Showing 63001 words to 66000 words out of 262509 words

Chapter 22 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21415

ta sauke ajiyar zuciya, ba jimawa baccin wahala ya kwashe ta. Sanyin asuba ne ya tashe ta, cizon sauron da tasha jiya da kukan da tay ya haifar mata da zazzaɓi, cikin rawar ɗari ta sauko daga kan katifar ta dunk'ule a waje ɗaya tana numfarfashi, kayanta data shimfid'a a ƙasa ta rarumo ta rufe jikinta saboda sanyin da take ji. Sai wajen ƙarfe 7 su Iman suka tashi daga bacci, kamar wasu ƴaƴan karnuka da faɗa suka tashi, gashi sun tsutstsula fitsarinsu a kwance, Allah ya taimaki Neehal ba su ɓata ta ba. Da ƙyar Neehal ta iya tashi ta ƙarasa toilet ɗin dake ɗakin ta yi fitsarin da ya matseta, da ƙyar take tafiya saboda jiri, ga yunwa dake nuk'urk'usar hanjin cikinta, rabonta da abincin tun lunch ɗin jiya da ta yi a gida.






Aunty Fauziyya kamar kullum tana jiyo hayaniyar yaranta ta shigo ɗakin da sauri, dan kullum da hakan take gane tashinsu, Neehal na rakub'e jikin kayanta tana ta rawar sanyi, cikin muryar marasa lafiya ta ce "Ina kwana Aunty." Wani mugun kallo Aunty Fauziyya ta watsa mata, a harzuk'e tana zazzaro ido kamar sabuwar kamu ta ce "Yana gidan Ubanki shi kwanan." Neehal bata kuma cewa komai ba, ita kuma Fauziyya ta ja ƴaƴanta sukai toilet, wanka ta musu ta shirya su cikin uniform ɗinsu, sannan suka fita falo dan karyawa. Uncle Umar ya ce wa Fauziyya "Ina Neehal ɗin, itama ta fito ta karya mana." A fusace Aunty Fauziyya ta ce masa "Ka san yar gold ce bata tashi ba har yanzu." Sai wajen ƙarfe tara Aunty Fauziyya ta ƙwalawa Neehal kira lokacin Uncle Umar ya fita, cikin hanzari Neehal ta taso dan wani bala'in tsoron matar take ji, k'osan Talatin ta bata da wani ɗan bread da ruwan bunu rabin ƙaramin cup a matsayin breakfast. Neehal ta bi abun da aka bata da kallo sannan ta fara ci tana yamutsa fuska saboda bakinta babu daɗi, yunwa ce kawai ta sa take ci, ga shi ita k'osai ba mutuminta ba ne, gara ma bread ɗin. Ruwan bunun kuwa ko kurb'a ba ta yi ba, dan tasan baza ta iya sha ba. Bayan ta gama cikin faɗa Aunty Fauziyya ta ce "Tunda ciki ya ɗauka, sai ki tashi ki haɗa kayan nan, ki kai tsakar gida ki wanke, sannan ki dawo ki share mun falo ki yi mopping, ɗakin da kika kwana ma haka." Cikin sanyi Neehal ta ce "Aunty ban da lafiya, kuma ban iya b......." "Ai ko cutar mutuwa kike yau sai kin mun aikin nan, dan Ubanki Jakar uwarki ce ni zan dafa miki ki ci kina daga kwance, zaki tashi ko sai na miki dukan mutuwa a gidan nan." Jiki na b'ari Neehal ta tashi ta fara haɗa kayan, duk da zazzaɓin dake damunta, amma saboda tsoron Fauziyya da take ji dole ta yi. Ba ta taɓa wanke_wanke ba a rayuwarta, sai a gidan Mama ne ma idan ta ci abinci Mama take sata ta dauraye flate ɗin da taci abincin. Ai kuwa Fauziyya ta sha asarar omo, gashi kafin ta gama ta jik'a jikinta jagab da ruwa, a haka ta yi share_sharen da mopping, Fauziyya kuwa tuni ta fice yawon mak'ota. Tana gama aikin ta yi daki ta kwanta akan tiles, zazzaɓi mai zafi ne ya rufe ta. Da Fauziyya ta dawo ta ga b'arnar Omon da Neehal ta mata, ta dinga surfa mata ashariya da masifa, da dukanta ma zata yi wata makociyarta data shigo ta hanata, ganin yanda Neehal ɗin take rawar sanyi. Da rana ma kiranta Aunty Fauziyya ta yi ta bata wata shinkafa da wake ƴar kaɗan a roba, ko man kirki babu a ciki. Lauma ɗaya Neehal ta yi ta ture ta koma ɗaki ta kwanta, Fauziyya ranar wuni ta yi tana zagin Neehal. Da daddare Uncle Umar ya lek'a ɗakin da Neehal take ganin Shiru_shiru bai ji motsinta ba tunda ya dawo, ganin ba ta da lafiya ya bata panadol da Paracetamol ta sha, ya kuma kawo mata lemo da ayaban daya shigo gidan da su har ɗaki, ta kuwa ci ayabar ba laifi dan tana sonta sosai. Fauziyya tayta kumbure_kumbure tana huci kamar zata naushi iska ganin abun da Uncle Umar ya yi wa Neehal. Washegari ma Neehal ce ta yi wanke_wanke da shara, jikin nata ya yi sauƙi tunda ta sha magani, sai dai bata warke sumul ba, ranar kam sai da Fauziyya ta mare ta akan ta'adin omon data mata. A daren Ranar Uncle Usman ya zo gidan yi musu sallama dan zai koma garin da yake aiki ne. Tsaraba sosai yayo wa Neehal da su Aiman ta sweet da chocolate, da zai tafi Neehal tai ta Kuka, Aunty Fauziyya ta tab'e baki a ranta ta ce 'Munafurcin banza.'








Tun daga ranar Neehal ce take wanke_wanke da shara da mopping da aiken gidan, yanda ka san baiwa haka Fauziyya ta mayar da ita, ga masifa da tsawa da bala'i. Wani matsifaffen tsoronta Neehal take ji, gashi idan Uncle Umar ya dawo ta haɗa wa Neehal sharri a gurinsa wai ta zage ta, haka zai zo yay mata masifa shi ma kamar zai dake ta. Kullum Neehal sai ta ci kuka ta gode Allah, kuma duk wani abu na amfani da Aunty A'isha ta sako mata acikin kayanta Fauziyya ta k'wace, kama daga MacLean, sabulan Wanka hatta bargonta duk ta k'wace. Yau kwanan Neehal goma sha biyu a gidan Uncle Umar, amma gaba-d'aya ta rame ta yi duhu saboda wahala, baza ka taɓa cewa itace yar gatan Ummanta da Abbanta ba. Kitson dake kanta ya tsufa ya dugurguje, ga farcenta ya fara taruwa, ta saba duk ran Friday Aunty'nta tana yanke mata, haka ma Mama idan tana gidanta, nan kuwa wanka ma ba kullum ake barinta ta yi ba. Ga rashin ishashshen abinci, abincin da yaro ɗan shekara biyar zai ci shi ake bata, shima kuma mara daɗi. Kullum da safe tana jin k'amshi ana soya k'wai da dankali amma ita ko ganin shi bata yi, haka ma naman miya ba'a bata ko gutsire. Misalin ƙarfe Uku na yamma Neehal ce tafe tana ta zuba sauri saboda gargadi'n da Aunty Fauziyya na mata akan kar ta daɗe, kayan miya zata siyo mata a can bakin titi, kuma daga gida zuwa bakin titi da ƴar tafiya, gaba-d'aya a gajiye take saboda aikin da tasha yau har da wankin kayanta ta yi, ga rana da ake k'walla wa a garin, gashi ba ta ci abincin rana ba kuma tana jin yunwa sosai gami da ƙishirwa, Aunty Fauziyya ta ce sai ta siyo mata kayan miyar sannan zata ci abincin. Ta shiga wani layi wanda daga shi sai titi, ta ga wani k'aton gida mai kyau, wani kyakkyawan matashi da ba zai wuce shekara 25 ba ne ya fito daga ƙaramar ƙofar gidan hannunsa ɗauke da robar ruwan faro mai sanyi. Tsayawa Neehal ta yi ta ƙura wa ruwan hannunsa ido tana maida Numfashi saboda gajiya, sau ɗaya matashin ya kalleta ya ɗauke kai ya nufi Motar dake fake a gaban gidan, Neehal ganin haka yasa ta ƙarasa kusa da shi da sauri ta ce...........✍️
















*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:47] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*












_By_
_Zeey Kumurya_














*2️⃣9️⃣*
















Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*


















..........."Uncle please zan sha ruwa." Kallonta ya yi fuska a sake ya ce "Oh sorry Dear take it." Neehal ta karb'i ruwan da yake miƙa mata tare da faɗin "Thank you." Murmushinsa Mai kyau ya mata, Neehal ta buɗe robar ruwan da sauri har tana yar da kuɗin kayan miyan bata sani ba, kai robar ta yi bakinta zata sha ruwan ya katse ta da sauri ta hanyar faɗin. "No, go there ki zauna sai ki sha." Ya ƙarashe maganar tare da nuna mata wani dakali dake kofar gidansu. Da sauri Neehal ta ƙarasa ta zauna ta fara quqqutar ruwan, sai da ta shanye tass sannan ta yarda robar. Matashin yana tsaye yana kallonta, haka kawai ya ji ya kasa tafiya, Neehal ta dafe cikinta saboda k'ullewar da ya fara mata saboda yunwar da take ji. Cike da tausayawa Matashin ya sunkuya ya ɗauki kuɗin da ta yar a ƙasa ya ƙarasa inda take, cikin tausayinta da ya d'arsar masa a zuciya lokaci ɗaya ya ce "Are you Ok?" Neehal ta girgiza masa kai ta ce "I'm felling hungry." Ya ce "Okay, sorry, wait for me here, I will come now." Neehal ta gyaɗa masa kai tana ƙara dafe cikinta. Cikin 5 minutes ya shiga gidansu ya fito hannunsa ɗauke da Cake wanda aka yi rapping ɗinsa, sai kuma lemon jarka guda ɗaya. Miƙa mata ya yi ta karb'a da sauri tare da kallonsa, a hankali ta ce "Thank you so much." Sannan ta fara cin Cake ɗin, ƙura mata ido ya yi ganin yanda take cin cake ɗin cikin nutsuwa tana lumshe ido, ita kuwa Neehal daɗi Cake ɗin ya mata ba kaɗan ba. Sai da ta kusa cinyewa sannan ta ɗauki leman ta sha fiye da rabin jakar, ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta ce "Alhamdulillah." Sai kuma ta miƙe zumbur kamar wadda aka tsikara ta fara ƙoƙarin tafiya, katse ta ya yi ta hanyar faɗin "Zo ki ɗauki sauran mana." Neehal ta ce "Na k'oshi ne." Ya ce "Are you sure?" Ta gyaɗa masa kai, ya ce "To ki tafi da shi gida anjima sai ki ci." Neehal ta waro ido waje ta ce "Aunty zata dake ni idan na je da shi gida." Miƙa mata kuɗin data yar ya yi ya ce "You forget." Neehal ta karb'a da sauri ta wuce. Cake ɗin data bari da lemo ya ɗauka ya shige Motarsa, yana fita titi ya hango ta a gurin mai kayan miya, an yi sa'a ita ma ta juyo suka haɗa ido, d'aga mata hannu ya yi yana murmushi itama ta mayar masa da murmushin tare da d'aga masa hannun, a gurin ya samu almajiri ya bashi ragowar Cake ɗin da lemon. Cikin sauri Neehal ta siyi kayan miyan ta koma gida, zuciyarta cike da tsoron Aunty Fauziyya, wani ɓangaren na zuciyarta ta kuwa farinciki take yau ta ci Cake ta sha lemo. Da masifa Aunty Fauziyya ta tare ta, ita dai tay shiru kawai tana kallonta tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Aunty Fauziyya cikin bala'inta ta ce "Shegiyar yarinya mai kama da aljanu, ana miki magana ki tsare mutum da wasu idanunki kamar na mage." Ta kamo kunnen Neehal ta murd'e da ƙarfi tana faɗin, "Gobe ma in ƙara aiken ki ki kuma zuwa ki zauna." Neehal ta saka kuka saboda zafin da ta ji a kunnenta, Aunty Fauziyya ta dungurar da ita a wurin tare da daka mata tsawar ta rufe mata baki. Kayan miyan ta wanke ta bata ta kai markad'e, ko tunanin bata abinci bata yi ba gashi har la'asar ta yi. Cikin mintuna ƙalilan Neehal ta dawo daga kai markad'en da yake anan mak'otansu ake babu nisa. Sai a sannan Aunty Fauziyya ta bata abinci a wani ɗan kwano, jallop ɗin shinkafa ce da cavage ce akai. Neehal ta kai abincin ɗaki ta ajiye a bayan kayanta, dan a koshe take. Aunty Fauziyya bata barta ta huta ba, sai da ta bata wankin uniform ɗin su Aiman, Neehal ta jijjik'a ta shanya dan ba wani iya wanki ta yi ba, sai dai tai ta goggoga sabulu ajikin kaya in ta ga ya yi kumfa sai ta d'auraye ta shanya. Bayan isha'i tana zaune a ɗaki tana yi wa su Aiman Homework, dan Yaran babu abun da suka iya sai dambe da zagi, ashar kala_kala sun iya narkawa kamar ƴaƴan maguzawa. Tun da Neehal ta zo gidan ita take musu Homework da Assignment ɗin islamiyya. Jin Uncle Umar ya shigo ta miƙe ta shiga falon ta gaishe shi, Allah ya so Aunty Fauziyya tana ɗakinta da sai ta k'ulla mata wani sharrin a gurinsa. Bayan ya amsa ta ce "Uncle Ina son na koma School da Islamiyya." Uncle Umar ya ɗan bata rai ya ce "To je ki sai na duba." Neehal ta tashi ta koma ɗaki ta cigaba da abun da take. Aunty Fauziyya ta fito daga ɗakinta tana yamutsa fuska ta ce "Me na ji yarinyar can tana ce maka ne?" Uncle Umar ya ce "Wai Makaranta take so ta koma." Aunty Fauziyya ta haɗe sosai ta ce "Kai kuma saka ta a makarantar zaka yi?" Ya ce "To ya zan yi, tunda Allah ya ɗora mun." "Ka dai ɗora wa kanka." Aunty Fauziyya ta faɗa tana keɓe fuska. Uncle Umar ya ce "Hmmm, tunanin ma makarantar da zan kaita nake, amma ina ga makarantar su Aiman zan kai ta." "Me? Makarantar su Aiman fa ka ce, dubu ashirin da biyar ɗin zaka biya mata? Tab'! To wallahi ka nemarwa kanka sauƙi, ka nemi Government School ka kaita." Uncle Umar ya ce "Ai na ga babu Government School a kusa ne shi ya sa." Aunty Fauziyya ta ce "Ga ta nan ana ginawa, ka bari idan an gama ginin sai ka kai ta mana." Daga haka suke rufe wannan chapter, suka kama wata. Washegari bayan Neehal ta gama shan akinta kamar kullum aka aike ta siyan kayan miya, yau ma ba ta ci abinci ba ta tafi, gashi abun da bata ci ma Aunty Fauziyya ta yi wato tuwo, tuwon ma miyar kuka.








Ta zo dai_dai layin da suka haɗu da mutumin jiya wanda ta rad'a masa suna *Uncle mai kirki* , har ta wuce gidan ta dawo ta tsaya a ƙofar gidan tana kallon gidan, a hankali ta ƙarasa jikin ƙofar ta fara knocking, 2 minutes tana tsaye sannan aka buɗe ƙofar. Faɗaɗa fara'a ta yi sosai kamar yadda shi ma yake fara'ar cike da mamakin ganin ta, yana sanye cikin ƙananan kaya wanda suka masa kyau sosai, sai tashi daddad'an k'amshinsa yake. Neehal ta ce "Ina yini." Yana murmushi ya ce "Lafiya k'alau." Juya wa ya yi ya ce "Come in." Neehal ta tsaya ba tare data bishi ba, ya juyo ya ce "Ya kika tsaya? Ki shigo mana." Neehal ta girgiza masa kai alamun a'a, ya ce "Why?" Ta ce "Ina jin tsoro." Da ƙyar ya lallaɓa ta ta shiga gidan, a BQ yake har ciki ta shiga ta zauna a falo a d'arare, haɗadd'iyar pride rice ya kawo mata a plate da bottle water da juice, da murna Neehal ta karb'a ta fara ci. Zama ya yi yana kallonta cikin tausayinta. Sai da ta ci ta yi ƙat sannan ta ce "Uncle ina Mamanka?" Ya ce "Tana cikin gida." Ta ce "Nan part ɗinka ne?" Ya ce "Ehh." Shiru ta yi tana ƙarewa falon kallo, cikin kulawa ya ce "What is your name?" Neehal ta ce "Neehal." Ya ce "Wow Nice name, real name ɗinki fa?" Ta ce "Fateemah." Ya ce "Wow! My mother's name." Neehal ta ce "And you?" Ya yi murmushi ya ce "Ahmad." gyaɗa kai ta yi tare da tashi da sauri ta ce "Zan tafi Uncle, zan siyo wa Aunty kayan miya, idan na daɗe zata zane Ni." Ya ce "To Princess, gobe ma zaki zo ko?" Neehal ta yi shiru can kuma ta ce "Ehh." Har bakin titi ya raka ta sannan ya dawo gida. Yau ma data koma gida sai da ta sha bala'in Aunty Fauziyya. Tun daga wannan ranar kullum sai aka aike ta sai ta biya gidansu AHMAD, ya bata lafiyayyen abinci ta ci da drinks, wataran kuma ice cream da snacks yake bata, choculate da sweet kam kullum sai tasha su ta more, idan ta koma gida kuma Aunty Fauziyya tay ta mata masifa, wataran har da duka akan dad'ewar da take, amma ko sau ɗaya bata taɓa tambayarta inda take zuwa ba. Idan ta bawa Neehal abinci sai ta k'ulle a leda ta faki idon Aunty Fauziyya ta fita ta bawa almajiri, tunda yanzu kullum a k'oshe take wuni, abincin dare ma kullum sai ta rage kaɗan take ci. Breakfast kawai take yi full a gidan. A hankali shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Neehal da Ahmad, kullum ta zo yana mata tambayoyi a game da rayuwarta, a haka ya gane marainiya ce kuma bata haɗu da uwar riƙo ta gari ba, hakan ya ƙara masa tausayinta a zuciyarsa sosai, kullum yana mata ƙarin haddarta na Alqur'ani tunda Uncle Umar ya ƙi saka ta a Islamiyya da School, haka karatun boko kullum yana mata lesson, sai ta yi fiye da awa biyu a gidansu, ta koma gida kuma ta ci duka, amma duk da haka gobe sai ta karsi zuwa.








Yau Sunday da misalin ƙarfe biyu na rana Neehal tana zaune ita kaɗai a ɗaki tana bitar haddarta, su Aiman kuma sun tafi Islamiyya. Uncle Umar ma baya nan, duk da yau Sunday amma ya fita tun safe shagonsa da yake sayar da kayan masarufi, kuma ba ya dawowa sai dare, kullum haka yake dama, Monday to Friday ma bayan sun tashi daga School ɗin da yake koyarwa can shagon yake wuce wa. Aunty Fauziyya ta tak'wala wa Neehal kira, Neehal ta miƙe da sauri ta fito waje. Aunty Fauziyya tana mata wani mugun kallo ta cilla mata kuɗi ta ce "Ɗauki kuɗin nan, ki je ki siyo mun kayan miya, kuma yau ma ki biya yawon naki da kika saba, wallahi dukan dana miki jiya Nafila ne akan wanda zan miki yau idan kika daɗe. Neehal ta ɗauki kuɗin ta koma ɗaki ta ɗauko Hijab da hula ta saka sannan ta fito ta tafi. Duk da gargadi'n da Aunty Fauziyya ta mata sai da ta biya gidansu Ahmad, dan dukan Aunty Fauziyya zuwa yanzu har jikinta ya saba da shi. Kamar kullum bayan ta yi knocking ya zo ya buɗe mata ƙofa ta shiga. Yau ba BQ ya kai ta ba, ainihin cikin gidan ya nufa da ita. A falon gidan ya zaunar da ita sannan ya nufi kitchen yana kiran sunan Mamy, Mamy wadda takasance ƙanwar mahaifiyar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login