Showing 246001 words to 249000 words out of 262509 words
Chapter 83 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
yar'mutan kankia
*Promo* *Promo* *Promo*
Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake.
#300-sau biyu a rana
#500 -sau ukku a rana
#700 -sau hudu a rana
Kiyi man wanann number magana danjin ynda zaki biya 08160508316
.........Cikin one week Ameen ya koyawa Neehal son sa da k'aunarsa, wata shak'uwa ce ta ƙara shiga tsakaninsu mai ƙarfin gaske, a yanda suke jin junansu a zuk'atan su ko 1 second basa son su yi ba tare da junansu ba. Ameen ƙarshe ne a iya soyayya da kula da tattali da tarairayar mace. Through out yana gida manne da Baby love ɗinsa suna zuba k'auna, Sallah ce kawai take fitar da shi zuwa Masallaci, sai kuma idan ta yi baƙi, dan kusan kullum a cikin Family ko friends ɗinta wasu sai sun zo mata, Haneefah ma ta zo ta wunar mata. Neehal ta yarda ta kuma gasgata cewa Ameen ba ƙaramin so yake mata, kwata_kwata yanzu babu wannan miskilancin bare haɗe rai. Ita ce ma take ɗan taɓa masa idan class ɗin ya motso mata. Neehal an samu abun da ake so tay ta zuba masa shagwab'a yana lallab'a ta. Sai dai har yanzu bata daina jin kunyarsa ba, tana dai ɗan daurewa ta ƙoƙarta ta nuna masa soyayya dan ta lura yana jin daɗin hakan sosai. Za su wuni tare manne da juna sai dare ya yi ta gudu ɗaki ta kulle, shi kuma ya yi amfani da spare key ya buɗe ɗakin ya bita ya nuna mata bai san wannan zancen ba, tay ta bab'b'ata fuska tana rigima amma duk da haka sai ya yi abun da take gudun, idan ya gama sai ya shiga aikin rarrashi.
Yau asabar, wanda ya kama kwana takwas da tarewar Neehal. Misalin ƙarfe goma sha biyu na rana tana tsaye a kitchen tana aikin girkin rana. Sanye take cikin wani straight skirt Black colour mai tsaga a baya, sai riga mai ƙaramin hannu light Brown, irin roban nan ce mai bin jiki, ta kama jikinta sosai. Kanta babu ɗankwali sai bana data saka kalar rigar jikinta, ta yi parking ɗin gashinta sai sheƙi yake ya sha oil na man kitso mai ƙamshi. Sauri take yi ta kammala aikin nata kar Ameen ya tashi daga baccin data bar shi yana yi, tun bayan kwana uku da Mama ta daina kawo musu abinci ita take girkinta. Idan zata yi girkin kodayaushe Ameen yana manne a jikinta, duk inda ta ɗora ƙafarta nan zai saka tashi, in ta yi complain ya ce taya ta aikin yake yi, alhalin ba haka ba ne delay ma yake ja mata a aikin nata, abun da zata yi shi in one hour sai ta yi kusan 2 hours. Tana aikin tana tunanin a ka'ida fa jiya Ameen zai bar gidanta ya koma gidan Hafsah, amma sai ta ga ya ƙara kwana. Ta yi ta mamakin abun amma dai bata yi masa magana ba, yau ma kuma ta ga bashi da alamar zuwa gidan Hafsan. Amma ta ƙudurce a ranta zata yi masa magana anjima akan hakan.
Ƙamshin turaren Ameen ta ji ya cika mata hanci da kuma sign na ana kallon ta, ta juya da sauri ta gan shi tsaye yana kallon ta, jikinsa sanye da single da threequarter wando. Bata ce masa komai ba ta juya ta cigaba da aikinta. Ya ƙarasa inda take a hankali ya rungume ta, ta baya tare da sakin ajiyar zuciya. Ta lumshe ido ta buɗe ta juya tana kallon shi tare da ɓata fuska ta lakuce masa hanci ta ce. "Wa ya ce ka tashi yanzu?" Ya langwab'ar kai ya ce. "Saboda kin tashi mana." Ta ɗan ture shi ta ce. "Ka koma baccinka ka bar ni in yi aikina." Ya jingina da jikin cabinet bai ce komai ba, sai kalar tausayi da ya yi da fuskarsa kamar sabon maraya. Ta juya ta cigaba da aikinta tana murmushi ƙasa_ƙasa. After 5 minutes ta juyo ta ce masa. "Ya da shiru kuma?" Ya ɓata fuska kamar wani yaro tare da ɗauke kai. Ta ƙarasa jikinsa ta saka hannayenta duka ta zagaye wuyansa ta ce. "Wa ya taɓa mun Yayana a tsakar ranar nan?" Bai kalle ta ba shi a dole fushi yake ya ce. "Ke ce mana, na zo zan taya ki aiki kin gwale ni." Ta kwanta a jikinsa ta ce. "Ka taya ni aiki ko ka ƙara mun wani aikin?" Ya zagaye bayanta da hannunsa ya ce. "Duk a cikin tayin aikin ne ai." Ta ɗago daga jikinsa ta ce. "To mu je a taya nin." Ya yi murmushi yana bin ta da kallo. Ta juya masa ido. Ya ƙara janyo ta jikinsa ya ce. "Ko dai barin aikin nan zamu yi ne mu je mu yi wani." Cikin shagwab'a ta ce. "Um,um Yaya baƙi fa zamu yi, sai sun zo bamu tanadar musu komai ba." Ya kwantar da kansa akan kafaɗarta bai ce komai ba. A haka ta cigaba da aikin yana jikinta kamar kullum. Sai da aka kira Sallar Azhar sannan ta samu ya bar ta ya tafi masallaci.
Bayan sun ci abinci sun yi wanka sun shirya suna zaune a parlour akan kujera 2 seater suna game a wayar Neehal aka yi knocking ƙofar parlour. Neehal ta bar jikinsa tana dariya ta yi masa gwalo sannan ta tashi cikin sauri dan kar ya cafko ta, ta nufi ƙofa. Haka take yi masa kodayaushe idan ta yi baƙi, ya yi murmushi tare da yi mata alamar zan kama ki ne. Kamar yadda ta zata Salma ce wadda ta raka ta gidansu Sadik ita da sistern ta. Neehal ta ce. "Sannunku da zuwa, amma fa na yi fushi sai yanzu zaku zo?" Salma ta ce. "Ki yi haquri, sai da muka yi girki ne." Neehal ta ba su hanya suka wuce sannan ta mayar da ƙofar ta rufe. Suka gaisa da Ameen cikin mutuntawa da fara'a sannan ya tashi ya shige ɗakinsa. Neehal bata zauna ba sai da ta kawo musu drinks da abinci da kayan snacks ɗin gararta. Suka ƙara gaisawa sannan Salma ta ce. "Amarya kin sha ƙamshi, kin ga yanda kika yi kyau kuwa? Anya kuwa idan Mama ta gan ki zata gane ki?" Murmushi kawai Neehal ta yi dan ita akaran kanta ta san cikin one week ɗin nan ta sauya. Sai bayan Magriba su Salma suka tafi, saurayin Salman ne ya zo ɗaukar su, har bakin Motarsa ta raka su. Ga mamakinta sai ta ga Sadik ne. Ta riƙe haɓa tana kallon sa cikin tsananin mamaki, shi kuma ya shiga tsokanarta da amarsu ta Ango yana murmushi. Ta dubi Salma zata yi k'orafi Salman ta yi saurin ce mata. "Bari na yi ki gani da idonki dama." Suka yi dariya gaba-d'aya sannan ta yi musu fatan Alkhairi suka yi sallama ta koma cikin gida, a ranta tana jin daɗin haɗewar Salma da Sadik . Da daddare suna shan fruits a falo ta dubi Ameen cikin nutsuwa ta ce. "Wai Yaya ba tun jiya ya kamata ka koma gidan Aunty Hafsah da kwana ba ne? Ya ɗago ya kalle ta bai ce komai ba amma fuskarsa ta sauya. Sai ta ji babu daɗi gabanta har fad'uwa ya yi saboda ta dad'e bata gan shi a cikin irin wannan yanayin ba. Sai ya daina shan fruits ɗin ma, ita ma ganin haka sai ta daina sha. Tana shirin tattare sauran yay mata wani kallo data san mana'ar shi, dole ta koma ta cigaba da sha. Sai da suka kwanta ta ga har lokacin ransa a b'ace yake sannan ta bashi haquri har da hawayenta. Ya rungume ta ya nuna mata komai ya wuce amma kar ta sake yi masa maganar. Abun ya bata mamaki ba kaɗan ba. Ta dinga tambayar kanta me zai saka Ameen ɗin ya yi haka?
Washegari da murna ta tashi dan Ameen ya gaji da rigimar da take masa na son ganin Mama ya ce zai kaita bayan Magriba ta gan ta. Da yamma tana aiki a kitchen ya shigo kitchen ɗin ya tsaya a kusa da ita. Ta dube shi tare da turo baki ta ce. "Kallon kenan?" Ya ce. "Na gaji da watching TV na zo kallon ki." Ta ɓata fuska ta ce. "Dan Allah Yaya ka barni in yi aikin nan, yanda ka koyi cin nan idan ban yi maka abinci ba me zaka ci?" Ya ce. "Au acici ma na zama?" Ta ce. "Eh mana, da ai baka cin abinci sosai." Ya ce. "A da ɗin ma Soyayyar ki da damuwar rashin mallakar ki ya saka hakan, yanzu kuma na same ki bani da wata sauran damuwa." Ta yi murmushi kawai. Ya kwanta a jikinta yana sakin ajiyar zuciya. Cikin shagwab'a ta ce. "Allah Yaya kana takura mun fa a gidan nan, zan haɗa ka da Mama fa." Ya ce. "Ke ce kike yin kyau ai ki yi ta ƙamshi mai daɗi, duk ki saka in zauce." Ta yi murmushi kawai ta cigaba da aikinta.
Bayan Magriba kamar yadda ya alƙawarta suka je gidan Mama. Murna da zumuɗin Neehal suka kasa b'oyuwa. Dije ce ta buɗe musu ƙofa, cikin murna ta rungume ta suka gaisa sannan ta shige ciki tana ƙwalawa Mama kira. Girgiza kai kawai Ameen ya yi ya zauna a falon ƙasa. A ɗakin Mama ta tatar da ita akan darduma tana jan carbi, faɗawa jikinta ta yi ta rungume ta. Mama ta shafa kanta cikin farin cikin ganin ta, ta ce. "Yau Amarya ce a gidan namu?" Ta rufe fuskarta da hannunta tana dariya. Mama ta ce. "Ina Ameen ɗin?" Ta ce. "Yana falon ƙasa, ina yini Mamana." Mama ta ce. "Lafiya ƙalau." Tare da bin ta da kallo ganin yadda ta ƙara kyau ta murje alamun tana cikin kwanciyar hankali. Ta ɓata fuska ta ce. "I missed you so much my Mum." Mama ta ce. "Nima haka Daughter, kwana biyu gidan ya mun faɗi Ni kaɗai, babu mai zuwa ya ɗane mun jiki, sometimes da shagwab'a sometimes da murna." Ta yi murmushi ta ce. "Ina Daddy?" Mama ta ce. "Yana masallaci, kin san sai an yi isha'i yake shigowa." Neehal ta gyaɗa mata kai sannan ta ce. "Mama yanzu wa ya ke yi miki girki?" Mama ta yi murmushi ta ce. "Ni nake abuna mana." Ta marairaice fuska ta ce. "Kullum kuma, ni bana son kina wahala." Mama ta ce. "Mene abun wahala? Kin fi so in jibge inta zama babu ɗan motsa jiki." Ta girgiza kai. Mama ta ce. "Ki bari In kin haifi Baby girl sai ki bani ita in ta girma sai ta dinga yi mun girkin." B'oye fuskarta ta yi a jikin Mama tana murmushi. A haka Ameen ya shigo ya same su. Bayan Daddy ya dawo ta je part ɗinsa, ya yi farinciki sosai da ganin ta da yanayin data gan ta a ciki. Ta zauna suna ta shan hirarsu. Shi kuma Ameen yana can Mama ta saka shi a gaba tana yi masa faɗan ƙin zuwa gidan su Hafsah. Tana mitar suka je part ɗin Daddy, shi dai Ameen bai ce mata komai ba. Suna zama ta dubi Daddy ta ce. "Ka yi masa magana ya je gidansu yarinyar nan tunda ni ya ƙi jin tawa maganar." Daddy ya ce. "Ba ƙi ya yi ba nina sani, baki san dalilinsa na ƙin zuwan ba, shi yasa kika ga ni ban shiga cikin maganar ba." Mama ta ce. "Babu wani dalili, kullum sai dai ya dinga ce mun zai je zai je amma ya ƙi zuwa, ita rayuwa ai komai ɗan haquri ne, dama haka zaman tare yake zo mu zauna zo mu saɓa. Amma yarinya ta kusa wata biyu a gida ka ƙi zuwa, sai yaushe kenan zaka je?" Ya ɗago cikin sanyin murya ya ce. "Ki yi haquri Mum, insha Allahu gobe da yamma zan je." Mama ta ce. "Yanzu na ji batu, ko kai fa, Allah ya kai mu goben lafiya." Suka amsa da Amin. Sai a yanzu Neehal ta gano bakin zaren, dalilin da yasa ba ya zuwa gidan Hafsah ashe yaji ta yi, ita fa ta ce ko waya bata taɓa ganin sun yi ba, kuma bai taɓa ce mata zai je gidan ba. Sai ta ji babu daɗi a ranta tausayin Hafsan ya kamata.
Mama ta kawo abinci nan part ɗin Daddyn, Neehal ce kawai ta ci kaɗan shi Ameen ko ruwa bai sha ba. Tana gamawa ya ce ta taso su tafi. Ɓata fuska ta yi ta ce. "Ni anan zan kwana." Bai ce mata komai ba ya yiwa su Mama sallama ya tashi ya fice. Har ta fara murna Mama ta ce. "Mu je in baki abun da zan baki ku wuce kar ya yi ta jiran ki." Ta shagwab'e fuska ta ce. "Mama ya bar ni kwanan fa." Mama ta ce. "Banga alama ba." Daddy ya yi murmushi ya ce. "Ki yi haquri Daughter ki je ku tafi, idan an kwana biyu sai ki zo ki kwanan." Ta gyaɗa masa kai sannan ta yi masa sallama suka fice da Mama. Ameen yana cikin Mota ya hango ta tana tahowa fuskar nan a keɓe, ya yi murmushi dama ya san Mama baza ta taɓa barin ta kwana ba. Ta buɗe Motar ta shiga ta ƙi kallon inda yake, ya kalle ta ya ga harda hawayenta. Ya matso ya kama hannunta ya ce. "Fasa kwanan kika yi?" Ta turo baki ta ce. "Mama ce ta koro ni, kuma kai ma ka ƙi tafiya, daka tafi ai zata barni in kwanan." Ya janyo ta jikinsa ya ce. "Tunda Mama ta koro mu sai mu tafi namu gidan mu ma." Ya kashe mata ido tare da rad'a mata wata magana a cikin kunnenta. Fuskarta ta yi saurin rufewa da hannunta tana murmushi ta ƙara cusa kanta a ƙirjinsa.........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*
*8️⃣7️⃣*
_By_
_Zeey Kumurya_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
Washegari tun safe Mama ta kira Ameen ta ƙara yi masa tuni akan zuwansa gidansu Hafsah. Da yamma ya shirya cikin manyan kaya light blue ɗin shadda. Neehal tana fesa masa turare ta ce. "Ka yi kyau fa sosai Yayana." Ya yi murmushi ya ce. "Duk wannan shiryanin da kike yi fa ba sai saka in fasa zuwa zancen da na yi niyya ba." Ita ma murmurshin ta yi ta ɗauko agogon da zai saka ta fara saka masa ta ce. "Ai bazan so ma ka fasa zuwa ba, ni me iya raka ka zancen ne ma." Ya janyo ta ya zaunar akan cinyarsa ya ce. "Kar fa ta yi miki duka budurwar tawa, ta ce dan iyayi kin rako saurayinta zance." Ta juya masa ido ta ce. "Idan ta san me take yi she will never do that." Ya yi murmushi tare da sauke ta ya miƙe tsaye ya kwashi wayoyinsa. Har bakin Mota ta raka shi ta yi masa addu'a, sai da rungume ta sannan ya shiga Motar ya tafi. Haka kawai ta ji zuciyarta babu daɗi bayan fitarsa dan ta san gurin Hafsat zai je. Wani abu wanda ta tabbatar kishi ne ya tokare mata a ƙirji. Ganin abun na neman yin yawa sai ta kunna karatun Alkur'ani a speaker, tana saurara tana kuma bi a hankali.
Cikin mintuna ƙalilan Ameen ya ƙarasa gidansu Hafsah. Ya yi horn mai gadi ya buɗe masa tangamemen gate ɗin gidan. Ya shiga ya ƙarasa parking space ya yi parking, a ransa yana tunanin ko yaya zai ga Hafsah da irin tarb'ar daza ta yi masa. Har yanzu haushin abun da ta yi masa bai bar cikin ransa ba, dan Mama kawai ya zo wannan bikon. A hankali ya fito daga cikin Motar cikin takunsa na nutsuwa da ƙasaita mai ɗaukar hankali. Ɗaya daga cikin yaran gidan ya aika domin ya yi masa iso. A ɓangaren Hafsah tun ranar data je gidan Aunty Safiyya bata dawo ba sai jiya, shi ma dan saboda yau da daddare Dad ɗinta zai dawo ne. A yau kuma Aunty Safiyya ta zo ta kawo mata magunguna da zata yi amfani da su wanda zai saka Ameen ya zo gare ta. Tun a yau ɗin ta fara amfani da magungunan, ta sha na sha ta turara jiki dana turarawa suka binne na binnewa. Aunty Safiyya ta tabbatar mata da a cikin kwanakin nan Ameen zai zo, dan aikin malamin da ya bayar da magungunan tamkar yankan wuqa yake. Aunty Safiyya ta ɗora mata da huɗubar banza ta rashin mutunci da jan ajin da zata yiwa Ameen idan ya zo.
Suna zaune a main parlour'n part ɗin Mom suna hira, masu aiki nata kaiwa da komowa suna shiryawa mai gidan delicious ɗin tarb'ar shi. Wanda Ameen ya turo ya shigo cikin girmamawa ya sanar musu da zuwan Ameen. Da sauri Hafsat ta kalli mahaifiyarta ta kalli Aunty Safiyya. Mom ta ce ta bayar da umarnin a je a shigo da Ameen ɗin. Aunty Safiyya ta ce. "Kin ga aikin Malam ko Hafsat? Zaki ga yanda zai rud'e yana roqonki ki zo ku tafi, ke kuma ki ja class ɗinki ki gaggasa masa maganganun da na ce miki." Hafsah da farin ciki ya cika mata zuciya saboda zuwan Ameen ta ce. "Insha Allahu Aunty, abun da kika ce babu fashi." Mom ta miƙe ta ce. "Bari na shiga ciki kafin ya shigo in fito in yi masa wankin babban bargo nima." Aunty Safiyya ta miƙe ta bi bayanta. After 3 minutes Ameen ya shigo parlour'n bakinsa ɗauke da sallama. Lokaci ɗaya daddaɗan ƙamshinsa ya cika parlour'n, Hafsah ta lumshe idonta tana jin yanda ta yi missing ƙamshin over a cikin ranta, Sai dai kuma ta ji ƙamshin nasa ya ɗan sauya ya sirka da wani, wanda ko tantama bata yi na Neehal ne, dan is like humra ta mata. Ta buɗe idonta tare da haɗe rai wani zafi ya ziyarci zuciyarta data tuna zuwa yanzu fa ya haɗa jiki fa da wannan yarinyar. Ko kallon inda yake bata yi ba balle ta amsa masa sallamarsa. Idanunta suna kan TV. Kansa ya yiwa mazauni a kujerar dake facing ɗin tata, ya shiga bin ta da kallo cikin mamakin yanda ta share shi. Ya danne zuciyarsa ya ce. "Hafsah Ya kike?" Ta juyo ta yi masa wani mugun kallo gami da