Showing 150001 words to 153000 words out of 262509 words
Chapter 51 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
ga bata ɗauka ba yay mata reply ɗin text ɗinta, tare da daɗaɗan kalaman soyayya a ƙarshe. Ta yi ɗan murmushi, sannan ta tashi ta je ta wanke fuskarta. Bayan Sallar Azhar tana zaune a ɗakinta da materials ɗin karatun ta tana dubawa. Mama ta shigo ɗakin ta ce mata. "Neehal Ahmad ya zo." Ta d'ago da sauri gabanta na wani irin fad'uwa saboda razana. Mama data kula da yanayin da ta shiga ta ce. "Ki je ku gaisa, yana ƙasa yana jiranki, kuma karki nuna masa wani abu, idan zai tafi i will explain to him." Neehal ta gyaɗa mata kai kawai. Kamar wadda k'wai ya fashewa a ciki ta tashi cikin sanyin jiki ta yane kanta da mayafin abayar dake jikinta. Ta ɗan gyara fuskarta sannan ta fesa turare kaɗan, sannan ta fice daga ɗakin cikin matuƙar sanyin jiki.
As always yana zaune akan carpet idanunsa akan steps. Ta sakko cikin nutsuwarta kanta a ƙasa, gabanta na cigaba da faɗuwa ta zauna a kusa da shi tare yin sallama. Yana murmushi ya amsa mata. Ta ce "Ina yini Uncle." Ya ce "Lafiya k'alau Princess, ya weekend?" Ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Ya School da aiki?" Ta ce "Alhamdulillah." Ya gyara zama tare da juyowa ya fuskance ta sosai ya ce. "Kin yi kyau, kullum kamar ƙara miki kyau ake Princess." Ta d'ago tare da ƙirƙirar murmushi akan fuskarta a ƙoƙarin ta na ganin bata nuna masa akwai wata damuwa ba, ta ce. "Ni ɗin kuwa?" Ya ce "To da wa?" Ta sake yin murmushi ta ce. "Ina Yarana?" Ya ce "Suna gida." Ta ce "Da fatan dai suna lafiya, kuma baka barin wani abu yana damar mun su?" Ya kafe ta da ido ya ce. "Suna lafiya, ni kam me zan bari ya damu ƴaƴan Aunty? Ai lallaɓa su nake kar Aunty ta ce ta fasa Aure na." Ta yi ƙasa da kanta da sauri saboda yanda ta ji bugun zuciyarta ya sauya, ta hasaso yanda yake cikin farincikin nan da nishad'i ya zai ji idan Mama ta yi masa bayanin ta kusa zama mallakin waninsa, daga yau ba zai ƙara zuwa su yi irin wannan zaman ba, duk soyayyar da ya nuna mata ta zama tahiri, a...... "Princess.!" Ya katse mata tunani ta hanyar kiran sunanta. Ta d'ago tay masa kallon cikin ido cikin dakiya. Ya lumshe ido ya buɗe su a cikin nata ya ce. "Tunanin me kike?" Ta ce "Babu komai Uncle." Ya karyar da kai ya ce, "Let me snap you, kin mun kyau sosai yau." Ya ɗauko wayarsa yay mata pictures, ita kuma tana ta murmushi, sannan ya ɗauke su tare. Ta karɓi wayar tana dubawa, hotunan sun yi kyau sosai. Ta yi murmushi ta cigaba da kallon pictures ɗin wayar, wanda fiye da rabi na twins ne. Ta tura wanda yay musu yanzu sannan ta tuttura wasu na twins da nasa ta whatsapp. Mama da kanta ta sakko ta shiga kitchen ta zubo masa abinci ta kawo masa, ya dinga yi mata godiya cikin jin kunya. Bayan Mama ta koma sama ya dubi Neehal ya ce. "Ina son Mama sosai, saboda kirkinta, da sanin darajar ɗan Adam gami da karamci." Ta yi murmushi kawai, sannan ta zuba masa abincin, yana ci suna hira, wanda Neehal ta ji kusan rabin damuwarta ta tafi. Sai da aka kira Sallar la'asar sannan ya tashi ya je masallaci ya dawo. Neehal bata sakko ba tana ɗakinta akan darduma bayan ta idar da Sallah, addu'a take yi akan Allah ya sanyayawa Ahmad zuciyarsa, Allah yasa kar abun da Mama zata faɗa masa ya yi hurting heart ɗinsa over.
Jin dawowarsa Mama ta sakko ta zauna akan kujera sannan cikin kulawa ta ce. "Neehal ta faɗa maka za mu yi magana ko Doctor?" Cikin fad'uwar gaban da bai san ko ta mecece ba ya ce "Eh Mama." Mama ta danne tausayinsa dake cikin ranta ta fara yi masa bayani, cikin tausasan kalamai ta yanda zai fuskanta. Da farko ji yay kansa ya masa wani irin juyawa, yawun bakinsa ya kafe kaf, dak'yar ya iya had'iye wani abu mai ɗaci da ciwo daya tsaya masa a mak'oshi ya ce. "Babu komai Mama, na fahimce ki, Allah kuma yasa hakan shi ya fi Alkhairi a gare mu gaba-ɗaya." Ya yi maganar cikin tsananin dauriyar zafin da zuciyarsa take masa. Bai kuma fuskantar abun da Mama take kuma faɗa masa ba, ya dai ji kamar haquri take ba shi da kuma ƴar nasiha. Ya gyaɗa mata kai kawai, ita kuma ta tashi ta nufi upstairs tana faɗin bari ta turo masa Neehal ɗin su yi Sallama. At the first bayan barin Mama falon ya d'ago kansa tare da lumshe idonsa yana fatan ya kasance mafarki yake ba gaske ba ne abun da Mama ta sanar masa. Ya yi imagine wai hakan na nufin ya rabu da Princess ɗinsa kenan har abada, nan da wani ɗan lokaci za'ai mata aure da wani ba shi ba. Innalillahi,wa'inna'ilaihirraji'un ya shiga maimaita a fili cikin sanyin murya mai cike da damuwa, har ya ji ya fara ɗan samun salama a cikin ransa. Neehal wadda da ƙyar Mama ta yaƙo ta, ta fito saboda ta ce bata san da idon da zata kalle shi ba, ta ƙaraso falon idanunta na shatatar hawaye, da ƙyar take iya ganin gabanta. Ya ƙura mata ido cikin sarewa da karayar zuci, karon farko a rayuwarta ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kuka. Ya runtse ido ya buɗe saboda yanda kukan nata yake taɓa masa zuciya. Ya tsotsi lips ɗinsa da suka bushe lokaci ɗaya saboda damuwa cikin marainiyar murya ya ce. "Please Princess Stop crying, ko so kike nima in yi kukan?" Ta girgiza masa kai. Ya d'ago kanta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma ya shiga share mata hawaye da shi. Ta bar jikinsa tana sakin ajiyar zuciya. Cikin muryar kuka ta ce, "I'm so sorry Uncle, I..." Ya katse ta da faɗin. "Me kikai mun Princess da zaki bani haquri? Na fuskanci bayanin Mama kuma na gamsu. Princess! Ba mu muke da ikon tsarawa kanmu rayuwa ba, Allah ne yake tsara mana. I'm a Muslim, na yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, tabbas rasa ki a cikin rayuwata ba ƙaramin rashi ba ne, amma kuma babu yanda zamu yi da ikon Allah. Karki damu akan wannan Please Princess, I knew you love me so much." Ta kalli fuskarsa yay mata murmushin da ya fi kuka ciwo tare da kamo hannunta ya ce. "Princess! Sau da yawa abun da zuk'atansu suke so ba shine Alkhairi a gare mu ba, sai mu ga wanda bama so ɗin ya fi zama Alkhairi a gare mu. Duk da na san kina son guy ɗin da zaki aura ba wai auren dole za'ai miki ba. Amma ko kaɗan ban ji a raina kin yaudare ni ba or something like this, abun da kikai shine dai-dai, kuma shine adalci. Tunda shi guy ɗin he came first before I came, abun da baza ka so ai maka ba kaima karka so kaiwa wani, dan haka ki daina damun kanki indai ni Ahmad ne na haqura, dama rayuwa cike take da farinciki da baƙinciki, idan ka yi haquri kuma zaka ga ribarsa a gaba, kuma komai zai wuce kamar bai faru ba." Ya yi shiru yana sauke numfashi, dan shi kansa ya san ba ƙaramin dauriya yake ba wajen ɓoye mata damuwarsa. Ta ƙura masa ido cikin mamakin kalamansa zuciyarta cike da tsantsar tausayinsa, ta san daurewa kawai yake dan ya ga ta damu kar ta tashi hankalinta. A hankali ta ce "Thank you so much Uncle, for your cares and everything to my life." Ya yi irin murmushin d'azu ya ce. "Nima na gode da k'aunar da kika nuna mun Princess, and I will never forget you in my life. Na gode Na gode sosai, da k'aunar kike wa ƴaƴana. Allah ya yiwa rayuwarki albarka, ya baku zaman lafiya ke da mijinki idan kun yi aure, ya kuma baku zuri'a d'ayyiba." Ta ce "Amin Uncle tare da kai." Ya ja karan hancinta ya ce, "Zan wuce sai mun zo biki." Dan ba ƙaramin dauriya yake ba, so yake kawai ya kadaice ya rarrashi zuciyarsa. Ta lumshe ido hawaye ya zirnano daga cikin idanunta. Kamar zai yi kuka ya ce. "Oh My God Princess, dan Allah ki bar kukan nan, baki san yadda nake jin zafi a cikin raina ba idan kina yi. Ta share hawayen bayan ta zare hannunta daga cikin nasa ta ce. "Na daina Insha Allah Uncle." Ya ce "Promise to me ko na tafi baza ki yi kuka ba." Ta ja hanci a hankali ta ce. "Ba zan yi ba Uncle Insha Allah." Ya shafi kuncinta ya ce, "Good lady, yanzu fa kin girma Princess, ko kina so twins ɗinki su gan ki kina kuka?" Ta girgiza masa kai. Ya ƙara kamo hannunta ɗaya ya ce. "Tashi mu je ki raka ni." Ta kalle shi sannan ta tashi ganin shima ya miƙe. Ya taune lip ɗinsa jin kamar zai faɗi tare da dafa hannun kujera yana ambaton sunan Allah. Ta ƙura masa ido kawai cikin damuwa. Ya d'ago yana murmushi ya ce, "Wannan kallon fa?" Ta ƙara waro masa manyan kyawawan idanunta haɗe da juya masa su sannan ta lumshe su a hankali. Salon nata ya shige sa ba kaɗan ba, bai san sanda ya dafa kafaɗunta ba ya yi kissed saman idanun, a hankali kuma ba tare da ta taɓa zato ba ta ji saukar lips ɗinsa akan nata. Ta sauke wani gwauron numfashi lokacin da ta ji yana kissing ɗinta, kafin a hankali ya janye fuskarsa daga ta_ta. Cikin raunin murya ya ce, "Good bye Princess, I love You.!" Sannan kamar wanda aka tsikara ya juya da sauri ya fice daga falon. Sai buɗe idanunta ta yi ta ga babu shi sai k'amshinsa da ya bar mata a jikinta da falon. Ta ja ƙafafuwanta da sukay mata nauyi ta ƙarasa kujerar dake kusa da ita, ta faɗa kanta ta fashe da kuka, a ranta tana faɗin. 'This means daga yanzu mun rabu da Uncle, rabuwa ta har abada.' Ta cigaba da kukan ta a gurin, ta ma manta da alƙawarin data ɗaukar masa na baza ta kuma yin kuka ba, akan rabuwar ta da shi.
Da ƙyar Ahmad ya iya jan ƙafarsa ya je parking space, yana zuwa ya buɗe Motar da ya zo da ita ya shiga ya zauna ya ɗora kansa akan sitiyarin Motar, yana jin zuciyarsa tamkar zata soye saboda zafin da take masa. Ganin abun yake tamkar almara, domin bai taɓa tunanin zai ƙara rasa Neehal a karo na biyu ba. Amma ya yadda da ƙaddara, ya kuma yarda wani ba ya taɓa auran matar wani. Zai dage da addu'a akan Allah ya cire masa sonta ko da ba duka ba daga cikin ransa, ya kuma bashi mace ta gari wadda zata kula da shi da marayun ƴaƴansa. Sai dai ya rasa me yasa wani b'arin na zuciyarsa yake tabbatar masa da bai rasa Neehal ba, yake nuna masa zai mallake ta. Ya sauke numfashi tare da addu'ar idan rabonsa ce ita, Allah ya bashi, zai je ya dage da addu'a. Sunan Allah yay ta maimaita a ransa, har ya ɗan samu nutsuwa. Cikin dauriya ya kunna Motar ya fice daga gidan bayan an buɗe masa gate ya nufi gidan Mamy. Yanda Mamy ta ganshi ya shigo a sanyaye kamar mai cuta ta san da matsala, a ɗan rikece ta tambaye shi me nene? Kamar zai ɓoye mata sai kuma ya sanar mata. Itama Mamy ta ji ba daɗi a ranta sosai, domin ta yiwa Ahmad sha'awar Neehal, dan ta yaba da hankalinta da nutsuwarta. Amma sai ta kwantar masa da hankali, ta ce ya je ya dage da addu'a Allah ya zaɓa masa abun da ya fi Alkhairi.
Har bayan Magriba Neehal bata daina kuka ba, Mama ta yi rarrashin ta yi nasihar ta yi faɗan amma ta ƙi barin kukan, har ta gaji ta ƙyale ta. Tana jin wayarta nata vibrate ana ta kiran ta amma ta ƙi bi ta kanta. Ga kanta dake ciwo saboda kukan da take. Bayan Magriban ne Ameen ya zo gidan, lokacin tana ɗakinta a kwance akan gado. Bayan sun gaisa da Mama ya tambaye ta Neehal ɗin, ta sanar masa tana ɗaki tana kuka, ko abinci bata ci ba tun safe. Bai tambaye ta dalilin kukan ba ya tashi ya shiga ɗakin. Ya zauna a gefen gadon ya kira sunanta, ta tashi zaune da ƙyar tana goge hawayen fuskarta, idanunta sun yi jajur. Cikin sanyin murya mai nuni da rarrashi yay mata Ƴar nasiha, akan kuka ba maganin damuwa ba ne, komai yake damun ka, ka kaiwa Allah kukan ka, shi zai maka magani. Sai gashi ta yi shiru, ya ce ta je ta wanke fuskarta ta zo ta ci abinci. Bata musa ba, ta tashi ta yi abun da ya ce. Mama ta cika da mamakin ganin cikin mintuna ƙalilan ta saki ranta, Alhalin ita tun yamma take fama da ita. Sai da ta ci abincin ta sha maganin ciwon kai sannan Ameen ya bar gidan.
Washegari kamar yadda Dad ya ce, Sadik ya zo gidan da yamma. Har part ɗin Daddy'n akai masa iso ya je ya same shi. Daddy yay masa ƴan tambayoyi, sannan ya ce ya bashi auran Neehal ya turo magabatansa. Ai Sadik ji ya yi kamar ya rungume Daddy dan tsananin farin ciki, yay ta zuba masa godiya. Ranar Neehal ta sha kalamai da soyayya a gurin shi kala_kala, ita kuwa tay ta masa dariya tana tunanin ranar da aka ɗaura musu aure kuma sai ya kusa mutuwa dan farinciki. Bayan sati ɗaya mahaifinsa da abokinsa da Yayan Maamah suka zo nema masa auren Neehal, tare da kuɗin na gani ina so. Daddy da Kawu Musa da Uncle Mahmud, da mijin Aunty A'isha, su suka karb'i kuɗin, aka saka ranar biki bayan ƙaramar Sallah da yardar Allah, lokacin Neehal sun yi graduation ba jimawa. Su Sadik baki ya ƙi rufuwa, saboda farincikin nan da watanni biyar zuwa shida zai angonce da masoyiyarsa. A ɓangaren Ahmad kuwa a washegarin ranar da ya zo ya koma Abuja, yana zuwa ya sanar da su Ummi abun da yake faruwa. Sun ji ba daɗi sosai har Abban su Ahmad, amma suka ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi. Ahmad ya bawa zuciyarsa haquri, bai bari damuwa ta masa illa ba, duk da ko d'igo babu abun da ya ragu na son Neehal a cikin zuciyarsa. Daga ya ji abun zai dame sa sai ya dinga maimaita kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un da hasbunallahu'wani'imal'wakil, ga zuciyarsa kullum cikin ƙarfafa masa gwiwar Neehal tasa ce take, kar ya fidda rai da samun ta. Kuma babu abun da ya canza wa Neehal daga yanda suke before, idan ya kira wa su Afrah ita a waya, ta ce su ba shi wayar yana karɓa su yi magana har da ƴar tsokana wani lokacin, sai dai ba ya mata zancen soyayya ko kaɗan, zumunci kawai suke yi. Itama Neehal ɗin ta yi ƙoƙari ta cire damuwar rabuwa da shi daga ranta. Ta yadda cewa Allah ya yi Sadik ne mijinta tun fil azal, ba Jameel, Anwar da Ahmad ba, tunda su sun rasu, Ahmad kuma shi yasa Allah ya raba su tun a farko, dan da ace ba su rabu da shi ba a lokacin da take gidan Aunty Fauziyya, da ko soyayya ba zata yi da Jameel da Anwar ba, tunda ga shi kuma tun lokacin yake son ta. Ta kwantar da hankalinta suna shan soyayyar su da Sadik. Sai dai tunda aka tsayar da lokacin bikin su take jin wani irin feeling a cikin zuciyarta, feeling ɗin data kasa tantance ko na mene ne, sai dai yana mata yanayin kamar tsoro ko fargaba, amma kuma tsoron da fargabar na mene? Sai kuma wani abu guda ɗaya, ɗan sakin fuskar data fara samu daga gurin Ameen da kulawa ya daina mata yanzu, sai ta gaishe shi ma ya ƙi amsawa, ita kuma hakan na damunta matuƙa, bata son ta ga yana yi mata irin wannan shariyar, sai ta ji duk ranta babu daɗi........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*6️⃣0️⃣*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
...........Da yamma Haneefah ta zo gidan, duk da tana fama da laulayi amma ta ce ba zata iya kwana bata ga lefen Besty ba. Bayan sun gaisa da su Mama ta hau sama gurin Neehal. A falo ta tarar da ita idanunta a lumshe tana sauraren karatun Alkur'anin da tasa a speaker. Haneefah ta ƙarasa inda take ta taɓa ta, tare da faɗin. "Amarya." Neehal ta buɗe idonta ta dube ta, ta yi murmushi ta ce. "Na'am Ango." Haneefah ta zauna a kusa da ita, ta ce. "Ya na ganki wani iri, ko baki da lafiya ne?" Neehal ta ce. "A'a k'alau nake, kawai yanayi ne." Haneefah ta ce, "Yanayin me? Ke da ya kamata a zo a tarar kina cikin farinciki da annashuwar kin kusa aure." Ta ƙarashe maganar da dariya. Neehal ta harare ta, ta ce. "Zan bar Maman shine zan dinga farinciki?" Haneefah ta ce. "Wannan duk na ɗan lokaci ne, kina jin zaƙin auren zaki ware, wuyarta ki shiga daga ciki, ke Auran fa da daɗi." Neehal ta ƙara hararar ta, ta ce. "Allah ya shirye ki, kin fi ƙarfi na." Haneefah ta yi dariya ta ce. "Ina Barrister? Na ɗauka zan shigo in same ki kina waya da shi kuna soyewa." Ta sauke numfashi ta ce. "Yana nan k'alau, ba mu jima da yin waya ba, ina Yah Faruq?" Haneefah ta ce. "Yana can Kogi State." Neehal ta ce. "Yaushe zaki koma ke?" Ta ce. "Next week insha Allah, tunda by Monday zamu gama exam." Neehal ta gyaɗa mata kai cikin ƙoƙarin ganin ta ɓoye Mood ɗin da take ciki. Ta