Showing 216001 words to 219000 words out of 262509 words
Chapter 73 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
laptop ɗinta ta zauna ta shiga lallatsawa. Har aka yi sallar isha'i bata tashi ba, da yake tana fashin Sallah ne. Sai wajen tara saura ta kashe system ɗin ta tashi, ta san yanzu Daddy'n ya dawo. Ta zira hijabi ta fice daga ɗakin ta nufi part ɗin Daddy. A dinning area ta same su suna dinner. Da fara'a Daddy ya ce. "Daughter sai yanzu? Na ɗauka ko bacci ya ɗauke ki ma." Ta ce. "A'a Daddy, aiki na ɗan rage." Dad ya ce. "Toh Masha Allah, Allah ya taimaka ya yi albarka Daughter." Cikin jin daɗin addu'arsa a gare ta da baya gajiya da yi mata a kodayaushe ta ce. "Amin Daddyna." Mama ta dube ta, ta ce. "Ki zauna ki zuba abinci ki ci." Bata yi musu ba ta ja kujerar kusa da Mama ta zauna ta zuba abincin ta yi Bismillah ta fara ci cikin nutsuwa.
Bayan sun gama cin abincin Neehal ta tattara kayan da suka bata ta wanke a kitchen ɗin part ɗin Daddy'n. Sannan ta koma Parlour'n sa ta zauna a ƙasan kujerar da yake kai. Cikin girmamawa ta ce. "Daddy gani, Mama ta ce kana son magana da ni." Daddy ya gyaɗa kai tare da duban ta cikin sanyin murya ya ce. "Ina son in tambaye ki ne Daughter kuma dan Allah ki faɗa mun gaskiya." Gabanta na fad'uwa ta ce. "Insha Allahu Daddy, indai na sani zan sanar maka." Daddy ya ce. "Yawwa d'iyar kirki, tambayar da zan miki akwai wanda kike so ne yanzu? Ma'ana akwai wanda kuke mu'amala ta soyayya wanda kike da burin aurar shi?" Neehal ta yi ƙasa da kanta cikin jin kunya, tun bayan rabuwar su da Sadik bata ƙara saurarar wani ɗa namiji da sunan soyayya ba, mutum ɗaya ne ma ya nuna yana son ta, a gurin aikinsu yake kuma dama shi ya daɗe yana nuna yana son nata, ita ce kawai bai yi mata ba. Daddy ya ce. "Kin yi shiru Daughter." Ta sauke numfashi cikin ladabi ta ce. "Babu kowa Daddy." Daddy ya ce. "Kin tabbata?" Ta gyaɗa masa kai. Cikin murmushi ya ce. "Toh Alhamdulillah, dama Yayanki Al'ameen ne ya zo mana da maganar yana son auranki, mun yi farinciki da jin daɗin hakan sosai, amincewarki kawai muke jira mu fara shirye-shiryen biki." Ai wata irin muguwar fad'uwar gaba ce ta riski Neehal, saboda tsabar firgicin da zuciyarta ta shiga fitar jininta har ƙara gudu ya yi. Tun daga sunan Yayanki Al'ameen yana son auranki da Daddy ya faɗa bata ƙara fuskantar sauran abun da yake cewa ba. 'Yaya fa, Yayana fa? Impossible, gaskiya ban ji dai-dai ba, ba shi Daddy yake nufi ba.' Ta faɗi haka a ranta. Mama dake nazartar yanayinta ganin yanda ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasa sai ta girgiza kai, dama ta san za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Daddy ya cigaba da magana. "Idan ba kya so Daughter ki faɗa babu mai miki dole, sai mu yi fatan Allah yasa haka shi yafi Alkhairi, ya kawo miki wani na gari." Ta d'ago kanta a hankali cikin ƙoƙarin son mayar da k'wallar data tarar mata a ido cikin rawar murya ta ce. "Daddy ban gane wanne Al'ameen ɗin kake nufi ba?" Dad ya ce. "Ameen dai na gidan nan." Sai ta ƙurawa fuskar Daddy ido kamar shine Ameen ɗin, ta san mafarki take yi babu ta yadda za'a yi a ce ta auri Yayanta, ta shiga addu'a da fatan Allah ya farkar da ita daga wannan rudad'd'en mafarkin da take. Muryar Daddy data ji yana faɗin. "Daughter!" Shi ya dawo da ita cikin nutsuwarta, ta tabbatar gaske ne ba mafarkin ba. Ta sauke numfashi sannan ta ce. "Na'am Daddy." Ya ce. "Karki saka kanki a cikin damuwa, it's your life no body will force you ki yi abun da bakya so kin ji. Yanzu ki tashi ki je ki nutsu ki yi tunanin abun da kike ganin ba zaki takura ba a rayuwarki, abun da yafi miki dai-dai zuciyarki tafi samun nutsuwa a kansa, da safe sai ki faɗawa Mamanki abun da kika yanke." Kamar wadda k'wai ya fashewa a ciki haka ta miƙe da ƙyar ko sallama bata yi musu ba ta fice daga falon. Mama da bata ce k'ala ba ta bita da kallo. Bayan ta fice ta sauke numfashi ta ce. "Dama na san haka zata faru Gen. Jibi yanda yarinyar nan ta firgice daka faɗa mata zancen nan, na san yanzu zuwa zata yi ta tayar da hankalinta tay ta tunani." Daddy ya ce. "Nima na san dole zata kaɗu da jin wannan batun, amma wannan ba abun tayar da hankali ba ne Fateemah, I assure you sai kin fi kowa murna da farinciki da Auran Neehal da Ameen bayan Auran Insha Allah. A kullum burinki da addu'arki Allah ya bawa yarinyar miji na gari wanda zai riƙe ta da amana ya samar mata da farinciki a rayuwarta, Ameen rainonki ne bani da haufi a kansa da waɗannan abubuwan kuma kema kin sani." Mama ta ce. "Duk na san wannan, kuma ni bacin Neehal ma ina duba Matarsa Hafsat, dududu yaushe aka yi auransu har da zai ƙara Aure, yarinyar nan baza ta ji daɗi ba." Daddy ya yi murmushi ya ce. "Wato kina taya ƴarki kishi kenan?" Mama ta ce. "Ba zancen kishi ba ne gaskiya ce." Daddy ya ce. "Wannan ai duk ba wata matsala ba ce, tunda Ubangiji ne ya ce a auri mata har huɗu idan mutum yana da halin yi zai kuma yi adalci a tsakaninsu, addu'a kawai zamu yi Allah ya haɗa kansu, shi kuma Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakaninsu." Mama ta ce. "Haka ne, Amin, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi."
Da jan ƙafa Neehal ta ƙarasa part ɗin Mama ta shige ɗakinta ta faɗa kan gado, da ƙyar ta iya zare hijabin jikinta saboda uban gumin da take haɗawa. Yaya fa, mijin Hafsah da bata k'aunarta shi su Daddy suke son aura mata, dan ita bata yarda Ameen ne ya ce yana son ta ba tafi tunanin kawai Daddy ya faɗa ne. Ita fa a tsarin rayuwarta sam bata son Auren mai mata, mai matar ma kuma Yayanta mijin Hafsat. Yaya masifaffe ta dinga yi masa magana idan sun yi Auran yana share ta. Ta turo baki kamar yana ganin ta tana hango yanda yake tsare gidan nan nasa. A fili ta ce. "Impossible, tunda Daddy ya ce sai na amince to zan ce masa ban amince ba kawai a bar zancen." Da wannan kalaman ta sauke ajiyar zuciya ta ji zuciyarta ta samu nutsuwa har ta samu k'warin gwiwar miƙewa ta rage kayan jikinta ta kashe light ɗin ɗakin ta kwanta. Sai dai me? Tana kwanciya wata zuciyar ta ce mata. 'Kina da hankali kuwa Neehal? Ɗan Mama da Daddy na cikinsu zaki iya kallon idonsu ki ce musu ba kya son shi baza ki iya auran shi ba? Mama da Daddy fa? Wanda ko wani suka kawo miki ba ɗansu ba bai kamata ki bijire musu ba.' Sai ta tashi zaune cikin sauri ta faɗin Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un. Ita dai gaskiya baza ta iya Auran Ameen ba, ta yaya zata iya kallonsa a matsayin mijinta? Ya zaman Auran nasu zai kasance? Sai ta fara hawaye cikin rashin mafita. Idan har ta bijirewa Daddy ta san bata yiwa kanta adalci ba, duniya ma sai ta zage ta, ita karan kanta ma zata ga baƙin kanta. To amma ita da wani ma suka kawo mata ba Ameen ba da sai ta amince, amma ita dai baza ta iya Auran Ameen ba, Yayanta ne fa. Ta yi 1 hour tana tunanin mafita amma ta kasa samowa, gashi Daddy ya ce da safe Mama zata tambaye ta abun da ta yanke a game da maganar. Wayarta ta lalubo bisa shawarar zuciyarta da ta bata na ta nemi shawarar wani, time ta fara dubawa ta ga sha ɗaya saura, to wa ma zata kira? Tambayar da yiwa kanta kenan. Dama Mama ce abokiyar shawararta, idan kuma ba ita ba sai Haneefah, Haneefah kuma zuwa yanzu ta san ta yi bacci, ko ma bata yi bacci ba ya yi dare ta kira ta a yanzu. Sauran waɗanda zata iya shawara da su kuma a duniya wanda ta san za su faɗa mata gaskiya da abun da zata yi na dai-dai sai Aunty Sadiya da Aunty A'isha. Su kuma Mama ƴar'uwarsu ce, ta yaya zata yi wannan zancen da su? Ta yi tunanin kaf danginta babu wanda zata iya kira dan ya bata shawara, wa ma ta shak'u da shi da zai bata time ɗinsa su yi magana? "Uncle Usman." Zuciyarta ta bata amsa, tabbas shi kadai ne zai bata shawara ya faɗa mata abun da zata yi na dai-dai. Ta latsa wayar ta lalubo Numbern sa ta yi dialing, duk da wata zuciyar na ce mata kar ta kira shi, ƙila yanzun haka yana tare da iyalinsa, amma duk da haka bata fasa kiran nasa ba because she is in needing solution. Bai ɗauki kiran ba har wayar ta katse. Dafe kanta ta yi hawaye na cigaba da zuba daga idanunta, fuskar Ameen kawai take hangowa a cukule, tana son ta hango shi as her husband amma ta kasa, ko dan ta yiwa Mama da Daddy biyayya sau ɗaya tak a rayuwarta akan abun da suke so wanda ita bata so, idan ta tuna tsantsar farincikin data gani a fuskar Daddy a d'azu da yake mata maganar sai ta yi tunanin ya zai ji idan ta ƙi amincewa, duk farincikin nan zai daina shi ne fa. To amma ita yanda zaman nasu zai kasance da Ameen a matsayin MATA da MIJI kawai take tunani, kuma matsalarta ba iya Ameen ba ne kaɗai har da Hafsat..........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*7️⃣6️⃣*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
..........Idanunta suka sauka akan kyakkyawar kamilalliyar fuskarsa mai cike da kwarjini, ta yi ƙoƙarin ɗauke kallon ta daga fuskarsa amma ta kasa. Wani irin kallo yake mata wanda yasa ta ji wani irin abu yana yawo a cikin jinin jikinta, kamar yadda zuciyarta take bugawa da ƙarfi. Kallon sa take yi yau as husband to be not as brother before, tunanin hakan yasa ta ji gabanta ya yi wani irin mugun faɗuwa, ya sakar mata wani murmushi wanda zata iya cewa ba'a taɓa murmushin da ya kayatar da ita kamar shi ba. Ta lumshe idonta da sauri wani baƙon abu yana cika zuciyarta a kansa, like kunya ko tsoro. Ta yi baya da sauri tare da buɗe ido tana ɗan turo baki gaba, zuciyarta ta bata shawarar ta zura da gudu ta koma ɗakinta, har sai ya bar gidan sai ta fito. Ta juya cikin sauri amma ko ɗaga ƙafarta bata yi ba ya kamo hannunta, ta juyo kamar zata yi kuka dan abun da take ji a game shi ƙara yawa yake yana neman hautsina mata zuciya, kuma bata taɓa jin hakan a gare shi ba a rayuwarta sai yau. Ta saci kallon fuskarsa ta ga ya haɗe rai kamar ba shi ya yi murmushi yanzu ba, ya tsatstsare ta da kyawawan idanuwansa wanda suke ƙara mata yawan abun da take ji a kansa a cikin zuciyarta. Murya ƙasa_ƙasa ya ce. "Can't you great me?" Ta shiga girgiza kai tsoronsa na ƙaruwa a ranta, cikin rawar murya ta ce. "Ina yini?" Bai ce komai sai kallon fuskarta da yake yi kamar mai neman wani important thing a fuskar. Ta yi ƙasa da kanta a ranta tana addu'ar Allah yasa Mama ta fito ko ta samu ya bar ta. Tana ji ya saki ajiyar zuciya a hankali sannan ya sakar mata hannu without saying anything ya nufi ɗakin Mama. Ta bi bayan shi da kallo tare da murgud'a baki, ganin kamar zai jiyo ta buɗe ƙofa ta fice da gudu. Ya juyo jin ƙarar buga ƙofa, ya girgiza kai kawai tare da yin murmushi sannan ya shige ɗakin Mama.
Mama tana shirya gogaggun kayanta a wardrobe ya shigo ɗakin da sallama. Ta amsa masa ba tare da juyo ta kalle shi ba. Ya zauna akan bedside drower tare da gaishe ta. Ta amsa masa tana rufe wardrobe ɗin sannan ta ƙaraso ta zauna a bakin gado. Tana duban sa cike da kulawa ta ce. "Ya su Hafsah?" Ya ce. "Lafiya k'alau." Mama ta ce. "Dafatan dai lafiya, tun ranar Friday rabon ka da gidan nan." Ya ce. "Lafiya k'alau Mum, weekend ɗin nan ban fita ba a gida nake wuni." Mama ta ce. "Okay." Sun taɓa hira kaɗan wadda majority akan aiki ne sannan ya yi mata sallama ya tafi. Bata yi masa zancen Neehal ba shi ma bai yi mata ba. Neehal kuwa tunda ta sauka ƙasa tana sauke numfashi ta shige ɗakin su Dije, ko abincin ma bata je ta ɗebo ba saboda tana tsoron kar Ameen ya sakko su ƙara haɗuwa, sai da ta ga fitarsa ta window'n ɗakin su Dije sannan ta fito. Da daddare Mama ta yi mata zancen Ameen akan jin ra'ayinta, dan Kawu Musa yau wayarsa biyu akan jin inda maganar ta kwana. Shiru ta yi ƙirjinta na luguden bugu. Mama dake kallon ta cikin nazari ta ce. "Neehal, ki kalle ni as your Mother ba mahaifiyar Ameen, ki faɗa mun abun da yake ranki kamar yadda kike faɗa mun a kodayaushe kin ji ƴar albarkata." Ta gyaɗa kai a hankali sannan ta ce. "Na amince." Mama ta ce. "Kin amince da me?" Ta kwantar da kanta a ƙafaɗar Mama ta ce. "Kin sani fa." Mama tana murmushi ta shiga shafa bayanta ta ce. "Da gaske Daughter maganar da kike faɗa mun tun daga zuciyarki take, bana son ki yi abun da ba kya so, in ba kya so you are free to say, no body will force you." Ta ƙara shigewa jikin Mama ta rufe fuskarta da hannunta ta ce. "Allah da gaske nake Mama." Mama ta faɗaɗa fara'a akan kyakkyawar fuskarta cikin tsokana ta ce. "Kina son Ameen ɗin kenan?" Da sauri ta cusa fuskarta ta ɓoye a jikin Mama tare da turo baki gaba. Mama ta shafa kanta cikin tsananin farincikin data manta rabon da ta yi kamarsa ta ce. "Masha Allah Neehal, Allah ya yi miki albarka ya inganta rayuwarki, ya baki ƴaƴa masu ladabi da biyayya kamar ki, Allah ya baku zaman lafiya yasa haka shi ya fi Alkhairi." Ta amsa da Amin a cikin zuciyarta. Ba ta kallon fuskar Mama amma a muryarta kaɗai tana jin irin farincikin da take ciki, kuma duk saboda ta amince da Auran Ameen ne, ina ga Daddy? Shi wanne irin farinciki zai ji idan ya ji wannan batun? Su saunawa suka saka ta a cikin farinciki a rayuwarsu? Babu adadi. Kenan data ƙi amincewa haka zasu ji babu daɗi a cikin ransu? Gwara da Allah yasa bata yi wannan gatobarar ba. Ta san bata son Auren Ameen ko kaɗan a cikin ranta, amma ta yiwa kanta alƙawari zata danne ta daure ko a fuska baza ta bari a gane ba, zata saka a ranta Allah ya yi Ameen ne mijinta, zata karb'i Auransa hannu bibbiyu idan Ubangiji ya yi hakan ta kasance. Amma tana mamaki da girmama abun a cikin zuciyarta ba kaɗan ba, YAYANTA MIJINTA, ko a mafarki bata taɓa tunanin hakan zata iya faru ba, ita mantawa ma take akwai aure a tsakaninsu da Ameen. As blood brother desame mother desame father take kallon shi. Wasu hawaye da bata san kona mene ba ta ji suna rige_rigen gudu akan kuncinta daga cikin idonta. Ta ƙara rungume Mama tare da fara kuka a hankali. Mama ta shiga bubbuga bayanta tare da faɗin. "Kunan na mene ne?" Ta ja majina bata ce komai ba. Mama ta d'ago da kanta tana kallon yanda take kukan ta ce. "Mene ne wai?" Ta girgiza mata kai kawai. Mama ta ce. "Iskanci ne kenan?" Cikin kukan ta ce. "Bana son na bar ki ne Mama." Mama ta yi murmushi tana jin tausayinta na cika mata zuciya, ta shiga share mata hawayen fuskarta tana faɗin. "Wa ya ce miki zaki bar ni dan kin yi Aure? Duk sanda kike son gani na zaki zo ki ganni ai." Cikin shagwab'a ta ce. "Ke baza ki zo ki dinga gani na ba?" Mama ta yi murmushi ta ce. "Zan zo mana, Amarya tun kafin a yi Aure har an fara zancen zuwa gida." Ta cusa kanta a jikin Mama cikin tsananin jin kunya. Mama ta ƙara rungume ta a jikinta tana jin tsananin farinciki a ranta, tabbas kamar yadda Daddy ya faɗa bata jin akwai wanda zai kai ta farinciki idan wannan al'amarin ya kasance. Bayan Daddy ya dawo Mama ta sanar masa yanda suka yi da Neehal. Farincikin da ya nuna ba zai misaltu ba, ya kira Neehal ta zo part ɗinsa wadda gaba-d'aya yanzu ta ji tana jin kunyarsa, ya dinga saka mata albarka tare da tarin addu'oi, har da tambayarta me take