Showing 258001 words to 261000 words out of 262509 words
Chapter 87 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
jira. Ya ƙaraso inda take ya tsugunna a gabanta yana kallon fuskarta ya ce. "What happened Baby?" Ta lumshe idonta kawai bata ce komai ba. With so worry ya ce. "Oh My God, Baby me ya faru? Ko baki da lafiya ne?" Ya shiga tattab'a wuyanta da fuskarta. Girgiza masa kai kawai ta yi. Ya kama hannunta ya ce. "Please Baby tell me abun da ya faru, hankalina ya fara tashi da ganin yanayinki, ko wani abu ya faru da bana nan?" Ta buɗe idonta tana kallon fuskarsa, damuwa ta hango ƙarara a cikinta, sai ta ji tausayinsa ya cika mata zuciya, daga dawowarsa ta saka shi cikin damuwa, haka yake ko yaya ya ga ta ɗan canza yanzu zai rud'e ya yi ta tambayar ta abun da yake damun ta, in ya gan ta a cikin damuwa kuwa rasa inda zai saka kansa ya ji daɗi yake. Hannu ta kai ta fara shafa fuskarsa ta ce. "Babu komai fa Mijina, kewar ka ce kawai take damu na." Ya saki ajiyar zuciya a hankali yana kallon cikin idonta ya ce. "Kin tabbata? Dan Allah idan wani abu yana damun ki Baby ki faɗa mun." Ta ce. "Da gaske fa Dear babu komai." Ya shafi cikinta ya ce. "Sorry My Boy, da na ƙi kula welcoming ɗinka, rigarmar Mamanka ta saka, yau ka hana ta bacci ka rama mana, Daddy missed you too." Murmushi ta yi tana jin yanda yake shafa cikin nata a dukkan jikinta, ta shafi lallausar sumar kansa ta ce. "Dama can ai ba baccin ake bari na in yi ba." Ya ce. "Ban da sharri dai Baby." Sannan ya yi kissing cikin nata, lumshe idonta ta yi tana sauke numfashi. Ya miƙe ya koma kusa da ita ya zauna ya janyo ta jikinsa ya ce. "Baby! Akwai abun da yake damunki wallahi, dan Allah ki faɗa mun, ganin ki a haka yasa gaba-d'aya na rasa nutsuwata." Ta saka hannunta ta rungume shi sosai tana shaƙar ƙamshinsa tare da sakin ajiyar zuciya, tabbas akwai abun da yake damun ta, kuma ba komai ba ne face yanda ta ga su Kawu Sani da halin matsin rayuwar da suka ce mata suna ciki, amma bata san ta ina zata fara faɗa masa ba. Ta fara shafa kafaɗarsa da hannunta ɗaya ta ce. "Da gaske yaya babu komai, Just I'm not in the mood." Ya ce. "Sorry, bari na yi wanka sai mu fita, na san zaki jin daɗin hakan, ina kike son mu je? Gidan Mama ko gidan Aunty ko gidan Aunty Sadiya ko gidansu little Neehal ko gidan Kawu ko wani gurin daban?" Ta ce. "Gidan Mama, daga nan sai mu biya inga namesake ɗina sannan mu je mu sha ice-cream, Gobe sai mu je gidansu Auntyn." Ya shafi kuncinta ya ce. "An gama Gimbiya Sarautar Mata." Ta ce. "Sarautar Ameen dai." Ya ɗago ta ya ce. "Me kika ce?" Ta yi dariya kawai. Ya ce. "Ni ban taɓa jin kin faɗi sunana ba sai yau, ƙara faɗa mu ji ko kin iya." Kafaɗa ta mak'e masa. Ya ce. "Shikenan mu je in yi waka." Ya miƙar da ita sannan shi ma ya miƙe suka shiga ɗakinsa. Ta taimakonta ya cire kayan jikinsa, ya ɗaura towel a k'ugu Sannan ya fara ƙoƙarin cire mata abayar jikinta. Ta riƙe hannunsa tana ɓata fuska dan ta san me yake nufi ta ce. "Ni fa ban jima da yin wankana ba." Ya langwab'e kai ya ce. "Yanzu kuma taya ni zaki yi." Cikin shagwab'a ta ce. "Ai na san ba iya wankan zaka tsaya ba, sai ka saka ni jik'a gashina da yamman nan." Bai ce komai ba ya cire mata abayar, ya janyo ta jikinsa ya kai bakinsa saitin kunnenta ya ce. "To ai ke ce Baby kullum ƙara kyau kike da......." Saurin rufe masa baki ta yi dan ta san me zai ce. Murmusawa ya yi ya ɗauke ta cak ya nufi toilet da ita.......Suna hanyar zuwa gidan Mama ne take sanar masa da zuwan su Kawu Salisu, anan ya gane dalilin damuwartata. Washegari ya tambaye ta address ɗin su Kawu Salisu, ta faɗa masa ba tare da tunanin komai ba. Yana fita ya aika yaransa suka siyo kayan abinci masu yawa ya haɗa musu da kuɗi ya ba su address ɗin su Kawu Sani ya ce sukai musu, bai faɗa mata ba sai daga baya take jin labari wataran ta kai musu ziyara suke faɗa mata, su ma suka ce bai ce a ce in ji shi ba, yaran da suka kawo kayan ne suka kwatanta musu shi anan suka gane shi ne.
Haka rayuwa ta yi ta tafiya, kwanaki na shud'ewa. Mama ta yi nacin Ameen ya mayar da Hafsah amma ya ƙi, ya ce idan ya dawo da ita ya san ba zai yi adalci a tsakanin su da Neehal ba, dan haka gara bai kwasarwa kansa zunubi ba, dan shi a yanzu babu gurbin wata ƴa mace a cikin zuciyarsa, Neehal ta kanainaye ko ina, dama can tun fil azal ita ce a ciki, ya Auri Hafsat ne kawai saboda matsawar da Mama ta yi masa a time ɗin akan ya yi Aure. Ita ma Neehal ɗin tana yawan yi masa maganar ya mayar da Hafsat ɗin ɗakinta, amma duk sanda ta yi masa maganar basa kwashewa ta daɗi, dan fushi yake yi sosai ya ce dama ya san ba son sa take yi ba. Daƙyar take samu ta lallab'a shi ya sauko. Lokacin da cikin Neehal ya shiga wata tara idan mutum ya gan ta sai ya tausaya mata saboda girman cikin, ƙafafuwanta duk sun kumbubbura. Hana ta aikin komai Ameen ya yi, shi yake komai na gidan kafin ya fita, daga baya kuma Aunty A'isha ta turo musu Maryam ɗinta take taya ta zama da aikace_aikace. E.d.d ɗinta saura one week Mama ta je ta ɗauko ta, ta dawo da ita gida. Ameen bai so haka ba amma babu yadda zai yi, sai dai kusan raba dare yake a gidan kafin ya tafi, a hakan ma sai Mama ta kora shi. Neehal tay ta yi masa dariya. Zuwa wannan lokacin Hafsah ta tabbatar Ameen ba zai taɓa dawowa gare ta ba, ta yi kuka ta yi dana sani mara iyaka, daga baya ta haqura ba dan ta daina son shi ba, sai dai fa har a yanzu tsanar Neehal na nan a cikin ranta, musamman da take ganin kamar ita ce silar rabuwar su da Ameen. An yi bikin Hameedah da wani abokin aikinta mai Mata da yake nacin son ta, a da ta ƙi shi sai da taga bata da kowa sai shi sannan ta amince masa, Tunda Ameen ɗin da take nacin so baya ta ita. Neehal bata je bikin ba saboda time ɗin ta yi nauyi sosai. Matar Ahmad ma ta haifi ɗanta Namiji watanni uku da suka wuce, su Afrah an yi k'ani sai murna, yanzu ma kullum cikin murna suke Auntinsu ta kusa ƙara haifo musu new Baby........
Ranar wata Alhamis cikin dare Neehal ta fara jin ciwo a jikinta, kusan kwana uku kenan tana jin jikin nata babu daɗi, amma ciwon na yau ya fi na kullum. Tun tana yi tana daurewa har ta fara nurk'ususu tare da salati, Mama take Sallah ta sallame ta yi kanta. Ganin Haihuwa ce ta kira Daddy a waya ta sanar masa, cikin hanzari ya baro part ɗinsa suka ɗauke ta da su kai asibiti da ita bayan Mama ta ɗauki duk abun da ake buƙata, Asibitin Nasarawa suka je inda Maman take aiki, dama a can take yin awu. Haka kawai Ameen ya ji ya kasa bacci a daren ranar, sai tashi ya yi ya yo alwala ya shiga yin Sallah. Mama da kanta ta karb'i haihuwar Neehal, sai kusan asuba Allah ya sauke ta lafiya ta santalo Ƴaƴanta Maza guda biyu masu tsananin kama da mahaifinsu. Ba tare an goge musu jiki ba Mama ta rungume su idonta cike da ƙwallar farinciki, sannan ta ɗorawa Neehal su duka akan cinyarta. Neehal tana kallon su ta ji gaba-d'aya zafin wahalar labour da ta sha ta gushe daga cikin zuciyarta, wata zazzafar k'aunar yaran ta maye gurbin su. Mama ta lek'a ta faɗawa Daddy ta ce ya kira Ameen ya sanar masa. Kiran sa Daddy ya yi ya ce masa ya zo suna asibiti Neehal ta haihu, ba tare da ya faɗa masa abun da ta haifa ba. Ga mamakin Ameen sai ya ji hankalinsa ya tashi, mukullin Motor kawai ya ɗauka ya fice cikin sauri. Sam zuciyarsa bata ta Babyn da ka haifa tana ga Neehal, so yake kawai ya gan ta ya ga halin data ciki, ya ga lafiyar jikinta.
Neehal tana kwance a ɗakin hutun da aka kaita ita kaɗai, Mama da Daddy suna can tare da Babies ɗin. Ameen ya shigo ɗakin kamar an jefo shi, ya ƙarasa gaban gadon ya kama hannunta yana kiran sunanta cikin damuwa. Bacci ya fara ɗaukar ta hakan yasa daƙyar ta iya buɗe idonta ta kalle shi. Ya ce. "Baby kina lafiya? Ya jikin naki? Mene yake miki ciwo yanzu? Kin sha wahala ko? Sannu Allah ya yi miki albarka." Ta ɗaga hannunta a hankali tana murmushi ta shafi sajen fuskarsa ta ce. "Yaya me yasa baka zo ba, ina ta kiran ka ina son na gan ka." Ya ƙanƙame hannunta a cikin nasa ya ce. "Ban sani ba ne Baby, ban san kina labour ba wallahi, da sai na zo mun yi tare, Mum bata faɗa mun ba." Ta ɗora hannunsa akan cikinta cikin shagwab'a ta ce. "Na sha wahala fa sosai Yaya, haihuwa akwai wahala, ni bazan kuma ba, karka kuma mun ciki ka ji." Ya kwantar da kansa akan ƙirjinta ya ce. "Sorry Baby, Allah ya saka miki da gidan Aljannah, sannu kin ji, yanzu ina ne yake miki ciwo?" Ta ce. "Duka jikina da kaina, more especially cikina." Kamar wanda aka tsikara ya ɗago kansa ya ce. "Sannu Allah ya baki lafiya, insha Allahu zaki samu lafiya soon." Ta gyaɗa masa kai. Ya shiga shafa cikinta ya ce. "Ina Babyn da kika haifa? Mece ce ko Namiji?" Kamar amsar tambayarsa sai ga Mama ta shigo ɗakin rungume da Baby, ya miƙe da sauri ya karb'e shi, Mama ta ce. "Ka jira ai in baka ko?" Ya yi murmushi tare da sakin wata kakkafar ajiyar zuciya, rungume yaron ya yi kam a ƙirjinsa cikin tsananin farin ciki. Ya koma ya zauna a gaban Neehal ya zubawa yaron ido kamar zai cinye shi yana murmushi, cikin ransa kuma yana godiya ga Allah. Mama ta miƙa masa dabino da Zamzam ta ce. "Ka tauna ka ba shi tare da ruwan, ka kuma yi masa addu'a ba kallo kawai ba." Neehal ta yi murmushi, Ameen ya yi kamar yadda Mama ta ce. Ya ɗago ya kalle ta ya ce. "Mum me yasa baki kira ni ba da tana labour?" Mama ta ce. "In ka zo me zaka yi?" Ya ce. "Addu'a mana." Mama ta ce. "Yanzu dai tunda ta sauka lafiya shikenan." Shigowar Daddy dake ɗauke da ɗayan Babyn ne ya hana shi magana. Ya saki baki yana kallon sa, Daddy ya ƙaraso ya miƙa masa Babyn yana murmushi ya ce. "Ga Al_hussain nan." Waro ido Ameen ya yi ya ce. "Dad! Twins ta haifa?" Sai kuma ya juya ya kalli Mama. Ta gyaɗa masa kai tana murmushi. Matsar da na hannunsa ya yi Daddy ya ɗora masa ɗayan akan cinyarsa, ya haɗa su duka ya rungume cikin tsananin farin cikin da bazai misaltu ba, yana ƙara godiya ga Allah da wannan baiwar da ya yi masa." Ya yi mintuna uku a haka sannan ya miƙa wa Daddy Al_hassan ya yiwa Al_hussain addu'a kamar yadda ya yiwa Al_hassan. Ya sunkuya dai-dai fuskar Neehal ya ce. "Thanks You so much Darling, ban san me zan ce miki ba saboda tsananin farin ciki, Allah ya yi miki albarka ya raya mana su, ya sa mu zamto ababen alfahari a gare mu." Idanunta a lumshe ta amsa da Amin cikin jin kunyar su Mama. Ya ɗago yana ɗan jijiiga yaron dake ta mulmul da baki saboda dabino da Zamzam da aka saka a bakin. Mama ta ce, "Tunda ba ki yi baccin ba tashi ki gwada feeding ɗinsu." Ta buɗe ido a hankali tare da tashi zaune tana yamutsa fuska. Ameen ya yi saurin saka mata pillow a bayanta ta jingina da shi sannan ya ɗora mata yaron akan cinyarta. Ƙurawa kyakkyawar fuskarsa ido ta yi tana jin duk duniya babu abun da take so kamar shi da ɗan'uwansa a yanzu, wani irin feeling take ji a kansu wanda baki bazai iya faɗa ba, wannan ita ce soyayyar ɗa da Uwa data ji ana faɗa kenan. Daddy ya miƙawa Ameen ɗayan ya fita dan zuwa Masallaci jin an fara kiran assalatu, Mama ta mara masa baya dan akwai abun da zata yi a office ɗinta yanzu. Ameen ya zauna a kusa da Neehal bayan fitar su yana murmushi ya ce. "Ki bashi mana." Ba tare data ɗauke idonta daga kan ɗanta ba ta ce. "Me?" Ya ce, "Abincinsu mana." Ta yi murmushi tare da zuge zip ɗin rigarta ta ciro Brest ɗin ta ɗan raba bakin yaron ta saka masa a hankali. Kamar bazai sha ba sai kuma ya fara zuk'a, ta ɓata fuska tare da runtse ido. Ameen da ya kura mata ido ya ce. "What?" Ta ce. "Zafi na ji." Ya matsa jikinta sosai ya ce. "Sorry." Ta shafa kuncin yaron hannunsa ta ce. "Kamarku ɗaya da su." Ya ce. "Eh mana, ai saboda na fi ki son su ne." Ta ɓata fuska bata ce komai ba. Gyara Babyn hannunsa ya yi ya rungume ta, kwantar da kanta ta yi akan kafaɗarsa idanunta akan yaranta, jin abun take kamar a mafarki, yau ita ce da ƴaƴa har biyu, gaskiya ikon Allah ya wuce gaban komai a rayuwa. A haka Mama ta turo ƙofa ta same su, saurin barin jikin Ameen ta yi tana ƙara yin ƙasa da kanta. Mama ta dube shi ta ce. "Baza ka yi Sallar ba ne kai?" Ya shafa kansa bai ce komai ba, ya miƙa mata yaron ya fita, ta bi shi da kallo sannan ta mayar da kallon ga Neehal ta ce. "Ruwan Nonon ya zo kenan?" Neehal ta ce. "Ban sani ba, yana dai ta tsotsa." Mama ta ɗauke shi ta saka mata ɗayan ta ce. "Shi ma bashi ya sha, idan ma bai zo ba sosai nan gaba zai zo."
Kafin ƙarfe goma na safe Mama ta rubuta musu sallama tunda lafiya ƙalau take ita da Babies ɗin. Da daddare Neehal tana zaune akan gado a ɗakin Mama ita da Ameen ya ce mata. "Baby Wanne suna za'a saka musu ne?" Ta ce. "Duk wanda kake so Yaya." Ya shafi kan na hannunsa ya ce. "Wannan tunda shine Babba a saka masa Muhammad, Sunan Ma'aiki S.A.W, mun kuma yiwa Daddy da Abba takwara." Sannan ya shafi kan na hannunta ya ce. "Wannan kuwa Abubakar Sadik." Ta yi murmushi ta ce. "Masha Allah, sunaye masu daɗi da asali, Allah ya raya su ya saka su biyo hali da dabi'un masu sunan." Ya ce. "Amin, me za'a na ce musu?" Ta yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce. "Sudais da Shureim." Ya ce. "Masha Allah, Allah yasa su kasance masu karatun Alqur'ani kamar masu sunan." Ta ce. "Amin." Suka cigaba da hirar su wadda gaba-d'aya akan yaran ne, idan ka ga yanda suke yiwa yaran sai ka rasa waye ya fi son yaran a cikinsu..... Tunda aka yi haihuwar kullum gidan cikin baƙi ƴan zuwa barka yake, Twins da Mamansu gwanin sha'awa kodayaushe tsaf_tsaf da su an shirya su cikin kaya masu kyau da tsada suna ta tashin ƙamshi. Da safe kafin Ameen ya tafi aiki yake zuwa sai kuma bayan Magriba idan ya dawo, idan ya ɗauki yaran nan daƙyar ake karɓar su daga hannunsa, Neehal kawai yake bawa su ta daɗin rai, ita ma wai dan saboda feeding ɗinsu ne. Saura kwana uku suna Hajiya ta zo, tunda ta zo ta sakawa Ameen ido, bai isa ya shiga sun zauna da Neehal a ɗaki ba sai ta fara mita tana cewa "Jego dai take yi Manne mata." Shi kuma yana sane sai yay ta yin wasu abubuwan yana ƙara kunna ta. Neehal tay ta yi musu dariya. Ana i gobe suna Ahmad ya zo ya ga Babies shi da twins, waɗanda farin ciki ya kusa kashe su saboda Aunty ta haifo musu k'anne guda biyu, kowa da nasa a cewarsu. Kayan Barka sosai Daddy ya siyawa yaran bayan wanda Ameen ya siya already tun kafin a haife su, ga waɗanda mutane suke ta kawowa, sai kayan suka yi yawa sosai Masha Allah. Ranar Suna aka sha shagali a gidan Mama, an yi komai cikin bajinta da wadata. Mai Jego ta sha kyau ita da Babies ɗinta har ma da Angon ƙarnin. Neehal ta cigaba da zama a gidan Mama, shi Ameen ya ɗauka da an yi suna zata koma, Mama ta ce sai bayan ta yi arba'in.
Yau Asabar wanda ya kama wata guda cif da haihuwar Neehal. Tana zaune a parlour ita kaɗai tana chatting a wayarta ta ci kwalliya ta yi kyau sosai sai tashin daddaɗan ƙamshi take. Ameen ne ya shigo parlour'n da sallama. Ta ɗaga kai ta kalle shi cikin mamakin ganin sa a dai-dai wannan lokacin, kasancewar time ɗin tsakiyar rana ne bai fi ya zuwa a irin time ɗin ba. Ta gyara zama tare da yi masa sannu da zuwa tana murmushi. Ya zauna a gefen ta yana kallon ta bai ce komai ba. Hannunsa ɗaya ta kama ta ce. "Ya dai?" Ya langwab'ar da kai ya ce. "Baby kullum ƙara kyau kike hankalinki kwance, but me ko bacci bana iyawa saboda rashin ki." Ta ce. "Who told you? Ina missing ɗinka sosai fa Yaya." Ya ce. "Ba wani nan, ni ban gani ba." Ta ce. "Me zan yi ka yarda to?" Ya ce. "Ki cewa Mum kin gaji ke gidanki zaki koma." Ta yi murmushi sosai bata ce komai ba. Ya ɓata