Showing 249001 words to 252000 words out of 262509 words

Chapter 84 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21445

harara ta murgud'a masa baki. Sandarewa Ameen ya yi saboda tsananin mamaki ya tambayar kansa abun da take nufi da hakan, ita da yi masa laifi ita ce kuma da yin fushi lallai akwaita da ƙarfin hali. Hafsah da duk zaton ta aikin Malam ne ya yi aiki ga Ameen har ya zo gidansu a yau ta miƙe cikin tsiwa da rashin kunya ta ce. "Ameen me ya kawo ka inda nake? Baka yi auranka ba ka wofantar da ni saboda butulci da rashin tabbas irin naku na maza? Sai yau zaka kwaso jiki ka zo gurina, ni kuma ga sauna sai na washe maka baki na bi ka ko?" Ran Ameen ya fara ɓaci amma bai ce komai ba sai kallon ta kawai yake. Hafsah da zigar Aunty Safiyya take yawo a cikin kanta ta ce. "Ka tashi ga ƙofa nan ka koma inda ka fito, ni Hafsat na gama Auranka har abada Ameen, kuma ina roqon ka da Allah ka sauwaqe mun ƙaddararre Auran ka, dan bazan iya zama da kishiya ba." Ran Ameen fa ya kai matuƙar ɓaci, a fusace ya buɗe baki zai yiwa Hafsah magana sai kuma ya fasa ya shiga furzar da zazzafan huci. Hafsat ta tab'e bakinta ta ce. "Idan ka cika dan Halak cikin Fateemah da Muhammad in ga takarar sakina a yau ba'a gobe ba." Cikin matuƙar fusata Ameen ya miƙe tsaye yana jifan ta da wani irin kallo, idanunsa har sun fara sirkawa zuwa ja saboda tsananin ɓacin rai. Ya yi ɗan taku ya ƙarasa gaban Hafsah ya ce. "Hafsat kin san me kike faɗa kuwa? Kina cikin hankalinki kuwa? Ni kike faɗawa haka?" Kafin Hafsah ta yi magana muryar Mom ta karad'e parlour'n da faɗin. "Sannu Ameen, na ce sannunka." Duk da yanayin ɓacin rai da yake ciki amma haka ya tsugunna ya shiga ƙoƙarin gaishe ta. Ɗaga masa hannu ta yi ta ce. "Riƙe gaisuwarka bana buƙata, yanzu kai Ameen dan baka da kunya ka iya takowa ka zo cikin gidan nan bayan wulaqanci da tozarcin da ka yi mata, ka yi mata kishiya sannan kuma ta taho gida ka ƙi biyo bayanta saboda gaka ishashshe ko? Ka fi ƙarfin zuwa biko. To bari ka ji in faɗa maka in baka sani ba ka sani, ƴata ta fi ƙarfin wulaqancin ɗa Namiji wallahi, me kake da shi? Me kake t'akama da shi? Abun takaicin ma ka rasa da wa zaka haɗa ta kishi sai da yarinyar da asalinta ubanta ba kowa ba ne, ƴar matsiyata da matsiyatan danginta suka kasa riqe ta." Aunty Safiyya dake bayanta ta tari numfashinta tana turo d'auri gaban goshi ta ce. "To ai Yaaya abun duk shiri ne, shiryawa aka yi, wannan munafukar uwar tasa ce ta shirya komai." Da sauri Ameen ya miƙe idanunsa sun yi jajur, ba zai iya jurar wannan cin mutuncin ba, abun ya bar kansa ya koma kan Baby love ɗinsa amma duk bai ishe su sai sun haɗa da mahaifiyarsa? Ba ƙaramin danne zuciyarsa ya yi ba na ƙin mayar musu da martani, ya juya kawai ya fice daga parlour'n ransa a matuƙar k'ololowar ɓaci. Bayan fitarsa a tsorace Hafsat ta ce. "Na shiga uku Aunty, maganin nan fa kamar bai yi masa aiki ba, ina jiran na ga ya yi kneeling a gabana yana bani haquri tare da bagging ɗina sai na ga ya tashi kamar zai dake ni." Ita ma Aunty Safiyya jikinta ya yi sanyi. Amma cikin ƙarfin hali ta ce. "Ya yi masa mana, ke baki lura ba da yanayinsa ba ne? Shegiyar tattaurar zuciyarsa ce ta saka bai nuna ba, amma muna nan dake abun zai cijo sa ne zaki ga ya dawo ni na faɗa miki, ke dai ki cigaba da yin yadda na ce miki kar ki yi kuskure." Hafsat ta koma ta zauna tana sakin ajiyar zuciya, ita dai tsoronta ɗaya kar ta rasa Ameen.












Tun bayan fitar Ameen ba jimawa Neehal tana zaune ta ji cikinta na ɗan juya mata kaɗan_kaɗan, ko kusa bata yi tunanin period zata yi ba, sai da cikin ya ɗan murɗa mata ta ji abu ya fara fita daga jikinta sannan ta yi realising. Mamaki ne ya kamata ganin yau sau ɗaya a rayuwarta tunda ta fara period ya zo mata ba tare da ta sha wahala ba. Ta miƙe ta shiga ɗakinta ta kimtsa kanta sannan ta kwanta akan gadon dan ba normal take jin ta ba, cikin ya ɗaure mata kamar kodayaushe idan tana period. Ikon Allah ne ya kawo Ameen gida lafiya dan saboda ɓacin rai ko ganin gabansa sosai baya yi. Neehal ta yi murmushi jin shigowar motarsa, duk da bacci ya fara fizgarta amma ta yage shi ta miƙe dan tarb'ar mijinta, zuciyarta cike fal da tsokanar sa da zata yi. A falo suka ci karo, ta tsaya turus tana kallon shi kamar wani mayunwacin zaki yanda yake huci. Cikin mamakin yanayinsa ta ce masa. "Sannu da zuwa." Bai ko kalli inda take ba ya tura ƙofar ɗakinsa ya shiga ya banko ƙofar da ƙarfi. Cikin fad'uwar gaban ganin yanayin da ya shigo ta bi bayan shi, amma tana tura ƙofar sai ta ji ta kulle. Ta tsaya tana kallon ƙofar kamar zata gan shi a jikin ƙofar sannan ta juya ta bar gurin zuciyarta babu daɗi. Zama ta yi akan kujera tare da yin tagumi da hannu bibbiyu tana tambayar kanta me ya ɓata masa rai haka? Tashi ta yi ta ƙara komawa bakin ƙofar ɗakin nasa ta shiga yin knocking amma ta ji bai buɗe mata ba. Sai ta ji haushi ta koma ɗakinta ta kwanta, ita ba ita ta yi masa laifi ba amma shine zai yi mata haka, tana yi masa magana ya share ta ya shiga ɗaki ya kulle, ta bubbuga masa ƙofa kuma yana ji ya ƙi buɗewa.












Shi kuwa Ameen yana shiga ɗakin ya cire rigar jikinsa ya cillar akan gado sannan ya ɗauki remote ya karo AC, dan ji yake gaba-d'aya jikinsa da zuciyna yi masa wani irin zafi suke masa, kwanciya ya yi rigingine ya lumshe idonsa tare da dafa kansa da yake yi masa ciwo saboda hayaniyar su Hafsat. Kalamanta dana Aunty Safiyya ne suke yi masa kuwwa a cikin kunne, Hafsat har ta yi tsaurin idon da zata ce masa idan ya cika ɗan Halak ta kira sunan iyayensa na ainihi ta ce ya sake ta? ita kuma k'anwar uwarta mai kama da Ngozi ta cewa Mama munafuka! Lallai zai shayar da su ruwan mamaki, wannan shine karo na uku da Hafsah ta yi masa Manyan laifuka a rayuwar Auransu. Kiran Sallar Magriba ne ya tashe shi dan dole ya yi alwala ya fita. Sai da ya kalli ɗakin Neehal sannan ya fice, a ransa yana addu'ar Allah yasa bata yi kuka ba. Ita tana can ma bacci ya ɗauke ta. Sai bayan isha'i ya dawo gidan, lokacin zuciyarsa ta fara sanyi sakamakon Sallah da zikirin da ya yi. Ya buɗe fridge ɗin parlour ya d'auko ruwa mai sanyi ya sha, ajiyar zuciya ya sauke ya nufi ɗakin Neehal. Lokacin bata jima da tashi daga bacci ba, ta shiga toilet ta fito kenan tana zaune a bakin gado tana latsa wayarta. Ya tura ƙofa ya shigo tare yin sallama, ba tare data kalle shi ba ta amsa masa. Ya tsaya a jikin ƙofa yana kallon ta, ta ɗan ɗago ta kalle shi ta tura masa baki sannan ta mayar da idonta kan wayarta. Ya yi murmushi sannan ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta, hannayensa duka biyu ya ɗora akan cinyarta, yana kallon fuskarta ya ce. "Baby yau babu magana." Ta ja numfashi duk wani haushin sa da take ji yana barin zuciyarta, ajiye wayar ta yi ta ɗora hannunta akan lallausar sumar kansa ta shiga shafawa bata ce komai ba. Ya kwantar da kansa akan cinyarta tare da saka hannunsa ya zagaye k'ugunta yana shaƙar daddaɗan ƙamshinta. Duk wani ɓacin rai da su Hafsat suka saka masa yana kallon kyakkyawar fuskarta ya ji ya gushe, yanzu kuma da kansa ke jikinta sai ya manta da shi ma gaba-d'aya. Ta ture kan nasa ta ce. "Bani da lafiya fa." Da sauri ya ɗago kansa ya ce. "Subhanallahi, da gaske baby baki da lafiya? mene ne yake damunki?" Ganin yanda ya yi maganar a rud'e sai ta ƙara narkewa ta ce. "Ciwon ciki na yi, kuma ka dawo ina maka magana ka ƙi kula ni." Ya tashi ya hau kan gadon ya janyo ta jikinsa cikin damuwa ya ce. "I'm sorry My love, raina a b'ace yake time ɗin ne, bana son na zauna kusa da nake kar na yi miki tsawa ko abun da baza ki ji daɗi ba akan laifin da ba ke kika mun ba." Ya kai hannu kan cikinta ya ce. "Yanzu ya jikin naki? Allah yasa dai baki sha wahala ba irin wadda kike sa?" Ta bar jikinsa ta koma ta kwanta akan gadon ta ce. "Sosai ma, kamar zan mutu." Dafe kansa ya yi ya ce. "Ya Salam! Sannu Baby, ko za mu je asibiti ne?" Ta ce. "Ya daina ai yanzu." Ya bi ta ya kwanta shi ma cikin jimami da damuwa yana ta jera mata sannu da riri tata, ita kuma tana zuba masa taɓara. Daga baya kuma sai ta saka masa dariya. Ya tsaya yana kallon ta ya ce. "What's funny?" Tana shafa sajen fuskarsa ta ce. "Wasa fa nake maka ban wani sha wahala ba." Ya sauke ajiyar zuciya tare jan karan hancinta ya ce. "Shine da zaki ɗaga mun hankali ko?" Ta ce "To ka yi haquri bazan kuma ba." Ya saka idanunsa a cikin nata ya ce. "Wai ciwon cikin ma na mene ne?" Ta yi murmurshin mugunta ta ce. "Kamar ya?" Ya ce. "Kin fini sani ai." Ta rufe fuskarta da hannunta tana dariya. Ya ɓata fuska ya ce. "Me yasa abun nan zai mun haka?" Juya masa baya ta yi cikin jin kunya. Ya juyo da ita da hannunsa ya kai hannun ya danna mata ciki. Ta kwabe fuska ta ce. "Ouch! Da zafi fa." Ya rungume ta ya ce. "Sorry, dannawa na yi dan ya yi ya zube da wuri." Ta yi murmushi ta ce. "In ka yi haquri ma is just 12 days ne zai tafi." Ya waro ido ya ce. "Ko 120 days ba, I already knew the days, is just 2 to 3." Ta ɓata fuska ta ce. "Dama saka mun ido kake yi?" Ya ce. "No, the way da kike acting ne ake ganewa, baki da aiki sai kwanciya kamar ruwa, ga taɓara da raki." Ta juya masa ido ta ce. "Yanzu na daina to." Bai kuma magana sai langwab'e kai da ya yi yana kallon ta. Ta san me yasa ya yi hakan, gwalo ta yi masa tana dariya ƙasa_ƙasa. Ya zira hannunsa a cikin rigarta ya ce. "Idan babu can ai da akwai nan." Ta zaro hannun nasa ta yi kalar tausayi ta ce. "Mu je mu ci abinci yunwa nake ji." Yana bin ta da wani irin kallo da idanunsa da suka fara sauya kala ya ce. "No let me take this first." Zata yi magana ya hana ta, ta hanyar haɗe bakunansu guri guda. Ta lumshe idonta a hankali tare da saka hannayenta duka a kansa tana shafa gashin kansa zuwa bayan wuyansa........














Washegari da yamma Ameen ya je gidan Mama, bai b'oye musu komai ba ita da Daddy na daga cin mutuncin da su Hafsat suka yi masa ba. Cikin tsananin mamaki Mama ta ce. "Yanzu Ameen Hafsan ce ta faɗa maka haka?" Ya gyaɗa mata kai zuciyarsa na yi masa k'una. Daddy ya ce. "To ai ni Mahaifinta ya kira ki ɗazu da safe, ya ce mun jiya_jiya ya dawo daga ƙasar ya tarar da wannan abun mara daɗin ji, amma a yanda muka yi magana da shi gaskiya ga dukkan alamu ba shi da masaniyar wannan cin mutuncin da suka yi." Mama ta ce. "Allah ya kyauta." Sannan ta dubi Ameen cikin lallami ta ce. "Ka yi haquri, Ni na tursasaka ka je, ban taɓa tunanin za'a yi haka ba." Ya ce. "Babu komai Mum kansu suka yiwa ai." Daddy ya ce. "Ban da abunku na mata mutumin da ya zo sulhu gurinku me ne na tsayawa na neman fitina da shi kuma?" Mama ta ce. "Shaid'an ne kawai, ka yi haquri Ameen tunda bata taɓa yi maka makamancin wannan laifin ba, karka yanke hukunci da baza mu ji daɗi ba dukanmu." Ya furzar da iska daga bakinsa ya ce. "Ta taɓa mun Mum, lokacin data yi barin ciki abortion ta yi ba miscarriage ba, and kuma suka je ita da k'anwar mahaifiyarta aka juya mata mahaifa wai ita bata shirya haihuwa yanzu ba." A tare Mama da Daddy suka kama salati cikin tsananin kad'uwa. Mama ta ce. "Ikon Allah, ko na ce shirme, wani yana nema wani yana gudu, shi Ubangiji ai ba'a yi masa wayo, Allah yasa mu dace." Haka suka cigaba da tattauna maganar Mama sai tausar Ameen take, ita bata son ya ce zai rabu da Hafsat. Dan yanda take hango zallar ɓacin rai a cikin idanunsa ta san zai iya aikata komai. Shi kuma Ameen wani irin d'aci yake ji a cikin zuciyarsa, ji yake tamkar a yanzu ne Hafsat ta b'arar masa da gudan jininsa. A lokacin ji ya yi kamar ya sake ta saboda tsabar baƙin ciki, amma ya taushi zuciyarsa ya haqura. By now kuma ta kai shi bango, dan haka dole ya yi mata abun da zai saka ta dawo cikin nutsuwarta da hankalinta, ta gane ba tsoronta yake ji ba kawaici ne kawai irin nasa yake yi mata. Daga gidan Mama gidansu ya wuce direct, ya tsaya a bakin gate daga waje ya ɗauko Joter da Pen ya rubuta abun da zuciyarsa ta bashi umarni. Bayan ya gama ya karanta sannan ya ninke takardar, horn ya danna mai gadi ya buɗe ƙaramar ƙofar gidan ya lek'o dan ganin waye, Ameen ya fita daga cikin Motar ya ƙarasa ya bashi papern ya ce ya bawa Hafsat sannan ya juya ya shige cikin Motarsa ya bata wuta ya bar layin, ya bar mai gadi da bin sa da kallo riƙe da takarda a hannu baki a sake..........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
_*⚡NEEHAL⚡*_














_By_
_Zeey Kumurya_














*ELEGANT ONLINE WRITER'S*












*8️⃣8️⃣*


















..........Hafsat tana zaune a ɗakinta tana tunanin Ameen data mayar da shi sana'arta, tun safe take tsammanin zuwansa dan jiya kusan kwana ta yi tana bankad'a magani da turara jikinta. Ɗaya daga cikin masu aikin gidansu ta yi knocking ƙofar ɗakinta, ta bayar da umarnin a shigo. Cikin ladabi Mai aikin ta sanar mata saqo aka bayar aka kawo mata ɗan aiken yana falo. Jikin Hafsat ya bata saqon daga gurin Ameen yake amma mai makon ta yi farinciki sai ta ji gabanta ya faɗi. Miƙewa ta yi suka fito tare da Mai aikin, a main parlour ta tarar da Mom da Aunty Jamila wadda ta zo yiwa Dad sannu da zuwa. Mai gadi dake tsaye ya risina ya gaishe ta sannan ya miƙa mata takardar tare da shaida mata in ji Ameen. Ta karɓa fuskarta da alamun mamaki. Duban Mum ta yi ta ce. "Kin ga wai takarda ce in ji Ameen." Mom ta ce. "Lallai Yaron nan, ya cika shegen miskilancin tsiya, may be ta ban haquri ce ya yo, dan girman kai ba zai zo ya bayar da bakinsa ba sai dai ya rubuto miki a takarda." Hafsah bata kuma magana ba ta buɗe takardar ta fara karantawa. Aunty Jamila dai kallo reaction ɗinta kawai take yi. Wani uban ihu Hafsat ta kurma da ya saka su Mom toshe kunnuwansu ba shiri. Lokaci ɗaya yanayin fuskarta ya sauya gumi ya fara tsatstsafo mata. Ta nufi mahaifiyarta a gigice tana nuna mata takardar da hannunta dake faman karkawa kamar yadda duk jikinta yake yi. Cikin rawar Muryar ta ce. "Mo..Mom..wai ya sake ni, saki ya rubuto mun, Mom ki duba ko idona ne bai gane mun dai-dai ba." Sai ta fashe da kuka. A razane Mom ta karb'i takardar ta duba. Aunty Jamila innalillahi..... kawai take maimaita cikin tsananin al'alabi. Durk'ushewa Hafsat ta yi ta shiga zunduma ihu tana faɗin. "Ameen kar ki yi mun haka Please, ka san ina son ka bazan iya rayuwa babu kai ba, Please ka ce mun wannan takardar bakai ka rubuta ta ba, wani ne ya copy note ɗinka ya rubuta dan ya raba mu. Na shiga uku...." Wani uban ashar Mom ta lailaya ta miƙe tana faɗin. "Lallai wannan yaron ya cika cikakken butulu, shegen yaro ni zai tozarta a idon duniya ya mayar mun da Ƴa ƙaramar bazawara? Lallai zai gane kuren sa a ƙasar nan, sai ya san ya taɓo mu wallahi." Aunty Jamila dake karanta takardar sakin da Mom ta yada a ƙasa ta ce mata. "A'a Yaya mu bi komai a sannu, ai saki ɗaya ne ma, insha Allahu za'a dai-daita su." Mom ta yi mata wani mugun kallo sannan ta juya ta ɗauki wayarta, jikinta na tsuma ta kira Aunty Safiyya ta ce ta zo gida yanzu_yanzu tana son ganin ta. Aunty Jamila ta koma kusa da Hafsah wadda haukan lokaci ɗaya ya kama ta, janyo ta jikinta ta yi ta shiga rarrashinta tana faɗa mata ta kasance musulmar k'warai mana mai yarda da ƙaddararta a duk yanda ta zo mata. Hafsah ko fahimtar abun da take cewa bata yi balle ta saurara. Mom da take jin kamar ta zunduma ihun ita ma irin na Hafsah ko zata ji daɗi a cikin ranta ta yi k'wafa sannan ta latsa wayarta ta lalubo numbern Mama ta yi dialing. Mama tana toilet a lokacin tana alwalar Sallar Magriba kiran ya shigo, ta ƙarasa alwalar ta fito sannan ta yi picking cikin mamakin ganin mai kiran nata, dan kiran farko har ya katse wani ya ƙara shigowa. Mama ta yi mata sallama. Mom bata bi ta kan sallamar ba ta ce. "Hajiya Fateemah kin aura wa ɗanki ƴarki ni kuma ya sakar mun tawa." Cikin shock Mama ta ce. "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, Ameen ɗin? Yaushe?" Mom ta ce. "Ki riƙe sallallaminki zai miki amfani wani lokacin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login