Showing 123001 words to 126000 words out of 262509 words
Chapter 42 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
ce mu zo yanzu kawai na duba jikin nata." Mama ta ce "Har tafiyar ta zo? Sai yaushe kuma zaku dawo?" Haneefah ta ce "Sai week ɗin da za'ai resuming School." Mama ta ce "To Allah ya kiyaye hanya, ki hau sama tana ɗakinta." Ta amsa sannan ta wuce upstairs. Tana kwance rigingine tana latsa waya Haneefah ta shigo ɗakin da sallama. Ta d'ago kanta da sauri ido waje ta ce "Amarya!" Haneefah ta ce "Na'am Ango." Neehal ta tashi zaune tana murmushi ta ce "Welcome dear." Haneefah ta zauna a bakin gado kusa da ita ta ce "Yawwa ya jikin naki? Gaskiya kina jin jiki Besty duk kin rame." Neehal ta ce "Da sauqi, ai na yi kyan gani ma yanzu." Haneefah ta ce "Sannu, Allah ya ƙara sauƙi yasa kaffara ne." Ta ce "Amin ƙawata, ina Yah Faruq?" Haneefah ta ce "Yana cikin Mota, tare muka zo." Neehal ta ce "Shine kuma kika bar shi a waje, ki ce ya shigo mana." Ta ɗauko wayarta a jaka ta kira shi ta ce ya shigo ciki. Neehal ta ce "Ko ke fa, ya amarci?" Haneefah ta ce "Mu sauka ƙasa ki tambayi Ya Faruq zai baki amsa." Neehal ta yi murmushi. Sun ɗan taɓa hira Haneefah ta sanar mata tafiyarsu Kogi, Neehal ta musu fatan sauka lafiya. Sannan suka sauka ƙasa inda suka tarar da Ya Faruq da Mama suna hira. Haneefah ta ɗauki juice ɗin dake gaban Ya Faruq tana duban Mama cikin zolayarta ta ce "Mama shi ne ni ba'a kawo mun ba sai shi?" Mama ta ce "Ɗana kawai na sani, ke ai gidan ba baƙon ki ba ne." Haneefah ta ce "Allah sarki ni Mama ta daina yina yanzu." Faruq ya yi murmushi tare da yiwa Haneefah gwalo a fakaice. Sannan ya dubi Neehal suka gaisa yay wa Neehal ya jiki yana tsokanarta gawa ta ƙi rami. Ana kiran sallar isha'i suka tafi saboda daga nan gidan iyayen Faruq za su biya. Bayan fitarsu Mama ta zubowa Neehal abinci ta tilasta mata ta ci, tunda ta ji sauƙi har tana iya surutu abincin ma zata iya ci. Tana tutturo baki ta fara cin abincin kamar bata so, kaɗan_kaɗan take tsakurar sa tana kaiwa baki kamar mai irgawa, gashi Mama ta ce sai ta cinye wanda ta zubo mata duka. Tana zaune ita kaɗai a falo fiye da mintuna ashirin akan abincin da ba wani yawa ne da shi ba, Ameen da Hajiya suka shigo Falon. Hajiya ta ce "Ke kaɗai ina Faɗiman? ta bar ki ke kaɗai kuma ke da ba lafiya ba" Ciki_ciki ta ce "Tana sama." Hajiya ta ce "To ya jikin naki?" Ta ce "Da sauqi." Hajiya ta ce "Ke gashi kin warware, ita kuwa waccan da na je dubowa tunda na je tana nad'e akan gado, sai masu aiki ne ke ta kai kawo." Neehal ta saci kallon Ameen wanda ya zauna akan kujera yana kallon Hajiya. Ta mayar da duban ta ga Hajiyan ta ce "To ai bata da lafiya ne." Hajiya ta ce "Duk da rashin lafiyar, amma kuma da rakin tsiya ma, sai langwab'ewa take kamar lagwani." Neehal ta ce "Dan ciwon ba'a jikin yake ba dole ki ce haka." Hajiya ta wuce sama bata tanka ba. Ameen ya tashi ya koma hannun kujerar da Neehal take kai ba tabo ba fallasa ya ce "How was your body?" Kanta a ƙasa ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Na ga kin ji sauqi har da magana haka." Ta ce "Ya jikin Aunty Hafsat?" Ya ce "Da sauqi." Ta ce "Allah ya ƙara sauƙi, ka yi mata sannu." Idansa akan abincin da take ta juyawa da spoon ya ce "Zata ji." Suka yi shiru dukan su, ita bata cigaba da jin abincin ba, shi kuma ya zuba mata ido. A hankali ta ji ya ce "Ki ajiye abincin mana idan kin k'oshi." Ta ɓata fuska cikin shagwab'a ta ce "Mama ta ce dole sai na cinye, kuma da ƙyar nake ci bakina babu daɗi." Sai kuma ta kalli fuskarsa iya gaskiyarta ta ce "Yaya ka cinye sauran Please kafin ta sauko." Ya ce "Uhm, jagwalgwalon naki zan ci?" Ta kalli abincin dan ita bata ga wani jagwalgwalawa da ta yi ba, ta turo baki ta ce "Taimakona fa zaka yi Please." Ya yi wani ɗan murmushi ya ce "Sai dai in zaki bani a baki." Ta kalle shi da sauri ta ga fuskarsa babu alamun wasa ya sha mur, kamar bashi ya gama maganar yanzu ba." Ta yi shiru ta rasa me zata ce, shi kuma ya tab'e baki irin zaɓi ya rage natan nan." Jin taku ta d'aga kai ta kalli steps, ganin Mama ce ke saukowa sai ta ɗibi abincin ta kai baki tana yamutsa fuska kamar mai cin kashi. Mama ta dube ta bayan ta ƙaraso cikin falon ta ce "Tashi ki kai kitchen ki rufe, cin ɗan wannan abincin fiye da 30 minutes kamar mai cin gandar da bata gama dahuwa ba." Ta miƙe da sauri ta nufi kitchen ɗin. Ameen ya raka ta da ido. Mama ta ce masa "Ya jikin Hafsan?" Ya ce "Da sauqi." Ta ce "Allah ya ƙara sauƙi, da safe Insha Allahu zamu zo ni da Dad mu duba jikin nata." Ya ce "Allah ya kai mu." Daga haka ya miƙe yay mata sallama ya tafi. Bayan Neehal ta yi Sallah suka yi waya da Sadik, sannan ta kwanta. Kafin ta kai ga yin baccin Mama ta shigo ta yi mata allura wanda da ƙyar ta bari aka yi dan bata son allura ko kaɗan, gwara ta sha magani duk da shi ma ba wani son shi take ba, amma duk da gwara shi sau dubu akan allurar. Tana cikin rakinta da shagwab'arta bacci ya yi awon gaba da ita.........✍️
*By*
*Zeey kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*5️⃣2️⃣*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
..........A hankali take tafiya kamar bata son taka ƙasa, as always shi kuma tunda ya hango ta ya ƙura mata ido. Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon ta zauna a kan carpet ɗan nesa da shi tare da kawar da kanta gefe, su Afrah kuwa gurinsa suka nufa, wayoyinsa guda biyu ya basu bayan ya kunna musu game, cikin murna suka karb'a suka fara yi. Ba tare da ta kalli inda yake ba kamar an mata dole ta ce, "Ina yini." Bai amsa ba sai tashi da ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna ganin yanayinta ya kira ainihin sunanta. "Fateemah." Ta d'ago ta dube shi cikin mamaki dan ko da can bai taɓa kiran ta da Fateemah ba. A hankali ta ce "Na'am." Ya ce "Jikin naki ne har yanzu?" Ta girgiza masa kai, ya ce "To me ya faru na ga ranki a ɓace, ko nine ba kya son gani ko kuma kawo miki su Afrah da na yi ne ba ki ji daɗi ba?" Ta ɗan saki fuskarta ta ce "A'a ba komai Uncle." Ya ƙara matsowa kusa da ita ya sassauta murya ya ce "To me yasa ba kya farin ciki, Please be happy, bana so na ganki a haka Pleaseee.." ya ƙarashe maganar da jan kalmar ƙarshe cikin wani irin wani salo da yasa ta ji wani iri a jikinta. Ta ɗan yi murmushi tana kallon shi ta ce "To na yi Uncle, ya kuka baro Mamy?" Shima yana murmushin ya ce "Lafiya k'alau, tana ta tambayar ki, ta yi zaton ma tare zamu zo." Bata kuma cewa komai ba ta miƙa masa wayarsa dake hannunta, ya karɓa tare da faɗin. "Oh, na ma manta, thank you." Yana ƙoƙarin zira wayar a aljihu ba tare daya latsa ta ba ta ce "An kira ka fa." Ta yi maganar cikin ɓata fuska. Cikin mamaki ya zaro wayar ya duba dan ba permanent sim ɗinsa ba ne a ciki bai yi tunanin wani zai kira shi a wayar ba. Tab'e baki ya yi bayan ya ga mai kiran ya saka wayar a aljihu ba tare da ya bi bayan kiran ba. Neehal ta ɗauke kanta daga kallon sa ta ɗan turo baki gaba. Ya saka tafin hannunsa ya taɓa goshinta ya ce "Har yanzu da sauran zazzaɓi a jikinki Princess, kina shan magani kuwa?" Ta ce "Uhm." Kawai. Ya ƙura mata cikin nazartar ta, ya lura kamar akwai abun da ke damunta tunda ta fito, ko kuma wacce ke cikin ɓacin rai. Ya ɗauke hannunsa daga goshinta ya d'ago hab'arta be serious ya ce "Neehal me yake damunki?" Ta lumshe idonta tare da girgiza masa kai tana ƙoƙarin saka hannunta ta cire nasa daga fuskarta. Ya riƙe hannun nata ya ce "Please talk to me Princess, ko kina so ki ganni a cikin damuwa nima?" Ta yi shiru. Ya ƙara tambayar ta, nan ma bata tanka masa ba. Ya sauke numfashi ya cire hannunsa daga hab'arta tare da sakar mata hannunta ya ce "Okay, Good bye Dear, tunda na fuskanci kamar nine ba kya son gani." Ta buɗe idonta da sauri sai hawaye sharr wanda bata san sanda suka zubo ba. Ya dafe kansa tare da faɗin "Oh my God, Dan Allah Princess me yake damunki ne, ko na miki wani abun ne da baki ji daɗi ba?" Ya yi maganar a ɗan ruɗe yana kallon ta. Ita kanta bata san me ya saka ta a cikin wannan yanayin ba, kuma ta yi ƙoƙarin ta danne kar ya fuskanta amma ta kasa. Ta turo baki gaba sosai ta ce "Ka ce mun tunda Maman twins ta rasu baka ƙara kula wata mace ba, and now kuma naga wata ta kira ka harda text, who is she?" Ta yi maganar iya gaskiyar ta. Sai yanzu ya gane bakin zaren, shi dariya ma ta ba shi ba kaɗan ba, amma yanda take a sama ɗin nan in ya dara ya san da matsala, musamman yanda ta tsare shi da kyakkyawan idanunwan nan nata tana jiran amsa. Ya danne dariyarsa ya ce "Oh wai Jamila, she is my cousin, ƴar ƙanwar Dad ce." Ta juya masa idonta ba tare da ta ce komai ba, amma bata gamsu da abun da ya faɗa ba. Ya yi ɗan murmushi tare da matsowa daf da ita, ya kai bakinsa dai_dai saitin kunnenta ya ce "Princess ce kaɗai a zuciyar Uncle ɗinta, since, now and for ever, daga ita kuma babu ƙari." Ta rufe fuskarta da hannunta cikin jin kunyar gano ta da ya yi. Ya yi ƴar dariya ya ce "Ashe Babin Uncle ta fara sonsa har da su kishi?" Ta juya masa baya a shagwab'e ta ce "Ni ba kishi nake ba?" Ya ce "To me kike? Jealous? Kamar zata yi kuka ta ce "Ni fa Allah ba kishi nake ba." Ya juyo da ita da hannunsa ya sa tafin hannunsa ya share mata hawayen data zubar d'azu, zuciyarsa fess da yanda ta nuna tana kishin nasa. Ya zubawa fuskarta ido yana jin kamar ya mayar da ita cikin jikinsa saboda k'auna. Jin maganar Afrah a kusa da shi yasa ya ɗauke idonsa daga kallon ta ya mayar kan yarinyar da take miƙo masa wayarsa tana faɗin "Daddy kiran Sallah ake a cikin wayar." Ya karɓa ya ce "To aje a yi alwala a yi Sallah." Ta ce "Tom Daddy." Ya yi mata kiss a goshi itama ta mayar masa tana dariya sannan ta nufi upstairs da ɗan gudunta tana cewa Amrah sai ta riga ta hawa saman. Jin haka itama Amrah ta kawo masa ɗaya wayar ta bi bayan ta. Neehal ta bi su da kallo cikin k'auna. Ya ce "Princess zan wuce?" Ta juyo ta ce "Sai yaushe?" Ya ce "Gobe da safe Insha Kafin na wuce." Ta ce "Allah ya kai mu." Ya miƙe tsaye yana faɗin "Amin." Itama miƙewar ta yi, ya ja karan hancinta ya ce "Bye, I love You." Ta ce "Allah ya kiyaye." Ya ɓata fuska tare da langwab'ar da kansa ya ce "Ba feedback?" ta yi murmushi bata ce komai ba, ya ce "Shikenan." Ta ce "Thank you for coming, and..." "Kawo miki twins ko?" Ya ƙarasa mata dan ya san haka zata faɗa. Ta yi murmushi tare da gyaɗa masa kai. Ya yi mata murmushin nan nasa mai kyau tare daga mata hannu sannan ya juya ya tafi. Ta sauke ajiyar zuciya bayan ya fice, a ranta tana faɗin 'Ko sallama bai yi da ƴaƴansa ba.' Ta juya ta haye upstairs, ɗakin Mama ta shiga ta tarar da ita tana ƙoƙarin shimfid'a darduma, su Afrah suna taya ta. Amrah ta ce mata "Aunty ina Daddy? Ya tafi?" Ta ce "Eh ya tafi gidan Mamy, amma gobe da safe zai dawo." Mama ta ce "Ki je ki yi alwala ki zo ki yi Sallah, tunda kin warke sai ki shiga kitchen ki yi masa something special gobe in ya zo sai ki ba shi ya tafi da shi" Ta ɓata fuska ta zauna a bakin gado ta ce "Mama ban fa warke ba, cikina ma tun safe ya fara mun ciwo." Mama ta ce "Allah ya sauwaqe." Daga haka ta tayar da Sallar ta. Miƙewa ta yi itama ta shiga toilet ta fito ta tayar da Sallar.
Daf da Magriba Sadik ya shigo gidansu a gajiye, a falon Maamah ya tarar da Hajiyarsu da Batul, Maamah kuma tana bedroom ɗin Abba tana gyara saboda ta karɓi girki da yammar nan. Ya zauna a kusa da Hajiya cikin mamakin ganin ta ya ce "Ƴar tsohuwar nan ke ce a gidan namu? Zuwa babu sanarwa, ai da kin faɗa dana taho miki da tsarabar goruba." Ta rank'washi kansa ta ce "Giginya zaka siyo mun ba goruba ba, ɗan nema kawai." Ya yi murmushi tare da miƙewa yana faɗin "Kin yiwa kanki tunda ba kya so, bari na shiga ciki na fito." Ta ce "To a fito lafiya." Batul ta ce "Sannu da zuwa Yaya." Ya ce "Yawwa, ina Maamah?" Ta ce "Tana ɗakin Abba." Bayan ya dawo daga masallaci Maamah ta kawo masa abinci yana ci suna hira da Hajiya har ta sako masa zancen Neehal inda ta ce "Abubakar ashe ka fara yunƙurin yi mini kishiya ban sani ba?" Ya yi murmushi ya ce "Har kin samu labari kenan?" Ta ce "Shine ma abun da ya kawo ni gidan nan yau?" Ya ce "Kamar ya Hajiya, ko duk kishin ne?" Ta sanar masa yanda suka yi da su Abba da Kawu a tak'aice." Sadik ya ajiye cokalin hannunsa fuskarsa na nuni da damuwa ya ce "Hajiya wannan zancen fa ba gaskiya ba ne, shati faɗin mutane ne kawai." Hajiya ta ce "Koma mene ne dai mahaifinka ya ce zai bincika, in ma gaskiya ne in ma ƙarya ne duk zai gano, amma kafin nan ka fara tuntubar ita yarinyar da zancen, idan har tana sonka da gaskiya saboda Allah kuma ba su da wata manufa akan kisan ake yi zata faɗa maka gaskiya da bakinta." Sadik ya marairaice ya ce "Insha Allahu Hajiya zan tambaye ta, Amma dan Allah Hajiya ko me zai faru karki bari su Abba su hana ni Aurenta, ina sonta sosai wallahi." Maamah dake sauraren hirar tasu cike da tausayin ɗan nata ta ce "Sadik, ka yi addu'a kawai, idan Alkhairi ce a gare ka Allah ya baka ita, idan kuma ba Alkhairi ba ce Allah ya baka wadda ta fita, sautari wani abun da muke so ba shine Alkhairi a gare mu ba, rashin sa a tare mu ya fi zama Alkhairi." Ya kalli mahaifiyar tasa ya ce "Shikenan Maamah, Insha Allahu zan cigaba da addu'a akan wacce nake yi." Hajiya ta ce "Shi ya fi dai, muma zamu taya ka da addu'ar, abun da mahaifiyarka ta faɗa gaskiya ne." Ya yi shiru cikin damuwa, amma a cikin ransa yana jin ba zai iya rabuwa da Neehal ba, kuma Insha Allahu itace matarsa."
Bayan su Neehal sun idar da Sallah ba jimawa Ameen ya zo gidan. Su Afrah suka tafi da gudu gurinsa suna faɗin "Oyoyo Uncle." Ya d'aga su ɗaya bayan ɗaya ya shilla yana murmushi. Sannan ya kamo hannunsu zuwa bakin gado ya zauna ya gaishe da Mama. A hankali Neehal ta dube shi ta ce "Ina yini Yaya." Ya kalle ta ya ce "Lafiya k'alau." Ta ce "Ya jikin Aunty Hafsah?" Ya ce "Da sauqi, ya naki jikin?" Ta ce "Alhamdulillah." Ya mayar da duban sa ga su Afrah ya ce "Yaushe kuka zo?" Afrah ta ce "D'azu Daddy ya kawo mu." Ya shafi kuncinsu bai ce komai ba. Mama ta ce masa "Ya aikin naku? Ya ce "Alhamdulillah, Hajiya ta wuce kenan?" Mama ta ce "Eh, tun safe ba ku yi waya ba ne?" Ya ce "Na ga missed call ɗinta tun safe, na kira ta kuma d'azu bata ɗauka ba." Mama ta ce "May be time ɗin suna hanya, amma mun yi waya kafin Magriba ta ce sun ƙarasa." Ya ce "Okay." Mama ta dubi Neehal ta ce "Zubo masa abinci, na san da ƙyar in ka ci tunda Hafsah bata da lafiya, suma su Afrah ki zubo musu." Ta ce "Toh." Tare da miƙewa ta fice. Ya ce "Allah yasa ina cin abin da kuka dafa." Mama ta ce "Koma mene haka zaka ci, har yanzu baka daina zaɓe zaɓen abinci ba ko Ameen? To tuwo na yi, itama Neehal yanzu ta gama cewa baza ta ci ba, na ce mata ta kwana da yunwa kuwa dan babu mai sake mun wani sabon girki yanzu, tunda ku tsurfar ku ta muku yawa." Ya yi ɗan murmushi tare da miƙewa ya fice daga ɗakin. Kitchen ɗin ya shiga inda ya tarar Neehal tana ƙoƙarin zuba miya. Ya ce "Kar ki zuba." Ta juyo ta dube shi ta ce "Ka fasa ci?" Ya gyaɗa mata kai. Ta ce "Na manta ashe fa baka cin tuwo, in dafa maka wani abun to?" Ya ce "Like what?" Ta ce "Akwai miya, sai ka faɗi