Showing 255001 words to 258000 words out of 262509 words

Chapter 86 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21398

a hanya ko bata ce masa tana so ba sai ya siyo mata, wani ta ci wani ta ƙi ci. A haka take lallab'awa take zuwa aiki, duk da ya hana ta ya ce ta ɗauki hutu ta ce masa ita bata son zaman gidan, ta fi son tana fita tunda ba wani jin jiki take sosai ba. Amma idan ta je gurin aikin ba wani abun arzik'i take yi ba rabi da rabi bacci ne, a yi ta tsokanar ta kuwa a gurin aikin, sai dai ta yi murmushi kawai cikin jin kunya. Ta ƙi barin Ameen ya faɗawa su Mama tana da ciki, wai ita kunya take ji. Ya yi dariya ya ce. "Indai Mum ce gani ɗaya zata yi miki ta gane, kin sani ke ma." Jin haka sai ta ƙi zuwa gidan Maman, sai dai kullum cikin faɗar tana son ganin Maman take, idan suka yi waya tay ta yi mata mitar ta ƙi zuwa gidanta. Ranar wata Sunday Daddy ya cewa Mama ta shirya ta je ta gano Neehal ɗin ta ga gidanta tunda bata taɓa zuwa ba. Ai kuwa ranar Neehal murna kamar me, ta shiga kitchen ta yiwa Mama abubuwa na tarb'ar ta. Sai yamma Maman ta je gidan. Neehal ta tafi da gudu ta rungume ta, Ameen ya bi ta da wani kallo data san ko na mene ne, juya masa ido ta yi tana murmushi. Mama ta zauna suka gaggaisa tana bin Neehal da ido, Neehal ta tashi ta je ta kawo mata abinci da drinks. Mama dai kallon ta kawai take yi tana noticing ɗinta, ta lura da yanda take yin komai a sanyaye da kuma yanda jikinta ya d'ashe ta yi wani irin haske. Ta yi sarving Mama ta koma kusa da ita ta zauna tana ta yi mata hira. Can ta kalli Ameen ta turo baki ta ce. "Mamana ta zo shine baza ka ba mu guri mu yi sirri ba?" Harararta ya yi bai ce komai ba. Ta kwanta a jikin Mama tana ɓata fuska. Kafin Mama ta tafi ta shiga ɗaki dan yin fitsari, bayan ta yi fitsarin ta fito daga toilet sai ta kwanta akan gado, duk yanda ta so daurewa kar ta yi bacci amma ina baccin ya ce bai san wannan zancen ba, saboda rabon ta da yi tun safe, tana kitchen tana ta aiki. Mama ganin shida saura ta yi ta dubi Ameen ta ce. "Ina Neehal ɗin ne? Tafiya zan yi fa." Ya ce. "Tun yanzu?" Mama ta ce. "Tunda na zo na gan ku mai zan zauna yi kuma." Ya miƙe ya shiga ɗakin Neehal, mamaki ne ya kama shi ganin ta kwance tana baccinta hankali kwance. Ya juya ya fita ya ce wa Mama. "Kin ga Mum daga shigar ta har bacci ya ɗauke ta." Mama ta ce. "Bacci kuma?" Ya gyaɗa mata kai. Tashi Mama ta yi ta shiga ɗakin ta zauna a gefen Neehal, tafin hannunta ta kama ta dudduba sannan ta kalli Ameen dake tsaye a bakin ƙofa ta ce. "Wani abu yana damunta ne ko ta yi rashin lafiya?" Ameen ya ce. "Tana yin zazzaɓin dare dai, amma yanzu da sauƙi tana shan magani." Mama ta ce. "Kun je asibiti?" Ya ce. "Eh." Mama ta ce. "Me aka ce yana damunta?" Ya shafa gashin kansa tare da yin ƙasa da kansa ya ce. "She is pregnant." Mama ta mayar da kallon ta ga Neehal cikin tsananin farin ciki ta shafi fuskarta ta ce. "Allah ya sauke ki lafiya Daughter, ya baku lafiya ke da unborn." Can ƙasan mak'oshi Ameen ya amsa da Amin. Dama Mama tun zuwansu Gombe data ga yanayin Neehal ɗin ta fuskanta. Ta miƙe ta fita Ameen ya bi bayanta dan yi mata rakiya, suna tafe tana ƙara faɗa masa yanda zai kula da Neehal da abubuwan da zata yi da wanda baza ta yi ba, tana kuma tambayar sa abubuwan da Neehal ɗin take yi. Sai daf da Magriba Neehal ta tashi, ta dinga yiwa Ameen mita akan ƙin tashinta da ya yi da Mama zata tafi, shi dai bai ce mata komai ba har ta gaji ta haqura, kiran Maman ta yi ta ji ya ta koma gida, Mama ta sanar mata lafiya ƙalau, sannan ta faffaɗa mata addu'oin da zata dinga yi a matsayinta na mai juna biyu, cikin jin kunya take amsa mata. Suna gama wayar ta juyo zata yiwa Ameen complain ya yi saurin cewa. "Bani na faɗa mata ba, ita ta gane da kanta, ai dama na faɗa miki." Ta yi murmushi kawai a ranta tana hasaso irin farin cikin da Mama ta yi da ta ji labarin cikin. Bata ƙara nutsewa da jin kunya ba sai da Daddy ya kira ta ya yi mata ya jiki, dan ta san definitely Mama ta sanar masa da batun cikin jikinta.












A ɓangaren Hafsah kuwa kamar yadda Dad ɗinta ya faɗa a ranar ta bi Aunty Jamila zuwa gidanta tana gunjin kuka. Saboda kuka da damuwar data saka kanta a ciki har jinyar kwana biyu ta kwanta. Bayan ta warware Aunty Jamila ta fara koyar da ita abubuwa kamar yadda Dad ya buƙata daga gare ta, da farko bata mayar da hankali akan abubuwan ba sai dai ta zauna ta yi ta koke_koke da tunane_tunane. Daga baya cikin dabara Aunty Jamila ta ce mata idan bata gyara dabi'unta ta koyi zaman rayuwar duniya ba babu ta yanda za'a yi Ameen ya mayar da ita, sannan ta fara mayar da hankali. Ta kan addini Aunty Jamila ta fara yi mata dan sai ya gyaru sauran abubuwan za su gyaru. Wata yarinya ƴar mak'otansu Aunty Jamila ta ɗauko take yiwa Hafsan karatun addini, za su yi ƙarin Alqur'ani da sauran littatafai. Ita kuma Aunty Jamila sai ta ƙara mata da bayanin wasu abubuwan akan addinin. Sannan kuma idan zata yi girki tare suke yi, dan Hafsan tana gani tana koya. A hankali Hafsah ta fara sakin jikinta zaman gidan Aunty Jamila ya fara yi mata daɗi, ta kuma mayar da hankali akan karatun da ake yi mata. Sai dai fa kullum da tunanin Ameen take kwana take tashi a ranta. Lokuta da dama tana zama tay ta tunanin zaman Auransu, babu shakka ita akaran kanta ta san Ameen ya yi haquri da ita, a kodayaushe idan ta yi masa laifi uzuri yake mata ya dinga nusar da ita aibun abun da ta yi masa, sannan yana iyakar ƙoƙarinsa wajen ganin ta gyara addinta ta ko yi ilimin addinin, ta kan tuna lokacin data zubar masa da ciki, da farko fushi ya yi mai tsananin gaske da ita, daga baya kuma ya koma yi mata nasiha da nuna mata girman lefin da ta aikata ga Ubangiji. A lokacin gani take kamar rashin wayewa ne yasa ya kasa fuskantar abun da take nufi na ta yi ƙanƙanta da fara tara ƴaƴa a yanzu, sai yanzu da ilimi ya fara ratsa ta sannan ta gane ashe ita ce mara wayewar da kuma tarin duhun jahilci a kanta. Ranar suna zaune lokacin an yi wata biyu da sakinta take bawa Aunty Jamila labarin magungunan da Aunty Safiyya ta dinga kawo mata a matsayin su ne za su janyo da hankalin Ameen gare ta. Aunty Jamila ta yi salati ta ce. "Yanzu ita Safiyya an girma ma amma bata bar halin yarinta ba na bin Malam tsibbu? To Allah ya shirya ta yasa ta gane gaskiya. Ita kuma Yaya tana kallo bata yi magana ba?" Hafsah ta ce. "Bata ce komai ba." Aunty Jamila ta ce. "Dama ita Yaya haka take, duk abun da zaka yi bata k'wabar ka, na dai-dai ko na rashin daidai. Ke kuma wannan ya ishe ki izna, ki gane komai na Allah ne, ɓata wayonki da kika yi kika bi ɓata shi yasa Ubangiji ya barku da halinku, da a ce Sallah kika dage da ita da addu'a kamar yadda kika dage da yin amfani da magungunan nan da watak'ila al'amarin bai kai har haka ba, amma da kika kasa tsayar da Allah a al'amarinki kin ga illar hakan ai, tunda maganin bai yi aikin komai ba. Mutane su yi ta asarar kuɗaɗen su saboda jahilci suna zuwa gurin wani mutum ɗan'uwansu wai da sunan shi zai biya musu buƙata, ya baku maganin k'arya da wofi ya ci kuɗinku a banza, ga kuma tarin zunubi a gurin Ubangiji, dan shirka ba ƙaramar masifa ba ce, Allah ya raba mu da ita." Hafsah ta gyaɗa kai ta ce. "Amin Aunty na gode da tunatarwarki a gare ni. Amma Aunty kullum sai na saka ran ganin Ameen, ko ya turo wani nasa, ko ya kira ni amma shiru har na kusa gama iddata." Cikin tausayinta Aunty Jamila ta ce. "Ki ƙara haquri Hafsah kin ji, komai rubutacce ne a gurin Ubangiji, ki fawwala masa komai, idan ya nufa akwai sauran zamanku da Ameen a gaba sai ki ga kin koma, idan kuwa iya zaman kenan sai ki yi haquri, Allah ya kawo miki wani na gari." Gyaɗa mata kai Hafsah ta yi a hankali jikinta duk ya yi sanyi akan Ameen, ta san tunda ya samu mace kamar Neehal zai yi wahala ya ƙara waiwayar ta a cikin rayuwarsa..........✍️










*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_












*9️⃣0️⃣*










*ELEGANT ONLINE WRITER'S*








```I DEDICATED ALL THIS NOBEL TO MY LOVELY MOTHER, ONE IN THE BILLIONS, ONE LIKE NO OTHER, SUPER WOMAN, *HAJIYA FATIMA KUMURYA* ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA MAI AMFANI, AMEEN.```












*SPECIAL THANKS TO*


*Abubakar Ak saraki,*
*Muhammad Kareem,*
*Mu'az,*
*S deen and*
*Yareema.*
*Mutanen kirki kenan wanda basa gajiyawa da yin share, Allah ya saka muku da Alkhairinsa.*














.........Rayuwa na tafiyarwa su Neehal yadda ya kamata cikin kwanciyar hankali da farinciki. Sosai Ameen yake k'aunar cikin jikinta tun kafin ya fito duniya, da daddare idan sun kwanta haka zai ta shafa cikin yana magana shi kaɗai, wai magana yake yi da ɗansa, wataran har ta yi bacci ta bar shi yana ta faman latsa mata ciki, da safe ma haka yana tashi zai ɗora daga inda ya tsaya wai gaisawa suke yi. Ita dai sai dai tay ta yi masa dariya, in ta gaji kuma ta ture hannunsa daga jikinta. Cikin Neehal ya shiga wata na uku lokacin farkon azumin watan Ramadan Haneefah ta haifi ƴarta mace mai kama da ita sak. Murna gurin Neehal ko ita ta haihu sai haka, ranar da ta je Barka daƙyar take bari a ɗauki yarinyar, tana hannunta ta rungume ta sai kallon ta take. Mommyn Haneefah ta yi ta mata dariya tana cewa in da rai ita ma kamar yau ne zata haifa, da yake gida aka mayar da Haneefan. Duk da azumi ne kuma ga laulayin da take fama da shi amma zuwanta uku kafin ranar suna. Ranar suna yarinya ta ci sunan Mommyn Haneefah Maryam, Haneefah ta ce Neehal za'ana ce mata. Neehal ta ji daɗin wannan karar da Haneefah ta yi mata sosai, kayan barka sosai Ameen ya siyawa takwararsu da ita kanta Haneefan, ita ma Neehal ta ƙara da nata kayan. Ba'a yi taron suna ba kasancewar azumi ne.








Wataranar Laraba Neehal tana kitchen tana girki da yamma ta ji ana knocking ɗin ƙofar parlour. Ta goge hannunta ta fito ta nufi ƙofar, lokacin cikinta ya fito ɗan wata shida, ya yi mata das a jikinta abun sha'awa, yanzu an bar laulayi. Sai da ta tambayi waye? Sannan ta buɗe ƙofar. Ɗaya cikin yaran gidan ne masu bawa flowers ruwa da yi mata aike. Bayan ya gaishe ta ya ce. "Hajiya wasu baƙi ne suka zo wai suna san ganin ki." Neehal ta ce. "Baƙi kuma? Maza ko Mata?" Ya ce. "Maza ne dattijai haka kamar almajirai." Neehal ta ce. "Kuma suka ce Ni suke son gani?" Ya ce. "Eh, dan sun ce daga can gidan Hajiya babba (Mama) aka turo su." Neehal ta ce. "Okay ka ce su shigo." Ta juya ta koma ba tare da rufe ƙofar ba a ranta tana Mamakin baƙin da aka ce ta yi, ɗakinta ta shiga ta ɗauko hijabi ta zira akan doguwar rigar abayar dake jikinta. Ta duba time ta ga biyar ta wuce lokacin dawowar Ameen gida ya kusa. Jin ƙarar turo ƙofa yasa ta fita parlour'n. Maza ta gani su biyu kamar yadda yaron gidan ya ce mata dattijai ne kuma kamar almajiran, tabbas ta san fuskokinsu amma ta kasa tuno inda ta san sun. A kan Carpet ta zauna tana bin su da kallo, su kuma sai aikin kalle_kalle suke a parlour'n suna baza ido a lungu da sak'o na cikinsa. Cikin girmamawa ta ce musu. "Sannunku da zuwa." Suka amsa da "Yawwa." Tare da dawo da kallon su gare ta. Ta ce. "Ina yininku?" Suka amsa mata sannan ɗaya daga cikinsu ya gyara zama ya ce. "Ikon Allah, Neehal ke ce kika zama haka? Girman ɗan Mutum babu wahala." Ta yi murmushi kawai. Ya cigaba da magana cikin sanyin murya. "Ga dukkan alamu baki shaida mu ba, amma hakan ba'abun mamaki ba ne bisa ga yadda muka wofintar da rayuwarki duk da kasancewar muna gari guda dake, Neehal Salisu ne da kuma Sani ƴaƴan Baffa mariki'n mahaifanki." Da mugun mamaki Neehal ta ɗago tana kallon su tare da tambayar kanta abun da ya hana ta gane su. Zuciyarta ta bata amsa da cewa 'Tsufan da suka yi mana' wanda ya wuce yawan shekarunsu a duniya, kuma ta manta rabon da ta gan su a, duk da Kawu Musa ya ce sun zo bikinta, amma da yake cikin hada_hada ake bata gan su ba. Cikin tsananin mamaki ta ce. "Kawu Sani da Kawu Salisu?" Kawu Sani ya gyaɗa mata kai. Ruwan hawaye fal cikin idonsa ya ce. "Mu ne Neehal, abun ya baki mamaki ko? Na ganinmu da kika yi a gidanki, mun zo ne mu roqe ki gafara akan abun da muka yi miki ko ma samu sassaucin k'uncin rayuwar da muka shiga, mahaifinki ya riqe mu tamkar ƴan'uwansa da suke ciki ɗaya a lokacin da yana raye haka ma mahaifiyarki, mahaifinki shine komai namu, ya yi mana komai a rayuwar nan, amma saboda butulci da wani tunanin banza da wofi muka wofantar dake ƴarsa ƙwaya ɗaya tal a duniya, muka yarda zumunci muka kasa riqe ki saboda muna gudun wahalar d'awainiya dake. Amma da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne sai gashi Allah ya ɗaukaka ki, mu kuma ya bar mu da iyawar mu, dan Allah Neehal ki yafe mana, wallahi muna cikin tsananin k'uncin rayuwa. Abun da zamu kai bakinmu ma gagarar mu yake, karayar arzik'i Ubangiji ya ɗoro mana lokaci ɗaya, hatta da muhallin da muke rayuwa a cikinsa ba mu tsira da shi ba, yanzu a wani rubab'b'en gidan haya muke tare da iyalanmu, shi ma wani bawan Allah ne ya ji k'an mu ya biya mana kuɗin shekara ɗaya....." Sai ya fashe da kuka.








Neehal Sarkin kuka har ta fara hawaye, ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Kawu ni ba ku yi mun komai ba dama, ko kun mun na yafe muku." Kawu Salisu yana matsar ƙwalla ya ce. "Kayya Neehal, ba iya wannan ne cutar da muka yi miki ba, Mahaifinki kafin ya rasu ya ranta mana wasu kuɗaɗe masu kauri da muka buƙata daga gare shi dan mu ƙara jarinmu, amma bayan rasuwarsa saboda son zuciya irin tamu muka ƙi kawo kuɗin a haɗa a raba muku haqqinku ku iyalansa, muka riqe saboda mun san ba mu da gadonsa, muna baƙin cikin a ce ba mu ci komai ba daga cikin dukiyarsa. Dan Allah ki yafe mana Neehal ko za mu samu sassauci a gurin Ubangiji bayan mutuwar mu." Neehal ta ce. "Na yafe muku Kawu, dan Allah ku bar waɗan nan maganganun komai ya wuce." Bata jira cewar su ba ta miƙe ta kawo musu drinks masu sanyi, ai ko bi takan cups ɗin data kawo ta ajiye musu ba su yi ba suka buɗe robar suka shiga kuk'k'uta. Kitchen ta koma ta ƙarasa girkin da take, ta zubo musu a cikin tire ta kawo musu. Shi ma ba su bi takan spoons ba suka saka hannu duk da tururin da abincin yake suka shiga zabga lauma, kana ganinsu ka ga wanda suke tattare da yunwa. Cikin mintunan da ba su fi biyar ba suka share abincin, suka fara sakin gyatsa. Neehal dai kallon su kawai take cike da tausayawa. Suna wanke hannu suka miƙe za su tafi suna zabga mata godiya, ɗakinta ta shiga ta tattaro duka kuɗin dake hannunta ta fito ta miƙa musu ta ce. "Kawu ga wannan a yi cefene, ku yi haquri bani da enough cash ɗin kuɗi a hannuna, amma insha Allahu cikin week ɗin nan zan zo har gida, sai ku bani address ɗin gidan." Ai kamar za su yi mata sujjada saboda murna da godiya, ita abun ma kunya ya bata. Sai da suka bata address ɗin sannan suka tafi. Tattare kayan gurin ta yi ta kai kitchen jikinta a sanyaye, ta dawo ta gyara gurin ta ƙara fesa room freshener a ɗakin. Hijabin jikinta ta cire ta zauna akan kujera ta fara tunanin rayuwa da yanda al'amuran cikinta suke wakana. Ta tuna su Kawu Salisu a da sanin data yi musu ƴan gayu ne masu ji da kansu, amma ƙarshe ga yanda Ubangiji ya yi da su, ba su da maraba da almajirai gashi duk sun tsofe. Ta tuna Uncle Umar da yanda shi ma rayuwa ta juya masa baya, ga ƴarsa Iman ta haifa masa ɗan gaba da Fatiha, Aunty Fauziyya kuwa ta koma kamar zautacciya saboda tension ɗin rayuwar da take ciki. Ta nuna a baya yanda duk suke jin daɗin rayuwarsu suke yin abun da suka ga dama, a lokacin ba sa tunanin akwai lokacin da zai zo da zasu girbi ABIN DA SUKA SHUKA, shi yasa aka ce a rayuwa ka yi mai kyau sai ka ga mai kyau a gaba. Allah yasa mu dace, Amin.












A haka Ameen ya dawo ya same ta. Ta ɗaga kai a hankali ta kalle shi tare da amsa masa sallamarsa. Ajiye kayan hannunsa ya yi ya tsaya yana murmushi, ta gane mai yake nufi amma sai ta kasa motsawa balle ta tashi ta yi masa abun da yake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login