ta ce "Kai tsohuwar nan baza ki bar mutum ya yi ƙiba ba, daga zuwanki ina baccina mai daɗi kin katse mini." Hajiya ta ce "Wanne irin baccin asara ne wannan har tsakar rana? Yaushe Faɗiman ta lalace har ta barki kike irin wannan baccin? Haka zaki je gidan mijin kina sakin baki kina sharar bacci." Neehal ta tashi zaune tana ƴar miƙa tare da yin salati. Hajiya ta ce "Ni ki yi ki tashi ki shirya ki raka ni gidan Aminu yaron kirki irin albarka in dubo sa, duk da ma sai jiya Uwartasa ta faɗa mun rashin lafiyar tasa, ban da haka da tuni ban zo ba." Neehal ta kalli agogon dake bangon ɗakin ta ce "Taɓ, sai dai direban Mama ya kai ki, ni school zan tafi yanzu ina da exam 12." Bata bi takan mitar Hajiya ba ta tashi ta shige toilet. Tana fitowa ta ga wayarta dake kan gado tana haske, ta ɗauka ta ga Ameen ne yake kiranta. Ta d'aga da sallama a bakinta, Al'ameen ya amsa mata. Ta ce "Ina kwana Yaya, ya jikin naka?" Ya ce "Da sauqi, me yasa jiya kika taho baki mun sallama ba?" Ta ce "I thought ka yi bacci ne lokacin." Ya ce "Ko dai kina sauri ki tafi saboda saurayinki zai zo?" Neehal ta ce "Allah ba haka ba ne Yaya" ya ce "Amma ai yazo ɗin ko?" Neehal ta yi shiru tana murmushi ƙasa ƙasa, ya ce "Uhm, to me yasa yau baki kira ni kin ji lafiyata ba?" Sai ta ji abun wani iri, ita da tun yana gida ma basa wata waya balle yanzu da ya yi aure, ko yana nufin dan bashi da lafiya ne bata kira ta ji jikin nashi ba? ta ce "Yanzu na tashi daga barci ne am sorry" Ya ce "Alright, i will call you later" Daga haka ya kashe wayar. Ta bi wayar da kallo kamar zata gan shi a ciki, daga baya kuma ta ajiye ta cigaba da sabgarta.








Hajiya tana duban Mama bayan ta gama rattabo mata yanda suka yi da Neehal ta ce "Wai niko Faɗima har yanzu yaran nan shiru babu labarin wani nasu?" Mama ta ce "Babu Hajiya har yanzu, tun muna zuba idon ganin kira har mun gaji." Hajiya ta ce "Ikon Allah, to ko dai ba ƴan ƙasar nan ba ne?" Mama ta ce "Waya sani ne, sai Allah." Hajiya ta ce "Allah ya kyauta, suna inane ma ban gansu ba." Mama ta ce "Suna makaranta, sai yamma suke dawowa." Hajiya ta ce "Allah sarki Janar, Allah ya saka masa da Alkhairi, shi da ba ya gajiya da aikin Allah"








Har Neehal ta shirya ta fito Hajiya bata tafi gidan Ameen, Mama ta tsayar da ita, ta ce idan ta gama girki sai ta raka ta da kanta. Tana falon ƙasa tana kallo, da Neehal zata wuce ta ce "Au baki tafi gidan Yayan ba?" Hajiya ta ce "Ban sani ba, tunda baza ki raka ni ba meye naki na tambayata na je ko ban je ba?" Neehal ta ce "Allah ya baki haquri, amma dai zaki zaunar mana har bikin Besty ko?" Hajiya ta ce "Gobe goben nan zan koma inda na fito, dubiya ce ta kawo ni dama." Neehal ta ce "Kai Hajiyarmu ki zauna ki yi babbar Sallah a nan." Hajiya ta ce "Um'um, in zauna ku ce na cinye muku nama, gidana zan tafi in yi sallah ta a can." Neehal ta ce "Tom Shikenan, Ni na wuce school." Hajiya ta ce "Allah ya tsare." Washegari kuwa kamar yadda Hajiya ta faɗa ta koma Gombe, ko gidansu Aunty Sadiya ba ta je ba sai su suka zo gidan Maman suka gan ta. Babbar Sallah saura kwana Biyar aka kawo lefen Haneefah, Masha Allah kaya sun yi kyau, Faruq ya yi ƙoƙari sosai, kaya masu tsada ya zuba mata, akwati goma ya mata cike taf da kaya. Ranar Haneefah ta sha tsokana gurin Neehal, tun tana biye mata tana ramawa har jikinta ya fara yin sanyi ta yi shiru. Ana i gobe Sallah mai ƙunshi ta zo har gida ta yiwa Mama da su Afrah, Neehal dai ba ta yi ba saboda kar ya ƙi fita kafin bikin Haneefah. An yi bukukuwan Sallah lafiya an gama Lafiya, Neehal kam babu inda ta je saboda aikin nama, gashi hutun school kwana uku ne kacal, dan ran huɗu ga Sallah ma tana da exam. Kuma ta so wannan Sallar ta zazzaga danginta, duk da basa nemanta amma ita baza ta biye ta su ba, kamar yadda Mama take faɗa mata a kodayaushe, Ta yi zumuncinta dan Allah ba dan su ba, shi zumunci dole ne. Ranar Asabar ɗin data kama saura kwana huɗu a fara bikin Haneefah su Neehal suka gama exam, hakan yasa ta kama hidimar bikin ƙawarta gadan_gadan. Ranar Thursday akai bridal shower, Amarya ta yi kyau sosai ita da k'awayenta, an yanka Cake an cashe. Ranar Friday kuma Kamu, shima Ranar Amarya ta yi kyau har tafi jiya ma. Su Neehal ƙirjin biki an cashe sosai, dan ma Sadik yana hana ta rawar gaban hantsi duk inda ta yi yana biye da ita, wai dan kar wani ya kula ta. Ranar Asabar kuma akai Mother's Day da yamma, da daddare kuma akai Dinner. Tunda aka fara bikin Ameen bai je ba sai ranar Dinner suka je shi da Hafsah. Aiko ranar Neehal ta ga takura, dan hana ta sakat ya yi. Tana shiga filin rawa zata hango idanunsa yana banka mata harara, ga shi ita ma kamar an mata asiri sai tay ta kallon inda yake. Ƙarshe ma tashi yay ya ja hannunta ya fara mata masifar wai tana ganin Maza a gurin amma sai Safa da Marwa take, gashi kayan jikinta sun kama ta. Allah ya taimake ta ranar Sadik bai zo ba, da bata san a gurin wa zata fi shan takura ba tsakanin shi da Ameen. Hafsah kuwa bata ma san me ake yi ba, tana can tana bawa idanta abinci, da Ameen ya tashi ma ta ɗauka waya ya tafi yi. Wata cousin ɗin su Haneefah ta cewa Neehal "Kai amma guy ɗin nan naki ya haɗu, kuma daga gani yana sonki sosai, gashi kun dace." Neehal ta yi murmushi tace mata "Yayana ne fa, kin ga matarsa can a gefensa." Yarinyar ta jinjina kai kawai, amma ita ta hango tsantsar kishin Neehal a tattare da Ameen. Washegari Ranar Lahadi da misalin ƙarfe Sha ɗaya na rana aka ɗaura Auran Haneefah da Angonta Umar Faruq. Tun lokacin ta fara kuka saboda tsokanarta da abokan wasa suka fara yi, jikinta ya yi sanyi duk rawar kan nan babu. Neehal ta ce "Ashe zan ga ranar da bakin tsiwar nan zai mutu." Duk da itama jikinta ya yi sanyi dauriya kawai take. Ranar kiɗan ƙwarya aka sha a cikin gida. Kafin Magriba ƴan ɗaukar Amarya sun zo, a lokacin kukan Haneefah ya tsananta kamar zata shid'e, Neehal ma tuni ta fara kuka. Mommy ma duk yadda taso daurewa amma sai da ta yi Hawaye da za'a fita da ƴartata tilo ɗaya a duniya. Sadik ne ya kai su Neehal gidan Amarya ita da wasu k'awayen Haneefah guda biyu, sai Ameerah ƴar Uncle Mahmud da ta zo bikin itama. A lokacin Neehal ta yi ƙoƙari ta daina kukan, amma kana ganinta ka san tana cikin bad mood, Suna Mota Sadik yana mata magana ma bata responding, ta kwantar da kanta a jikin kujera idanunta a lumshe. Sai da su Afrah dake kan cinyarta yake hirar. Sune na ƙarshen barin gidan Amarya, a haka ma da dabara suka fito saboda Haneefah riƙe Neehal ta yi wai ba za su tafi ba. Gidan Amarya ya yi kyau Masha Allah, Mommy da dangin Abban Haneefah sun mata kaya na ƴaƴan gata, komai ya ji Masha Allah. Sai fatan Allah yasa gidan zamanta ne na har abada, ya kuma ba su zaman lafiya ya kau da fitina a tsakaninsu. Da wani irin ciwon kai Neehal ta dawo gida, sallah kawai ta yi ta bi lafiyar gado, ba jimawa bacci ya ɗauke ta saboda tarin gajiyar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login