Showing 174001 words to 177000 words out of 262509 words

Chapter 59 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21449

"Mama!" Mama ta sauke wahalallen numfashi muryar Neehal ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi. A hanzarce ta ce. "Na'am, Daughter kin tashi? sannu kin ji." Ta ƙarashe zancen da kama hannayen Neehal duka a cikin nata. Neehal ta gyaɗa mata kanta wanda take jin sa kamar dutsen dala saboda nauyin da yay mata, ta fara hawaye ta ce. "Mama da gaske ne ba mafarki na yi ba Sadik ya ɓata an sace shi?" Mama ta mayar da k'wallar data tarar mata a ido dan kar ta ƙara karyar wa Neehal zuciya ta ce. "Eh Daughter, amma za'a gan shi Insha Allah, ana nan anata neman sa da cikiyar sa tare da addu'a." Neehal ta fashe da kuka mai karyar da zuciya ta ce. "Me nay musu Mama? Su waye suka ɗauke mun Sadik? Me yasa basa san na yi aure kamar kowa? Ya Allah in wani laifin nay maka ka yafe mun w....." Mama tay saurin rufe mata baki tana faɗin. "Ya isa haka Neehal, ki bar wannan maganganun kar ki je ki yi sab'o, gashi baki da lafiya. Ki yi haquri komai kika gani ya samu bawa rubutacce ne a rayuwarsa tun fil azal daga Ubangijin sa, wannan abun ƙaddarar ki ce da mu baki ɗaya, amma baza mu gaji da kaiwa Allah kukan mu ba, da shi kaɗai muka dogara kuma shi zai yaye mana, jarrabawa ce Neehal, kowanne Mumini akwai irin tasa, ki kwantar da hankalin ki Insha Allahu za'a ga Sadik." Ta lumshe ido hawaye masu d'umi na zubo mata, bata taɓa jin ta tsani rayuwarta irin yau ba, ta gaji da cutar da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da ake yi saboda ita. "Ya Allah kar ka ba su ikon cutar mun da Sadik, My Sadik where you? Ka dawo gare ni karka tafi ka barni kamar yadda su Anwar suka tafi suka bar ni Please, i'm in needing you in my life, please my Sadik come back to your wife." Abun da take faɗa a ranta kenan cikin ɗacin zuciya, kamar ta cire zuciyarta ta yar haka take ji saboda zafin da take mata. Har yanzu bata bar fatan ace zata farka daga wannan mummunan mafarkin da take ba, zuciyarta ta kasa yarda cewar da gaske ne abun da yake faruwa. Mama ta d'ago ta tana faɗin. "Tashi mu je ki yi wanka ko zaki ji daɗin jikinki, ki kuma rama sallolin dake kanki, sai ki sha ko tea ne ki sha magani, na ji jikin naki da zafi zau alamun zazzaɓi." Bata musa wa Mama ta ɗaure ta sakko dak'yar tana cize lip ɗinta hannunta dafe da kanta, Mama ta taimaka mata ta kai ta toilet ta yi wanka tare da brush ta ɗauro alwala sannan suka fito, kayan data cire ta mayar ta zira hijabin Mama ta tayar da Sallah, a zaune ta yi sallolin da ake bin ta duka ta haɗa isha'i da ake yi yanzu, ta daɗe tana addu'a cikin kuka a sujjadarta ta ƙarshe akan Allah ya bayyana Sadik, ya kuma kawo mata ƙarshen wannan al'amarin. Bayan ta idar ta lallaɓa ta koma kan gado ta kwanta, Mama bata ɗakin ta fita hado mata tea, wanda tana da yaƙinin a halin k'uncin da take ciki a yanzu ba zai iya shiga bakinta ba balle har ya wuce ta mak'oshinta ya tafi cikinta. Bata san musawa Maman ne kawai, amma ita a yanda take jin zuciyarta da Allah zai ɗauki ranta a yanzu da ta yi murna da hakan fiye da wannan rayuwar da take ciki. Mama ta dawo ɗakin ta ajiye mug ɗin hannunta ba tare da yi magana ba, sannan ta juya ta kuma fita dan ɗauko mata magani, sauri take saboda tana son ta yi ta kawo mata maganin sannan ta je gurin baƙin da suke rage a gidan, dan fiye da rabin mutanen d'azu duk sun koma gidajensu tunda maganar biki ta tashi. Ta buɗe ƙofar falon kenan da nufin fita suka yi karo da Ameen dake ƙoƙarin shigowa...........✍️










*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*6️⃣5️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*














..........Bayan Sadik ya gama cin abinci suka haɗu gaba-ɗaya a Parlour'n Abbansa, shi, Abba, Maamah, Umma, Hajiya, Kawu da mahaifiyar Maamah da ƙannen Abba guda biyu. Abba ne ya fara magana da faɗin. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Masha Allah, muna ƙara godewa Ubangiji buwayi gagara misali, mai mayar da farin ciki zuwa baƙin ciki, da mayar da baƙin ciki zuwa farin ciki. Kwana takwas i war haka zuk'atanmu cikin tsananin farin ciki suke, amma cikin ikon Allah washegari sai ya canza mana zuk'atanmu zuwa baƙin ciki da fargaba da tsoro gami da zullumi. A yau kuma sai ya sauya mana su da tsananin farin ciki, muna fata kuma ya yarje mana mu cigaba da kasancewa cikin farin ciki har ƙarshen rayuwarmu, Ubangiji Allah kar ka ƙara maimaita mana irin wannan tashin hankalin da muka shiga har ƙarshen rayuwarmu." Suka amsa da Amin gaba-ɗayan su. Kawu ya kalli Sadik ya ce. "Masha Allah Abubukar, mun ji daɗin dawowar ka cikin k'oshin lafiya wanda ba mu taɓa zaton haka ba, babu irin sak'e_sak'en da ba mu yi ba akan ɓatan ka, mu ce kidnappers ne, mu ce ko masu satar mutane ne, mu ce ko kai ka gudu da kanka, mu ce ko asiri akai maka ka bazama duniya, babu abun dai ba mu ayyana ba, sai daga baya muka gane bakin zaren, amma duk da haka muna son jin ƙarin bayanin abun da ya faru daga gare ka wanda shi zai sa mu ƙara tabbatar da abun da muke zargi." Sadik ya sauke numfashi cikin sanyin murya ya ce. "Misalin ƙarfe uku na daren ranar ina cikin yin Sallah na ji kamar motsi a bayan ɗakin da nake, wanda ga dukkan alamu ƙofar BQ ta baya ake bugawa da ƙarfi. Na cigaba da Sallah ta ba tare da tunanin komai ba a raina, amma kafin na sallame Sallar na ji an banko ƙofar falo da ƙarfi, gabana ya faɗi ba shiri na sallame Sallar na tashi na je na lek'a window, bana ganin Parlour'n sosai saboda babu wadataccen haske, amma ina iya hango alamun mutane a Parlour'n, kuma ɗakin da nake ciki suke tunkarowa. Na tsaya ina cigaba da kallon ikon Allah, cikin mintuna ƙalilan na ji ana dukan ƙofar ɗakin da nake, na koma bakin ƙofar da sauri na ƙara locked ɗinta, sannan na koma ƙarshen ɗakin ina ambaton sunan Allah tare da neman ɗaukin sa. Kawai sai gani na yi an banko ƙofar ɗakin ta faɗi ƙasa an ɓalle ta ɓal. Na firgita sosai tsorona ya ƙaru, ban gama zullumun ba na ga ana haske ɗakin da wata fitila mai hasken tsiya, sannan aka dallare mun fuskata da ita, hakan yasa ban tantance adadin mutanen da suka shigo ba, balle naga kammanin su, na fara kare idona saboda hasken fitilar dake ƙoƙarin yi masa illa, ba tare da sun ce mun k'ala ba na ji sun watsa mun wani abu a fuska kamar powder, lokaci ɗaya na ji numfashi na yana ƙoƙarin ɗaukewa, kaina ya fara wata irin juyawa, na ji ƙafafuna sun kasa ɗauka ta, na tafi luuu zan faɗi ƙasa, daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba. Sai farkawa na yi na gan ni a wani ƙaramin ɗaki a kwance akan wani ƙaramin gadon ƙarfe. Na shiga bin ɗakin da kallo kwanyata na tariyo mun last abun da ya faru, na yunƙura da sauri da nufin in tashi amma sai hakan ya gagara, na ji jikina kamar ba nawa ba, kamar an zare mun lakar jikina, kamar an zuk'e mun jinin jikina, na kasa d'aga ko da ɗanyatsana ne duk iya ƙoƙarin yin hakan da na yi kuwa. Idanuna ne kawai suke iya aiki a jikina suma ba kamar da ba, dan sun mun wani irin nauyi. Na shiga ƙarewa ɗakin kallo a tunanina ko zan iya tuno ɗakin da nake, ko na taɓa zuwan sa a rayuwata. Amma babu abun da na gane, na kasa tantance dare ne ko rana lokacin. Na lumshe ido ina tunanin me na yi aka kawo ni nan? Su waye suka zo har gida suka ɗauko ni saura awanni kaɗan d'aurin Aure na? Bayan ku san minti talatin ina ta yiwa kaina tambayoyin da ba ni da amsar su na ji an turo ƙofa a hankali an shigo ɗakin, na buɗe idona da sauri ina kallon mai shigowar, wani ƙaton mutum ne dogo fuskarsa a rufe da bak'ar face maks ta roba, ƙwayar idanunsa kawai ake gani wanda suka kasance jajaye ne. Na buɗe bakina da na ji ya mun nauyi da ƙyar na ce. "Who are you? What do you want to me?" Kamar da dutse na yi magana bai ce mun k'ala ba, ƙarasowa kawai ya yi ya tattab'a jikina, ni kuma ina cigaba da yi masa tambayoyin dalilin da yasa suka kawo ni gurin. Ya fita bayan ya gama tattab'a jikina, jimawa kaɗan ya dawo da abinci da ruwa a hannunsa, ya ajiye a gefen gadon sannan ya tayar da ni zaune, ya buɗe abincin ya turo mun gabana sannan ya tashi ya fita. Na bi shi da kallo har ya fice, ban ko kalli inda abincin yake ba balle na yi tunanin ci. Bayan wasu mintuna ya ƙara dawowa ɗakin, ganin ban ci abincin ba sai ya kalle ni kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Ya rufe abincin ya kamani na tashi ina jin jikina kamar ba nawa ba saboda rashin k'wari, wata ƙofa dake cikin dakin ya nufa da ni, yasa hannu ya tura ƙofar ta buɗe sannan muka shiga, ashe toilet ne. Ya zaunar da ni akan toilet sannan ya juya ya fita, na gane mai yake nufi in ina jin wani uzurin in yi kenan. Na tashi da ƙyar ina layi na kunna pampon sink na yi alwala, duk da ban san ƙarfe nawa ba, ban kuma san sallar da zan yi ba, amma na san a lokacin baza a rasa sallar da ake bina ba wadda ban yi ba. Bayan na idar da alwalar na fito dak'yar ina jin kamar iska zata ɗauke ni saboda rashin k'warin jiki. Na tarar da darduma a shimfid'e a tsakiyar ɗakin, bangon ɗakin kuma ta inda dardumar take fuskanta alamun nan ne gabas an saka wani ƙaton agogon bango mai 24 hours a jikinsa, na ga a lokacin ya nuna ƙarfe bakwai da mintuna na safe. Sai dai na kasa gane time ɗin na wacce rana ne, safiyar ranar juma'ar d'aurin Aure na ce ko kuma wata ranar ce daban? Na ƙarasa gaban agogon sai na ga ashe har da rubutun days mitsi_mitsi a cikin sa, a yanda ya nuna kuma safiyar ranar juma'a ce. Na sauke ajiyar zuciya sannan na tayar da Sallah, na yi Sallar asubahin dake kaina. Bayan na idar na zauna na rafka tagumi zuciyata cike da tsantsar tashin hankalin sabon al'amarin da ya same ni, wanda ban san dalilin sa ba amma na fawwalawa Allah komai, na shiga roƙon sa akan ya kare ni daga dukkan wani mai nufi na da sharri mutum ko na aljan. Sai kuma na fara tunanin gida da mahifina da sauran ƴan'uwa, dan na san zuwa yanzu an farga da rashin gani na a gidan, an fara nema na hankali a tashe. Ina zaune inata tunanen gida da dalilin sato ni da aka yi aka kawo wannan gidan har goma na safe ta yi. Na tashi da sauri kamar wanda aka tsikara na nufi ƙofar ɗakin na fara ƙoƙarin buɗewa amma na jita a kulle gam, ni kuma jikina babu k'wari balle na yi yunƙurin buɗe ta. So nake in yi ihu ko wani zai jiyo ni ya kawo mun ɗauki amma k'warin muryar ihun ma bani da shi. Idan na tuna ranar ne fa d'aurin Aure na sai hankalina ya ƙara dugunzuma ya kai k'olokuwar tashi. Na zube a bakin ƙofar jin jiri na neman yarda ni, babu irin tunanin da ban yi ba akan kawo ni gurin da akai. Na ce ko wani abokin aikina ne yake jin haushina yasa a sato ni? Ko kuma kidnappers ne? Ko kuma wani case ɗin na yi daya ɓata wa wani rai ya k'ullace ni? shine zai saka a zato ni ranar Aure na a matsayin ɗaukar fansa. Ni kaɗai a ɗakin babu alamar wani yana inda nake, ko kukan tsuntsu ban ji ba balle na wasu dabbobin ko na mutum. Ina nan zaune aka buɗe ƙofar ɗakin aka shigo, na d'ago da sauri sai na ga mutumin d'azu ne, hannunsa ɗauke da take away da ruwa da lemo, ya ajiye a gabana ba tare da ya yi magana ba ya juya ya fita. Ni kuma kamar an ɗaure mun baki na kasa yi masa magana, duk da tarin tambayoyin dake raina. Na yi ball da abincin da ƙafa cikin tsananin takaici, na san zuwa lokacin ahalina da abokan arzik'i da amaryata suna can cikin tashin hankalin ɓata na.








Haka na wuni ni kaɗai a ɗakin cikin tunanin mafita, Sallah ce kawai take tayar da ni idan na ga lokacin ta ya yi. Har bayan Magriba ko ruwa ban kurb'a na saka wa cikina ba, yunwar ma da ƙishirwar ko jin su bana yi, ko ma ina ji bata su nake ba. Kafin isha'i mutumin ya ƙara dawowa ya kawo mun wani abincin da ruwan. Na tashi da sauri cikin ƙarfin hali dana zuciya na cakumi mutumin ina tambayar sa dalilin yasa suka kawo ni nan? Me nay musu? Kamar wani kara haka mutumin ya yakice ni daga jikinsa ya dank'wafar da ni a ƙasa ya juya ya fice. Na rarrafa a ƙoƙarina na ganin na riƙe ƙofar kafin ya rufe, amma tuni ya ja ta sai motsin saka mukulli a jikinta na ji. Na kwanta akan carpet ɗin dake malale a ɗakin cikin tsananin damuwa. Sai da takwas ta wuce sannan na miƙe ina layi na shiga toilet na ɗauro alwala na yi Sallar isha'i, na ƙara da nafila a cikin kowacce sujjada ta ina roƙon Allah ya fitar da ni daga cikin wannan riskin da nake ciki. Ina kan sallaya mutumin ya sake shigowa, na zuba masa ido in ga mai kuma ya shigo yi, da yake ɗakin akwai hasken wani farin k'wan wuta guda ɗaya dake sak'ale a bango. Ga mamakina sai na ga ya kama ni ya kai ni kan gado ya kwantar, na bishi da kallon mamaki, ban gama mamakin ba na ji ya juya ni gefe ya d'aga jallabiyar jikina ya tsikara mun allura. Daga nan na fara ganin bibbiyu, cikin mintuna ƙalilan bacci ya yi gaba da ni. Ban farka ba sai ƙarfe shida saura na safe, na bi ɗakin da kallo, sai na ga fankar sama tana wulwulawa, na juya b'arin damana sai na ga Television ta bango manne a bangon dakin, sai wani abu mai kama da GO TV a ƙasan ta da remotes biyu a kansa. A gefen ta kuma wani ɗan table ne an ɗora Alkur'ani izifi sittin akai. Mamaki fa ya kusa kashe ni, na shiga tambayar kaina abun da mutanen nan suke nufi da ni? Ko duk a cikin salon cutarwar da za su mun ne? Ko kuma wani abu suke nema a guri na? Na yunƙura na tashi sai a lokacin na lura da bargon dake lullub'e a jikina, kaina kuma ashe akan pillow yake. Sai na rasa da yaran da zan fassara wannan al'amarin da na tsinci kaina a ciki. Haka na yunƙura na sakko daga kan gadon, jikina a matuƙar sanyaye kamar jiya na nufi toilet. In tak'aice muku zance haka na kasance a cikin ɗakin nan, kullum za'a kawo mun abinci da ruwa da lemo safe, rana, dare. Da farko bana ci, sai daga baya dana ji yunwa na neman yi mun illa sannan na fara ci ba don daɗi ba. Kuma duk dare sai mutumin nan ya mun allurar nan, wanda na fuskanci ta bacci ce, amma asuba tana yi zan farka. Hakan yasa jikina kodayaushe babu k'wari, ya yi mun wani irin lagwab. Ban taɓa wanka ba sai sau ɗaya da na ji kamar zan mutu saboda k'aik'ayin da jikina yake mun, a toilet ɗin akwai kat'on soap na wanka da toothpaste da brush sabo. Tun ina tambayar mai kawo mun abinci wanda ban taɓa ganin fuskarsa ba dalilin da yasa suka ɗauko ni suka ajiye ni a gurin, har na haqura na daina na zubawa sarautar Allah ido da ganin iya gudun ruwan su, amma har na baro gurin ba su taɓa ƙoƙarin cutar da ni ba, Alkur'ani nan shi ya zamo abokin hira ta, shine nake karantawa wuni guda cur, hakan yasa nake samun nutsuwa a cikin zuciyata. Kwana na huɗu aka kawo mun jallabiya guda biyu da ƙaramin wando, da har na ƙi sakawa sai kuma na ɗauka na saka, da na yi tunanin ina Sallah kar kayan jikina su yi dattin da baza su yi Sallah ba, Tunda ban san ranar fita ta daga gurin ba. Jiya da ya kasance kwana na shida a wannan ɗakin na lek'a waje ta window, sai na fuskanci kamar gida ne inda nake ciki, saboda dana lek'a like bayan gida na gani. Yau na tashi kamar kullum na yi Sallah na ɗan taɓa abincin da aka kawo mun kaɗan, sannan na ɗauki Alkur'ani na fara karatu. Wajen sha biyu lokacin na ajiye Kur'anin inata ta tunane_tunane na, mutumin nan ya shigo ɗakin. Ya ɗauke Alkur'anin gaba na ya ajiye akan table ɗin nan, sannan ya fito da wani baƙin k'yalle ya ɗaure mun idanuna tamau, ina tirje_tirje da yi masa ihun ya rabu da ni amma bai kula ni ba. Na ji an ƙara buɗe ƙofar ɗakin an shigo, daga nan kuma sai ji na yi sun kama ni mun fice daga ɗakin. Inata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login