Showing 171001 words to 174000 words out of 262509 words

Chapter 58 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21377

gyaran murya sannan ya fara magana kamar haka. "Zamu fara da Addu'ar Ubangiji Allah ya bayyana mana wannan yaro a duk inda yake, ya kuma kare shi yasa yana hannu na gari, idan kuma kamar yadda ake tunanin sace shi aka yi, to Ubangiji Allah ya toni asirin waɗanda suka sace shin cikin gaggawa." Gaba-ɗaya suka amsa da "Amin ya Allah." Daddy da hannunsa ke dafe da kansa ya d'ago yana girgiza kai ya ce. "Amma fa wannan abun akwai rikitarwa da tayar da hankali ba kaɗan ba." Mama ta sauke numfashi tare da janye tagumin data rafka, cikin sanyin murya mai nuni da tsantsar damuwar da take ciki ta ce. "Tabbas a yau na yarda da maganar Sadiya 100%, ko shakka babu wanda ya kashe Jameel shi ya kashe Anwar, haka nan kuma shi yasa aka sace Sadik yanzu ma, kuma duk saboda Neehal." Daddy ya ce, "Ni kuma bana tunanin hakan gaskiya." Cikin takaici Uncle Usman ya ce. "To idan ma hakan ne waye yake aikata hakan? kuma akan me? Me yarinyar nan tay masa?" Cikin dashashshiyar muryar da ta ci kuka ta k'oshi Aunty A'isha ta ce. "Na fi tunanin koma waye son ta yake, shi yasa baya son kowa ya aure ta." Aunty Sadiya ta ce. "So?" Sai kuma ta yi ɗan murmushi ta ce. "Hmm, duk wanda yake aikatawa Neehal wannan abun ba son ta yake ba, wata mummunar manufar ce da shi a gare ta." Uncle Mahmud ya ce. "Me yasa zaki ce haka Haleemah? Nima zuciyata ta fi yarda da abun da A'isha ta faɗa na wani ne yake son Neehal ɗin, shi yasa yake kashe duk wanda zata aura, yanzu kuma sai ya sace Sadik ya canza salo." Aunty Sadiya ta miƙe ta yi taku hannayenta cikin juna tana zira yatsunta a tare tana zarewa, sannan ta ce. "Idan har dagaske son ta yake son Allah ba ƙoƙarin cutar da ita ba me yasa ba zai bayyana kansa a gare ta ba? Me yasa ya san idan har ya bayyana kansa a matsayin wanda yake kashe mata duk wanda zata aura saboda yana son ta ya san baza ta taɓa amincewa da auren shi ba, amma kuma yake aikata hakan? Ya kamata Ku yi tunani da kyau akan wannan idan har son ta yake da gaske ba zai taɓa aikata mata haka ba, kamar yadda na faɗa wata mummunar manufar ce da shi a gare ta, ko kuma akwai wani abun da yake son gudanarwa da ita, amma kuma Allah bai ba shi sa'a ba har yau, kuma ga dukkan alamu mummunan kudirin sa a kan ta da zarar ta yi aure ba zai samu ba, shi yasa yake aikata hakan." Gaba-ɗaya suka yi shiru suna kallon ta kowa yana auna maganganun ta a mizanin hankali. Ta koma ta zauna sannan ta dubi wani sashi na Falon ta ce. "A binciken da nake gudanarwa fiye da shekara akan al'amuran Neehal akwai wanda nake zargi, kuma a Ƴan kwanakin nan wasu alamomi suka ƙara ƙarfafa mun zargin nawa a kansa." A hanzarce Daddy ya ce, "Wa kike zargi Barrister? Ki yi gaggawar sanar mana in saka a damk'o sa a bincike sa." Uncle Umar ya ce, "Wannan haka ne, kuma shine abun yi, domin kuwa wannan abun ya yi yawa, mun gaji, muna san sanin gaskiyar al'amarin." Suka gyaɗa kai gaba-d'ayan su alamun haka ne. Aunty Sadiya ta ce. "Zargi nake ban tabbatar ba, shi yasa ba zan sanar muku a yanzu ba, na fi son sai na samu cikakken evidence k'wakwk'wara." Uncle Mahmud ya tari numfashinta da faɗin, "Amma ai a tsarin doka ma ana gudanar da wanda ake zargi a gaban shari'a, ko da ba'a tabbatar ya aikata lefi ba, ke me yasa baza ki faɗa ba?" Hajiya da bata yi magana ba tun d'azu sai yanzu ta ce. "Gaskiya ne, ya kamata ki faɗi wanda kike zargin, in ma ba shi ba ne wataƙila sanadiyyar hakan sai ki ga an gano gaskiya." Umma ta ce. "Haka ne, Sadiya ya kamata ki faɗa mana wanda kike zargi domin a san abun yi a kansa." Aunty Sadiya ta numfasa ta ce. "Ku yi haquri, na san zuciyoyinku a zak'e suke da sanin ko waye, amma ku sani wannan case ɗin na Neehal ya sha banban da case ɗin laifukan da muka saba ji da gani, idan har ban yi takatsantsan ba to zan iya kwana a ciki." Abba ya ce. "Kamar ya? Ba bincike ba ne? Ai idan aka gane mutum ba shi da hannu a ciki sakin sa za'a yi." Aunty Sadiya ta ce. "Ku dai yi haquri, Insha Allahu nan ba da jimawa komai zai bayyana, mu dai kawai mu dage da addu'a." Kawu Musa ya ce. "To Allah yasa mu dace, amma ba kwa tunanin ko akwai wani da suka samun saɓani da yarinyar nan ya k'ullace ta yake aikata mata wannan abun?" Mama ta ce. "Bana tunanin haka gaskiya, dan Neehal bata da abokin faɗa a rayuwarta, na san wani lokacin bata da haquri idan aka ɓata mata rai, amma bana jin zata yiwa wani babban abun da zai sa ya dinga bin ta da wannan mummunan abun a matsayin ɗaukar fansa ko hukunci." Kawu Musa ya ce. "To idan ba haka ba kuwa zata iya yiyuwa ko shi Gen. da ya kasance babban mutum mai tare da ƴan adawa a ƙasar nan saboda shi ake aikata wannan abun, domin a ɓata masa suna ko kuma dan wata manufar daban." Suka yi shiru cikin alamun nazari. Daddy yana jinjina kai ya ce. "Kuma fa Alhaji Musa zancen ka akwai k'amshin gaskiya, dole ne in tsaurara bincike akan wannan al'amarin, domin kuwa na san zuwa yanzu sunana dana iyalina ya fara ɓaci a idon duniya." Uncle Mahmud ya ce. "Wannan shawarar ta yi, kuma ita ma Neehal ɗin ya kamata a tuntube ta akan maganar da Alhaji Musa ya yi ta farko, akan ko sun taɓa samun matsala da wani, like criminal person haka, ko kuma wani da suka samu saɓani ya taɓa yin wani mummunan ƙudiri a kanta a matsayin ɗaukar fansa." Abba ya jinjina kai ya ce. "Ya kamata kam, domin komai zai iya faruwa, tunda mu har yanzu lalube muke a cikin duhu, muna neman gaskiyar al'amari." Umma ta ce. "Har wannan ƙawarta_ta itama a tuntube ta ko san wani abu akai, tunda kodayaushe suna tare." Aunty A'isha ta ce. "Wai Haneefah kike nufi?" Umma ta ce. "Ehh." Aunty A'isha ta ce. "Insha Allahu duk zamu yi ƙoƙarin yin hakan, Allah Ubangiji dai ya toni asirin masu aikata wannan abun da gaggawa, ko zuciyoyinmu zasu samu salama." Suka amsa da Amin, kuma kowa ya yi na'am da wannan shawarwarin da aka bayar. Aunty Sadiya dai kawai kallon su take bata ce komai ba, cikin ranta tana tunanin wani abu daban. Uncle Usman ya ce, "Ni Neehal ɗin ma nake tausayawa, yarinya duk za'a sa ta tsani kanta da rayuwarta, dan babu wanda zai so a ce ana rasa rai ta dalilin sa, ko kuma an cutar da wani." Kawu Musa ya ce. "Wallahi fa, tunda k'uruciyarta za'a ɗora mata tension ɗin da ya fi ƙarfin kanta." Umma ta ce. "Ƙaddara ce, wadda ta riga fata, babu yanda zamu yi, sai dai mu yi addu'ar Allah ya tsayar haka, kuma da izinin Allah komai zai zo ƙarshe, zai kuma zama tarihi kamar ba'ai ba." "Haka muke fata." Cewar Uncle Umar. Hajiya ta ce. "Tana kwance har yanzu ko?" Aunty A'isha ta ce. "Eh, tunda akai mata allurar bacci bata farka ba har yanzu." Mama ta ce. "Bari mu gama sai in je in tashe ta, na ga yamma ta yi sosai Magriba ta gabato, gwara ta tashi ta yi sallolin dake kanta." Hajiya ta ce. "Ni fa da wannan abun ya faru na yi zargin ko dai aljanu ne da yarinyar nan." Kawu Musa ya ce. "Zata iya yiyuwa su ɗin ne ma, amma kuma shi sha'anin jinnu ba haka yake ba akan al'amarin Aure, yawanci tun kafin maganar aure ta yi nisa suke tarwatsa abun, ko kuma ki ga yarinya ta girma sosai babu mashinshini, amma indai ba turo su akai ba zai yi wahala su yi kisa, in ma zasu yi kisan ba ta hanyar harbi ba, sai dai kawai a wayi gari a ga mutum ya rasu." Umma ta ce. "Tabbas haka ne, dan na taɓa ganin yarinyar da irin wannan ya faru da ita, ita auranta aljanin ya yi, da farkon ƴan'matancinta tana samari, daga baya kuma sai suka daina zuwa dif, sai daga baya aka gane aljanin ne ya aure ta." Aunty A'isha ta ce. "Subhallahi, Allah ya kiyaye mu da zuri'armu baki ɗaya. Suka amsa da Amin. Uncle Mahmud ya ce. "Hakan ma zata e yiyuwa, kin san su ma aljanun babu abun da ba za su iya ba, sai a gwada yi mata magani a ga ko Allah zai sa a dace." Kawu Musa ya ce. "Allah yasa mu dace, yasa mu fi ƙarfin zuk'atanmu, ya kare mu daga abun da yafi ƙarfin mu, ya raba mu da mummunar ƙaddara." Suka ƙara Amsawa da Amin. Abba ya nisa ya ce. "Ni fa ina da wata shawara, a gani na tunda duk wannan abun da ake yi mun fahimci saboda kar yarinyar ta yi aure ne, auren ne ba'a son ta yi, me zai hana a ɗaura mata Auren kawai ta tare a gidan mijinta ba tare da duniya ta sani ba, kun ga kenan daga lokacin da tai auran koma waye yake bibiyarta da mugun nufinsa ta yi auranta, magana ta ƙare." Uncle Usman ya ce. ,"Tunanin dana yi d'azu kenan nima, na ce a ɗaura mata auran a yau, amma Daddy'n ta ya hana." Dad ya ce. "Ba wai na ƙi ba ne, abubuwa guda biyu na duba, na farko iyayen yaron Sadik nan baza su ji daɗi ba idan muka ɗaurawa Neehal Aure a yau, zasu yi tunanin ba ma mu damu da ɓatan ɗansu ba ta auran ƴarmu kawai muke, alhalin kuma duk mun fuskanci ko na ce muna tunanin saboda da ita aka sace shi, duk da ba ma fatan hakan. Na biyu kuma ita kanta yarinyar bazai yiyu tana cikin halin baƙin ciki da tashin hankalin ɓatan Sadik sannan mu ƙara mata da wata damuwar mu daura mata aure da wanin sa ba da sanin ta ba, may be wanda zamu aura matan bata son shi, kun ga mun jefa ta a cikin wata damuwar bata gama fita daga wata ba." Suka jinjina kai gaba-d'aya cikin gamsuwa da bayanan Daddy. Mama ta ce, "Maganar ka gaskiya ce Gen. Amma in dan wanda Neehal zata aura ne ba mu da matsala da wannan, dan ta son yaron nan Ahmad Baban twins, shima kuma yana son ta, gashi yaron kirki ne ba shi da matsalar komai haka ma iyayensa, amma kamar yadda ka faɗa koda za'ai mata auran ba yanzu ba, mu ɗan jira zuwa wani lokaci kafin nan Insha Allahu mun warware daga cikin wannan matsalar, dan yanzu babban burin mu Allah ya bayyana mana Sadik cikin k'oshin lafiya." Haka dai suka ci-gaba da tattaunawa, shi Daddy yana ganin gwara a jira bayyanar Sadik idan ma Auren za'ai wa Neehal a aura mata shi. Uncle Mahmud ya ce, kamar hakan da wuya, tunda a rabuwar da suka yi ɗazu da danginsa sun nuna ko Allah ya bayyana shi ba zai auri Neehal ba, kuma ba ya jin yanda suka ɗauki zafi akan al'amarin zasu amince ta cikin ruwan sanyi. Suna cikin tattaunawar ne Aunty Sadiya ta ce. "Wai ina Ameen ne? Yau gaba-d'aya duk wannan abun da ake ban gan shi ba." A ɗan firgice Daddy ya ce. "Bai zo gidan nan ko da safe ba? Ni sai ma yanzu da kikai magana na yi released ban gan shi ba yau kwata_kwata ko a gurin d'aurin Auren." Cikin damuwa Mama ta ce. "Nima rabo na da shi tun jiya da rana, to ina yaron nan ya shiga?" Hajiya ta ce. "Matar shi ma haka ta ce, kuma tun safe take kiran wayarsa a kashe." Kawu Musa ya ce. "Subhallahi, Allah dai yasa lafiya yake." Uncle Ahmad ya ce. "Insha Allahu yana lafiya k'alau, kun san halin Ameen, may be ya samu wannan labarin ne shi yasa bai zo ba saboda tashin hankali." Daddy ya ce. "To kuma sai ya kashe wayoyinsa, Ameen da koyaushe wayoyinsa a kunne suke." Mama da gabanta ke faɗuwa ta ce. "Bari na dauko wayata na kira shi mu ji ko zata shiga yanzu." Uncle Mahmud ya ce. "Bari na kira shi ba sai kin tashi ba." Ya ƙarashe zancen tare da zaro wayarsa daga aljihun gaban rigarsa. Yana kira ta shiga, sai dai har ta katse bai ɗauka ba. Mama ta ce, "To ina Yaron nan ya shiga ya bar wayar tasa kuma?" Daddy da yanayinsa ya nuna rud'ewa ya ce. "To shi kuma me ya faru da shi?" Umma ta ce. "Babu komai Insha Allahu, tunda wayar ta shiga zai biyo bayan kiran ko anjima ne, wataƙila ba ya kusa da wayar ne, ku kwantar da hankulanku, kar ƙarawa kanku wata damuwar, mu yi masa addu'a kawai." Sukay shiru kowa da tunanin da yake a cikin ransa. Kiran Sallar Magriba ne ya tashe su.










A ɓangaren su Abban Sadik su ma bayan dawowar su daga masallaci suka zauna zaman cigaba da tattaunawa akan al'amarin. Suma kamar su Daddy sun amince dalilin Neehal aka sace Sadik, har wasu k'annen Abba na cewa k'ila ma da haɗin bakinta, tunda ita ce last wanda ya yi waya da ita cikin dare. Abba ya ce, ya yarda ta sanadin Neehal aka sace Sadik, shi ma hakan zargi yake ba wai ya tabbatar ba ne, amma sam ba zai taɓa yarda da saka hannunta ko haɗin bakinta a sace shin ba, dan ya san baza ta taɓa cutar da Sadik ba. Kuma batun waya da suka yi, ai idan aka duba Sadik ɗin ne ya kira ta ba ita ta kira shi ba, bare ace akwai abin da ta shirya a wayar suka yi. Abby ya ce duk wannan maganganun ba su ne mafita ba, mafita kawai a dage da addu'ar Allah ya bayyana Sadik. Maamah ta farfaɗo, amma ko magana bata iya yi, ƴan'uwan ta na kanta suna yi mata firfita. Ƴan'biki kuwa duk an watse cikin alhakin abun, sai ƴan'uwa na jiki ne da baƙin nesa sukay saura, al'amarin dai babu daɗin ji ko kaɗan, abun tausayi da rud'ani.








A ɓangaren Ahmad al'amarin ya rud'a shi fiye da tunanin mai karatu, musamman da Zahra ta sanar masa abun da ta ji ana faɗa a gidansu Neehal lokacin da suka riski labarin ɓatan Sadik, cewar samarinta biyu na baya ma kashe su aka yi. Abun ya matuƙar ɗaure masa kai da jefa shi cikin tunani, Neehal ta sanar masa samarinta biyu sun rasu, amma bata ce masa kashe su akay ba. Idan kuwa har haka ne ya tabbatar da akwai wata b'oyayyiya kenan a rayuwar Neehal ko kuma ya ce wata babbar matsala. A gefe guda kuma tausayinta mai tsanani ne ya cika masa zuciya, a ransa ya dinga faɗin wannan wanne irin zalunci ne ake mata haka? Wunin yau gaba-d'aya cikin tunanin al'amarin ya yi shi, ya kulle kansa a ɗakin da yake sauka a gidan Mamy, Sallah ce kawai take fito da shi. Hankalinsa in ya yi dubu yau a tashe yake, ba ya son wani mummunan abun ya samu Princess ɗin sa, yanda yake jin zuciyarsa ba abun da yake buƙata sama da ya je ya ga halin da take ciki, dan ya san tana can tana kukan nan nata, ya san hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, abun da yake ƙara d'aga masa hankali da Zahra ta ce har suma ta yi. Twins ma waɗanda su Ummi suka taho da su gidan Mamy sai kuka suke suna kiran Aunty, da ƙyar Ummi ta lallame su suka ci abinci. Ummi saukar su kenan ita da Abban su Ahmad suka tarar da wannan mummunan labarin, hakan yasa ba su wani jima ba a gidan Mama suka yo gidan Mamy tare da Mamin da ta je bikin ita ma, tunda maganar biki kuma ta tashi tunda babu Ango. Zuciyoyinsu babu daɗi ko kaɗan, wuni suka yi suma suna jimanta wannan al'amarin mai rikitarwa. Neehal da ahalinta sun ba su tausayi sosai, more especially ma Neehal da ƙarshe komai a kanta zai ƙare.










Mama tana zaune a bakin gadon Daddy, ta saka Neehal dake kwance a gaba tana kallon ta cikin tsananin tausayawa bayan ta idar da Sallah. Tunanin rayuwar Neehal kawai take da irin jarrabawoyin da take gamuwa da su a rayuwarta, tun tana ƙarama aka kashe mata iyayenta, ta tashi a wahalce a hannun iyayen riƙon ta, bayan ta dawo hannunta da zama kuma danginta suka nuna suna ƙin ta ƙuru_ƙuru ba k'aunarta suke ba, ta san wannan abun ma yana damun ta, boyewa kawai take tana barin abun a cikin ranta. Bayan ta isa aure kuma ta fara fuskantar wannan challenges ɗin, abun ya yi mata yawa a ƙananun shekarunta. Daga nan Mama ta fara tunanin abun da suka tattauna d'azu, and she noticed one thing a zaman d'azu da akai game da Aunty Sadiya, tana magana ne kamar mai habaici a gurin, tana kuma yin wani irin kallo kamar na gargadi' ko kuma na tuhuma. Gashi ta ƙi faɗar wannan ta ce tana zargin, Mama ta kasa gane me Aunty Sadiyan take nufi da kuma inda ta dosa, amma ta k'udurce a ranta zata tambaye ta idan sun keɓe. Sai kuma ta juyar da akalar tunanin nata kan Ameen bugun zuciyarta na ƙaruwa, tana tambayar kanta ina ya shiga? Me yake yi har yanzu bai zo gidan ba? Kuma ana ta kiran shi ba ya pick. Bayan shigowar ta ɗakin ta masa kira ya kai sau biyar amma bai ɗauka ba.






A hankali Neehal ta buɗe idonta da yay mata nauyi ta sauke su akan fuskar Mama. Cikin muryar marasa lafiya dake fita da ƙyar ta ce.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login