Showing 198001 words to 201000 words out of 262509 words

Chapter 67 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21387

an aiko mata da saqon mutuwa ta fara magana cikin amon murya da faɗin.........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*7️⃣0️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
















......."Barka da zuwa Muhammad Tafida, ƙungiya na farin ciki da kasancewar ka a cikinta. A kodayaushe muna san irinku masu tsantsar riƙo da addini a cikin mu, domin mu mun fi son mu ɓata shiryayyu su koma ɓatattu, wannan shine burinmu akodayaushe." Sannan ta dubi Kabir ta ce masa. "Aikinka yana kyau mai jan kai bawan mai jan kai, a yau za'a ƙara maka matsayi a cikin wannan ƙungiya, sakamakon kawo mana wannan babban mutum cikinta da ka yi. Markus da Jamus suna alfahari da kai." Na dubi Kabir na dube ta ba tare da na gane inda maganganunta suka dosa ba. Ina son na yi magana amma na kasa koda motsa labbana ne balle na iya sarrafa harshena. Na yi ƙoƙarin juyawa na fice daga ɗakin kamar yadda na yiyyi d'azu amma na kasa, daga nan ma ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai farkawa na yi na ganni kwance akan wani irin gado ɗan ƙarami, babu komai a jikina sai jan k'yalle ɗaure a hannuna da kaina da ƙafata. Na yunƙura na tashi sai na ga mutane mata da maza kusan hamsin zagaye da gadon da nake, dukkanin su tsirara haihuwar uwarsu sai ɗan jan k'yallen nan kamar na jikina. Suna watsa mun wani jan abu ajikina wanda na fahimci jini ne, suna kuma yin wani abu da bakinsu kamar wak'a amma da wani irin yare irin nasu na matsafa. Na gaza yin komai sai bin su da ido, Kabir kawai na gane a cikinsu sai wannan ƙatuwar matar dake facing ɗina tana mun wani irin kallo. Sun daɗe suna yin abubuwan su akaina, su shaƙa mun hayak'in wannan, su fesa mun wancan su watsa mun wannan, haka dai sukay ta yi. Sai na ji gaba-ɗaya jikina kamar ba nawa ba, kamar an canza ni, na ji zuciyata da ƙwaƙwalwata kamar ba su taɓa sanin abu a cikin duniyar nan ba sai waɗannan mutanen. A tak'aice dai a ranar na zamto member na wannan ƙungiyar ba dan son raina ba sai sanadiyyar la'anannen abokina, kuma duk abun da suka saka ni in yi bana musu nake yi. Ni ban sani ba ashe har mun kwana a gidan, wannan farkawar da na yi ma tsakar dare ne. Sai washegari da hantsi sannan aka bani kayana na saka muka baro gidan ni da kabir, bayan Sarauniya kamar yadda na ji suna kiran wannan ƙatuwar matar ta kafa mun sharad'an zuwa kullum wannan gidan ana aikin ƙungiya tare da ni. Ta tabbatar mun babu abun da zan nema a duniyar nan in rasa komai girman buƙata_ta da burina zan samu, sannan kuma dole duk aikin da ƙungiya ta saka ni in yi shi komai wahalarsa, kuɗi kuwa idan suna bautawa mutum sai sun bauta mun a duniyar nan saboda yawan kuɗin da zan yi. Ta kuma raɗa mun suna jaririntah, sauran ƴan ƙungiya kuma suna kira na autan ƙungiya. Jikina kamar ba nawa ba muka taho gida ni da Kabir dake ta murmushin farinciki da jin daɗi. Ni dai kawai kallon sa nake ina jin kaina ya mun wani irin nauyi kamar duka mutanen duniyar a kaina suke. Sai da muka shigo cikin gari sannan na fara dawowa nutsuwata, hankalina ya fara dawowa jikina. A fili na ce. "Shikenan na zama matsafi ɗan shan jini kenan?" Na yi tambayar cikin tsananin mamaki da al'ajabi. Kabir ya tuntsure da dariya ya ce. "Harkar akwai samu na gidana, zaka yi bala'in kuɗi nake faɗa maka mutumina, na san inna faɗa maka gaskiya tun kafin mu zo baza ka taɓa amincewa ka biyo ba, shi yasa kawai na kawo ka. Na daɗe ina son saka a cikin wannan harkar dan na san ƙungiya tana buƙatar irinku masu tsoron Allah." Ban san lokacin da nay masa wata muguwar shak'a ba, ya yi saurin taka burki. Ina huci na ce masa, "ka cuce ni Kabir ka cuci rayuwata, yanzu mai zan ce da Ubangiji na da kuma iyalina akan wannan mummunar harkar daka saka ni a cikin ta? Mene ribarka na mun hakan Kabir? Wanne laifi nay maka a rayuwar nan ka zaɓi sanya ni cikin wannan mummunar harkar? Wacce irin tsana kai mun har haka? Dan wannan ba k'auna ba ce." Ya k'wace jikinsa dak'yar daga shaƙar da nay masa yana mayar da numfashi ya ce. "Aikin gama ya riga ya gama, duk wani hargagi da zakai baza ka taɓa fita daga cikin ƙungiyar nan ba har abada, ƙungiya ce da in aka shiga ba'a fita, sai dai in mutuwa ka yi." A hasale na ce masa ƙarya yake, kuma zai sha mamakina, ni da ƙara zuwa wannan gidan har abada. Anan muka rabu da Kabir baram_baram ya fice ya bar mun Motata ina girmama rashin imani da son duniya irin na Kabir, ko kaɗan ban taɓa sanin yana wannan harkar ba, dan ban yi zaton son duniyar tasa har ya kai haka ba. Bayan na koma gida na tarar da Fateemah duk ta tayar da hankalinta akan rashin dawowata gida jiya. Tana gani na ta saka kuka ta ce. Indai har ina son zama da ita daga ranar in bar siyasa, ta gaji da wannan bala'in yawa_yawan, ga wani mummunan mafarki da ta yi a daren jiya a kaina. Na tabbatar mata daga ranar na bar siyasa har abada, dama ko bata faɗa ba na yi niyyar dainawa saboda a sanadinta na faɗa wannan mummunar harka. Saboda tana cikin murnar gani na bata lura da canjin yanayin da nake ciki ba. Amma tay ta tambaya ta inda na je na kwana, na sanar mata wani ƙauye muka je campaign motarmu ta lalace mana a hanya. Tay ta mun wani irin kallo kamar bata yarda da abun da na ce mata. First maganar data fara fitowa daga bakinta a lokacin in rabu da Kabir Ginyau domin ba mutumin arzik'i ba ne, bata son alaƙa ta da shi, dan ta san duk inda na je tare muka je da shi. Na ce mata Insha Allahu na rabu da shi kenan. Daren ranar ban iya runtsawa ba saboda tsananin damuwa, na yi dana sanin, sanin Kabir a rayuwata babu adadi. Na yi kuka, na yi kaico da rayuwata, na tsani kaina, na dinga addu'ar Ubangiji ya ɗauki raina a daren in huta, da dai in cigaba da rayuwa a matsayin ɗan shan jini. Washegari safiya tana yi na ji hankalina gaba-d'aya ya yi gurin matsafan nan, na ji kamar zan mutu idan ban je gurinsu ba. Lokacin ina aiki ban yi retired ba, na shirya da zummar zuwa gurin aiki na fita, ina fita na kira Kabir na ce ya zo ya kai ni gidan jiya dan ba zan iya gane hanya ba. Kabir ya zo ya dinga mun dariya yana faɗin dama ya ce ba zan taɓa iya fita ba daga ƙungiya ba da kaina zan koma, to sun riga sun gama tsaface ni na zama na su. Tun daga wannan rana idan ban je gidan nan ba yau to gobe zan je. Amma ko sau ɗaya ban taɓa kwana a can ba, duk da kowanne member akwai ranar kwanansa a gidan, dan an fi yin aiki cikin tsakiyar dare. Ni kaɗai ne bana kwana saboda ban san me zan faɗawa Fateemah ba idan na je na kwanan, ina zan ce mata ina zuwa? Sarauniyar ƙungiya tana matuƙar sona a cewarta, hakan yasa ko da an ce a yi abu na ƙi yi bata iya hukunta ni, saɓanin sauran members da babu wanda yake iya yi mata musu. Ni kuma ina sane nake ƙin yi wani abun idan ta umarce ni, saboda ta yi zuciya ta kashe ni. Dan wallahi ina cikin ƙungiyar ne kawai amma bana so, ni kaɗai na san baƙin cikin da nake ciki a sanadiyyar kasancewa ta a cikin wannan ƙungiya, kodayaushe cikin yiwa Kabir Allah ya isa nake, tunda shi ya jefani a cikin wannan iftila'in, kuma har abada ba zan yafe masa ba. Babu abun da ake aikatawa a cikin wannan ƙungiyar face zallar rashin imani da shirka da tsantsar tsafi. Zaku sha mamaki idan kuka ji manya da wasu daga cikin masu mulki a ƙasar nan wanda ake musu kallon mutanen kirki amma suna cikin wannan ƙungiya. Lokaci ɗaya na sauya daga aihin Muhammad Tafida na, na koma wani daban, na watsar da duk abokaina saboda tsoron kar su gano mummunar hanyar dana faɗa, ƴan ƙungiyar nan su suka zama aminaina da su kaɗai nake hulɗa. Dole ne ko kuma in ce sharad'i ne na wannan ƙungiya, duk wanda yake cikinta sai ya yi tarayya da ƴarsa ta cikinsa budurwa, idan kuma macece ta yi da ɗanta saurayi wannan tilas ne ga kowa. Amma naga su members ɗin ƙungiyar kamar hakan ba ya damun su, daɗi ma suke ji da murnar hakan, wasu ma ba ƴaƴa ɗaya suke ɓatawa ba, in sun kai goma ƴan'matan da samarin duk sai sun ɓata su, wasu ƴaƴan ma sanadiyyar hakan suke rasa ransu. Iyayen kuma su fi kowa nuna damuwa da zak'ewa akan al'amarin a idon duniya. Wanda ba shi da yar ko ɗan ne kawai ake masa uzuri, amma za'a ba shi wani aikin a madadin wannan ya yi, ko lalata ƙananan yara mata da maza, ko kuma wani babban saɓon ga Ubangiji. Nima hakan ce ta kasance da ni, bani da ƴa mace dan haka aka bani aikin ɓata ƙananan yara mata ta hanyar yi musu fyaɗe. Kai tsaye na ce ba zan iya ba, duk da ina cikin wannan ƙungiya amma imanina bai tafi duka daga cikin zuciyata ba. Manyan ƙungiya suka mun caaa aka da masifar dole sai na yi, ai ba fin su na yi ba da za'a saka ni abu ina ƙin yi, amma Sarauniya ta tsawatar musu ta ce su rabu da ni, ta san ya zata yi da ni. Haka na cigaba da rayuwa cikin takatsantsan da ɓoye abun da nake aikatawa, dan babu wata alama da zata nuna maka ina wannan mummunar harkar idan ka gan ni, ba ma ni kaɗai ba, duka yan ƙungiyar idan suka fito cikin gari haka ne, ko iyalanmu ba su isa sun gane ba.










Na karb'i riƙon Neehal a lokacin da Fateemah ta zo mun da shi gidana saboda Allah ba dan wani abu ba, kuma Allah ne shaidata akan hakan. Tun kafin nan dama ta saba zuwa mana hutu tun iyayenta suna da rai, haka kawai na ji ina son yarinyar tamkar ƴar cikina dana haifa haka nake kallon ta. Da zuciya ɗaya nake riqonta kuma nake yi mata komai. Watarana lokacin Neehal ta kusa shekara da dawowa hannunmu gaba-d'aya da zama Kabir ya zo gidana. Ban shigar da shi ciki ba saboda bana son Fateemah ta san muna tare sai muka zaune a farfajiyar gidan. Muna zaune sai ga Neehal an dauko ta daga makaranta ta dawo, tana hango ni ta taho da gudu ta rungume ni kamar yadda ta saba, nay mata Welcome sannan ta gaishe da Kabir ta wuce cikin gida. Kabir ya bita da kallo sannan ya dube ni ya ce wannan yarinyar fa? Na haɗe rai dan na san halinsa da maitar mace komai ƙanƙantarta nay masa bayanin yanda take a gurina. Ya jinjina kai bai ce komai ba, ashe shi ya k'udurce abun a ransa, washegari muna zuwa ƙungiya ya ce ai ina da 'ya mace budurwa ƙarya nake na ce ban da ita. Cikin mamaki na ce musu da gaske ban da ƴa mace ta cikina, ɗana ɗaya ne tal a duniya kuma namiji ne, kuma Kabir ya fi kowa sanin haka. Kabir ya bayar da labarin ganin da yaywa Neehal jiya a gidana. Sarauniya ta yi bincike a ƙwaryar tsafinta sai ga fuskar Neehal ta bayyana. Ta dube ni ta ce. Tunda ni nake ciyar da Neehal nake shayar da ita nake tufatar da ita kamar ƴar cikina take a yanzu, dan haka ƙungiya tana buƙatar budurcinta. Na ce gaskiya ba zan iya cutar da ƴar amana ba marainiyar Allah. A fusace Sarauniya ta ce mun. Dole in yi, in ba haka ba su kashe iyalina su kashe ni kuma sannan wani a cikin ƙungiya ya karb'i budurcin Neehal ɗin. Hankalina idan ya yi dubu ya tashi a ranar, dan na san duk abun da sarauniya ta faɗa zata iya aikata fiye da hakan ma. Ba zan so in rasa matata da ɗana ba, kuma ba zan so a ɓata rayuwar Neehal ba. Dan haka na yanke wata shawara, na nuna musu na amince zan yi abun da suke so, amma a lokacin Neehal ta yi yarinta su ɗan bari ta ƙara girma. Da ƙyar suka amince da abun da na faɗa, dan a cewar su wanda ba su kaita ba ma ana musu fyaɗen. Na dawo gida hankali a tashe cikin rashin sanin mafita, ni ba'a abun in ce Fateemah ta mayar da Neehal gurin ƴan'uwanta ba dan tserayar da rayuwarta ba, ta ce mun akan me? Na dai ƙudurce a raina komai zai faru sai dai ya faru amma ba zan taɓa haikewa Neehal ba har abada, gwara na rasa raina dana aikata wannan abun kunyar. Ni babban tashin hankalina da suka ce ko ban aikata mata da kaina ba wani zai aikata mata. Ban taɓa sanin ina son Neehal sosai ba sai a wannan lokacin, Na saka ido sosai akanta saboda na san tsaf zasu iya ɓullo mata ta wata hanyar, musamman Kabir da kodayaushe cikin zancen ta yake. Haka shekaru suka shud'e ina ƙara bawa ƙungiya excuse akan Neehal, na rasa me yasa su kuma suka damu da ita over, kodayaushe cikin yi mun nacin in yi in far mata suke, wai hakan ba ƙaramin cigaba zai ƙarawa ƙungiya ba, yarinyar ta musamman ce gashi nima ban taɓa yiwa ƙungiya irin wannan aikin ba shi yasa suka damu da abun. Lokacin da na yi released soyayyar Neehal da Jameel sai na ce ya turo a yi auransu idan dagaske yake, Fateemah ta ce, na bari ta ɗan yi karatu mana tunda time ɗin candy kawai ta yi. Amma na ce a'a, dan so nake kawai na aurar da ita na huta da fargaba a kanta, a ganina idan ta yi aure ai dole su haqura da batun. Ban san a inda Kabir ya samu labarin Engage ɗinsu ba dan ban faɗa masa ba saboda bana son ya sani. Amma sai tsintar maganar na yi a ƙungiya, aka dinga zazzaga mun masifa wai ina son cin amanar ƙungiya ne, na ce musu danginta ne suke son aurar da ita ba ni ba ne. Sai suka ce to duk yadda za'a yi a yi a fasa batun bikin nan, ko kuma in karɓo musu abun da suke so kafin lokacin bikin. Na amsa musu kawai amma ban aiwatar ba. Wallahi ban san ya aka yi ba, ban kuma san ta yanda aka kashe Jameel ba, kuma bani da masaniya a lokacin da suka shirya kisan. Sai da aka yi sannan nake ji a ƙungiya Kabir ne ya shirya komai. Sarauniya ta tabbatar mun da cewar haka zasu yi ta yiwa duk wanda zai auri Neehal, tunda ni taurin kai gare ni na ƙi yi musu abun da suke so. Manyan ƙungiya sun so hukuntani amma Sarauniya ta hana, ni kaina ina mamakin yanda Sarauniya bata iya hukunta ni duk laifin da zan yi, ita da bata da tausayi da imani ko kaɗan. Duk uwar bautar da kake mata kana mata laifi na rana ɗaya zata rufe idonta ta azabtar da kai.










Abun da ya taimake ni akan Neehal ƙa'ida ne kowa shi zai yi amfani da ƴarsa, wani ba zai taɓa replace ɗinsa ba a ƙungiya, wannan dalilin ne yasa ba'a bawa wani damar keta wa Neehal haddi ba sai ni. Ban taɓa tunanin zasu kuma kashe Anwar ba a lokacin dana bashi auran Neehal, na yarda Ubangiji ne ke rayawa da kashewa rayuwar kowa a hannunsa take, dan haka sai kwanan mutum ya ƙare zai mutu. Ga dukkan alamu ba su samu labarin auren Neehal da Anwar da wuri ba sai gab da za'a kawo lefen ta, wallahi shi ma kamar kisan Jameel ban san sanda aka shirya kisan aka kashe shi ba. A lokacin hankalina yay matuƙar tashi domin na san idan aka cigaba da tafiya a haka akwai matsala, tunda dole hankalin mutane zai dawo kan abun, za'a fara zargin lallai da wata a ƙasa. Na rasa ya zan yi, na rasa hanyar neman mafita. Challenges da barazanar dana samu a ƙungiya baza su faɗu ba akan wannan al'amarin, wai ina ta raina musu hankali shekara da shekaru na ƙi yin abu. Ni kuma na ƙudurce a raina gara na mutu dana aikatawa Neehal wannan mummunan abun. Lokacin da Fateemah ta zo mun da batun tattaunawar da suka yi da su Sadiya akan suna zargin da akwai wanda yake aikata kisan su Anwar hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin na san tabbas idan tafiya ta yi tafiya asirina zai iya tonuwa. Ban tabbatar da hakan ba sai lokacin auransu da Sadik. Domin ƙungiya ba su san da bikin ba sakamakon ɓoye zancen bikin da kay sai da ya zo daf sannan aka bayyana, ana i gobe d'aurin Aure cikin dare sun tura a kashe Sadik aka tarar baya nan an sace shi. Hankalin ƙungiya ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin sun gane da alamun akwai wanda yake bibiyar al'amuransu kenan, nima hankalina ya tashi ba kaɗan ba dan bana son asirina ya tonu duniya ta san halin da nake ciki. Duk zuwa masallacin da na ce ina yi mu yi karatu ba can nake zuwa ba, gidan ƙungiya nake zuwa mu kwana muna bincike dan gano waye yake bibiyar al'amuranmu amma har yau mun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login