Showing 78001 words to 81000 words out of 262509 words
Chapter 27 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
a gaban mudubi tana ɗaura d'ankwalin atamfar dake jikinta, ɗinkin riga da skirt ne ya mata das a jikinta. Bayan ta gama ɗaura d'ankwalin ta saka ɗan kunne fashion mai kyau kalar one colour na jikin atamfar, sannan ta ɗaura agogo a left hand d'inta, ta zira abun hannu a right. Masha Allah ta yi kyau sosai small pink lips ɗinta sun sha white lipstick sai k'yalli suke. Su Afrah dake zaune a kan carpet ɗin bakin gado suna break, ganin ta miƙe ta ɗauki mayafinta dake kan gado suka miƙe su ma da sauri suna haɗa baki gurin faɗin "Zan biki Aunty." Neehal ta kalle su ta yi murmushi sannan ta kama hannuwansu ta ce "Bana faɗa muku school zani ba, ku bari idan na dawo da yamma za mu je unguwa Insha Allah." Suka gyaɗa mata kai ba dan ransu ya so ba. Neehal ta yi picking goshinsu sannan ta ce su tafi ɗakin Mama ta musu wanka idan sun gama break ɗin. Ta yafa mayafinta wanda ya kasance babba ne amma ba me kauri sosai ba, sannan ta ƙara fesa perfumes ɗinta ta zira plate shoe d'inta ta ɗauki jakarta da car key ɗinta ta fice daga ɗakin tana yi wa su Afrah bye_bye. A falo ta tarar da Mama ta ce mata "Mama zan tafi sai na dawo." Mama ta ce "Allah ya kiyaye ina yaran fa?" Ta ce "Suna ɗaki suna break in sun gama na ce su zo ki musu wanka." Mama ta ce "To Allah ya bada sa'a, ki kula da titi fa kuma kar ki manta da addu'a." Neehal tana fita daga falon ta ce "Insha Allah Mamana, bye." A parking space kamar yadda Daddy ya ce mata Motar ta tana can, a nan ta ganta. Ta sa key ɗinta ta buɗe murfin Motar da bismillah sannan ta yi addu'a ta shiga zuciyarta cike da farin ciki, gaba-d'aya damuwar data kwanta da ita daren jiya a ranta ta ji duk ta gushe, Daddy ya faranta mata ba kaɗan ba, a rayuwarta tana son ta ga tana driving, tun da Daddy ya so siya mata Motar amma Mama ta hana. A hankali take driving ɗin cikin nutsuwa da kula, sai dai ba ta yi nisa da tafiya ba ta ga wata Motor kamar tana binta a baya, ba ta kawo tunanin komai a ranta ba, tafi zaton may be hanya ce ta haɗa su ɗaya da mai motar, sai dai yanda take driving ɗin a hankali ya ci a ce mai Motar ya zo ya wuce ta kamar yadda wasu motocin ke yi. Cikin ikon Allah ta ƙarasa har cikin Bayero lafiya, kuma har ta zo bakin gate ɗin makarantar Motar na biye da ita a baya. Ƙarfe biyu suka gama last lecture ɗinsu, ko Sallah bata tsaya yi ba ta yi wa Freinds ɗinta sallama ta yo gida, saboda tana son ta je gidansu Haneefah ta nuna mata sabuwar Motarta.Tana fita daga get ɗin makarantar ta hau kan titi kenan ta mudubi ta ga kamar motar d'azu ce ke kuma binta, ita tama manta da batun wata motar d'azu, dan ta yi tunanin mai Motar shima Bayeron zai je a d'azun. Gabanta ya yanke ya faɗi tsoro ya fara ziyartar zuciyarta, hakan yasa ta shiga karanto Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, da hasbinallahu'wani'imal'wakil. Har ta ɗan samu nutsuwa a ranta ta cigaba da driving ɗinta. Wata zuciyar na faɗa mata ƙila ma ba Motar d'azun ba ce irinta ce kawai. Sai dai kuma kamar ɗazun duk inda ta yi nan Motar itama take bi, har tafiya ta fara yi a slow wai dan ta ga ko Motar zata zo ta wuce ta amma still dai motar tana bayan tata..........✍️
*Na so page ɗin ya fi haka tsawo, amma tun daren jiya ban jin daɗi, yanzu ma dauriya na yi na muku wannan ɗin*
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:50] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*3️⃣5️⃣*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
...........Har ta ƙarasa gida Motar tana biye da ita a baya. Sunayen Allah tsarkaka take ambata a ranta, kuma cikin k'udurarsa da ikonsa ya kawo ta gida lafiya. Sai da ta shiga layinsu sannan ta ga Motar ta daina bin ta. Tab'e baki ta yi a fili ta ce "Allah kai ne sarki, Allah ka kare ni daga dukkan wani mai nufi na da sharri, Allah da kai na dogara kuma kariyarka nake roqa a kodayaushe." Da haka ta shiga cikin gida ta yi parking motar sannan ta fito a gajiye ta yi cikin gidan. Zulai ce ta zo ta buɗe mata ƙofa, "Sannu da zuwa." Ta faɗa tana bata hanya. Neehal ta ce "Yawwa Aunty zulai, ya gida." Zulai ta ce "Lafiya k'alau." Daga haka Neehal ta wuce sama. Ɗakinta ta nufa ta ajiye handbag ɗinta, ganin su Afrah ba sa dakin ta fito ta nufi ɗakin Mama. A kan gado ta tarar da su sun baje suna bacci, da alama kaɗaici ne ya ishe su, tunda ta san ba su fiya baccin rana ba. Mama bata nan ta je aiki, dama ta san ba zata dawo ta same ta ba. Ɗakinta ta koma ta shiga toilet ta ɗan watsa ruwa tare da yin tsarki ta ɗauro alwala, bayan ta idar da Sallah ta sauka ƙasa ta zuba abinci a ƙaramin plate ta ci. Ganin har uku ta wuce yasa ta koma sama da sauri dan shiryawa. Wayarta ta ɗauka ta ga missed call na Uncle Usman, murmushi ta yi sannan ta siyi kati daga banki a sim ɗinta na 5k sannan ta kira shi. Yana d'agawa ta ce "Assalamu alaikum." Uncle Usman ya amsa mata, ya ƙara da faɗin "Daughter kin manta da ni ko?" Neehal ta shagwabe fuska kamar yana ganin ta ta ce "Haba Uncle ni na isa in manta da kai a rayuwata? ai ɗiyar kirki bata taɓa mantawa da ubanta ko dan neman albarkarsa." Uncle Usman ya yi murmushi mai sauti ya ce "To ƴar gidan Uncle, ya school ya office." Neehal ta ce "Lafiya k'alau Alhamdulillah, ina Auntynah da takwarata?" Ya ce "Suna nan k'alau, dafatan dai komai lafiya ko Neehal?" Ta ce "Lau lau my Uncle, ya kasuwa?" Ya ce "Kasuwa Alhamdulillah, gashi ma ta hana ni zuwa in ga ƴata." Neehal ta ce "Babu komai Uncle, Allah ya taimaka. Nima Insha Allahu wannan hutun da zamu yi zan yi ƙoƙari in zo Niger ɗin." Uncle Usman ya ce "Allah ya kai mu ya kawo ki lafiya." Neehal ta ce "Ameen." Ya ce "Ya Mama da Daddy da Aunty A'isha da Aunty Sadiya da wajen su Hajiya?" Ta ce "Duk sunanan lafiya k'alau." Uncle Usman ya ce "Masha Allah, haka ake so Allah ya yi mana jagora. Ni kwa na ce Neehal har yanzu ba kya zuwa gidan Ya Umar da Gabasawa?" Neehal ta had'iye wani abu da ya tsaya mata a mak'oshi ta ce "Bana zuwa Uncle, tun da duk sun nuna ba sa son na rab'e su, kowa na je inda yake sai ya dinga wulaqanta ni kamar wadda ba jininsu ba, na rasa me nay musu, mutuwar iyayena ce lefi a gare su ko kuma riqona da Mama take yi? Dama Uncle idan iyayen mutum sun rasu sai ya zama abun ƙyamar a cikin zuri'arsu?" Ta ƙarashe zancen hawaye na zuba akan kuncinta. Uncle Usman ya danne ɓacin ransa ya ce "Don't cry Daughter please, ba dan na saki kuka na tambaye ki ba, na tambaye ki ne saboda ina son sanin ko an samu cigaba sai dai kash bayananki sun tabbatar mun jiya i_yau ake bata sauya zani ba, amma har su Mubarak ɗin Ummi suma ba kya zuwa wajensu?" Neehal ta ce "Ai Ka san yanzu ba sa Gabasawa suna Lagos acan suke neman kuɗin su, amma Mama ta ce Insha Allahu watarana zata kai ni gurinsu da kanta, tunda ba ni da kamar su a duk faɗin duniyar nan." Uncle Usman ya ce "Allah ya ba da iko." A ransa yana jinjina ƙoƙari irin na Mama da kullum ita dai burinta ta ga Neehal tana zumunci da danginta kamar kowa, wani b'arin na zuciyarsa kuwa cike yake fal da tausayin Neehal. Ganin har yanzu kamar bata saki ranta ba da zancen su Uncle Umar da yay mata sai ya kawar da zancen inda cikin sigar tsokana ya ce "To a bani labarin sabon surikina." Murmushi ne ya zubce mata ba tare da shirya yin sa ba sai dan yanayin yanda Uncle Usman ya yi maganar, don sosai take jin k'uncin da ɓacin rai a duk lokacin data tuno da yanda danginta suka manta da rayuwarta a cikin tasu rayuwar. Uncle Usman ya ce "Ko baza a bani ba, na ji kin yi shiru!" Neehal ta ce "Ai babu ne Uncle." Ya ce "Kai haba, Ni dai na san my Daughter bata da baƙin jini, sai dai idan korar surukan nawa take." Neehal ta ce "Dagaske babu Uncle." Uncle Usman ya ce "Allah ya kawo na gari to, mu sha biki mu rak'ashe." Neehal ta yi murmushi cikin jin kunyarsa, wani b'arin na zuciyarta kuma fargaba ce fal a ciki, dan ita ba ma ta kawo wa kanta aure a yanzu, to idan ma zata yi auren wa zata aura? Sun ɗan taɓa hira kaɗan wanda gaba-d'aya zolayarta Uncle Usman yake, har sai da ya ji ta ware tana ƙyalƙyala dariya sannan suka yi sallama bayan ya ce ta gaisar masa da Mama da kyau. Bata ajiye wayar ba ta kira layin Haneefah sai da ta katse wa sannan Haneefah ta d'aga. Neehal ta ce "Matar nan kin yar da ni." Haneefah ta ce "Faɗi da babbar murya, bacin yarwa ma har bi takanki na yi na take ƴar rainin hankali kawai." Neehal ta yi murmushi ta ce "Me yay zafi haka Besty?" Haneefah ta ce "Abun kan wuta mana, tun jiya na kira ki amma sai yanzu zaki kira ni." Neehal ta ce "Ki yi haquri ƙawata, yanzu dai ba ma wannan ba kina gida in zo in nuna miki wani abu." Haneefah ta ce "Ina gida, Nima da ma akwai abun da nake son faɗa miki." Neehal ta ce "To gani nan zuwa." Daga haka ta katse wayar. Kukan twins ta jiyo a falo, da sauri ta fita dan ganin mene ne. Abun da bata taɓa gani sun yi ba wato faɗa shi ta tarar suna yi, Amrah tana ta dukan Afrah ita kuma tana kuka. Ɗaukar Afrah ta yi tare da hararar Amrah ta ce "Me tay miki kike dukanta?" Amrah ta ce "Ita ta fara duka na." Afrah cikin ta ce "Ƙarya take ban dake ta ba." Neehal ta sauke Afrah ta tsugunna ta rungume su duka a jikinta ta ce "Ku daina faɗa kun ji babu kyau." Suka gyaɗa mata kai, Amrah ta cewa Afrah "Am sorry." Afrah ta ce "Me too." Neehal ta rungume su cikin k'aunarsu tana murmushi. A hankali kuma ta raba su da jikinta ta miƙe tsaye tana faɗin "Mu je in shirya Ku mu tafi unguwa." Afrah ta ce "Aunty gurin Daddy'nmu za mu?" Neehal ta ce "A'a ai ban san inda yake ba." Cikin sauri Amrah ta ce "Abuja, a Abuja yake." Neehal ta ce "Tom Shikenan, soon za mu je Insha Allah." Wanka ta musu ta shirya su sannan itama ta shirya tay wa su Dije sallama suka tafi. Ta kira layin Mama bata d'aga ba sai text message ta mata ta sanar mata ta tafi gidansu Haneefah. Abun mamaki da ɗaure kai gidansu Haneefan ma sai da ta ga Motar nan tana bin ta a baya. Kamar ɗazu addu'a ta shiga yi a ranta har suka ƙarasa. Haneefah ta yi murna sosai da ganin sabuwar Motar Neehal, kamar ita yi Motar. Bayan ta gama tsallen murna suna zaune a kan gadonta su Afrah kuma suna falo gurin Momy, Neehal ta cewa Haneefah "Me kika ce zaki faɗa mun idan na zo?" Haneefah ta ce "Hmm, jiya Abban Abuja ya zo (wan mahaifinta kenan) ya cewa Mommy Iyayen ya Faruq sun je sun tsaida ranar bikinmu nan da three months masu zuwa." Neehal ta waro ido tana murmushi ta ce "Dagaske kike Haneefah?" Haneefah ta ce "Zan miki ƙarya ne to." Neehal tana dariya ta ce "Ban iya guɗa ba dana rangad'a ta yau, Ya Faruq ya ga ji da iskancinki kenan na ja masa rai da kike, amma na ji daɗi sosai ƙawata, Allah ya kai mu lokacin ya sanya Alkhairi." Haneefah ta ce "Amin, ni kuma ban ji daɗi ba, na so an fara bikinki kafin nawa na rak'ashe son raina." Neehal ta mata gwalo ta ce "Sai kuma Allah ya yi ni zan rak'ashe ɗin a bikinki." Haneefah ta ce "Ba komai, idan bikin naki ya zo nima aje auran zan yi a gefe in sha sha'ani na." Neehal ta ce "Allah ya sa lokacin kina da tsohon ciki ma, sai mu ga ta tsiya." Haneefah ta jefe ta da filo tana faɗin "Ba Amin ba muguwa ƴar buk'ulu." Sai bayan Magriba suka koma gida, a koma wa gida dai Neehal bata ga Motar nan tana binta ba, in ma tana binta ɗin ita dai bata gan ta ba, ko dan duhu ya fara ne oho. Washegari Friday bayan Neehal ta dawo daga school da yamma Mama ta ce ta shirya su je ita da su Afrah ta yi musu shopping ɗin kayan sawa da duk wani abun buƙata. Suka shirya suka tafi, kaya sosai Neehal ta jidar wa su Afrah, sannan suka biya suka sha Ice cream sannan suka dawo gida. Yau dai ba ta ga Motar nan ta bi ta ba kwata_kwata, ko da safe da zata school. Hakan yasa ta ji hankalinta ya ɗan kwanta ba kamar jiya ba da ta kwana cikin zullumi da fargaba.
Bayan Sallar Magriba Neehal tana sama tana yin wani Assignment Amrah ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama, Neehal ta amsa mata ba tare da ta ɗago ba. Amrah ta ce "Aunty Mama ta ce ki zo Uncle Sadik ya zo." 'Sadik kuma?' ta tambayi kanta gabanta na fad'uwa ba tare da ta san dalili ba. A hankali ta dubi yarinyar ta ce "Ki ce ina zuwa." Amrah ta juya ta fice daga ɗakin da gudunta. Neehal ta tattara takardun gabanta ta ajiye akan bedside locker sannan ta ɗauko mayafi ta yafa ta fito falo. Mama tana zaune tare da su Afrah suna kallo a Falon. Neehal ta dube ta, ta ce "Mama wai Ya Sadik ne ya zo?" Mama ta ce "Eh, yana ƙasa yana jiran ki." Bata kuma cewa komai ba ta nufi ƙasa. Yana zaune a kan kujera as always idan ta sakko gurinsa yana ta latsa waya, k'amshinsa ne ya ziyarci hancinta, ta lumshe ido tana jin wani irin yanayi na bin jikinta tare da canzawar bugun zuciyarta. Sosai Sadik ya mata kyau ba kaɗan ba, yana sanye cikin ƙananun kaya, sumar kansa baƙi sidik sai k'yalli take. Cikin sanyin jikin data rasa na mene ta ƙarasa ta zauna a kujerar kusa da shi tare yin ƙasa da idonta tana sauke numfashi a hankali. Murya ƙasa_ƙasa ta yi masa sallama. Ya d'ago kansa a hankali fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mata tare da mayar da wayarsa cikin aljihu. Kamar bata son magana ta ce "Ina yini." Idanunsa na kanta Ya ce "Lafiya k'alau, ya study?" Ta ce "Alhamdulillah, ya su Maamah?" Ya ce "Suna lafiya, ta ce na gaishe ki ma." Still kanta na ƙasa ta ƙi d'agowa ta ce "Ina amsawa, ya aiki?" Ya ce "Aiki gashi nan muna ta fama Alhamdulillah." Ta yi shiru ba ta ce komai ba, shi ma shirun ya yi yana jiran ya ji ko zata tambaye shi dalilin yasa kwana 2 bai kira ta ba kuma bai zo ba. Tsawon three minutes suna haka, katse shirun na su ya yi da faɗin "Neehal !Kamar wani abu na damunki ko?" Lumshe idonta ta yi tana jin yanda sunanta ya ƙara daɗi a cikin muryarsa, sai ta ji kamar ta ce ya ƙara maimaitawa. Girgiza masa kai ta yi alamun a'a. Ita kanta ba zata ce ga abun da yake damunta ba, amma tabbas daga lokacin da Amrah ta zo ta faɗa mata Sadik ya zo ta ji sauyi a zuciyarta wanda bata san ko na mene ba. Sadik ya yi ƙoƙarin jan ta da hira amma ta ƙi sakin jikinta, ko d'ago kanta ta kasa yi, amma sai ta tsinci kanta da son jin muryarsa a wannan lokacin, ta ji bata son ya yi shiru da magana ko na second ɗaya ne. Shi kuwa Sadik jikinsa ne gaba-d'aya ya yi sanyi, dan yau da shirinsa ya taho na bayyana wa Neehal abun da ke zuciyarsa game da ita, amma kuma yanayin da ya ganta a ciki ya kashe masa gwiwa. Suna haka kamar a mafarki Neehal ta ji k'amshin Ameen, da sauri ta d'ago kanta ta kalli ƙofa. Shine kuwa yake ƙoƙarin shigowa falon, samun kanta ta yi da ƙura masa ido fuskarta ɗauke da murmushin da bata shirya masa ba, rabon data gan shi tun ranar da ta je gidansa, sati ɗaya kenan yau, sai ta ga ya ƙara mata kyau da haske ya yi wani fresh abunsa, alamun angoncin ya karɓe shi. Ameen ya ƙaraso inda suke fuskarsa ba yabo ba fallasa ya yiwa Sadik sallama tare da miƙa masa hannu. Cikin fara'a Sadik ya miƙa masa nasa hannun suka yi musabaha sannan ya gaishe shi. Ko kallon inda Neehal take bai yi ba ya nufi sama, Neehal data kasa ɗauke idonta daga kansa cikin sanyin murya ta ce "Yaya ina wuni." Ba tare da ya juyo ba ya ce "Fine." Tare da wucewa sama abinsa ya bar musu daddad'an k'amshinsa a falon...........✍️
_*Yanzu labarin zai fara sauya salo, sannu_sannu bata hana zuwa.......*_
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:51] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*3️⃣6️⃣*
............Runtse idanunta ta yi tana jin ba daɗi akan abun da