Showing 126001 words to 129000 words out of 262509 words
Chapter 43 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
abun da kake so in dafa maka." Ya ce "Okay, dafa mun ko mene ma." Ta ce "Toh." Ya juya ya fice. Ta dauko tukunya ta ɗauraye sannan ta zuba ruwa ta kunna gas ta ɗora. Ta buɗe frizer ta ɗauko kayan salad ta zauna ta fara yankawa kafin ruwan ya tafasa. Mama ce ta shigo kitchen ɗin ta dubi tukunyar data ɗora ta sannan ta dube ta, ta ce. "Me kike yi haka?" Ta ce "Yaya zan dafawa abinci, kin san ba ya cin tuwo." Mama ta ce "Oh, yanzu kin warke kenan zaki iya girki?" Ta ce "To Mama naga bai ci abinci ba, kar ya zauna da yunwa, kuma ba wani girki mai wahala zan yi ba." Mama ba ta ce komai ba ta juya ta fice. Mintuna kaɗan ruwan ya tafasa, ta ɗauko macaroni ta zuba fiye da rabin leda. Bayan ta gama ta juya a plate ta kai masa falo ta ajiye a gaban sa. Ya dube ta ya ce "Thank you." Sannan ya sauko daga kan kujerar da yake ya zauna a kan carpet, ya dubi abincin ya ce "Take another spoon." Ta koma ta ɗauko ta kawo masa, bai karɓa ya ce "Zauna mu ci." Ta ce "Yaya na k'oshi." Yay mata wani kallo, ba shiri ta zauna suka fara ci tare. A takure take sosai saboda ba su taɓa cin abinci tare ba, kanta a ƙasa take cin abincin ta kasa d'agowa ta kalle shi. Shi kuwa kallon ta ya ma fi cin abincin nasa yawa. Ba su fi rabin abincin ba ta ce ta ƙoshi, ya ce bata isa ba sai sun cinye duka. Dama Mama ta gama masa mitar tunda yasa a yi masa girki, to kar ya bar mata sauran abinci ko d'igo ya cinye duka. Haka ta haqura suka ƙarasa ci. Bayan sun gama ta ɗauke plate ɗin ta kai kitchen, su Afrah ta zubawa ragowar abincin a plate ɗin, kafin ta fito har ya fice daga falon. Ta wuce sama ta kai musu abincin, ta tarar su Cake ma suke ci da yoghurt. Ta ajiye abincin ta ce in sun gama sa ci, sannan ta fita zuwa ɗakinta. Tana ɗaukar wayarta ta tarar da missed call ɗin Sadik har huɗu, da chaji ma zata saka wayar, amma dai ta kira shi duk da ta ji an fara kiran isha'i, ya d'aga ya ce mata idan ya dawo daga masallaci zai kira ta.
Bayan an yi Sallar ya kira ta, ta daga suka gaisa ya tambaye ta jikinta ta sanar masa ta ji sauƙi. Cikin damuwa ya ce "Wifey wai me yake faruwa ne?, kwana biyu naga gaba-ɗaya kin canza mun, kafin ki yi rashin lafiyar nan idan na kira ki sometimes da daddare sai in ji call waiting, ina tsoron kar wani ya mun ƙafa fa." Ta yi shiru dan ita kanta ta san tunda Ahmad ya shigo cikin rayuwarta ta canzawa Sadik, dan ma yana da haquri da wani ne da tuni sun yi faɗa, ko kuma inda ita ce yake mata haka bata san ya za tay ba. Cikin sanyin murya ta ce "Ka yi haquri Husby, ni kaina na san ban kyauta maka ba, amma babu abun da ya faru, kuma babu wanda yay maka wata ƙafa balle hannu, har yanzu kai kaɗai ne a zuciyar Neehal." Cikin jin daɗi ya ce "Dagaske Wifey?" Ta ce "Gasken gaske ma, Ya Sadik ina da kai me zan yi da wani ɗa_namiji kuma?" Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Har na ji daɗi a raina, dan bana son abun da zai raba ni da ke." Ta ce "Insha Allahu Husby zamu rayu tare har ƙarshen rayuwarmu." Ya ce "Amin Amin Wifey." Suka Cigaba da hirar su ta masoya Sadik ya sanar mata Insha Allahu gobe zai zo, akwai maganar da yake son su yi. Ta ce Allah ya kai mu lafiya sai ya zo ɗin. Bayan sun gama wayar ta yi tagumi ta fara tunani, tabbas ta san zuciyarta Sadik take so, so mai tsanani ma kuwa, amma abun da ta rasa ganewa matsayin Ahmad a gurin ta, da farko tana masa kallon like ɗan'uwanta na jini, amma a kwanakin nan lissafin yana ƙoƙarin sauyawa a cikin zuciyarta game da shi. Ga kuma tausayinsa mai tsanani da take ji, saboda koda bai faɗa ba tana hango sonta mai tsanani a cikin kwayar idonsa, ga kuma yaransa da Allah ya ɗora mata kaunarsu, bata jin zata iya jurar Ahmad ya auri wata matar ta riƙe masa su Afrah, ta san kuma koda bata aure shi ba in ta ce masa ya bar mata su zai bata, amma ta san Mama baza taɓa yarda da hakan ba. Last abu kuma da yake damunta shine, ko zata yi auren at this time ko baza ta yi ba sai Allah, za'a barta da wanda zata aura ɗin ne ko za'a kashe mata shi kamar su Anwar?.... Shigowar su Afrah ya katse mata tunanin da take. Suka haye jikinta suka ce ta kira musu su Ummi, ta kira Zahra bayan ta ɗauka sun gaisa ta ba su wayar, suka yi mata surutun su sannan ta kaiwa Ummi wayar itama suka yi magana, har Dad ɗin su Ahmad yau sun gaisa da Neehal. Ta gaishe su cikin girmamawa su kuma su kay ta saka mata albarka. Bayan sun gama wayar ta ja su toilet tay musu wanka, tana shirya su suka dame ta akan ta kira musu Daddy'nsu. Ta kira shi kuma bai d'aga ba. Bayan ta shirya su, ta kama hannunsu suka nufi part ɗin Daddy dan su gaishe shi. Sai da goma ta wuce ta dawo part ɗin Mama ɗauke da Amrah a hannunta, Mama kuma ta biyo ta da Afrah dan har sun yi bacci. Bayan ta yi wanka ta sha magungunanta ta kwanta, lokacin sha ɗaya saura ƴan mintuna, ta ɗauko wayarta ta tarar da missed calls ɗin Ahmad, ta bi bayan kiran nasa, sai da ta kusan katsewa ya ɗaga cikin muryar bacci suka ɗan yi magana kaɗan, ya sanar mata fita suka yi da Mamy bayan ya koma gida, shi yasa bai kira ta ba, sai bayan sun dawo ya ga missed call ɗinta. Suna gama wayar itama bacci ya ɗauke ta.
Washegari Neehal ta tashi da ciwon cikinta, amma bai yi tsanani sosai ba. Sai wajen ƙarfe goma na safe ya tasar mata sosai, gashi Mama bata nan ta tafi gurin aiki tun 8. Ganin yanda take nuk'urk'usu da juyi akan gado su Afrah suka sauka ƙasa da gudu suka kira su Dije. A tare suka dawo da yaran. Dije ta riƙe mata hannu cikin tausayawa ta ce "Sannu Neehal, ina maganinki yake a ɗauko ki sha?". Tana hawaye ta buɗe baki da ƙyar cikin rawar murya ta ce "Yana ɗakin Mama." Zulai ta tafi da sauri ta duba amma bata gani ba. Ta dawo ta cewa Neehal "A ina take ajiyewa ban gani ba." Neehal ta taune lip ɗinta ta tashi zaune da ƙyar ta nuna musu wayarta, Dije ta ɗauko da sauri ta miƙa mata, ta karɓa ta cire key ta yi dialing ɗin Numbern Mama ta miƙa musu, ba tare da ta yi magana ba ta koma ta kwanta, hannunta dafe da mararta dake barazanar fashewa dan ciwo da murd'awar da take mata. Har wayar ta katse Mama bata ɗauka ba, suka ƙara kira bata ɗauka ba. Cikin damuwa Zulai ta ce "Bata ɗauka ba Neehal." Ta fashe da kuka saboda azabar ciwo, dama Maman ta ce mata yau surgery zata yiwa har mutum uku, ta san may be ta shiga theatre room ɗin shi yasa bata ɗauki wayar ba. Cikin Kukan ta ce "Ku kira Yaya ko Daddy su zo mutuwa zan yi." Su Afrah suka saka kuka ganin yanda take kukan itama. Zulai ta yi searching sunan Yaya ta kira. Sai da ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka. A gaggauce Zulai ta sanar masa abun da yake faruwa, yana gurin aiki amma ya ce gashi nan zuwa gidan. (This week Ameen ya dawo Kano da aiki kamar yadda ya sanar da Mama, and an ƙara masa matsayi from captain to lieutenant Colonel.) Dije ta riƙe hannun Neehal tana zuba mata sannu, Zulai ta sauka ƙasa dan ɗauko ruwa ta tofa mata addu'a ta sha ko Allah zai sa a dace kafin Ameen ɗin ya ƙaraso. Bata kai ga ɗauko ruwan ba ta ji ƙarar door beil, ta nufi ƙofar da sauri ta buɗe cikin addu'ar Allah yasa wanda zai iya taimakon Neehal ɗin ne Allah ya kawo musu. Ahmad ta gani, ta bashi hanya ya shigo falon, cikin girmamawa ta gaishe shi. Ya amsa mata da fara'arta sannan ya tambaye ta Neehal, ta sanar masa bata da lafiya tana sama kuma Mama bata nan. A rikice ya ce su je ya ga jikin nata.
Suna shiga ɗakin, su Afrah suka tashi da gudu suka nufe shi. Amrah ta ce "Daddy Aunty bata da lafiya, sai kuka take." Bai bi takan yaran ba ya ƙarasa bakin gadon ya kamo hannun Neehal a ruɗe, lokacin ta galabaita matuƙa sai numfarfashi take kamar zata shid'e. Ya sunkuyo a hankali ya ce "Princess! Me yake damun ki?" Zulai ce ta faɗi amsa da faɗin "Ciwon ciki take." Ya ce "Okay." Ta buɗe idanunta da ƙyar ta kalle shi, sai kuma ta saka kuka cikin azabar ciwo ta buɗe baki da ƙyar ta ce "Uncle ka kai ni gurin Mama Please mutuwa zan yi." Ya shafa fuskarta cike da tausayawa ya ce "Sorry dear, zaki samu sauqi soon Insha Allah." Ya dubi su Dije ya ce "Dama tana yin irin haka?" Suka ce "Eh." Ya miƙe da sauri dan ya gano mai yake damunta, ya ce musu yana zuwa zai je ya dawo yanzu. Afrah ta ce "Daddy ta kai ta hospital please." Ya ce "No yanzu zan dawo na bata magani." Cikin sauri ya fice daga gidan ya je wani pharmacy ya siyo allura ya dawo gidan. Kafin ya dawo har ta yi amai a ƙasan gadon, su Dije suna cikin gyara wurin ya dawo. Ya haɗa allurar sannan ya hau kan gadon ya d'ago ta a hankali. Ta faɗa jikinsa ta k'ank'ameshi sosai cikin gigitar ciwo. A hankali ya d'aga rigar jikinta tare da ɗan zame dogon wando jikinta yay mata allurar. Ta saki gwauron numfashi tare da ƙoƙarin barin jikinsa, ya ƙara riƙe ta da kyau da ɗaya hannunsa, ɗayan hannun kuma yana mulmula mata wurin allurar. Fita su Dije su ka yi da kayan da suka gyara inda tay aman. After 5 minutes har lokacin tana jikinsa, ta yi lamu a jikinsa tare da lumshe ido, ga dukkan alamu ta fara samun relief, sai ajiyar zuciya take saukewa akai_akai. Amrah ta ce "Daddy ta ji sauqi ko? tunda ka yi mata injection?" Ya gyaɗa mata kai. Afrah ta saki ajiyar zuciya ta ce "Thank God." Neehal ta fara ƙoƙarin tashi daga jikinsa dan tun sanda ta yi amai ta ji jinin ya fara zuba a jikinta, kuma gashi bata saka pad ba tana tsoron kar ta yi stain a jikinsa. Ya ƙi bata damar hakan sai ma ƙara gyara mata kwanciya da ya yi a jikinsa, ji yake kamar ya mayar da ciwon jikinsa, a hankali ya ce "Princess ya jikin?" Ta gyaɗa masa kai kawai, ya fara gyara mata gashin kanta wanda ya ɗan barbaje har saman fuskarta ya ce "Allah ya baki lafiya Baby." Ta jinjina masa kai kawai, ita so take ta bar jikinsa amma ya hanata, gashi sai ƙara jin zubar jinin take a jikinta, tana tunanin ma ta ɓata shi. Turo ƙofar ɗakin akai da ƙarfi hakan yasa ta buɗe idonta da sauri ta kalli ƙofar, Ahmad ma ƙofar ya kalla. Ameen ne ya shigo ɗakin, yana sanye cikin uniform ɗinsu na sojoji wanda suka ƙara fito masa da kwarjininsa, suka kuma matuƙar yi masa kyau.........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*5️⃣1️⃣*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
..........Washegari da misalin ƙarfe goma na safe, Neehal tana cikin bacci ta ji muryar Hajiya tana tashin ta. Ta buɗe ido da ƙyar tana duban ta cikin muryar bacci ta ce "Bani da lafiyar ma ba zaki bar ni na huta ba?" Hajiya ta ce "To tafiya zan yi na tashe ki mu yi sallama ƴar nema." Ta tashi zaune tana hamma tare da yin salati. Ta dubi Hajiya ta ce "Kai Hajiya yanzu tafiya zaki yi kamar wadda ake kora? Ki ɗan ƙara mana kwana biyu mana." Hajiya ta ce "Ba zan zauna ba, yau a Gombe mahaifata zan kwana, in kuma na ƙara dawowa garin nan to sai dai in bikin na zo insha Allah." Neehal ta ce "Zaki yi shekaru kuwa baki zo ba, indai bikina ne." Hajiya ta riƙe baki ta ce "Ikon Allah, ka ga shashashar yarinya zatai wa kanta mugun baki, to in ba ki yi aure ba jiƙa ki su Faɗiman za su yi su shanye? ko kuma zama zaki yi kuna goga ƙafaɗa da ita a gidan?" Neehal ta sauko daga kan gado bata tare da tankawa Hajiya ba ta shige toilet. Hajiya ta ce "Kya shige banɗaki mana ja'irar kashi kawai, da kai kamar k'ullin magani." Ta ƙaraci mitarta sannan ta fice daga ɗakin. Bayan Neehal ta fito daga toilet ɗin ta saka kaya sannan ta hau gyaran dakin nata, tana cikin gyaran Mama da Daddy suka shigo. Daddy ya ce "Daughter da kanki kike gyaran ɗaki ke da ba ishashshiyar lafiya ce da take ba." Ta yi murmushi tare da ajiye filon dake hannunta ta ce "Ai na ji sauƙi Daddy na." Mama ta ce "Masha Allah, Allah ya k'aro sauƙi." Ta amsa da Amin, sannan ta gaishe su. Daddy ya ce "Jiya da daddare na zo ganin jikin naki na tarar kina ta bacci, ƙwaƙwa da dabidon da kika ce mun kina so yana cikin fridge na bawa Mamanki ta ajiye miki." Neehal ta ce "To Daddy na, na gode sosai." Ta kalli Mama ta ce "Allah yasa dai babu wanda ya ci mun." Mama ta ce "Tunda kowa irin ki ne ba, Ki sauka ƙasa ki yi break zamu je gidan Ameen yanzu mu dubo Hafsah." Neehal ta ce "Hajiya ta tafi ne?" Mama ta ce "Tana falo yanzu dai zata tafin." Bin su Mama ta yi suka sauka ƙasa tare, har parking space ta raka su, tay wa Hajiya sallama wadda direban Mama zai kai ta gidansu Aunty A'isha da Aunty Sadiya daga can zai wuce ya kai ta Gomben. Bayan ta koma cikin gidan ta haɗa tea ta sha ta ɗan ci Irish sannan ta sha maganinta. Suna zaune a falon ƙasa suna hira da su Dije suka ji ƙarar door beil, Zulai ta tashi ta je ta buɗe, a zaton Neehal Mama ce ta dawo amma sai ta ji muryar waɗanda bata taɓa tsammani ba wato Afrah da Amrah suna kwad'a kiran sunanta. Ta tashi tsaye da sauri tana kallon su cikin shock. Suka taho da gudu suka rungume ta. Ta tsugunna itama ta rungume su duka cikin tsananin farincikin ganin su. Ta d'ago su daga jikinta har lokacin fuskarta na ɗauke da mamaki ta ce "Sweethearts wa ya kawo ku?" Suka haɗa baki gurin faɗin "Daddy ne, Aunty ina Mama?" Ta ce "Ta fita unguwa amma yanzu zata dawo." Afrah ta ce "Aunty ya jiki? Daddy ya ce baki da lafiya kar mu zo mu cika miki kunne da surutu." Ta shafi kuncin yarinyar ta ce "Da sauƙi Dialing ina Daddy'n." Amrah ta nuna mata bakin ƙofa inda yake a tsaye hannunsa hard'e a ƙirjinsa yana kallon su, ga trolley ɗin kayan su Afrah a gefen sa." Ta ƙura masa ido tunda suna ɗan nesa da juna baza su iya haɗa ido ba, yau sanye yake cikin manyan kaya wanda suka yi masa kyau sosai, tunda take bata taɓa ganin sa da manyan kaya ba sai yau. Ya fara takowa a hankali zuwa inda suke, ganin haka yasa su Dije suka tashi suka nufi kitchen dan kawo masa drinks.
Ta ɗauke idonta daga kallonsa da sauri ta mayar ga su Afrah tana murmushi ta ce "Welcome dear, I missed you alot." Amrah ta ce "Missed you too Aunty." Ta ce "Ya school? Dafatan dai kuna karatu sosai?" Suka gyaɗa mata kai. Ta ce "That's is good, ina Ummi da Aunty Zahrah da Ammi?" Afrah ta ce "Suna gida mun bara su, Aunty Zahrah ta ce zata biyo mu Ummi ta hanata." Ta zauna sosai a kan carpet ɗin falon ta ɗaura su duka akan cinyarta suna yi mata hira, ko ƙara kallon inda Ahmad yake bata yi ba. Shi ma bai ce mata komai ba sai zama da ya yi yana kallonsu. Har su Dije suka dawo falon suka ajiye masu drinks da snacks. Ganin da gaske ba kula shi zatai ba ta yaranta kawai take sai ya cewa su Afrah su tashi daga jikinta ba su ga bata da lafiya ba. Yaran suka tashi da sauri suna faɗin "I'm sorry Aunty." Neehal ta ɓata fuska ba ta ce komai ba, ta miƙe ta kamo hannunsu da nufin su wuce sama, a hankali kanta na ƙasa ta ce "Ina kwana." Ya k'ank'ance ido yana dubanta ya ce "Lafiya, ya jikin naki?" Ta ce "Da sauƙi." Ya ce "Allah ya ƙara sauƙi." Tare da miƙewa ya ce wa su Afrah su ya kai su gidan Mamy, da yamma sai ya dawo da su. Neehal ta ce "Daga zuwanku, dan Allah ka bari idan Mama ta dawo sai mu je tare." Ya ce "Ke da baki da lafiya kuma zaki fita, idan kin ƙara warwarewa sai ku je, tunda za su kwana biyu a nan." Bata ce komai ba ta saki hannun yaran ba don taso ba. Ya kama hannunsu suka juya za su tafi, ta kalli abubuwan da su