Showing 51001 words to 54000 words out of 262509 words
Chapter 18 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
Afrah sama, wanda tuni sun yi bacci. Ɗakin Mama ta shiga ta tarar da ita tana operating system. "Sannu da aiki Mama." Ta faɗa lokacin da take zama a kusa da ita, Mama ta ce "Yawwa sai yanzu ya tafi?" Ta ce "Eh." Mama ta ce "Ina yaran?" "Sun yi bacci." Neehal ta amsa, Mama ta ce "Sun dai ci abinci ko?" Neehal ta ce "Na basu popcorn kafin mu fito." Mama ta ce "Popcorn abinci ne?" Neehal ta ce "Da yawa suka ci ai, kuma da suna jin yunwa za su faɗa mun." Mama ta ce "Alright." Neehal ta ɗan yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce "Mama ki yi haquri akan abin da na yi, na gane gaskiya kika faɗa." Mama ta ce "Shikenan na ji dad'i da kika gane haka, wai har yanzu ba'a kira ki ba akan Yaran nan? tun d'azu nake so na tambaye ki kuma sai na sha'afa." Neehal ta ce "Ba a kira ba." Mama ta d'ago ta dube ta karon farko tun shigowar ta ɗakin ta ce "Bana son ƙarya fa Neehal kin sani, ki faɗa mun gaskiya ko sun kira." Neehal ta ce "Allah Mama ba'a kira ba, sai dai ko yanzu da na sauka ƙasa." Mama ta ce "Amma na yi mamaki, more than five Radios banda Televisions amma a ce ba'a samu wanda ya san su ba, Sadiya ma ta kira ni ta tambaye ni, Dad ma haka." Neehal ta ce "Nima Mama na yi mamaki, dan ko kirana akai sai na yi tunanin ko su ne." Mama ta jinjina kai kawai, Neehal ta ce "Mama kun yi waya da Yaya kuwa?" Mama ta ce "Ya zo ma d'azu." Neehal ta waro Ido ta ce "Amma shine bai neme ni ba." Mama ta ce "Ya tambaye ki na ce kina ɗaki a kwance, ko kina ta k'uncin zan je in kira ki ne." Neehal ba ta ce komai ba ta tashi ta fice tana turo baki gaba, cikin takaicin Ameen ya zo amma ba su haɗu ba, shima kuma ko ya shigo ɗakin ya ganta. Gyarawa su Amrah kwanciya ta yi ta cire Hijab ɗin jikinta ta shiga toilet dan ɗauro alwala.
Goma saura Sadik ya ƙarasa gida, kamar yadda ya yi zato duka ƴan gidan nasu suna zaune a falon har Abbansu, bakinsa ɗauke da Sallama, gaba-d'aya suka zuba masa ido tare da amsa masa sallamar. Kusa da mahaifiyarsa ya je ya zauna a ƙasan kujerar da take ya mata sannu da gida, sannan ya gaishe da Abbansa da kishiyar Maamah wadda suke kira da Umma, k'annenshi kuma suka gaishe shi. Abbansa ya ce "Abubakar daga ina haka?" Sadik ya yi ƙasa da kansa tare da shafa sumar kansa, Abban ya kalli Maamah Wadda ke murmushi ƙasa_ƙasa yana murmushin shima, Umma kuwa tab'e baki ta yi ta ce "Hmmmm, Sadik dai ya soma ɓata wayonsa da yawon dare, da dai ba ya yi amma yanzu....." "Wacce irin magana ce wannan Ruqayyah kike yi?" Abba ya katse Umman a ɗan fusace, Maamah da annurin fuskarta ya ɗauke lokaci ɗaya jin kalaman Umma ta sauke numfashi cikin jin daɗin yanda Abban ya katse Umman ga aikabata mata ɗa da take ƙoƙarin yi." Sadik ma ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin yanda zugar Umman bata samu shiga ba a gurin Abban kamar yadda ta saba kodayaushe. Umma ba ta da aiki sai yi masa sharri a gurin Abbansa, kuma Maamah ba ta isa ta yi magana ba sai ta saka kuka ta ce tana nuna mata iko akan Sadik dan ta ga ita ba ta ƴaƴa maza, ai itama ɗanta ne ba zata cutar da shi ba. Shiru Umma ta yi ganin yanda Abban ya haɗe rai. Shima Abban shiru ya yi ganin yaransu na falon, miƙewa Sadik ya yi ya nufi bedroom ɗinsa dan yana da aikin da zai yi akan wani case da yake bincike akai.
Asalin Mahaifin Sadik mutumin Kano ne, ɗan kasuwa ne da yake da rufin asirinsa dai_dai gwargwado. Mahaifiyar Sadik kuma ƴar asalin garin Maiduguri ce kabilar Shuwa, aure ne ya kawo ta Kano. Fara ce kyakkyawa ga gashi har baya, a gurinta su Sadik suka gado kyau. Umma kuwa ƴar asalin jihar Kano ce, iyayenta a cikin gari suke, Maamah ba ta fi shekara 5 da aure ba Abba ya auro Umma, lokacin an haifi Sadik yana yaro. Ana zaton wuta a mak'era sai aka same ta a masak'a, domin kuwa Umma ce take da tsananin kishi da shegen makirci, ita kuwa Maamah da zuciya ɗaya take zaune da Umma, kuma duk kasancewarta Shuwa ba ta nuna wannan kishin na hauka, ga ta da haquri da addini. Su Sadik su biyar ne kawai a gurin mahaifinsu, a ɗakinsu su uku ne, Shine babba sai k'aninsa mai bi masa Bashir, sai autarsu Batul. Ita kuma Umma ƴaƴanta biyu kuma duk mata ne, kuma ta fi shekara goma kafin Allah ya bata haihuwar. Makirci kala_kala Umma ta dinga haɗawa Maamah a gurin Abba kafin ta haihuwa, wai Maamah tana mata gorin haihuwa. Hakan yasa Abba ya ce ƴaƴan Maamah itama ƴaƴan ta ne tunda Ƴaƴansa ne dan haka tana da iko akansu. Tun daga wannan rana fa Umma ta samu damar yiwa Sadik sharri iri_iri a wajen Abbansa, a matsayin tana faɗa masa gaskiya wadda Maaman take bo'yewa a cewar ta, kasancewar Abba matafiyi ne bai fiya zama a gari ba, saboda sha'anin kasuwancinsa. Haka Abba zai samu Sadik yay ta masa faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, itama Maamah bata tsira da faɗan Abban. Inda Allah ya taimaka kakarsu Sadik mahaifiyar Abba tana son su sosai, to wani sharrin idan Umma ta k'ulla ita take taka mata burki ta ci mata mutunci, ta kuma hana Abba ɗaukar hukunci akan Sadik ko Maamah. Ita kuwa Maamah kullum cikin tausar Sadik take tana ba shi baki akan Abinda Umma take masa, duk da abun na damunsa amma haka yake haquri ba ya nuna ɓacin ransa saboda nasihar mahaifiyarsa. Bashir ne ma sarkin zuciya wataran yake ƙoƙarin tankawa Umma idan ta ƙure shi akan abun da takewa Mahaifiyarsa da ɗan'uwansa, duk da shi ɗinma tana masa ba tsira ya yi ba, amma shi tana ɗan shayin shi ganin yaron a tsaye yake, Sadik kuwa haqurin mahaifiyarsa ya ɗauko shi yasa tafi raina shi kuma tafi tsanar shi.
Misalin ƙarfe 11 na dare Maamah ta kwankwasa masa ƙofa, yana zaune gaban laptop, ya d'ago ya dubi ƙofa tare da faɗin "Come in." Maamah ta shiga bakinta ɗauke da Sallama, ya amsa mata ya ƙara da faɗin "Au Maamah ke ce, na ɗauka ma Basheer ne." Maamah tana murmushi ta ce "Ni ce Son ya aiki?" Ya ce "Alhamdulillah gashi muna ta fama." Maamah ta ce "Allah ya taimaka ya bada sa'a." Ya amsa da "Ameen." Cikin ladabi. Maamah ta dube shi ta ce "Daga ina kake ne Sadik?" Sunkuyar da kanshi ya yi yana murmushi ya ɗan sosa kai ya ce "Gidan su Neehal." (Da yake Maamah ta san Sadik yana zuwa gurin Neehal.) Maamah ta yi murmushi ta ce "Ka baro su lafiya?" Ya ce "Eh, tana gaishe ki ita da Mama." Ta ce "Ina amsawa." Ta miƙe tay masa sai da safe sannan ta fice zuciyarta fal da farin ciki, kullum addu'arta Allah ya bawa Sadik mace ta gari yay auransa ko ya huta da addabar Umma da kuma faɗan mahaifinsa, tunda ba su isa dai sun bi shi gidansa sun masa ba.
Washegari Mama ta koma bakin aiki, Neehal kuma gidansu Haneefah ta je dan yi musu ban gajiya ita da Twins ɗinta. Bayan sati ɗaya, Neehal ta koma gurin aiki, kuma har yanzu babu wanda ya kira akan su Afrah. Kullum Mama cikin saka ran kira take amma sai ta ji shiru, abun yana ɗaure mata kai sosai, dan yanda aka baza hotunan su Afrah a gidajen Televisions ya ci ace wani nasu ya gani, kuma kullum sai an yi cikiyar iyayensu a gidajen rediyo da Talabijin. Yau Juma'a Neehal aikin safe ta yi, 12pm da mintuna ta dawo gida, kasancewar Ran Monday za su yi resuming School Mama ta ce ta shirya ta je gidan Ameen, kar ta koma School ta zo bata samu damar zuwa ba, tunda every weekend tana gurin aiki, Monday to Friday kuma tana school. Ameen ɗin kuma yana ta yiwa Mama mitar ta hana Neehal zuwa gidansa. Neehal murna kamar ta kashe ta dan ba ƙaramin kewar Yayan nata ta yi ba, dan tunda yay aure ko waya ba su taɓa yi ba, kuma kusan kullum sai ya zo amma ba sa haɗuwa, duk time ɗin da zai zo tana gurin aiki. Cikin Sauri ta shirya Twins ɗinta itama ta shirya, ana sakkowa daga masallaci Driver ya tafi kai su, dan ita ba ta san gidan ba, duk da tana jin mararta na mata ciwo kaɗan_kaɗan amma ta daure, dan tana faɗa Mama cewa za ta yi ta fasa zuwan wani lokacin ta je, ita kuwa zuciyarta cike take da kewar Yayan nata............✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:44] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*2️⃣4️⃣*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
...........Direct gida Ameen ya nufa da ita, domin ya san duk taimakon da za a bata a asibiti Mama za ta bata. Mama tana zaune a falo tana azkar ɗin yamma ta ga Ameen ya shigo mata da ƴa a hannu, a ruɗe a tashi tana dubansa ta ce "Al'ameen me ya same ta?" Sai da ya kwantar da Neehal a kan kujera sannan ya ce "Mama ciwon cikinta ne ya tashi." Mama ta ƙarasa inda take tana mata sannu, Neehal dai hawaye kawai take. Mama ta ce Ameen ya kai mata ita sama bari ta haɗa allura ta mata, insha Allah ciwon zai lafa mata yanzu.
Bayan 10 minutes Neehal har ta samu bacci saboda allurar da Mama ta mata, Mama dake zaune a gefen ta ta sauke ajiyar zuciya cikin tausawa Neehal ɗin, gyara mata kwanciya ta yi daga ruf da cikin da ta yi sannan ta fice. Ameen yana falo tare da Twins har time bai tafi ba. Ameen ya dubi Mama ya ce "Ya jikin nata?" Mama ta ce "Alhamdulillah ta samu ya lafa mata har bacci ya ɗauke ta, dama haka ciwon nata yake kamar aljanu, lokaci ɗaya zai zo amma tana shan magani ko aka mata allura zata ji sauƙin shi 70%." Jinjina kansa ya yi kawai, a ransa yana mamakin wannan ciwon nata da baya jin magani, dan idan bai manta ba kusan 10 years kenan Neehal take fama da shi. Sun ɗan taɓa hira da Mama akan rashin bayyanar wanda ya san su twins har yau, sannan yay wa Mama Sallama ya tafi. Ko da ya koma gida Hafsah bata nuna masa komai na ɓacin rai ba, sai ma tambayarsa jikin Neehal da ta yi. Washegari da Neehal ta tashi lafiya k'alau ta tashi, sai dai ɗaurewar ciki kawai wanda duk lokacin period ɗinta haka yake mata, sai ta gama take jin ta normal.
*ABUJA*
Tun ranar da aka ba da cikiyar su Afrah misalin ƙarfe goma 12 na rana, budurwar nan ce zaune a falon gidansu tana kallon ASTV, 12 na yi aka fara labaran rana. Hankalinta ba ya kan TV'n dan bata damu da kallon labarai ba, kamar an ce ta d'ago idanunta suka sauka a kan hotunan twins ana cikiyar iyayensu. Wata muguwar zabura ta yi gabanta na tsananta bugu, ba ta san sanda ta cillar da wayar hannunta ba a matuƙar razane cikin ƙaraji ta ce "What?" Mahaifiyarta ce ta fito daga bedroom tana dubanta da kyau ta ce " *Safeenah*! Ke da waye na ji kamar kina ƙara?" Tattaro nutsuwarta ta yi ta lalubi remote ta kashe TV dan kar mahaifiyartata ta ga cikiyar su Afrah da ake, ta sunkuya ƙasa ta ɗauki wayarta sannan ta dubi Mahaifiyartata ta ce "Ba komai Momma." Daga haka ta miƙe ta shige ɗakinta gumi na karyo mata ta ko ina a jikinta. Tab'e baki Momma ta yi ta wuce kitchen. Wani narkeken ashar Safeenah ta danna ta fara zarya a ɗakin a fili take faɗin "Lallai Gaye ya ha'ince ni, amma wallahi sai ya yi dana sanin cin amanata da ya yi." Ganin surutu ba mafita ba ne a gareta yasa ta ɗauki wayarta data cillar akan gado ta lalubo Numbern Aminiyarta kuma abokiyar shawararta. Bugu ɗaya ta ɗauka cikin tsananin tashin hankali Safeenah ta fara mata magana. "Na shiga uku Saudart, Gaye ya cuce ni ya ha'ince ni ashe Yaran nan be kashe su ba yar da su ya yi." "Ke wa ya faɗa miki haka?" Saudat ta tambaye cikin tarar numfashi. Safeenah na kuka ta ce, "Gashi nan na gani ana cikiyarsu a gidan TV an tsince su a Kano, yanzu ya zan yi ƙawata dan Allah ki ba ni shawara, ina tsoron kar asirina ya tonu." Ta ƙarashe zancen tamkar Numfashinta zai bar jikinta saboda tashin hankali. Saudat ta ce "Kin ga ƙawata ki kwantar da hankalinki, in dai ina raye ba zan bari hawayenki ya zuba ba, ki bani nan da zuwa yamma zaki sha mamaki, Gaye kuma zamu haɗu da shi zai san mu ya ha'inta." Safeenah zata yi magana ta ji wayar ta katse, zama ta yi a ƙasa dab'as tare da dafe kanta cikin rashin sanin abun yi. Ta san Saudat shu'umar kanta ce, yarinya ce mai buɗaɗɗan ido, ga shegen bin bokayen tsiya, a makarantar ABU Zaria suka haɗu da Safeenah har suka zama abokan juna. Ita Saudat ƴar cikin garin Zaria ce, ita ta bawa Safeenah shawarar tasa a sace su Afrah a kashe su, ita kuma ta haɗa ta da su Gaye sukai mata aikin. Yinin ranar cikin fargaba da tsoro Safeenah ta wuni, har wata yar ƙaramar rama ta yi, kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin firgici. Kamar yadda Saudat ta mata alƙawari da yamma ta kirata ta shaida mata ta je gurin wani boka ya mata aiki akan ko da mutum ya ga cikiyar su Afrah a rufe bakinsa ya kasa magana akai, kuma ta tabbatar mata aikin bokan tamkar yankan wuk'a yake. Wannan magana ta Saudat ita ta sanyaya wa Safeenah rai, domin kuwa ta tabbatar aikinsu ya ci tunda gashi har an fi sati amma babu wanda ya yi magana akan ya ga cikiyarsu Afrah da ake ta yi, kuma inda an gani za ta ji labari tunda gidansu ɗaya da Kakarsu Afrah ta wajen uwa, Safeenah ƙanwar mahaifiyar Su Afrah ce ubansu ɗaya. (Tsafi gaskiyar mai shi, Allah ka tsare mana imaninmu, Ameen ya Allah.) Su kam gidansu Mahaifin su Afrah ba su da nutsuwar wani kallon TV, kodayaushe suna zaryar asibiti hakan ya sa ba su ga cikiyar da ake ta yi ba. A ɓangaren su Kakarsu Afrah ta wajen uwa ma haka ne, tashin hankali bai barsu damar wani kallon TV ko sauraren Radio ita ƴaƴanta ba, hakan ya sa suma ba su ga cikiyar ko sun ji ta ba.
Ranar Laraba Neehal ta dawo daga school da yamma ta tarar da Aunty Sadiya wadda zuwanta kenan gidan daga wurin aiki ta biyo ta gidan. Neehal ta rungume ta tana faɗin "Auntyna oyoyo." Aunty Sadiya na murmushi ta ce "Oyoyo my Daughter, Ya school?" Neehal ta ce "Alhamdulillah, sai yau ma ni na koma." Aunty Sadiya ta ce "Allah ya taimaka, saura semester uku ku gama ko?" Neehal ta ce "Insha Allah." Mama ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da ruwa da glass cup, ta ajiye a gaban Aunty Sadiya, Aunty Sadiya ta ɗauki ruwan tana faɗin "Sannu Yaya, kamar wata baquwa sai kin kawo mun drinks." Mama ta ce "Ai na ga daga gurin aiki kike, kuma yanayinki ya nuna kin gaji." Aunty Sadiya ta ce "Hmmm bari kawai Yaya, yau tun 7 na fita office sai yanzu na samu kaina, case ɗin wannan Yarinyar da na ce miki an mata fyaɗe ne har yanzu ya ƙi ƙarewa, so kike ku murd'e gaskiya ƙarshe ma idan ba ai wasa ba su kori shari'ar." Mama ta ce "Ai Allah ya fi su, kuma insha Allahu zai baku nasara." Aunty Sadiya ta ce "Allah ya amsa." Neehal ta dubi Mama tana turo baki gaba ta ce "Mama na dawo fa." Mama ta ce "Ai na ganki." Neehal ta ce "Ai ba ki yi welcoming ɗina ba." Mama ta ce "To bari in ɗauke ki in goya ki uwata." Neehal ba ta ce komai ba ta tashi ta wuce sama tana ɓata rai. Aunty Sadiya ta yi murmushi zuciyarta cike da tausayin Neehal. Neehal tana shiga ɗakinta ta tarar da twins sun ba je kayan kwalliyarta akan gado suna ta yaɓa wa fuskarsu. Suna ganin ta shigo suka fara kifkifta idanuwa, dan tasha yi musu faɗa akan in ta fita su daina yi mata b'arna a ɗaki. Cike da takaici take kallonsu, ganin yanda suka bata jikinsu da bedsheet da janbaki, ta ƙaraso cikin ɗakin tana faɗin "Sannun ku da aiki." Afrah ta nuna Amrah ta ce "Aunty ita ta ɗakko miki." Amrah tai sauri ta ce "Ba ni ba ce ita ce." Neehal ta ce "Ku sauka ni ku bari guri." Sauka suka yi daga kan gadon da sauri suna mutsitstsika janbaki a ƴan'yatsunsu. Tattare kayan da suka barbazar mata akan gadon ta yi, sannan ta cire zanin gadon ta kai toilet. sai da ta sake wani sannan ta kamo su Afrah ta cire musu kayan jikinsu ta musu wanka, sukwa sai murna suke an ƙara yi musu wanka, dan suna k'aunar wanka a rayuwarsu suga suna ta facal_facal da ruwa.
Bayan Mama ta kawo wa Aunty Sadiya abinci ta ci, sannan ta tattara duka hankalinta akan Mama ta ce, "Yaya maganar Neehal ce fa ta biyo da ni." Mama ta ce "Ina jinki Sadiya me ya faru." Aunty Sadiya ta sauke numfashi cikin jimanta al'amarin ta ce "A binkicen da na yi ya