Showing 219001 words to 222000 words out of 262509 words
Chapter 74 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
so ya yi mata a rayuwar nan wanda zata ji daɗi? Ta ce masa babu komai ai ita ya gama yi mata komai a rayuwa. Ta kasa tantance tsakanin shi da Mama wa ya fi wani farinciki da amincewarta. Da daddaren Ameen ya kuma dawowa gidan, Neehal tana falon ƙasa tana kallon wani series firlm ɗin India da take matuƙar so, bata ji sallamarsa ba sai k'amshinsa ne ya sanar mata da zuwan sa. Ai kuwa da sauri ta miƙe ta nufi upstairs, ya bi ta da kallo kawai yana sakin wani munafukin murmushi. A balcony suka ci karo da Mama, garin saurin da take har da tuntube ta yi. Mama ta ce. "Subhallahi, ki dinga kallon gabanki mana kina tafiya a hankali, kuma lafiyarki kuwa na gan ki kamar a firgice?" Tana sassauke numfashi ta ce. "Babu komai." Tare da shigewa falo. Mama ta tab'e baki ta sauka ƙasa abinta. Ta tarar Ameen ya zauna har lokacin bai bar murmushin da yake yi ba, ta yi masa wani kallo sannan ta zauna a kujerar dake facing ɗinsa. Suka ƙara gaisawa sannan Mama ta ce masa. "Ya na ga ka dawo?" Ya kama haɓa da hannunsa ɗaya ya ce. "Oh Mum, dan na dawo gidanmu laifi ne?" Mama ta ce. "Baka da gaskiya ne shi yasa na tambaya." Ya waro ido ya ce. "Rashin gaskiya kuma Mum?" Mama ta ce. "Ka fi ni sanin me ka yi ai." Ya yi murmushi ya ce. "I don't know fa." Mama ta ƙara ta tab'e baki ta ce. "Ai baza ka taɓa sani ba, wannan muskilancin naka yana k'ona mun rai, ka turo a sanar mana abu kuma ka san an sanar manan and still you can't say anything about it." Ya shafa kansa yana murmushi sosai ya ce. "Mum, what do you want me to say?" Mama ta ce. "Abun da ka je ka faɗa a zo a faɗa mana." Ya yi shiru still yana murmushi bai ce komai ba. Mama ta shiga mitar abun da yake ranta, harda ce masa alfarma ta yi kawai ta ba shi Neehal amma ba dan halinsa ba, babu yanda zata yi da Kawu Musa ne kawai. Shi dai murmushi kawai yake yi. Daga baya kuma ta koma yi masa faɗa da faɗin. "Ga Neehal nan Ameen, idan Allah ya yi auranku na baka amanarta, ka riƙe ta da amana dan Allah, ka ga yarinyar nan bata da kowa sai Allah, marainiyar Allah ce, idan ka zalunce ta Ubangiji bazai bar ka ba." Ji ya yi jikinsa ya yi sanyi, soyayyar Neehal da k'aunarta gami da tausayinta na ƙara narkar masa da zuciya. Daga nan part ɗin Daddy ya je wanda dama shi ya kira shi yana son ganin sa, shi ma faɗa da nasiha ya yi masa duk akan ya riƙe Neehal da amana ne. Neehal kam bata kuma fitowa ba tunda ta shige ɗaki dan bata san ta fito su haɗu kar ta je bai tafi ba. Wani irin tsoronsa da kunyarsa Ubangiji ya ɗoro mata tun daga lokacin data fara tursasawa zuciyarta karɓar sa a matsayin mijin da zata aura.
A daren Daddy bai jira komai ba ya kira Abba da wasu cousins ɗinsa ya sanar musu abun da yake faruwa, ya kuma faɗa musu a cikin week ɗin nan yake son akai kuɗin Auren Neehal gidan kawunta. Mama ta ce masa saurin me yake har haka? Ya ce mata baza ta gane yanda yake d'okin abun ba ne, a yanzu ba shi da wani sauran buri a rayuwarsa bayan ya ga Auran Neehal da Ameen..... Kamar yadda ya faɗa ranar Asabar wanda ya kama kwana biyar da yin maganar da yamma suka kai kuɗin na gani ina so gidan Kawu Musa. Ranar Neehal ji ta yi gaba-d'aya kamar ba ita ba, ita ce yau aka karb'i kuɗin Auranta da Ameen? Sai ta dinga jin abun kamar a mafarki, ta tabbata dai Auransu za'a yi da Ameen, ɓoye kanta ta yi a ɗaki ta ci kuka ta k'oshi. Su Daddy ba su baro gidan Kawu Musa ba sai da aka tsayar da lokacin biki wata uku masu zuwa, a haka ma da ƙyar Kawu Musa ya yarda, ya ce abun tunda duk na gida ne no need a ja lokaci, in san ransa ne bai ƙi a yi bikin a cikin two weeks masu zuwa ba. Da Daddy ya zo yana faɗawa Mama ta ce, ta san wannan duk shirin Ameen ne, shi yake zuwa yana zubawa Kawu Musa sintiri akan maganar bikin. A ranar bayan Magriba Ameen ya zo gidan kamar kullum, sai dai tun daga ranar da Neehal ta zura masa da gudu bai kuma ganin ta ba, dan b'uya take yi a ɗaki, ana yin Magriba zata shige ɗakinta ta kulle dan ta san shine time ɗin zuwansa gidan, bata fitowa har sai ta tabbatar ya tafi. Shi kuwa yana sane da ita da duk b'uyan da take, kuma ya san duk saboda shi ne, ƙyale ta kawai ya yi ya ga iya gudun ruwanta dan ya san akwai ranar ƙin dillanci. A ranar Mama ta ce masa ya sanar da Hafsat maganar bikin, ya amsa mata duk da bai so hakan ba, da ya so sai abun ya matso daf sannan ya sanar mata, amma yaya zai yi tunda Mama ta bayar da umarni dole ya bi. Bayan isha'i ya koma gidansa, ya tarar da Hafsat Hakimce a falon ƙasa ta ci uwar kwalliya ta tarb'arsa..........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*7️⃣5️⃣*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
.........Ta ja gwauron numfashi ta sauke tana ƙoƙarin komawa ta kwanta wayarta ta fara vibrate alamar shigowar kira. Ta ɗauki wayar ta duba wake kiran nata, ganin Uncle Usman ne ta sauke ajiyar zuciya a hankali tare da picking kiran ta kara a kunnenta. Cikin muryar dake nuni da damuwa tay masa sallama, ya amsa mata. Ta ce. "Uncle an wuni lafiya?" Ya ce. "Lafiya k'alau Neehal, dafatan kina lafiya?" Ta sauke numfashi ta ce. "Lafiya k'alau Uncle." Uncle Usman ya ce. "Masha Allah, naga kiran ki, ina wanka ne kika kira ni, Allah yasa dai lafiya dan na ji muryarki wani iri kuma kira a daren nan." Idonta ya ciko da k'walla, ta daure ta ce. "Dole ce tasa na kira ka yanzu Uncle, da na so na bari sai da safe amma ina buƙatar magana da kai urgently." Uncle Usman ya ce. "To! Allah yasa lafiya dai?" Ta ce. "Lafiya k'alau, kawai shawararka nake nema akan wani al'amari, Allah yasa bazan takura ka ko Aunty ba?" Uncle Usman ya ce. "Haba babu komai Daughter, Aunty'n ki ta yi bacci ma ita." Neehal ta gyara zama ta bawa Uncle Usman labarin duk yanda suka yi da su Daddy, ta kuma faɗa masa ita bata son Auren. Uncle Usman ya sauke numfashi ya ce. "Mene abun damuwa anan Neehal? Ai wannan abun farinciki ne mu a gurinmu ba kaɗan ba, Ameen mutumin kirki ne, iyayensa ma haka kuma kin fi kowa sanin hakan." Ta ce. "Na sani Uncle, amma Yaya fa, ni dai baza iya auransa ba Allah." Uncle Usman ya yi murmushi ya ce. "Mene da Yayan?" Ta turo baki tana hawaye ta ce. "Kai ma ka san halinsa, kuma yana da mata fa." Ta ƙarashe maganar hawaye na zuba daga idonta. Uncle Usman ya yi ƴar dariya sannan ya ce. "Ina ruwanki da matarsa, zamanta daban naki daban." Ta yi shiru bata ce komai ba. Cikin serious ya cigaba da magana. "Neehal, zan faɗa miki gaskiya a matsayina na uba a gare ki, ki cire wani abu mara kyau na Ameen daga cikin zuciyarki, alkhairinsa da na iyayensa a gare ki zaki duba, ki tuna ajiye komai nasa da ya yi ya ɓata lokacinsa da energy ɗinsa dan ganin ya samo miki mafita a rayuwarki, abun da ya yi saboda ke aiki ne na siyar da rai amma duk da haka sai da ya yi duk dan saboda ya ga ya cire ki daga cikin damuwar rayuwar da kike ciki. Alkhairin iyayensa a gare ki kuma ba zai fadu ba saboda tarin yawansu, ki tuna barazana da Daddy ya fuskanta saboda ke, amma duk dan ganin bai ɓata miki rayuwa ko ya bari an ɓata miki ba ya zaɓi duk wata barazana da abun da za'ai masa, kuma duk saboda ke." Cikin tsananin mamaki ta ce. "Uncle a ina ka san wannan labarin?" Uncle Usman ya ce. "Aunty A'isha ce ta kira ni ta sanar mun tun lokacin da abun ya faru, har ma na kira Daddy da Mama na jajanta musu." Ta jinjina kai kawai. Uncle Usman ya ce. "Ki ajiye duk waɗan can abubuwan dana lissafa miki, ki duba Ameen ɗin shi karan kansa, mene ne aibunsa daza ki ƙi shi? Ɗan Adam tara yake bai cika goma ba Neehal, ki yi addu'a kawai Allah ya tabbatar muku da Alkhairi ya kau da fitina a tsakaninku, amma ta yaya ma zaki ce baza ki amince ba, ko a fuska karki bari ki nuna damuwar da za su gane bakya so, ɗansu ne fa Neehal na cikinsu, ko da basu furta ba amma baza su taɓa jin daɗi ba idan kika ƙi ɗansu, muma baza mu ji daɗi ba." Nasiha sosai Uncle Usman yay mata. Ba dan ranta ya so ba ta ce masa ta amince, zata cewa su Maman ta amince. Yay murna sosai ya dinga saka mata albarka. Sai ɗaya suka gama wayar, ta tashi ta shiga toilet ta canza pad ta dawo ta kwanta. Babu bacci ko d'igo a idonta, idan ta tuna gobe fa tana cewa Mama ta amince shikenan kamar yadda Daddy ya ce za'a fara shirye-shiryen bikinsu sai ta ji hawaye sun zob'o mata, shikenan zata zama Matar Yayanta Ameen shi kuma Mijinta? Idan ta tuna ba son ta yake ba sai ta ji hankalinta ya ƙara tashi, ko kuma idan ta tuno Hafsat da dama can ba k'aunarta take ba, ina ga ta aure mata miji? Amma duk da haka dole zata amince kamar yadda Uncle Usman ya ce mata, Mama da Daddy basu cancanci butulci daga gare ta ba. Ta sha kuka sosai kafin bacci ya ɗauke ta ba tare data sani ba.
Da safe da ta tashi idanunta jajur duk sun kumbura haka ma fuskarta saboda kukan da ta sha, ta shiga toilet ta yi wanka ta dinga dirzar fuskar saboda ta ware, bayan ta fito ta shirya harda ƴar kwalliyarta ta rambad'a kwalli duk dan kar Mama ta gane ta yi kuka. Ƙarfe takwas da ƴan mintuna ta fito ta sauka ƙasa. Ta tarar da Mama a kitchen tana haɗa breakfast. Ta tsaya a bakin ƙofa ta ce. "Barka da safiya Mama." Mama ta juyo ta ce. "Yawwa, kin tashi lafiya?" Ta ce. "Lafiya k'alau Mama." Mama ta ce. "Masha Allah." Tana bin ta da kallo. Ta kirkiro murmushi ta ce. "Bari in taya ki aikin Mama." Mama bata ce komai ba, ta ƙaraso suka ci-gaba da aikin tare. Dauriya kawai take yi amma ita kaɗai ta san halin da zuciyarta take ciki, gabanta sai faɗuwa yake saboda tunanin kar Mama ta tambaye ta abun da ta yanke akan maganar Auran Ameen. Allah ya taimake ta har suka gama aikin Mama bata ce mata ko ƙala ba. Tare suka yi breakfast da Maman, sai bayan sun gama ta tashi zata tafi Mama ta ce ta koma ta zauna. Ƙirjinta na luguden bugu ta koma ta zauna, dan ta san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi. Mama ta kalle ta na sakanni sannan cikin sanyin murya ta ce. "Kuka kika yi jiya da daddare ko Neehal?" Ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da girgiza mata kai. Mama ta ce. "Hmmm, Neehal bazan taɓa yi miki dole akan abun da ba kya so ba, haka ma Dad ɗinki, ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa, indai ba kya son Auren Ameen babu mai yi miki dole." Ta d'ago da kanta a hankali tana danne kukan da yake ƙoƙarin kufce mata ta ce. "Da gaske fa Mama ban yi kuka ko na damu ba." Mama ta ce. "Any way dai, ni dai abun da zan faɗa miki karki saka damuwa a ranki, i know You very well, kuma karki tursasawa zuciyarki karɓar abun da ba kya so, rayuwarki ce bata wani ba karki cuci kanki, ki yi abun da zuciyarki bata so." Ta yi shiru bata ce komai ba. Mama ta ce. "Yanzu zaki gidan Sadiyan ne? Har ta kira ni a waya tana kin taho, kamar aka ce mata a hanya kika kwana, ita da bata jira." Ta yi murmushi ta ce. "Auntynah kenan, she missed me that is why." Mama ta ce. "Ki je ki gaishe da Daddy sai ki tafi, make sure kin dawo gidan nan before Asr, zamu je shopping kin sani." Ta miƙe ta ce "Insha Allah." Kafin sha ɗaya ta je gidan Aunty Sadiya. Aunty Sadiya ta tarb'e ta cikin farinciki tare da tsokanar ta da wata sabon gani. Bayan sun gama gaggaisawa suna cikin hira Aunty Sadiya ta ce mata. "What going on Neehal naga kamar kina cikin damuwa?" Ta girgiza kai a hankali tana jin damuwar zuciyarta na ƙaruwa ta ce. "Babu komai Aunty." Aunty Sadiya ta ce. "Baki iya ƙarya ba Neehal, shi yasa kina yi ake gano ki, faɗa mun mene ne? Yanayin ki ya nuna cikin damuwa" Ta yi shiru k'walla na cika idanunta. Aunty Sadiya ta yi ɗan murmushi saboda ta san dawar garin, Mama ta kira su ta faɗa musu komai ita da Aunty A'isha tun jiyan. Cikin lallami ta ce. "Kin yi shiru Neehal." Ba tare data d'ago ba ta ce. "Aunty ban san me zan ce miki ba ne." Aunty Sadiya ta ce. "Abun da yake damunki zaki faɗa mun." Ta turo baki ta ce. "Daddy ne ya ce wai Yaya zan aura." Murmushi Aunty Sadiya ta yi ta ce. "Kamar ya? Wanne Yayan?" Ta ce. "Yayana fa, Aunty ki duba abun nan, ta yaya zan iya Auran Yaya?" Ta yi maganar cikin marairaicewa. "Ta yadda kowacce mace take Auran mijinta mana." Cewar Aunty Sadiya tana dariya. Ta fara hawaye ta ce. "Aunty kin san halin Yaya fa, Ni tsoron shi nake, kuma kuma.... Yana da matarshi fa." Aunty Sadiya ta ce. "Rigimammiya, wannan rigimar taki ai sai Ameen ɗin." Bata ce komai ba sai cinno baki data ƙara yi. Aunty Sadiya ta gyara zama tare da dafa ƙafaɗarta, seriously ta ce. "Neehal! Bai kamata Auran Ameen ya dame ki ba ko kuma ya saka ki cikin damuwa ba, kin san Ameen kin san komai nasa fiye da kowacce mace da zai aura a duniya, haka kema ya san komai naki. You know Ameen is a good person, ke zaki faɗi hakan ga wasu ma. To mene abun damuwa dan kin aure shi, mu kanmu sai mun fi jin daɗi da farincikin hakan, hankalinmu sai yafi kwanciya, bamu da fargabar yanda mijinki zai riƙe mana ke ko kuma fargabar wanne irin ƴan'uwan miji zaki haɗu da su. Batun matarsa kuma ba'a kanta zaki zauna ba ita ma ba'a kanki zata zauna ba, hasalima kowaccen ku gidanta daban." Ta ɓata fuska ta ce. "Ai ita yake so, ni ba ya so na." Aunty Sadiya ta danne dariyar dake ƙoƙarin k'wace mata dan ta gano mutuniyar tata har da kishi a lamarin nata ta ce. "Wa ya faɗa miki? Yana son ki mana, in ma ba ya son ki sai ki koya masa son naki, sai ka ce ba rainon Yaya Fateemah ba?" Ta juya ido ta ce. "Ai nima bana son shi." Wannan karon Aunty Sadiya kasa danne dariyarta ta yi saboda yanda Neehal ɗin ta yi maganar. Ta ɗan dara sannan ta ce. "Allah ya shirya ki Neehal." Nasiha ita ma Aunty Sadiya ta yi mata tare da ƙara nuna mata qualities ɗin Ameen, kamar dai yanda Uncle Usman ya faɗa mata jiya, a ƙarshe dai ita ma ta ce ta dage da addu'a kawai tare da neman zaɓin Allah. Wajen ƙarfe uku ta koma gida, ana yin la'asar suka fita shopping ita da Mama, sai daf da Magriba suka dawo. Bayan Magriba ɗaya daga cikin staff ɗin gidan ya zo ya cewa Mama ta yi baƙo. Ta ce masa ya je ya shigo da shi part ɗinta. Baƙon yana zaune a falon ƙasa ta sauko, mamaki gami da fara'a suka bayyana akan fuskarta ganin Alhaji ne Uban gidan Abban Neehal. Cikin murya mai cike da fara'a ta ce. "Alhaji kai ne a gidan namu yau? Sannu da zuwa." Alhaji Ali ya yi murmushi yana riƙe da sandar dake taimaka masa gurin tafiya ya ce. "Ni ne Hajiya, da fatan mun same ku lafiya?" Mama ta zauna akan carpet ta ce. "Lafiya k'alau Alhaji, da fatan an zo lafiya? Ya hanya? Ya Iyali? Ya ƙafa?" Alhaji Ali ya ce. "Alhamdulillah, komai lafiya k'alau, ƙafa gata nan sai godiyar Ubangiji, a