Showing 75001 words to 78000 words out of 262509 words
Chapter 26 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
kar Neehal ɗin ta ƙara zuwa inda yake tun da ta zaɓi bare akan sa. Haka dai suka dawo Abuja rai babu daɗi, sosai Mama ta ji takaicin yanda ƴan'uwan mahaifan Neehal suka banzatar da ita, ta yi Allah wadai da zumuncin wannan zamani na ganin ido, dan ta san da iyayenta suna raye baza su mata haka ba. Neehal cikin danginta na Uwa da Uba da Uncle Usman da Ummi kawai suke waya, sai kawu Musa wani lokacin, lokaci zuwa lokaci kuma tana ziyartar Ummi. Riqon da Mama take wa Neehal ko ɗan data haifa da cikinta iya shi zata masa, Mama tana k'aunar Neehal sosai har cikin ranta, haka ma Daddy. Babu yanda za ai ka gane ba su suka haife ta ba, wanda bai sani ba ma ba ya gane wa. Dan ko a school da *Fateemah Muhammad Tafida* take amfani. Sunan Daddy kenan (Muhammad Tafida) amma Neehal da sunan Abbanta take amfani, Tafidan kawai ta ƙara, da yake sunan ɗaya ne duk Muhammad shi yasa ba'a gane wa. Daddy yana da kuɗi sosai kasancewar ya riƙe matakai na soja kala_kala har zuwa matakin ƙarshe wato General, kuma dama can zuri'arsu masu arzik'i ne. Asalin su Daddy su ma fulanin Gombe ne kuma ƴan'uwa ne na jini da su Mama, da Mahaifin su Daddy da Hajiyar su Mama cousin ne. Su Daddy su uku ne a wajen mahaifinsu, Yayansa Namiji mai suna Hamza sai shi, Haj.Saratu Maman Hameedah ita ce Autarsu. Iyayensu duka sun mutu ba jima wa, su ma su Mama mahaifinsu ya rasu daf da bikin Aunty A'isha da Abba. Daddy ya fara harkar siyasa, amma ganin siyasar ƙasar nan babu Allah a cikinta Mama ta ce gaskiya ya daina tun da dama bai yi wani suna acikinta ba, ba dan ya so ba haka ya haqura sai dan farincikin Maman kawai. Ameen shi kaɗai Mama da Daddy suka haifa a duniya, daga kan shi Allah bai ƙara ba su haihuwa. Kamar Ameen da Mama ɗaya sak tamkar an tsaga kara, bambamcinsu kawai shi Namiji ne Mama kuma mace ce, haka ma a halaye da d'abi'u duk nata ya yo, kama daga kan tsafta, addini, kyauta, iya mu'amala da mutane, tsare gaskiya ko mai ɗacinta, da kuma rashin tsoro. Ko dan shi Namiji ne,har ya fi Mama rashin tsoro da dakiyar zuciya, sai kuma Allah ya ɗora masa miskilanci tun yana ƙaramin sa. A ɓangaren aiki ne ya gaji Daddy shi ma ya zama soja. Sosai Neehal take tsoronsa, idan ya zo gida weekend sai ta zama salihar ƙarfi da yaji, dan abu kaɗan za tay ya balbale ta da faɗa dan yana da zafin zuciya, amma fa duk zuwan da zai yi da ƙatuwar ledarsa ta tsarabar Neehal yake zuwa, idan ƴan fara'ar suna kansa wataran yana sakar mata fuska. Neehal kam tana son Yayanta sosai, tana jinsa tamkar yayanta uwa ɗaya Uba ɗaya. Komai nata Yayanta Yayanta, sai dai wani lokacin in ta je gurinsa ya koro ta, ta dawo tana aikin turo baki, Mama ta ce mata "Dama wa ya aike ki gurinsa kin san hali." A hakan dai shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su. Shekarar Neehal shida a gurin su Mama Daddy ya yi retire, hakan yasa suka dawo Kano da zama gaba-d'aya, lokacin Neehal ta gama Secondary school tana 17_18 years. Ta yi saukar haddar Alqur'ani mai girma shekara biyu da suka wuce. A gurin registration ɗin Jamb suka haɗu da Haneefah, har suka yi musayar contact ɗin juna, sai da za su tafi gida suka gane ashe ma unguwarsu ɗaya. Tun daga time ɗin suka zama k'awaye sosai har Mama suke zumunci da Mommy'n Haneefah, ita ma Haneefah marainiya ce, mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama. A wannan lokaci Allah ya yiwa Ummi Yayar Abba rasuwa, Neehal ta ji mutuwar sosai kuma ta sha kuka. Duk da tarb'ar da Mama ta samu a gurin dangin Neehal bata daina kai ta tana gaishe da su ba, tun da jininta ne su, babu yanda zata yi da su, daga baya da Neehal ɗin ta girma da kanta ta cewa Mama dan Allah ta daina kai ta, ganin yanda suke wulaqanta ta da nuna halin ko'in kula a gareta kamar wadda ta je neman wani abu gurinsu, ko sau ɗaya babu wanda ya taɓa tako wa gidan Mama da sunan ya zo ganin Neehal. Ita kuwa Neehal tuni ta cire su daga ranta, yanda suka manta da ita a rayuwarsu itama ta manta da su. Da Uncle Usman ɗinta kawai take zumunci wanda shi ma ya yi aure suna zaune da matarsa a can Niger. Neehal kyakkyawa ce doguwa mai dirin jiki dai_dai misali da dogon gashi, ga ta ƴar gayu ce dan tana son gayu sosai, ko da yake ba ta ɗauka a ƙasa ba dan Mama ma akwai gayu da kwalliya, zai yi wahala ka ga hannu da ƙafarta babu jan lalle idan ka ganta baza ka ce ta haifi Ameen ba, ga iya girki, shi yasa duk ta kanainaye zuciyar Daddy, ba ya ganin kowacce mace sai ita. Aunty A'isha ta haifi yarinyarta mace mai suna Maryam, Aunty Sadiya ma ta haihu ɗanta Namiji.
Tun da Neehal ta fara zama budurwa Ameen ya daina sakar mata fuska kwata_kwata, wani lokacin kuma sai ta fito zata unguwa sai ya ce sai ta koma ta canzar shigar da ta yi ba zata fita a haka ba, babu yanda ta iya haka zata koma ta sake. Sannan ko ya ya ji k'amshin turare a jikinta kuwa sai ta koma ta sake wanka wai babu kyau ba zata fita tana k'amshi ba, janbaki wannan idan tasa sai ya ce sai ta goge shi. Mama da ta ga abun na shi bana ƙare ba ne ta taka masa burki ta ce bai isa ya takurawa Ƴarta ba, tun da ba shi ya haifar mata ita ba. Sannan fa Neehal ta samu salama ya ɗan sararara mata. Allah ya ba wa Neehal farin jinin samari tun da ta fara tasowa, amma bata kula su saboda ba a bata damar hakan ba a gida. Jameel shine saurayin data fara kulawa da sunan soyayya, ɗan Kano ne amma a Abuja suka haɗu a wani Mall, a lokacin ya takura mata da naci har sai da ta ba shi phone Number ɗinta. Tun yana kiranta tana ƙin d'aga wa har dai ta fara sake masa. Jameel matashi ne Black beauty, gashi da nutsuwa hakan yasa Neehal ta ji ya kwanta mata a rai. A hankali soyayyarsa ta fara mamaye zuciyarta. Tun kafin tafiyarsu ta yi nisa ta gabatarwa da Mama shi, Mama ta yi murna sosai ta kuma sanar da Daddy dan a san abun yi. Mahaifin Jameel ba boyayyen mutum ba ne kasancewarsa ɗan siyasa ne, Daddy ma ya san sa. Soyayya sosai Neehal suka sha da Jameel kamar ba gobe, sai dai bayan an yi Engagement ɗinsu ba jimawa ya fita aka bishi aka harbe sa ya mutu. Mutuwar Jameel ta girgiza duk wani makusancinsa ciki har da Neehal kuwa, dan tun daga lokacin da ya rasu ta zama so silent. A lokacin ne kuma Jamb ɗinsu ta fito, sai dai Neehal ba ta ci point sosai ba duk da Kasancewar tana da ƙoƙari, Haneefah kuwa ta ci point da yawa, amma ganin Neehal bata ci ba harma ta yi apply a Kano state polytechnic sai itama Haneefah ta ce can zata ta fasa zuwa University tun da besty'nta ba can zata yi ba, ita ma ta yi apply a poly. Sun fara karatu cikin nasara a Management kasancewar su duka ƴan art ne, department of mass communication suke, dama ita Neehal choice d'inta kenan, burinta a rayuwa ta ga ta zama Jonorlist. Da wata shekarar ta zagayo suka sake yin Jamb, wannan karan ma Haneefah ce ta ci Neehal ba ta ci ba. Dole tasa Haneefah ta yi apply a Bayero University Kano inda ta fara karantar law, Neehal kuma ta ci gaba da Polytechnic ɗinta. Tana siwes suka haɗu da Anwar, da farko shi ma ba ta kula shi sosai, sai daga baya ta saki jiki da shi suka fara soyayya fiye da ma wadda suka yi da Jameel. Cikin ikon Allah Neehal ta gama school ɗinta successfully, bata taɓa carry over ba balle spill, tun kafin ta gama ta siyi D.E Form a Bayero ta cike da waiting result. Bayan ta karb'i result ɗinta suka bata admission direct level two ta ɗora karatunta, lokacin ita ma Haneefah ta shiga level two ɗin, sai matakin karatunsu ya zo ɗaya. Ba jimawa da shigar ta Bayeron aka yi Engagement ɗinsu da Anwar. Duk kawo kuɗin Neehal ɗin da za'ai sai Mama ta aikawa ƴan'uwan Neehal, amma daga ƴaƴan Baffa har Uncle Umar babu mai zuwa, Kawu Musa ne kawai yake zuwa a karb'i kuɗin da shi, Uncle Usman kuma ya yi nisa ba ya samun zuwa, ya kance sai bikin Neehal ɗin zasu zo shida iyalansa.
A lokacin da aka yi engaged ɗin Neehal aka buɗe gidan Television na ASTV. Wani abokin Daddy ne ya buɗe, hamshaqin mai kuɗi ne kuma sananne ne a ƙasar nan. Da kwalin Deplomer aka ɗauki Neehal aiki a gidan TV'n, Haneefah kuma da S.S.C.E Daddy ya sa aka mata alfarma ita ma aka ɗauke ta. Neehal abun nema ya samu ta zama Jonorlist sai murna. Kafin Neehal ta fara aiki sai da aka kai ruwa rana da Ameen, dan da farko cewa ya yi baza ta yi ba. Mama ta ce, A nan bai isa ba kuwa, wanda zai aure ta ma bai hana ta ba sai shi ɗan karere. Har wannan lokacin dukiyar Neehal tana hannun Uncle Umar yana juya ta, babu wanda ya ce masa k'ala a kanta, su Fauziyya da aka ga Neehal a gidan TV baƙin ciki kamar ya kashe ta, musamman da ta ga yanda ta ƙara kyau ta zama ƴar gayu wanke hannu ka taɓa, gashi ko ta ina samun masoya take rututu a faɗin ƙasar nan.
*CIGABAN LABARI.............✍️*
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:48] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*3️⃣4️⃣*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
.............Washegari bayan an yi sallar asuba, Daddy ya dawo daga masallaci Mama ta sanar masa abun da Aunty Sadiya ta faɗa mata, dan jiya bai dawo da wuri ba shi ya sa bata faɗa masa ba. Zarya yake ta yi a ɗakin baccinsa, Mama kuma tana zaune a gefen gado ta yi tagumi cikin tunanin mafita. A hankali ta ɗago da idanunta da ba su samu isasshen bacci ba a daren jiya saboda fargaba ta dubi Daddy ta ce "Daddy ka zauna mana, ka bar wannan safa da marwar ka zo mu nemi mafita akan wannan al'amarin." Daddy ya sauke numfashi tare da goge gumin da ya kwanta a kan goshinsa ya ce "Al'amarin ne ya girgiza ni ba kaɗan ba Doctor." Mama ta sauke tagumin data rafka bata ce komai ba. Daddy ya zauna a kan bedside locker yana fuskantar Mama ya ce "Zuciyata ta kasa yarda da wannan abun Doctor, ba zan taɓa yarda saboda Daughter ake wannan kisan ba gaskiya." Cikin karaya Mama ta ce "Saboda me zaka ce haka? Kar fa ka manta mahaifan Neehal ma fa kashe su a kai, kuma har yau an kasa gano waɗanda suka yi kisan da kuma dalilin da yasa aka kashe sun. Haka su Jameel suma har yau an kasa gano waɗanda suka kashe su, ai ko aljanu ke kisan nan ya ci ace zuwa yanzu asirinsu ya tonu." Daddy ya ce "Ka da ki la'akari da haka, zata iya yiyuwa mahaifan Neehal b'arayi ne suka kashe su ko kuma wani mak'iyin Abbanta, kin san idan mutum ba ya k'aunar ka a shirye yake da ya aikata komai a kanka. Sannan na biyu kuma Jameel, mahaifinsa ɗan siyasa ne abokan hamayya babu abun da baza su iya ba suma a kan mutum, tun lokacin da aka kashe Jameel tunanin da kowa ya yi kenan ciki har da mahaifinsa. Sai kuma Anwar, wanda shi kaɗai ne ma babu wani dalili a rayuwarsa da a yi tunanin zai sa a kashe sa." Mama ta sauke numfashi ta ce "Yanzu dai a takaice kana son ka ƙaryata abun da Sadiya ta faɗa kenan? Ko kuma kana son ka kwantar mun da hankali ne kamar yadda ka saba a kodayaushe idan ka ganni a cikin damuwa? Daddy! Wannan maganar ba fa ƙaramar magana ba ce, ina tsoron abun da Sadiya ta faɗa ya tabbata." Daddy ya ce "Ko kaɗan ba ina nufin na ƙaryata Sadiya ba ne domin akan aikinta take, kuma ban san hujjar data gani ta faɗi haka ba, kawai dai ina son nusar dake wani abu ne." Mama ta ce "Wanne abu zaka nusar da ni? Hmm Daddy kenan, ni fa na riga na gano ka, kawai kana san kwantar mun da hankali akan wannan al'amarin ne." Daddy ya yi shiru domin tabbas abun da Mama ta faɗa haka ne, yana son ya kwantar mata da hankali ne kawai amma tabbas shi ma maganar ta girgiza zuciyarsa ba kaɗan ba, ya manta rabon da ya ji abun da ya firgita zuciyarsa irin wannan. Mama ta ce "Ya Allah ka bayyana mana gaskiyar wannan abun, ka tona asirin duk wanda yake da hannu a cikin wannan al'amari da gaggawa." Daddy ya ce "Ameen ya Allah, abun da ya dace dama mu dage da yi kenan addu'a, Insha Allahu gaskiya zata bayyana." Kusa da Mama Daddy ya dawo ya kama hannunta ganin damuwa ƙarara a fuskarta ya ce "Please Doctor ki rage damuwar nan da kike, kin san Neehal ɗin ma idan ta ganki a haka itama zata shiga damuwar ne, ina jarumtar dana san ki da ita ne? Haba matar soja uwar soja." Mama ta sauke numfashi ta ce "Idan ka ga na daina damuwa to naga na aurar da Neehal, shine kawai hankalina zai kwanta." Daddy ya miƙe ya ce "Insha Allahu zaki gani, ai shi aure hab'o ne idan lokacinta ya yi dole sai ta yi, fata kawai Allah ya kawo mata miji na gari, wanda zai riqe mana ita da amana ko bayan ranmu." Mama ta ce "Ameen ya Allah." Daddy yana buɗe wardrobe ɗinsa ya ce "Yanzu ita Neehal ɗin akwai wanda take kulawa ne?" Mama ta ce "Gaskiya a sani na babu kowa." Daddy ya ce "Wannan yaron da yake zuwa fa wani ɗan fari dogo haka?" Mama ta ce "Sadik kake nufi wai?" Daddy ya ce "Ehh, Barrister ne shi ko?" Mama ta ce "Ehh, a unguwar su A'isha gidansu yake." Daddy ya ce "Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Mama ta ce "Ameen." Car key Daddy ya miƙawa Mama ya ce "Gashi ki ba wa Daughter." Mama ta karb'a cikin mamaki ta ce "Mota ka sai mata?" Daddy ya ce "Ehh mana, alƙawarin dana mata ne tun sanda ta gama Polytechnic kika hana a bata a time ɗin." Mama tana murmushi ta ce "Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi ya tsare, ai yanzu ta ƙara hankali zan bar ta ta yi driving ɗinta. Mun gode sosai fa Allah ya ƙara buɗi mai albarka" Daddy ya ce "Ameen ya Allah. Mama ta miƙe ta ce "Bari in je inwa Daughter albishir, na san zata yi farin ciki sosai." Daddy ya yi murmushi cikin jin daɗin ganin Mama na murmushi, saɓanin d'azu da damuwa ke kwance a kan fuskarta. A duk duniya abun da ke d'aga masa hankali kenan ya ga iyalinsa a cikin damuwa, da yana yanda zai yi da sai ya magance wa Neehal wannan K'ADDARAR data shigo cikin rayuwarta, amma babu yanda zai yi komai rubutacce ne tun fil'azil daga Ubangiji Mai girma da ɗaukaka, amma ya ɗaukar wa kansa alk'awari sai inda ƙarfinsa ya ƙare a game da binkicen wannan al'amari, a matsayinsa na k'wararren soja.
Zaune a kan darduma Mama ta tarar da Neehal ta jingina jikinta a jikin gado, Sallamar Mama yasa ta ɗago da kanta tare da amsa mata. Mama ta zauna a bakin gado tana dubanta. Neehal ta ce "Ina kwana Mama." Mama ta ce "Lafiya k'alau, me ya samu idanki?" Neehal ta girgiza mata kai, Mama ta ce "kuka kika yi ko? kuka dai ba ya maganin duk wata damuwa, addu'a ita ce kawai mafita." Neehal ta gyaɗa mata kai. Mama ta kalli su Afrah dake bacci ta ce "ƴan rigimart taki ba su tashi ba kenan?" Neehal ta ce "Ehh ni Mama dama ina son na faɗa miki me zai hana a saka su a makaranta kafin Allah ya bayyana iyayensu, kin ga idan na tafi school ko aiki kema in kin tafi asibiti sai su kaɗai fa a gidan, su Aunty Dijee ma kin ga suna zuwa islamiyya da yamma." Mama ta ce "Hakane kin kawo shawara mai kyau, ranar Asabar in Allah ya kai mu sai a kai su tahfiz, ranar Monday kuma sai na kai su school." Neehal ta ce "Allah ya kai mu." Mama ta ce Ameen, ga saqo in ji Dad ɗinki." Neehal ta miƙa hannu dan karɓar abun da Mama take miƙo mata tana faɗin "Saqon mene?" Kafin Maman ta bata amsa ta gani da idonta, waro ido ta yi waje tana murmushi ta ce "Mama kar dai ki ce mun wannan nawa ne Dad ya siya mun Mota?" Ita ma Mama tana murmushin ta ce "Ban ce ba to, amma ni dai saqo aka bani kuma na isar." Neehal ta rungume Mama da sauri cikin farin ciki ta ce "Alhamdulillah, amma fa Dad ya iya surprise." Mama ta ce "D'aga mun jiki ni, sai a kula da titi sosai tare da kasancewa cikin addu'a a kodayaushe." Neehal ta ce "Insha Allah Mamana." A take Neehal ta tafi part ɗin Daddy ta masa godiya sosai, Mama ce ta yi musu breakfast yau dan ta san murna ba zata bar Neehal ta musu cikin nutsuwa. Ƙarfe tara da ƴan mintuna Neehal ce zaune