Showing 189001 words to 192000 words out of 262509 words
Chapter 64 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
babu komai a cikinsa ta tsinci kanta, ta zube a bakin ƙofar cikin matsanancin tsoro da fargabar wanda ta gani, shirun sa da yanda ya tsaya yana kallon ta ya tabbatar mata da shine wanda yake ƙoƙarin keta mata haddi, me ya haɗa shi da wannan ƙungiyar wadda bata tantama ta matsafa ce? Ko shi ma member ne a cikinta? Ta tambayi kanta. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." Ta shiga maimaitawa a fili cikin sark'ewar numfashi. Addu'a da fatanta ɗaya Allah ya farkar da ita daga wannan mummunan mafarkin da take, dan ta kasa yarda a gaske ne wannan baƙin al'amarin yake faruwa da ita. Wanda take masa kallon jigon rayuwarta anya zai aikata mata haka? Wanda take kallo a matsayin bangon rayuwarta a ce da shi ake ƙoƙarin gurɓata mata rayuwa, wannan wacce irin ƙaddara ce ta kuma samun ta? Wacce irin rayuwa take yi ne a duniyar nan? A fili ta furta. "Ya Allah idan wani laifin nai maka kake jarabta ta Allah ka yafe mini ka sassauta mun wannan jarabawar, Ya Allah karka tabbatar da abun da nake zargi, Allah karka ɗora mun abun da ya fi ƙarfi na." Ta zauna akan gwiwoyinta ta shiga bubbuga kanta a jikin kofar ɗakin cikin rashin sanin mafita da abun yi, ƙwaƙwalwarta_ta ta tushe gaba-d'aya ta ƙi bata space ɗin ma da zata yi tunani, idanunta kamas ko k'walla babu a cikinsu, kukan ma ya ƙi zuwar mata balle ta ji sauqin yaƙin wutar da ake a cikin zuciyarta.......
Tunda bayan fitar Daddy su Mama suke ta amsa kiran wayar mutane, ƴan'uwa da abokan arzik'i ana ta tambayar ko an ga Neehal. Mak'ota da wasu mutanen suna ta zuwa jaje. Ƙarfe sha ɗaya da mintuna Hajiya ta ƙaraso gidan, ta zube a falon ƙasa inda su Mama suke da Abba yayan Daddy wanda bai jima da zuwa gidan ba shi ma. Salati kawai Hajiya take yi tana hawaye. Mama tay mata sannu da zuwa cikin muryarta dake fita da ƙyar saboda tsananin damuwa. Su Aunty ma suka gaishe ta tare da bata baki akan ta yi haquri. Hajiya ta ce. "Wanne irin haquri zan yi? Ku daina bani wani haquri ni, ku bar ni in yi kukana, wannan wanne irin bala'i ne yake bibiyar yarinyar nan? Dan na tabbatar sace ta aka yi." Mama ta jinjina kai tare da sauke numfashi. Dan itama zuwa yanzu ta fi zargin sace Neehal ɗin akay. Gashi Daddy shiru tunda ya fita bai dawo ba, ana ta trying Numbers ɗinsa basa tafiya.
Gajiya Neehal ta yi da bubbuga kan nata ta zauna dab'as tana sauke numfashi, sai ta ji kamar wani abu yana tokarinta a cinya. Ta kai hannu ta taɓa gurin sai ta ji abu a cikin aljihun rigarta. Cikin sauri ta dage hijabin jikinta ta zira hannu ta zaro ƙaramar wayarta da tashin hankali ya mantar da ita tana jikinta. Hannunta har rawa yake wajen kunna wayar, sai kuma ta kama waige_waige kamar mai tsoron kar wani ya gan ta. Numbern Mama ta lalubo da ƙyar saboda ko gani bata yi sosai ta yi dialing, amma sai kiran ya ƙi tafiya, tay ta trying kusan sau 20 amma ya ƙi tafiya, wayar ma gaba-d'aya emergency ta koma, sim ɗin ya ɗauke alamun babu network. Cillar wayar ta yi gefenta cikin takaici, ta zauna sosai ta jingina kanta dake barazanar fashewa saboda ciwo a jikin ƙofar ɗakin, bata san kuma mai zai faru da ita next ba, ko zasu biyo ta har nan ɗin ne su cimma buƙatarsu a kanta? Ko kuma wani sabon shirin muguntar suke kuma yi a kanta? Duk wannan ba shine abun da ya fi damunta ba a yanzu, damuwarta me ya kawo mutumin data gani a ɗakin da aka kaita? Ko fitar da ita ya zo yi daga gidan? Amma me yasa da ya gan ta ya ƙi magana? Ya ƙi ce mata komai? Me yasa data fito bai biyo ta ya kama hannunta sun fice daga gidan nan ba? Me yasa? A fili ta ce. "Dan Allah ka zo ka ce mun zuwa ka yi ka cece ni ba wai da kai ake ƙoƙarin cutar da ni ba, idan har hakan ta kasance ƙwaƙwalwarta baza ta ɗauki wannan al'amarin ba, zuciyata bugawa zata yi in mutu......!"
Tun daren jiya da Ameen ya bar gidan Mama ya koma gidansa ya kulle kansa a ɗakinsa dan a halin da yake ciki ba ya buƙatar takurar Hafsat. Wata ƴar ƙaramar laptop ya ɗauko ya shiga operating, ga dukkan alamu aikin da yake yi mai matuƙar mahimmanci ne duba da yanda ya bayar da hankalinsa duka a kan aikin, yana yi yana kiran Numbobin Neehal tare da addu'ar Allah yasa su shiga, ya ɗaukarwa kansa alƙawarin duk inda Neehal take sai ya nemo ta ko da zai rasa ransa a gurin yin hakan, saboda dalilai guda biyu. Na farko saboda Mahaifiyarsa, ba zai iya jurar ganin Mama cikin wannan tashin hankalin da take ciki ba, wanda bai taɓa ganin ta a cikin irinsa ba tsawon rayuwarsa, dan haka dole sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Na biyu kuma yana son sanin gaskiya akan wani al'amari da yake zargi, al'amarin da idan abun da yake zargi ya tabbata to tabbas da akwai babbar matsala, matsalar da zata girgiza rayukan mutane da yawa. Har asuba yana operating system, sai da aka kira sallah sannan ya tashi duk ya haɗa zufa duk da A.C dake ɗakin, sai da ya watsa ruwa sannan ya ɗaura alwala ya fito ya tafi masallaci. Hafsah ta cika ta yi fam akan shiga ɗaki da Ameen ya yi ya kulle, kishi ya cika ta dan ko tantama bata yi saboda ɓatan Neehal ya aikata hakan. Kwana ta yi tana jan tsaki da ƙwafa tare da addu'ar Allah yasa kar a ga Neehal ɗin shegiyar yarinya, ko kuma in an gan ta a gan ta a mace kowama ya huta. Dan tun gabatowar bikinta da Sadik ta rasa gane kan Ameen, har yanzu kuma bai dawo dai-dai ba, kullum cikin damuwa da shegen bincike_bincike yake, wanda ta san duk akan al'amarin Neehal ɗin ne. Bayan ya dawo daga Masallacin ɗakin Hafsat ya zarce, ya tarar da ita kwance lullub'e da bargo babu alamun ta tashi ta yi Sallah. Ya shiga tashin ta a hankali. Ta buɗe ido da yake baccin nata ba wani nisa yay ba, sai da aka shiga sallah ya ɗauke ta. Ta riƙe hannunsa idanunta ƙur a kansa, cikin kissa ta ce. "Baby." Tana tashi zaune. Bai amsa mata ba sai zare hannunsa da ya yi daga cikin nata yana haɗe rai, ta kuma san dalilin hakan saboda bata tashi ta yi Sallah akan lokaci ba ne. Sai ta ƙara riƙe hannunsa cikin damuwa ta ce. "Baby a kwana ɗaya har ka faɗa, nima jiya kwata_kwata ban samu bacci ba, saboda damuwar ɓatan sister, sai yanzu gab da Asuba na ji ya ɗauke ni, dan Allah ka kira Mum ka tambaye ta ko an ga Neehal ɗin, ko kuma an samu labarin inda ta je, hankalina gaba-d'aya a tashe yake." Ya saka ɗayan hannunsa ya shafi gashin kanta cikin sanyin murya ya ce. "Go and pray First." Ta gyaɗa masa kai cikin nuna tsantsar damuwa. Ta sakar masa hannunsa ta sauka daga kan gadon ta shiga toilet zuciyarta fal da murna, dan yanda ta ga yanayin Ameen ta san babu wani daddaɗan labari, ta k'udurce a ranta tana idar da Sallah zata kira Mama dan jin ƙarin bayani, a zuwan da damuwar abun ta kwana kamar yadda ta nunawa Ameen. Shi kuwa da ya koma ɗakinsa ɗorawa ya yi daga inda ya tsaya a aikin da yake yi, babu alamun yana da niyyar fita yau.....
Neehal tana nan zaune a bakin ƙofa ta ji ana taɓa handle ɗin ƙofar ta waje. Ta zabura ta miƙe tsaye ta manne a jikin bango jikinta na ƙyama, jin an turo ƙofar ɗakin ta runtse idanta a tunaninta sun biyo ta nan ne domin su far mata. Jin shiru har na wasu sakanni bayan turo ƙofar yasa ta buɗe ido, farin saurayin nan da ya kawo mata abinci d'azu ta gani yana kallon ta. Ya tako a hankali zuwa gaban ta ya kama hannunta ya ce. "Ki nutsu ƴan'mata, zan fitar dake daga gidan nan yanzu amma sai kin nutsu kin kuma yi komai cikin lura. Da sauri Neehal ta gyaɗa masa kai alamun gamsuwa. Ya ce. "Ki zauna anan, yanzu zan je na lalata wutar gidan haske ya ɗauke, kafin su gyara Insha Allahu zan fitar da ke. Cikin marainiyar murya Neehal ta ce. "Na gode, na gode sosai bawan Allah." Ya jinjina mata kai sai kuma ya juya da niyyar fita idanunsa suka sauka akan wayarta dake tsakar ɗakin, ya waro Ido cikin alamun mamaki. Da sauri Neehal ta zo ta tattare wayar data tarwatse ganin yanda yake kallon ta, ta haɗa ta ta kunna ta. Bai ce komai ba ya juya ya fita. Neehal ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ƙara dialing Numbern Mama, amma still bata tafiya network is not available ake rubuta mata. Kamar ta yar da wayar sai kuma ta zira ta a cikin aljihun rigarta. Ta koma ta rakub'e a kusurwar ɗakin tare da rafka tagumi da hannu biyu. Bayan mintuna biyar ta ga hasken ɗakin ya ɗauke sai duhu dumɗum, ta ƙara mannewa a cikin bango jikinta na ƙyarma. Ko minti biyu ba'ai ba ta ji an turo ƙofar ɗakin an shigo, muryar saurayin ta ji yana faɗin. "Taso da sauri ba mu da ishashshen time." Neehal ta tashi cikin sauri kamar yadda ya ce ta yi inda ta ji sautin muryarsa saboda bata ganin sa, sai da ta matso kusa da shi ne ma ta ga alamar duhun mutum a tsaye, ya kamo hannunta cikin raɗa ya ce. "Duk inda nasa ƙafata ki saka taki, amma sai kin yi sauri fa dan yanzu zasu gyara wutar, kuma gidan nan gaba-d'aya a zagaye yake da CCTV camera, duk inda muka gilma akwai masu kallon mu." Neehal ta gyaɗa masa kai. Ya buɗe ƙofar suka fita yana jan ta, dan gudun ma gagarar ta ya yi ta kasa yin sa, sai faɗuwa take musamman idan suka zo gurin shan kwana, amma kuma sai ta miƙe zumbur saboda tamkar gudun ceton rai take. Suna fitowa daga corridor ɗin gidan wutar gidan ta dawo, saurayin ya waro ido waje cikin alamun tsoro, dan ya san kafin sukai bakin gate waɗanda suka gyara wutar sai sun gan su, ya tsaya ya fara tunanin mafita. Neehal ta shiga kalle_kalle a makeken harabar gidan. Bai gama tunanin ba ya ji alamun tafiya, ya yi saurin jan hannun Neehal suka zagaya baya, suna zuwa bayan ya hangi mutum uku suna tahowa, ya yi saurin yin ƙasa tare da jan Neehal suka b'uya a bayan wani gini. Ta daf da ginin mutanen ukun nan suka zo suka wuce, ɗaya daga cikinsu har da juyowa, ai kaɗan ya rage Neehal bata saki fitsari ba. A tare suka saki ajiyar zuciya bayan mutanen sun ɓace wa ganin su. Saurayin ya miƙe hannunsa cikin na Neehal ya ce. "Gudu zaki yi sosai mu samu ki fita daga gidan nan, dan na san zuwa yanzu sun fara nemanki, mintuna kaɗan kuma ya rage ragowar ƴan ƙungiya da sarauniya su ƙaraso gidan nan dan bikin murna." Neehal da zuwa yanzu ta fara sarewa ta gyaɗa masa kai numfashinta na fita da ƙyar. Ya ja hannunta suka falfala da gudu yana yi yana waiwaye, cikin ikon Allah har suka ƙarasa gate ɗin gidan babu wanda ya gan su. Sai dai gate ɗin a kulle yake da gark'amemen ƙwado. Saurayin ya dafe kansa cikin takaici dan gaba-d'aya ya manta da akwai sauran rina akaba, wato ta yanda zasu fice daga gidan. Kallon ɗakin mai gadi ya yi sannan ya juyo ya kalli Neehal wadda ke ƙoƙarin sumewa. Ya ja ta dan tafiya ma neman gagarar ta take, a bakin ƙofar ɗakin mai gadi suka tsaya, ya zaunar da ita shi kuma ya tura ƙofar ya shiga. Mai gadin yana zaune kishingid'e, jin an shigo ya tashi zaune sosai. Saurayin ya ƙaƙaro murmushi ya ce. "Malam Buba ana hutawa ne?" Malam Buba ya washe baki ya ce. "A'aa, Malam sagiru kai ne, sannu da zuwa farin mutum ganin ka Alkhairi ne." Sagir ya ce. "Yau an gama abinci da wuri, kuma baka zo ka kawo kwano ba." Buba ya ce. "Ai na ga lokaci bai yi ba ne shi yasa." Sagir ya ce. "Ka san yau muna da shgali fa shi yasa aka gama da wuri, yanzu dai ɗauko kwanan naka kar wanda ya fi maik'on ya ƙare." Buba ya ƙyalƙyale da dariya ya tashi ya ɗauko flaks ɗin da ake zuba masa abinci ya miƙawa Sagir, Sagir ya karɓa ya buɗe ya ce "Dan daurayo shi dai a bayan gida Malam Buba, na ga da ɗan maik'o a cikinsa." Buba ya ce. "Toh Sagiru daɗina da kai akwai tsafta." Sagir ya yi murmushi kawai yana wurwurga idanunsa a ɗakin yana neman inda zai ga makullan gidan. Cikin sa'a ya ga malam Buba ya ajiye su akan wani ɗan table ya shige toilet. Jikinsa har rawa yake ya ɗauka tare da juyawa ya fice daga ɗakin da mugun gudu, inda ya bar Neehal anan ya tarar da ita. Ya kama hannunta suka nufi get ɗin da gudu, ya lalubo key ɗin ƙofar ya shiga bubbud'e makullan gidan kusan guda goma, yana yi yana waiwaye. Yana gama buɗewa ya hango Buba ya fito daga ɗakinsa a gigice, ya kama ƙaramar ƙofar gate ɗin ya buɗe ya tura Neehal waje sannan shi ma ya fita, ya damk'i hannunta suka falfala suka yi gabas da mugun gudu. Tafiya sosai suka yi sannan Neehal ta faɗi tana numfarfashi, cikin magana da ƙyar ta ce. "Ruwa, ruwa." Sagir ya ce. "Ki yi haquri ban san inda zan samu ruwa in baki ba, kuma dole anan zan barki in koma gidan da muka fito in karɓi hukunci na." Neehal ta ƙura masa ido ta ce. "Me yasa ka san za'a hukunta ka, ka taimake ni? Me yasa zaka koma gidan da da mutanen cikinsa babu Allah a ransu? Ka zo mu gudu tare mana." Sadik ya girgiza mata kai ya ce. "Duk inda na shiga a faɗin duniyar nan sai sun nemo ni, idan ban koma ba a yanzu za su tsotse jinin mahaifiyata wadda ita kaɗai ta rage mun a duniya, ni kuma da haka ta faru gwara ni su kashe ni." A ruɗe Neehal ta ce. "Tsotse jini kuma? Suna shan jini ne?" Sagir ya gyaɗa mata kai ya ce. "Eh suna shan jini, matsafa ne, kuma nima ina cikin su." Neehal ta waro Ido ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, me ya kaika cikinsu? kuma gashi ba kai kala da marasa imani ba." Sagir ya ce. "Baza ki gane ba ƴan'mata, amma abun da zan faɗa miki rashin imanin yan ƙungiyar nan ya wuce duk inda kike tunani, ni zan koma kafin azzaluman ƙungiyar da sarauniya su ƙaraso." Neehal ta ce. "Me yasa ka taimake ni?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce. "Saboda Yayanki Al'ameen, ya taɓa mun wani taimako da bazan taɓa mantawa da shi ba a rayuwata, kalamanki na d'azu a lokacin da na kawo miki abinci su suka tunzura ni akan na taimake ki, domin na san kamar yadda kika faɗa da ƙanwata ce na ga ana ƙoƙarin keta mata haddi sai inda ƙarfina ya ƙare a ceton ta duk da bani da ƙanwar ban san daɗinta ba ni kaɗai iyayena suka haifa. Dan haka na yi amfani da wannan damar gurin sakawa Ameen da Alkhairin da yay mun na taimake ki, domin na san da zarar sauran ƴan ƙungiya sun zo babu abun da zai hana su aiwatar da ƙudirinsu a kanki sai dai wani ikon Allah. Ni ne na bar ƙofar ɗakin da kika shiga a buɗe saboda na san idan kin samu kin kub'uta nan zaki fara tunkara dan neman tsira." Ta ce. "Ta ya ya ka san ni ƙanwar Ameen ce?" Sagir ya yi murmushi ya ce. "Na sani kawai." Neehal ta ce. "Ya sunan ka?" Ya ce. "Sagir." Ta ce. "Na gode sosai Yaya Sagir da taimakon da ka mun, amma ina tsoron kar su kashe ka saboda ka fito da ni." Sagir ya ce. "Karki damu baza su taɓa kashe ni ba." Neehal ta sauke ajiyar zuciya numfashinta na fita da sauri_sauri. Sagir ya miƙe da niyyar tafiya Neehal ta tsayar da shi da faɗin. "One more question." Ya tsaya yana kallon ta bai ce komai ba. Ta ce "Wanda waɗannan mutanen suka kaini ɗakinsa shine wanda yake ƙoƙarin keta mun haddi? Shine wanda aka ce mun my virginity is for him? Shi ma ɗan ƙungiyar ne? Yana shan jini?" Sagir ya ce. "Kin ci sunanki ƴar jarida, Tamboyoyinki kuma amsar su gaba-d'aya *Eh* ce." A razane Neehal ta ce. "Real him ɗin shi fa, not fake face maks ɗin daya saka, kasan kuwa matsayin shi a gurina?" Sagir na ce. "Na sani kuma shi ne." Neehal ta dafe ƙirjinta da sauri saboda wata irin bugawa da zuciyarta ta yi a million. Hakan ya yi dai_dai da jin vibration ɗin wayarta da ta yi. Sagir ya juya ya tafi cikin sauri. Ta zaro wayar daga cikin aljihun rigarta da ƙyar saboda yanda kanta yake juya mata, ta danna gurin picking ba tare data duba mai kiran ba. Ameen wanda tun safe ya ɗora da kiran Numbobin Neehal sai yanzu cikin sa'a ya ji ɗaya ta shiga. A hanzarce ya ce. "Miemerh." Cikin magana da ƙyar ta ce. "Yaya...!" Ya ce. "Where are you?" Ta ce. "I dont know, please Yaya ka zo ka ɗauke ni." Ameen ya sauke doguwar ajiyar zuciya ya ce. "Okay I will come now Insha Allah, ki bar wayar a kunne." Bai jira amsar ta ba ya katse kiran. Ya miƙe da sauri ya ɗauko wata laptop ɗinsa ya kunna ta ya shiga latsawa yana kwafar Numbern da suka yi waya da Neehal yanzu yana sakawa a ciki, sannan ya ɗauko wani abu mai kama da waya