Showing 6001 words to 9000 words out of 262509 words
Chapter 3 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
ta ce "Akwai patients d'in da zan duba ne" Neehal ta ce "Toh, idan mun tashi zan biya Zoo road na siyo popcorn a'one" Mama ta ce "In ma a 10 ne ba damuwata ba ce, kin san Yayanki na gida ai, 8: 15 in ba ki dawo ba, ke da shi ne" Neehal ta ɓata fuska ta yi gaba, Haneefah ta yi wa su Mama sallama, Mama ta musu addu'a suka tafi, Hajiya na faɗin "Wai yaushe zaku kai ni gidan talabijin d'innan naku ne nima a hasko Ni a ciki?" Suna jin ta suka mata shiru. Parking space suka nufa suka shiga Mota Driver'n Neehal ya ja su zuwa *ASTV* fitaccen gidan TV'n da ya shahara a nan ƙasarmu Nigeria dama nahiyar Africa baki ɗaya.
Ƙarfe 8 kamar yadda Neehal ta ce suka tashi daga gurin aiki, bayan sun gama gudanar da shirin *'Yancin mata* wanda suke yinsa duk Ranar Asabar da misalin ƙarfe 7 na dare zuwa 8. Su na gamawa suka yi sallama da ma'aikatan gidan TV suka nufo gida, Neehal ta yi_ta yi Haneefah ta bita ta gidansu kamar yadda take yi wani lokacin amma ta ce ita gida za ta wuce, sai da suka biya suka fara sauke ta sannan suka wuce, da yake duk ba su da nisa, gabad'aya a cikin Nasarawa G.R.A suke har ASTV'n. Driver na parking Neehal ta fito, ganin Motar Dad a gurin alamun ya dawo ta ji daɗi a ranta, dama yau gabad'aya ta yi missing ɗinsa. Part d'in Mama ta nufa, ta shiga falon bakinta ɗauke da sallama, gabantane ya faɗi ganin Ameen zaune shi kaɗai a falon ya na latsa waya..........✍️
*Ku yi haƙuri da wannan, har yanzu jikinnawa ne sai addu'a, dan kar ku ji shiru ma yasa na yi wannan ɗin, insha Allah next page za mu shiga cikin gundarin labarin, Nagode da addu'oinku Masoya.🙏❤️*
*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*0️⃣5️⃣*
.............Tab'e ɗan ƙaramin bakinsa ya yi tare da ɗauke kansa daga inda suke. Neehal ta janye hannunta ta na sauke Numfashi ba ta ce komai ba, saboda abun ya mata wani banbarakwai, duk da Anwar ko hannunta bai taɓa riƙe wa ba amma sai ta ji wata irin kunyarsa ta rufe ta. A hankali ta daure ta ce "Nagode sosai Ya Anwar" Anwar ya yi murmushi ya ce "Kin ga yanda hannunki ya yi wa zoben kyau kuwa?" Neehal ta yi ɗan murmushi idanunta na kan hannunta da zoben yake sanye dass kamar an gwada ta ce "Hannun nawa ne ma ya yi wa zoben kyau, ba ma zobenne ya yi wa hannuna kyau ba?" Anwar ya ce "Eh mana, ai ke ko kwalliya ki kai ke ki ke wa kwalliyar kyau ba ita take miki ba" kafin Neehal ta ce wani abu Ameen ya ƙaraso kusa da su, Anwar ya yi sauri ya ce masa "Yayanmu Barka da dare" Ameen ya ɗan saki fuskarsa ya na mik'owa Anwar hannu ya ce "Yawwa barkan mu" suka yi musabaha Anwar ya gaisheshi ya amsa sannan ya wuce ba tare da ya kalli ko inda Neehal take ba, saɓanin ita kuma da ta zira masa na mujiya. Anwar ya kalle ta ganin ta bi Ameen da ido ya ce "Ya dai Queen?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya, zuciyarta babu daɗi ganin yanda Ameen ya shareta, ya ƙi kulata, Alhalin yau ba su haɗu ba kwata_kwata, ta rasa me yasa kwana biyunnan yake mata haka, duk da ma can shi mutum ne ba mai sakewa ba kuma ga miskilanci, amma ya na nuna mata kulawa sosai a matsayinta na k'anwarshi tilo guda ɗaya...... Anwar ya katse mata tunaninta ta hanyar faɗin "Wai me yake farune na ga kamar kina cikin damuwa Neehal?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya a karo na biyu ta ce "Bakomai Ya Anwar" ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai kawai tare da ƙoƙarin boye damuwarta dan kar ya fuskanci wani abu. Anwar ya duba tsadadden agogon hannunsa ya ce "Shikenan Queen bari na je gida na ga time ɗin Sallah ya yi" Neehal ta ce "Ba ka ci cake din ba kuma?" Ya ce "Na k'oshi ne" Neehal ta bata fuska ta ce "Please ya Anwar ka ci mana" ba tare da ya ce komai ba ya buɗe Plate d'in da'aka rufe cake d'in ya d'au 1 ya gutsira ya ajiye, ya na kallonta ya ce "Thank you" Neehal ta ce "Ka ƙara Mana, wannan ai baka ci ba" ya ce "I'm sorry dear, ciki na ya cika ne" Neehal ba ta kuma komai ba, Anwar ya Mik'e ya ce "Bye sai mun yi waya?" Neehal ta mik'e ta na faɗin "Mu je in raka ka" Suka jera su na tafiya har inda ya yi parking Motarsa ta raka shi, tsayawa su ka yi ta dubeshi ta ce "Thank you so much ya Anwar for your time, da kuma kyautar da ka ba ni, Allah ya sa ka da Alkhairi ya ƙara buɗi" Anwar ya ce "Ni ma Nagode sosai dear, kuma na ji daɗi, Allah ya barmu tare" Neehal ta ce "Amin, Allah ya kiyaye hanya ya tsare, ka gaida Ammi" ya ce "Amin, za ta ji Insha Allah bye" Neehal ta ɗaga masa hannu ta na murmushi, shima d'aga mata hannun ya yi ya buɗe motar sa ya shige" Neehal ta juya ta koma cikin gida. Su Dije ta faɗa wa su je su ɗauko cake ɗin su cinye, Mama da Hajiya duk suna ɗaki tasan jiran Sallah su ke yi, itama ɗakinta ta shiga ta faɗa toilet ta dauro alwala ta fito ta bi jam'i itama.
Misalin ƙarfe tara na dare Hajiya ce zaune a falon sama ita da Ameen, Hajiya sai washe baki take tana zubawa Ameen hira, da alama dai ya cika mata aljihunta da kuɗi, Neehal ce ta fito daga ɗakinta, ganin Ameen ta ɓata fuska tare da turo baki gaba, Hajiya ta bi ta da kallo ta ce "Har Auwar ɗin ya tafi?" Neehal ta gyad'a mata kai kawai, Hajiya ta ƙara faɗin "To kuma mene ki ke ta ɓata rai, kamar za ki kai duka?" Neehal ba ta kula ta ba ta zauna a kasan kujerar da suke. Ameen ya d'ago ya na kallonta a hankali ya ce "I saw your missed call since?" Neehal ta ce "Uhm" kawai, ya ce "What Happen?" muryarta na rawa ta ce "Nothing" ƙoƙarin maida kwallar da ta cika mata ido ta yi, wadda batasan dalilin ta ba. Ameen ya maida hankalinshi kan wayarsa bai ƙara cewa komai ba, Neehal ta tashi ta koma ɗakinta.
Ta na shiga ta hango wayarta na haske alamun a na kira, ɗauka ta yi ta duba ta ga Anwar ne, ɗaga wa ta yi ta kara a kunnenta ya yi sallama ta amsa masa ta ƙara da faɗin "Ka je gida lafiya?" Ya ce "Lafiya ƙalau" Ta ce "Nagode fa ya Anwar sosai" Ya ce "Kin san fa ban san yawan godiyar nan, kin kai na miki komai Neehal a rayuwarnan, kuma kin san wani abu?" Neehal ta ce "A'a" Ya ce "Wannan ring d'in kyautar da na ajiye zan miki ce ranar aurenmu, kuma kawai sai na canza shawara na ce bari na kawo miki kawai" Neehal ta ce "Aiko na ji daɗi sosai Ya Anwar ɗina, Allah ya bar k'aunah." Ya ce "Ameen My Queen." Hirarsu suka cigaba da yi cikin nishaɗi, duk da Neehal ba ta wani jin daɗi a ranta kawai daurewa ta ke yi.
Washegari gari Uncle Mahmud k'anin Mama ya zo da sassafe ɗaukar Hajiya za su wuce Gombe, Neehal kafin ta wuce School suka yi Sallama dan lecture din safe gareta. Kwanaki na ta tafiya Rayuwa ta na wucewa, sai gashi har satika huɗu sun shud'e, a wannan week ɗinne kuma su Neehal za su gama exam ɗinsu ta second semester Level two (2), sosai Neehal ta zama silent saboda kusantowar bikinta, Tsakaninta da Ya Ameen kuwa ba ta sauya zani ba, tsakaninta da shi gaisuwa ce kawai sai kuma kyauta da tsarabar da yake yo mata a duk satin duniya idan ya dawo gida weekend bai fasa mata ba, amma kwata_kwata ba ya sakewa da ita, ita kuwa Neehal hakan ba ƙaramin damunta ya ke ba.
Yau Laraba ƙarfe 12 Neehal ta fito daga exam, ta na cikin tafiya ta ji a na kiranta da faɗin *"Fateema Tafeedah*" juyawa ta yi ta ga best freind ɗin ta ce a school ɗin Zee, tsayawa ta yi har Zee ta ƙaraso inda take, Zee ta ce "Fateemah tafiya za ki yi" Neehal ta ce "Ehh" Zee ta ce "Tun yanzu, yau ba shiga Library kenan?" Neehal ta ce "Na gaji ne, bacci ma nake ji, da daddare kawai na yi karatun" Zee ta ce "Ok sai mun yi waya tunda gobe bamu da exam" Neehal ta ce "Ba za ki zo ke da su Meesha ku karb'i Ankonku ba?, gobe fa Aunty Sadiya za ta kawo duka" Zee ta ce "Allah ya kai mu goben, za mu shigo da yamma mu karb'a insha Allah" Suka yi sallama Neehal ta tafi. Ta na zuwa gida ta wuce sama ta shiga ɗakinta ta kwanta ta na tunanin rayuwarsu tun daga k'uruciya, haka kawai ta ji kuka ya kufce mata ta shiga rera shi, sai da ta ga ji dan kanta ta yi shiru, dan babu mai rarrashin ta a kusa, Toilet ta shiga ta dauro alwala ta dawo ta zauna kanta na mata wani irin ciwo, ga yunwa dake nuk'urk'usar cikinta dan bata karya ba ta tafi school. Da k'yar ta daure ta yi Sallar sannan ta sakko ƙasa, tea ta haɗa mai kauri tasha, duk da tasha tea d'in amma ba ta dena jin ba daɗi a jikinta ba, haka dai ta daure ta shiga kiciniyar ɗora girki kar Mama ta dawo ta tarar ba ta yi ba. Washegari ta tashi ba ta jin daɗin jikinta ko kaɗan, amma ta ta'allak'a hakan da period ɗinta da ya kusa, dan ta na cin wahala ba kaɗan ba idan za ta yi. Ta na kwance a kan gadonta lullub'e da duvet Mama ta shigo ɗakin, Janye duvet d'in Mama ta yi ta na faɗin "Neehal wanne irin bacci ki ke haka har 10 ta wuce ba ki tashi ba?" Neehal ta buɗe idonta a hankali ta ce "Ba na jin daɗi ne Mama" Mama ta ce "Ayya sorry Daughter, Month ɗinki ya yi ko, ki tashi ki lallaɓa ki yi wanka ki sha ko tea ne, sai kisha magani" Neehal ta ce "Ai bai zo ba,ciwon kawai na ke ji" Mama ta ce "Ki dai tashi ki sha" Neehal ta yunk'ura ta tashi zaune tana taune lips d'inta.
Ƙarfe 12 Aunty Sadiya ta ƙaraso gidan da atamfofi da leshuka da yadin bridal shower na k'awayen amarya, aka zube su a falo. Neehal ta na kwance a kan doguwar kujera ba ta ko motsa ba duk da ta na jin duk budurin zuwan Aunty Sadiyan, sai ma runtse idanunta da ta ƙara yi zuciyarta na bugawa. Aunty Sadiya ta kalli sashen da take ta ce "Neehal lafiya kuwa take bacci da ranar nan?" Mama ta ce "Ba ta jin daɗi ne, ciwon mararta ne ya tashi, amma na bata magani tasha, shine bacci ya ɗauketa" Aunty Sadiya cike da tausayawa ta ce "Ayya Allah ya ba ta lafiya, Amarya ba lafiya ai babu kanta, dan ma insha Allahu ta na yin Aure za ta dena ciwon marar" Mama ta ce "Allah ya sa, kin san ta da shegen shan zak'i kamar me, na hanata na hanata amma ta ƙi denawa" Aunty Sadiya ta ce "Allah ya sauwak'e, bari na kira Haneefah ta zo ta ɗibi na freinds ɗinsu" Mama ta ce "Ya kamata kam, tunda bikin ya matso su kai ɗinkuna, nima bari na ɗibi na mutanena." Su na duba kayan su na cigaba da tattaunawa akan bikin, Mama ta na sanar da Aunty Sadiya Abubuwan da za'ayi, ba wani jan bikin za'ayi ba, Events uku kawai za'ayi, daga Kamu/Mother's day, sai Dinner da Yini, sai bridal shower na k'awayen Amarya. Gabad'aya sun riga da sun yi bucking na events din da za'ayi, duk wata siyayya ta Amarya itama sun kammala ta, yanzu lefe kawai suke jira sai a sanya satittikan bikin. Sai da Haneefah ta zo sannan ta tashi Neehal daga baccin gasken da ya d'auketa, ta tashi zaune ta na taune lips ɗinta, ka na ganinta ka ga mai cuta, Aunty Sadiya da Haneefah suka shiga yi mata sannu. Mama ta kawo mata abinci ta ɗan tsakura ta ci ta ƙara shan magani, ranar dai haka ta wuni ba ta jin daɗi, Anwar da su ka yi waya hankalinshi ya tashi da ya ji ba ta da lafiya, sai da ya zo ya duba ta da daddare hankalinsa ya ɗan kwanta, tun da ya ga jikinta ba rijib take a kwance ba. Washegari, ta tashi jikin nata da sauƙi, dan period d'in nata bai zo ba har yau, yau ma exam d'in safe ce da su, amma ba ta dawo ba gida da wuri ba, saboda sun tsaya ɗaukar pics da friends ɗinta, tunda sun gama exam d'in sai dai fatan samun result mai kyau, suka yi sallama da freinds ɗinta su na faɗin sai sun zo bikinta, ita dai Neehal yaƙe kawai take yi dan zuciyarta babu daɗi ko kaɗan. Ta na dawowa gida Mama ta sanar mata da zuwan wadda za ta mata gyaran jiki daga Maiduguri gobe Insha Allah, Hajiya ma goben za ta zo tunda ran Lahadi za'akawo lefe amma maza ne za su kawo.
Da daddare Neehal ta na kwance a ɗakin Mama, sai juyi take akan gado saboda murd'awar da cikinta yake mata, hawaye ne kawai yake fita daga idanunta, wani amai ne ya taho mata ta tashi da gudu ta nufi toilet ta shiga kelayashi, ta na yin aman ta na jin fitar jinin a jikinta, Ta na sassauke Numfashin azaba ta gyara jikinta ta sanya pad, kuskure bakinta ta yi ta janyo ƙafarta da ta fara riƙe mata ta dawo ɗaki ta kwanta. Mama ta shigo ɗakin ta dube ta cikin tausayawa ta ce "Sannu Daughter ya jikin?" Neehal ta ɗaga mata kai kawai, Mama ta ce "Allah ya ƙara sauƙi" Sosai Mama take tausayin Neehal lokacin period ɗinta, saboda azaba take sha ba ta wasa ba, ciwon mara, baya, k'ugu duk take yi, ƙafafunta duka su riƙe, yau ko gurin aiki ba ta je ba, sai Haneefah ce ta je ta maye gurbinta. Time ɗin da Dad ya zo dubata bacci ya ɗauke ta. Washegari dai da ta tashi jikin nata da sauƙi sai dai ba ta warware tas ba. Da safe ta na cin Irish da soyayyen kwai ɗin da Mama ta kawo mata ta tilasta mata ta sha Ameen ya shigo ɗakin, jin kamashin turarensa ya sa ta d'ago kanta da sauri ta na kallonsa, gabanta ne ta ji ya fad'i ba ta san dalili ba, satar kallonsa ta shiga yi ta ga ya canza sosai ba kamar kwanaki ba, ramar da ya yi duk babu ita sai ma wani fresh da haske daya ƙara, lumshe idonta ta yi a hankali ta ce "Ina kwana?" Kamar bai ji ba sai kuma can ya ce "Lafiya, ya jikin? Ba ta yi mamakin sanin ba ta da lafiya da ya yi ba, domin kowa na gidan ya san time ɗin period ɗinta saboda azabar da take sha a lokacin yin period ɗin nata. Cikin raunin murya ta ce "Da sauƙi" Juyawa ya yi ya fita ganin Mama batanan, a falon ƙasa su ka haɗu da Mama ta dawo daga part din Dad, Mama ta na dubanshi ta ce "Welcome, har ka zo kenan?" Ya ce "Ehh, ina kwana?" Mama ta ce "Lafiya ƙalau, ya aiki" Ya ce "Alhamdulillah, ya naku?" Mama ta ce "Lafiya ƙalau" Zai nufi part d'in Dad Mama ta ce "Idan ka dawo ina son ganinka" Ya ce "Toh." Misalin ƙarfe goma na safe Aunty Sadiya da Aunty A'isha da yarinyar gurinta Maryam su ka zo gidan, domin yin snacks na karɓar kayan lefe, Neehal dai ta na shan Magani ta kwanta bacci ya ɗauketa dan jiya ba ta samu wani baccin kirki ba, saboda ciwo. Yauma ba ta samu damar zuwa gurin aiki ba, Hajiya da yamma ta ƙaraso gidan da tulin kayanta dan sai bayan biki za ta tafi, wadda za ta yi wa Neehal gyaran jiki Mama ta kira ta, ta ce ta bari sai Monday tun da Neehal ɗin ba ta jin daɗi. Bayan sallar isha'i bayan su Mama sun gama aiki ta samu Ameen a ɗakinsa, Ameen ya tattara duka hankalinshi akan Mama jin ta ce za su yi Magana. Mama tana dubanshi ta ce "Gobe za ka koma Lagos ko jibi?" Ya ce "Gobe da safe" da mamaki Mama ta ce "Da safe kuma?" Ya ce "Ehh" Ta ce gobe fa za'akawo lefen Neehal kuma sai da yamma, kuma maza ne za su kawo" Ya ce "Am sorry Mum, amma ba zan samu damar tsayawa ba, dan akwai wani important thing da zan yi" Mama ta ce "Sunday ce fa, saboda gudun haka fa ya sa aka sa weekend, kar wani uzurin ya tsaida wani" ya yi shiru bai ce komai ba, Mama ta mik'e ta ce "Dole ne koma uzurin mene da kai ka jira a karb'i kayan da kai, ka ji na faɗa maka" Ta na faɗin haka ta fice daga ɗakin, Ameen ya bita da kallo.
Washegari Sunday Ranar kawo kayan lefe, tun safe su Mama su kai packagin kayan snacks d'in da soyayyen naman kaza gami da lemuka, yamma kawai suke jira masu kawo kayan su zo. Neehal yau ta lallaɓa ta shirya ta tafi gurin aiki, duk da Mama ta so hanata amma ta ce mata ta ji sauƙi za ta iya zuwa. Mama na kitchen Ameen ya shigo ya same ta da shirinsa na tafiya. Mama ta masa wani kallo bayan ta amsa sallamar da ya yi, Ya ce "Ina kwana Mum" Mama ta ce "Lafiya k'alau" Ya ce "Am sorry Mum zan wuce Lagos