Showing 114001 words to 117000 words out of 262509 words

Chapter 39 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21482

Mama a gurin Ummi na kira ta, dan nasan in ma ba lafiya zata sanar mun, amma jin bata ce mun akwai matsalar komai ba sai hankalina ya ɗan kwanta, amma kewarki gaba-d'aya ta hana ni sukuni. Kwana ukun nan da ban ji muryarki ba gaba-ɗaya bana cikin nutsuwata, yau dai na kasa jurewa na ce sai na zo na gan ki." Ta lumshe idonta cikin sanyin murya ta ce "Nima na yi kewar ka Uncle." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai. Ya ce "To me yasa kika daina ɗaukar kira na." Ta buɗe idonta tana kallon fuskarsa ta ce "Babu komai fa Uncle ka yarda da ni." Ya ce "Uhm, salon ki tayar mun da hankali ne kawai ko?" Ta ce "A'a, i'm sorry ba zan kuma ba." Ya ce "Shikenan Princess." Ta ce "Ina yarana, me yasa baka zo mun da su ba?" Ya ce "Bari na yi sai next week idan sun yi hutun school sai na kawo miki su." Ta ce "Allah ya kai mu, Ya su Ummi?" Ya ce "Duk suna nan lafiya lau." Hira suka sha sosai yau, dan ita kanta sai yanzu ta tabbatar ta yi kewarsa ba kaɗan ba. Anan ya yi Sallar Magriba, yau kam ya ci abinci kaɗan a gidan saboda gudun ɓacin ran Princess ɗin tasa. Sai kusan isha'i ya tafi zuciyarsa cike da nishad'i, saɓanin kwana biyun da suka wuce wanda ya yi su cikin damuwa. Itama Neehal anata ɓangaren cike take da farincikin kasancewa da Uncle ɗin nata a yau. Bayan ya koma gidan Mamy tai ta tsokanarsa tana faɗin "Ai fa yanzu dole yay ta musu zarya a Kano tunda zuciyarsa tana nan." Murmushi kawai yake mata baya cewa komai.








Bayan Sallar isha'i Mama tana falon sama tana kallo wayarta dake hannun kujerar da take kai a zaune ta fara ringing. Ta ɗauko ta duba tare da d'agawa ganin Aunty A'isha ce ke kiran. Ba tare da gaisuwa ba Aunty A'isha ta ce "Adda Fateemah! Yanzu Mai_gidan su Abban Neehal ya kira ni ya sanar mun cewar an samu nasarar kama mutanen da suka kashe Abban Neehal ɗin da Ummanta........✍️
















*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*4️⃣8️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*








```Ku yi haquri da rashin ganin update akan lokaci, kun san an ce idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi.```














..........Cikin hanzari mai nuni da tsantsar mamaki Mama ta tari numfashin Aunty A'isha da faɗin. "Da gaske A'isha?" Aunty A'isha ta ce "Dagaske mana Adda, shi Alhaji Alin ne tun bayan rasuwar su Abban Neehal ba jimawa ya kamu da rashin lafiya, aka fitar da shi Saudiyya ake masa magani. Ashe duk wannan shekarun da suka wuce abun yana ransa, sai a ƴan watannin da suka wuce ya samu lafiya ya dawo Nigeria. Shine yana dawowa yasa aka duk'ufa da binkicen waɗanda suka yi kisan a lokacin da ya samu labarin har yanzu ba'a gano su ba. Yanzun nan shi ya kira ni da kansa muna gama waya da shi na kira ki, ya sanar mun cewa tunda ya dawo ƙasar nan yake neman mu, amma bai samu labarin inda muke ba, sai daga baya tunanin ya je gadon ƙaya inda muka zauna ya zo masa, to a wurin wata mak'ociyarmu aka samo masa Number ta." Mama ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Alhamdulillah, Allah mun gode maka, yanzu ya ake ciki game da waɗanda suka yi kisan? Ya sanar miki ko su waye suka yi?" Aunty A'isha ta ce "A'a bai sanar mun ba, ya dai ce mun suna hannun Police a halin yanzu, ranar Monday za'a shiga kotu a yanke musu hukunci tunda sun amsa laifunsu, sauran bayani kuma ya ce sai mun haɗu." Mama ta ce "Ki ji wani ikon Allah A'isha, shekara fiye da goma sai yanzu Allah ya toni asirinsu, Allah ya ƙara tona asirin duk wasu masu laifi a cikin duniyar nan." Aunty A'isha ta ce "Ameen ya Allah, wallahi adda ba ki ji yanda na ji daɗi ba, Alhaji Ali ya cika ubangida na gari da ya tsaya tsayin daka ganin jininsu Abban Neehal bai tafi a banza ba." Mama ta ce "Allah ya saka masa da Alkhairi ya biya shi da gidan Aljannah." Aunty A'isha ta ce"Amin ya Allah, ya ce akai masa Neehal yana son ya gan ta." Mama ta ce "Aiko bai faɗa ba dole mu je har gida mu yi masa godiyar wannan jajircewar da ya yi, gobe gobe ma Insha Allahu za mu je, a wacce unguwa yake da zama?" Aunty A'isha ta ce "A rijiyar zaki, ya turo mun da address ɗin gidansa ta message." Mama ta ce "To Insha Allahu da safe za mu je, bari in je in sanar da Daddy wannan abun al'ajabi da farincikin." Aunty A'isha ta ce "Tom shikenan da safen zan biyo ta nan sai mu wuce, nima bari in je in sanar da Abban Maryam, in kira Sadiya itama in sanar mata." Mama ta ce "Allah ya kai mu goben, sai mun yi waya." Daga haka suka yi sallama.






Mama ta dafe kanta tana sauke numfashi, zuciyarta cike da d'oki da zumud'in jin asalin zancen, domin ta san wa ya kashe su Abba ko kuma wa ya turo a kashe su, da kuma son sanin ko mutum ɗaya ne ya yi kisan su Abba da su Anwar? A ɓangaren Aunty A'isha itama tunanin da take yi kenan. miƙewa Mama ta yi ta nufi part ɗin Daddy cikin sauri dan ta sanar masa halin da ake ciki.










Cike da mamaki da kaɗuwa Daddy yake duban Mama bayan ta gama sanar masa da abun da yake faruwa. Zuwa can ya nisa ya ce "Allah buwayi gagara misali, dama an ce duk wanda yay kisan kai da wuya ya mutu Ubangiji bai toni asirinsa ba, saboda haqqin rai ba ya taɓa barin mutum ya zauna lafiya a duniya." Mama ta ce "Wannan haka yake, Allah ka raba mu da mummunar ƙaddarar da zata kai mu ga dana sani, su kuma azzaluman mutane irin waɗannan Allah ka cigaba da tona musu asiri!" Daddy ya ce "Amin Amin Doctor." Mama ta cigaba da magana. "Mutum bai ji ba bai gani ba kawai saboda rashin imani a zo har cikin gidansa a kashe shi saboda neman duniyar da kowa sai ya bar ta, mutane ba sa tuna Allah a ransu, ba sa tunanin inda suka kashe mutum ya je suma komai daren dad'ewa za su je." Cikin jimantawa Daddy ya ce "Ai ke dai ki bar mutum kawai Doctor, amma in dai duniya ce gata nan ta ishi kowa, kuma Duk *abin da mutum ya shuka* dai *shi zai girba* , walau na sharri ko na Alkhairi." Sun zanta akan al'amarin sosai sannan Mama ta miƙe dan zuwa ta sanar da Neehal itama.










Tana kwance ruf da ciki akan gadonta, system ɗinta na gabanta tana latsa ta cikin kwarewa, idanunta sanye da siririn glass mai ɗan duhu, wanda bata fiya amfani da shi ba, sai irin wannan lokacin idan zata yi using system. Mama ta shigo ɗakin tare da zama a bakin gadon bayan ta yi sallama. Neehal ta amsa mata tare da tashi zaune ta cire glass ɗin fuskarta ta ajiye a gefen ta. Mama ta ce "Aikin ne har yanzu baki gama ba." Ta ce "Na kusa ƙarasawa saura kaɗan, zuwan Uncle Ahmad ne ma ya tsayar da ni." Jinjina kai Mama ta yi tare da juyowa ta fuskance ta sosai ta ce "D'azu Auntinki ta kira ni take sanar mun an kama waɗanda suka kashe su Ummanki." Neehal ta waro Ido waje cikin kaɗuwa ta ce "Su waye Mama?" Mama ta kwashe duk yanda suka yi da Aunty A'isha ta sanar mata. Kuka ta saka cikin kukan take faɗin "Mama me su Umma suka musu da suka kashe su? Su waye waɗannan mutanen da suka raba ni da mahaifana rabuwa ta har abada a rana ɗaya? Me nay musu suka zaɓi mayar da ni marainiya?" Kuka take sosai mai ban tausayi, mutuwar su Umma ta dawo mata sabuwa fil a cikin ranta, duk da a lokacin da suka rasu tana ƙarama amma har yanzu gawar iyayenta kwance cikin jini bata daina hango ta acikin idanunta ba, kuma har ta koma ga mahaliccinta ba zata taɓa mantawa ba. Mama ta rungume ta a jikinta cikin tsananin tausayinta, tare da rarrashinta da kalamai masu taushi har ta samu ta bar kukan. Mama ta d'ago ta tana share mata hawaye ta ce "Komai rubutacce ne daga Allah, Ubangiji ya riga ya tsara rana ɗaya Umma da Abba za su rasu kuma a lokaci ɗaya, ko da waɗan can Mutanen ba su kashe su ba idan kwanan su ya ƙare dole su bar duniya. Dan haka addu'ar mu kawai suke buƙata a halin yanzu, ita ce kawai soyayyar da za mu nuna musu. Mutuwa dole ce Neehal, mu ma nan zaman jiranta muke, fatanmu Allah yasa ta zo mana cikin sauqi." Cikin matuƙar sanyin jiki Neehal ta ce "Haka ne Mama, Allah ya ji k'an Umma da Abba da ma dukkan musulmin da suka riga mu gidan gaskiya, mu kuma Allah yasa mu cika da imani." Mama ta ce "Ameen dan darajar Annabi." Lumshe idonta ta yi bata kuma cewa komai ba, cikin zuciyarta kuwa ji take dama a bata dama ta kashe azzaluman mutanen da suka kashe mata iyaye da hannunta, saboda wata muguwar tsanar su data cika mata zuciya. A hankali ta yi baya ta kwanta akan gadon saboda sarawar da ta ji kanta ya yi mata lokaci ɗaya. Mama ta janyo system ɗin da take amfani da ita ta yi saved na aikin da take sannan ta kashe ta, ta ɗora ta akan bedside locker. Shafa fuskar Neehal ta yi cikin raunin zuciya da tausayinta, cikin kulawa ta ce "Ki yi addu'a idan kina jin zuciyarki babu daɗi ba wai ki yi kuka ba, idan kin kasa barci kar ki kwanta ki yi ta tunane_tunane, ki tashi ki kaiwa Allah Kukanki." Ta gyaɗa mata kai ba tare data buɗe idonta ba. Mama ta kashe mata light ɗin ɗakin sannan ta fice zuciyarta babu daɗi. Iyayenka ko da ace baka san su ba kana jariri suka rasu idan ka girma aka baka labarinsu dole ka ji feeling a kansu da son kasance tare da su, balle ita da tana da ɗan wayonta suka rasu, dole abun ya dinga taɓa mata zuciya. Kuma da a ce mutuwa suka yi kamar kowa ba kashe su a kay ba, abun ba zai dinga damun ta over ba. Amma yanzu gani zata dinga yi kamar da ba'a kashe su ba da suna raye har yanzu....










Washegari kafin ƙarfe goma sha ɗaya na safe sun gama shiryawa dan zuwa gidan Alhaji Ali, Neehal dai kamar mai cuta komai a sanyaye take yin sa. Daren jiya kam ko wayar love ɗin data saba bata iya yi ba, da ta tashi da safen nan ma ko bi takan wayar bata yi ba. Sai da Mama ta ce mata ta kira gurin aikinsu ta sanar musu ba zata samu damar zuwa yau ba sannan ta ɗauki wayar. A time ɗin ne ta ga missed call ɗin Sadik, Ahmad har ma da Ameen wanda kiran nasa ya bata mamaki. Ahmad kam har da text yay mata ya sanar mata ya wuce Abuja, dama tun jiya ya faɗa mata da sammako zai yi ya koma. Bata bi kiran ko ɗaya daga cikinsu ba saboda tana cikin mood ɗin da ko doguwar magana bata son yi.










A lokacin itama Aunty A'isha ta ƙaraso gidan, bayan sun gaggaisa suka rankaya suka tafi a Motar Mama wanda direban Maman ne zai kai su. Suna tafe suna ƙara jimanta al'amarin a tsakanin su. Neehal dai ta yi shiru kawai tana sauran su. Aunty A'isha ta dube ta, ta ce "Daughter baki da lafiya ne?" Mama ce ta bata amsa da faɗin "Tun jiya dana faɗa mata zancen nan shine duk ta koma haka." Aunty A'isha da itama dauriya kawai take dan mutuwar tsohon Mijin nata da abokiyar zamanta ta dawo mata sabuwa a ranta. Ta kwantar da kan Neehal a ƙafaɗarta bata ce komai ba. Mama ta ce "Na kira Hajiya na faɗa mata, ta ce zata zo kafin Monday a yi zaman kotu da ita." Aunty A'isha ta ce "Allah ya kai mu, ya kuma sa a ƙarƙare shari'ar a ranar, kin san shari'ar ƙasar nan tsaf zasu iya cewa sun d'age shari'ar." Mama ta ce "Ai tunda waɗanda suka yi laifi sun amsa babu buƙatar wani jan magana na daban, hukunci kawai za'a yanke musu dai_dai da abun da suka aikata." Aunty A'isha ta ce "Haka muke fata dama." Bayan sun ƙarasa gidan Alh Ali Aunty A'isha ta kira shi ta sanar masa, ɗaya daga cikin ma'aikatan gidansa ya aiko ya shigar da su. A wani babban falo aka sauke su, dattijuwar matarsa ta karɓe su hannu bibbiyu dan ta san da zuwan nasu. Alh.Ali ya yi mata bayanin komai. Kuma ta shaida fuskar Aunty A'isha dan kafin Abba ya rasu suna ɗan zuwa tsohon gidansu idan abu ya samu. Tana ganin Neehal ta ce "Wannan yarinya kamar an tsaga kara ita da mahaifiyarta." Da kanta ta musu jagora har falon Alhaji Ali. Yana zaune shi kaɗai a falon yana kallon labarai suka yi sallama, ya amsa musu cikin sakin fuska. Suka ƙarasa suka zauna matar tasa ta ce "Ga iyalan Alh.Muhammad sun ƙaraso." ya yi murmushi yana duban Neehal ya ce "Masha Allah, wannan ce Amaryar tawa?" Suka yi murmushi dukan su, Neehal ta ƙarasa ta tsugunna a gabansa ta gaishe shi. Ya amsa mata cikin fara'a da kulawa, su Mama ma suka gaishe shi, ya amsa musu. Aunty A'isha ta ce "Ya jiki kuma Alhaji? Ashe cuta ka sha Wlh ba mu da labari." Ya nuna ƙafarsa ya ce "Ciwon Ƙafa ne ya sako ni a gaba, na fi shekara biyar a zaune bata takuwa, kuma tunda muka je Saudiyya ake ta maganin, sai yanzu Ubangiji ya kawo sauqi." Mama ta ce "Subhallahi, Lallai kasha jinya Alhaji, Allah Ubangiji ya ƙara sauƙi yasa kaffara ne." Suka amsa da "Ameen." Ya dubi Aunty A'isha ya ce "Ya ƙarin haquri rashin su Alhaji Muhammad, tun bayan rasuwar su ba mu ƙara haɗuwa ba, na samu labarin ma kin yi aure." Aunty A'isha "Haquri Alhamdulillah, ai tun bayan dana gama takaba na yi aure." Ya ce "Masha Allah, Allah ya raya zuri'a ya ƙara haqurin zama da juna. Su kuma Alh. Muhammad Ubangiji Allah ya ji k'ansu ya gafarta musu." Suka amsa da Ameen gaba_ɗaya. Daga nan suka shiga tattaunawa akan abun da ya kawo su. Inda Alhaji Ali ya sanar musu da cewa. "Bayan ya dawo daga Saudiyya ne ya bibiyi al'amarin, inda aka tabbatar masa har yanzu ba a gano wand'anda suka yi kisan ba, hankalinsa ya tashi ya dinga faɗa akan rashin tsaurarara bincike na ƙasar nan da ba'ayi, sannan ya saka lauyoyi da jami'an tsaro su binkito masa. To ana cikin haka ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kisan su Abba ya fito daga gidan yari bayan shekaru takwas daya shafe a gidan yarin, bisa laifin fashi da makami da aka kama shi da shi, dama irin ƴan daban nanne da masu kuɗi da ƴan siyasa suke amfani da su dan cimma wata buƙata ta su, daga zarar buƙatar tasu ta biya kuma da su da banza duk ɗaya ne a gurinsu. Bayan ya fito ya nemi wanda sukay kisan su Abban tare wanda shine yakasance kamar babbansu a jan ragamar aikin, ya buk'aci daya ba shi cikon kuɗin aikinsa, shi kuma wancan ɗin sai ya hana shi ya ce ya cinye. To saboda baƙin cikin cinye masa kuɗin da aka yi shine ya ɗauki alwashin sai ya tona musu asiri in ya so kowa ya rasa duk a kama su. Da kansa ya kai kansa Police station ya faɗi laifinsa, aka kuwa yi ram da shi nan take, sannan ya faɗi inda sauran biyun suke su ma aka je aka kamo su. Da farko su sun musa, amma da suka ji duka sai suka fadi gaskiya, suka ce tabbas su sukai kisan amma su ma wani mutum ne ya ba su kwangilar yin kisan. Yanzu haka suna Bamfai a tsare, Ranar Monday Insha Allahu za'a yi shari'ar a babbar kotun jiha, dan yanke musu hukunci dai_dai da abun da suka aikata. Sai dai har yanzu sun ƙi faɗar wanda ya saka su aikin, dan su yaran biyun dama ba su san shi ba, babban nasu ne ya san shi. Amma ana saka rai Insha Allah za su faɗi koma waye a zaman kotu, lauyoyinmu suna ta faɗi tashi akan haka. Na samu duk wannan bayanan ne ta bakin amintaccen lauyana wanda shi ne lauyan da zai tsaya a gaban kotu a matsayin lauyan iyalan Alhaji Muhammad Gabasawa dan ganin kotu ta bi musu hak'k'in su." Sai bayan Azhar su Neehal suka baro gidan nasa zuciyoyinsu cike da al'ajabi.








Ranar Asabar sai ga Hajiya ta zo Kano kamar yadda ta faɗa. Kwanakin nan da zazzaɓi mai zafi Neehal ta yi su, dan ko falo bata iya takowa ba tana kwance, ko toilet zata sai Mama ta taimaka mata. Ranar Monday ranar shiga kotu ta tashi jikin nata da ɗan dama, har ta yi wanka da kanta ta shirya. Daa Mama ta ce ta zauna a gida ba sai ta je court ɗin ba, amma ta ce zata iya zuwa ai ta ji k'warin jikin nata. Ƙarfe tara da ƴan'mintuna suka bar gidan gaba-ɗayansu har su Dije da Daddy zuwa court, dan ƙarfe goma za'a saurari ƙarar. Duk wannan abun da yake faruwa Ahmad da Sadik ba su sani ba dan Neehal bata sanar da su ba, tunda ko waya bata yi da ɗayan su ba saboda rashin lafiyar da take. Idan sun kira ta Mama ce take d'agawa. Sadik ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login