Showing 234001 words to 237000 words out of 262509 words
Chapter 79 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt
ɗan jima sannan ya dawo ɗauke da sabon duvet, ya lullub'a mata a jikinta sannan ya je ya rufe ƙofa ya dawo ya kashe light ya kunna bedside lamp. A hankali ya hau kan gadon ya kwanta ya shiga cikin bargon tare da janyo ta jikinsa, ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da lumshe idonsa yana ƙara cusa fuskarsa a jikinta dan sosai ƙamshin jikinta ya yi masa daɗi tare yin tasiri a gare sa. Ta motsa tare da buɗe idonta a tsorace saboda yadda ya ƙwaƙume ta a jikinsa, dama baccin ba wani nisa ya yi ba. Ta zare jikinta da sauri ƙirjinta na dokawa a million ta tashi zaune tana keɓe fuska kamar zata yi kuka. Ya ɗan ɗago yana kallon fuskarta ta cikin ɗan hasken bedside lamp, shi dariya ma ta bashi yanda ta yi da fuska kamar wadda ta ga dodo ko fatalwa saboda tsoro. Ya kama hannunta a hankali ya ce. "What happening?" A shagwabe ta ce. "Bacci fa nake ji sosai, dan Allah Yaya ka koma ɗakinka ni bazan iya bacci kana nan ba." Ya janyo ta gaba-d'aya ta faɗa jikinsa ya saka hannunsa ya matse ta, yana jin yanda jikinta yake rawa saboda tsoro. Ɗayan hannun nasa ya kai kanta ya shiga shafa gyararren gashin kanta slowly. Dai-dai kunnanta ya kai bakinsa ya ce. "Relax, babu abun da zan miki." Ta buɗe baki zata yi magana ya hana ta ta hanyar ɗora finger ɗinsa akan lips ɗinta ya ce. "Shiiiii.....Just sleep." Ta turo baki tare da lumshe idonta tana sakin ajiyar zuciya a hankali. Mamakin Ameen take ba kaɗan ba, ko kaɗan bata yi tunanin zai kalli ɗakin da take ba ma a yau a yanda yake nuna mata a baya balle har ya shigo su kwana tare, shi yasa babu fargaban hakan ko kaɗan a ranta, amma yanzu ya dasa mata fargabar, sai faman mammatse jikinta take guri ɗaya kamar wacce take kwance kan a ƙaya, a matuƙar tsorace take sai faman jan numfashi take tana saukewa. Saboda tarin gajiya da ciwon kai da baccin dake kanta cikin mintuna ƙalilan bacci ya kuma ɗauke ta ba tare data sani ba. Ajiyar zuciya ya sauke jin saukar numfashinta, ya ɗan rabata da jikinsa tare da gyara mata kwanciyarta, ta wani dunk'ule jiki kamar dafaffiyar kaza. Ya tsurawa fuskarta ido yana sakin murmushi shi kaɗai, yanda yake jin kansa a yau ba zai misaltu ba, sosai yake cikin farin ciki da nishad'i gami da annashuwa. Ya saka finger ɗinsa guda ɗaya yana zagaye lips ɗinta da shi, zabura ta yi amma bata farka ba, ya ƙara yin murmushi ganin gaba-d'ayanta a tsorace take. Imagine yanda bata jin daɗin jikinta a yanzu ya yi mata wani abu, ya san idan bata fasa masa kunne da ihunta ba to sai an jiyo kukanta a mak'wabta. Yanda take uwar raki, ko yaya ciwo yake ta yi ta kuka kenan, ina kuma ga ya yi mata abun da ya san dole sai ta ji jiki. Bai san tsawon lokacin da ya ɗauka yana kallon ta tare shafa kanta zuwa fuskarta ba cikin shauƙi, a haka dai bacci ya ɗauke shi.
Da asuba kusan makara suka yi saboda dukkan su da tarin gajiya a jikinsu. Ameen ne ya fara tashi lokacin har an shiga Sallah, ya tashe ta sannan ya shiga toilet ya yi alwala a gaggauce ya tafi masallaci. Daƙyar ta iya tashi dan ji ta yi kamar ta koma ta cigaba da baccin, dan bai ishe ta ba. Ta dai cize ta tashi ta shiga toilet ta yo alwalar ta fito ta ɗauko hijabi a cikin jakar kayanta ta zira ta tayar da Sallah. Bayan ta idar ta ɗauko wayarta a cikin hand bang ɗinta ta yi karatun Alkur'ani tare da azkar ɗin safe, Alhamdulillah ta ji sauƙin jikin nata da ciwon kan sosai. Har gari ya fara haske bai dawo daga Masallacin ba, ta miƙe ta yi locked ƙofa sannan ta kwanta ta koma baccinta. Bata jima da kwanciya ba ya dawo gidan, duk abun da ya san zata buƙata na toilet ya kwaso ya kawo mata, sannan ya cire jallabiyar jikinsa ya hau kan gadon ya jawo ta jikinsa suka cigaba da baccin tare. Wannan karon ta riga shi tashi. Ta buɗe idonta a hankali ta sauke su akan kyakkyawar fuskarsa, baccinsa yake yi hankali kwance. Ta zame jikinta daga nasa a hankali ta tashi zaune, a lokacin ta gane babu riga a jikinsa, ta ƙurawa faffaɗan ƙirjinsa dake ɗauke da farar fata da kwantaccen ƙananun gashi ido. Sai ta ji kamar ta kai hannu ta shafa su amma sai ta kasa. Jin ta take kamar a mafarki, wai yau ita ce kwance gado ɗaya da yayanta akan ƙirjinsa? Abun har yanzu bai daina bata mamaki ba. Ta yunkura da nufin ta sauka ta ji ya riƙo ta, ta kalli fuskarsa da sauri ta ga still idanunsa a rufe suke. Ta yi ƙoƙarin k'wace jikinta ya buɗe idanunsa dake lumshe saboda bacci ya ce. "Where are you going?" Ta yi ƙasa da kanta cikin kunya a ranta tana addu'ar Allah yasa bai san ta tsaya kallon shi ba. A hankali ta ce. "Toilet." Ya jawo ta jikinsa ya ce. "Me zaki yi?" Ta yi shiru tana rarraba ido cikin tsoro kamar ace kyat ta ruga da gudu. Ya shafi saman idonta ya ce. "Matsoraciya." Sannan ya sake ta. Ta ɓata fuska tare da sakin ajiyar zuciya ta sauka daga gadon. Tana mitar abubuwan da yake mata a ranta, fargaba fal a cikin ranta na kar abun ya wuce haka. Sai ta fara tambayar kanta 'anya kuwa Yayanta data sani a da shine na yanzu? Wannan kamar ba Yayanta ba an canza mata wani' ga abubuwan da yake mata ko kunya ba ya ji, ko dama haka mazan suke ba su da kunya ne? Ta yi mamakin ganin sabon toothpaste da brush da robar jower jel da takarcen sabulan wanke toilet na ruwa, sai kuma sabbun towels guda biyu an yi hanging ɗin su a cikin toilet ɗin. Brush kawai ta yi ta fito, tana son yin wanka amma bata san a yaya zata iya fitowa idan ta yi wankan yana ɗakin ba, sai kawai ta yi fitsari ta wanke toilet ɗin duk da babu dattin komai a cikinsa ta fito. Ta tarar baya ɗakin ya fita sai mayen ƙamshinsa mai kama guri, gaba-d'aya ya gama ɗakin. Cikin murna ta koma cikin toilet ɗin ta yi wanka tana addu'ar Allah kar ya dawo da shi ɗakin har sai ta gama shiryawa. Adduarta ta karɓu kuwa, har ta gama ta fito ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa bai dawo ba, tana cikin d'aura ɗankwali ya shigo ɗakin da sallama, ta amsa masa ba tare da ta juya ta kalle shi ba. Ya tsaya a kanta yana kallon ta har ta ƙarasa ɗaurin nata. Cikin sanyin murya ta ce "Ina kwana?" Bai amsa ba sai tsugunnawa da ya yi a gabanta tare da lek'a fuskarta ya ce. "Kwalliyar ce ba'a son in gani ake boye mun?" Ta rufe fuskarta da hannunta zuciyarta ta fara bugun da take yi mata a duk lokacin da suka yi over close. Ya cire hannun nata ya matsar da fuskarsa daf da tata ya ce. "Wai wannan wacce irin kunya ce da ta ƙi ƙarewa? Ko sai na yi maganinta ne?" Ta shagwab'e fuska tare da turo baki gaba. Ya ƙurawa lips ɗin nata ido, a hankali kuma ya ɗora nasa soft lips ɗin akan nata, bata yi aune ba ta ji ya haɗe bakunansu guri guda ya shiga bata hot kiss. Abun ya zo mata a bazata hakan yasa lokaci ɗaya jikinta ya d'auki rawa, gaba-d'aya ta ƙara firgicewa da al'amarin sa, amma duk da haka sai da sak'onsa ya ratsa dukkan jikinta, ta dinga jin wani irin abu tun daga kanta har tafin ƙafarta yana yawo a cikin jininta. Yanda yake kissing ɗin nata kamar zai cinye mata baki shi yake ƙara tsorata ta, ta yi ƙoƙarin k'wace kanta amma ta kasa, ƙara jawo ta jikinsa ma ya yi alamun ba shi da niyyar bari. Ƙarar knocking ƙofar parlour ce tasa ya sake ta a hankali yana sauke numfashi gami da ajiyar zuciya. Runtse idonta ta yi tana jin kamar ƙasa ta tsage ta shige dan kunya, ita kam ta ga ta kanta Ameen zai kashe ta da wannan abubuwan da yake mata. A kasalance ya tashi ya fita daga ɗakin idanunsa har sun fara sauya kala. Ta buɗe idonta a hankali tana jin lips ɗinta kamar har yanzu suna cikin bakinsa, ta kai hannu ta shafa lips ɗin nata tare da lumshe idonta, tana jin jikinta kamar ba nata ba.
A hankali ta tashi ta ɗauko wayarta ta duba time, ƙarfe goma sha ɗaya saura na safe ta gani. Gyaran ɗakin ta shiga yi bayan ta gama ta fita da niyyar gyara falo suka ci karo da Ameen. Ya kama hannunta ya ce. "Mu je mu yi breakfast Mamanki ta kawo mana abinci." Ta yi ƙasa da kanta kewar Mama na ƙara cika mata zuciya, cikin sanyin murya ta ce. "Waya kawo breakfast ɗin?" Ya shafi kuncinta ya ce. "One of our soldiers staff." Bata kuma magana ba ya ja hannunta suka ƙarasa tsakiyar falon inda abincin yake akan Centre Carpet. Har ya d'auko plates da cups da spoons da kayan tea duk ya ajiye a gurin, tana mamakin yanda yake ɗauko mata duk abun da ya san zata buƙata in time tun kafin ta yi yunk'urin ɗaukowar, Shi da a gida komai sai dai a ɗauko masa yana daga zaune. A ranta ta ce. 'Ko Matarsa yakewa hakan shi yasa itama yake mata.' Haka kawai ta ji gabanta ya fadi tunowa da ta yi da Hafsat..........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*
_*By*_
_*Zeey Kumurya*_
*8️⃣3️⃣*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
.........Saurin yin ƙasa da kanta ta yi daga kallon sa tare da amsa masa sallamarsa. Ya ajiye ledodin hannunsa a gaban gadon sannan ya zauna a kusa da ita. Ba tare data kalle shi ba ta ce. "Sannu da zuwa." Ya amsa mata a can ƙasan mak'oshi, sannan cikin kulawa ya ce. "Kin ci abinci?" Ta ce. "Eh." Ya ce. "Na dare fa nake nufi bana rana ba." Ta girgiza masa kai alamar a'a. Ya ce. "Okay sakko mu ci wannan." Ya yi maganar yana nuna ledodin gabansu. Ta ce. "Akwai sauran abincin da Mama ta kawo fa." Ya ce. "Mu je ki bani na kaiwa mai gadi sai mu ci wannan ɗin." Ta miƙe ba tare da ta yi magana ba ya bi bayanta. Abincin duka ta juye masa sannan ta ɗauko plates da cup da spoon kamar yadda ta ga ya yi jiya. Sai a lokacin ta tuna data tashi yau da safe ba ta ga ragowar kazar jiya ba. Ta kai kayan ɗakinta ta zauna jiransa, mintuna kaɗan ya dawo, ya zauna a ƙasan gado ya janyo ledar kazar ya ce. "Me kike jira baki fara ci ba?" Ta nuna masa kansa da hannunta, tana ƙoƙarin sarving ɗinsu ya katse ta da faɗin. "I forgot something." Ta kalle shi da alamun tambaya, ya ce. "Je ki yi alwala." Ta ce. "Na yi Sallah fa." Ya ce. "Wata zamu sake." Ba tare da tunanin komai ba ta je ta yo alwalar, kafin ta fito har ya shimfid'a musu darduma. Ya miƙe bayan ta saka hijabinta ya ja su suka yi Sallah raka'a biyu, ya dad'e yana yi musu addu'ar zaman lafiya da wanzuwar farin ciki a rayuwar auransu a cikin sujjadarsu ta ƙarshe. Bayan sun idar ya kama kanta ya yi mata addu'a kamar yadda ma'aiki (S. A. W) ya koyar da mu ga sabbun ma'aurata, sannan ya umarce ta data yi masa shi ma kamar yadda ya yi mata. Bata yi musu ba ta yi masan, ya ce su je su ci kazar. Tare suka ci amma wannan karon bai bata a baki ba, ko taɓa ta bai yi ba bai nuna alamar ma zai yi hakan ba, hakan yasa ta ji daɗi amma duk da haka a takure take jin ta, masifar tsoron da take ji a ɗazu ne dai ya ɗan ragu tun da ta ga bai yi mata komai ba tunda ya shigo ɗakin. Bayan sun gama tana tattare kayan ta ce. "Jiya ya ka yi da ragowar kazar nan?" Ya ce. "Tun a daren na kaiwa mai gadi." Ta gyaɗa masa kai sannan ta fice da kayan. Sai da ta dauraye su sannan ta komo ɗaki, ta tarar ya fita baya ɗakin. Ajiyar zuciya ta saki ta jin daɗi sannan ta rufe ƙofar ɗakin, toilet ta shiga ta yi ƴan uzurarrikanta, ta fito ta cire kayan jikinta ta saka wani riga da wando masu taushi na bacci, ta mitsitsika humra a jikinta kamar yadda mai gyaran jikin da ta yi mata ta ce tana yi duk dare sannan ta kashe light ɗin ɗakin ta kwanta ba tare da ta kunna bedside lamp ba. Bacci take ji sosai, ta bararraje akan gado tana murna a ranta zata yi baccinta cikin kwanciyar hankali babu fargaba da tsoron komai a ranta. Sai dai ko 5 minutes ba ta yi da kwanciyar ba ya turo ƙofa ya shigo, a lokacin bacci ya ɗan fara ɗaukar ta. Ta buɗe idonta a hankali gabanta na fad'uwa. Kunna torchlight ɗin wayarsa ya yi ganin ɗakin da duhu, ta yi saurin runtse idonta tana addu'ar Allah yasa idan ya ga bacci take ya k'yale ya koma ɗakinsa. Shi kam dama abun da yake so kenan, so yake ta saki jikinta sai ta sakankance sai ya dawo ɗakin. Ya ɗan tsaya yana haska ta sannan ya hau kan gadon ya yaye bargon data rufe jikinta da shi. Tana jin shi ta ƙi motsawa duk dan ya yi tunanin bacci take. Ya haske fuskarta yana murmushi cikin sanyin murya ya ce. "I know you are not sleeping." Ta buɗe idonta kaɗan tana kare fuskarta da hannunta bata ce komai ba. Ya matsar da wayar daga saitin fuskarta sannan ya matsa jikinta ya saka hannunsa akan lallausan gashinta ya fara shafawa a hankali. Ta sauke ajiyar zuciya a hankali tare da lumshe ido saboda yanda ƙamshinsa yake ratsa k'ofofin hancinta, a shagwab'e ta ce. "Yaya I want to sleep." Ya ajiye wayar hannunsa sannan ya ɗauki kanta ya ɗora akan cinyarsa, cikin wata irin murya da idan da za'a ce mata Yayan nata yana da ita baza ta yarda ba ya ce. "Ni kuma tunanin ki da san kasancewa dake ya hana ni bacci *Baby love*." Saboda tsananin mamaki bata san lokacin data buɗe idonta cikin sauri ta kalle shi ba, dan tabbatar da abun da ta ji ba kunnenta ne ya jiye mata ba dai-dai ba. Ya ja kumatunta tare da kashe mata ido ya ce. "It's so amazing ba?" Ta yi shiru kawai tana kallon shi. Ya yi murmushi, sannan ya rank'wafar da fuskarsa daf da ta_ta, cikin murya mai kama da rada ya ce. "Na san zaki yi mamaki idan na ce miki am in love with you tun lokacin da ban san menene so ba, ban ma san me kalmar son take nufi ba, lokacin kina only 5 years a duniya da muka zo gidanku da Mama kika zo kina mun ihu a cikin kunnena. Tun ranar tunanin ki yake manne a cikin raina, da shi nake kwana nake tashi. Sometimes sai in zauna ni kaɗai idanuna a lumshe ina hango ki a cikin raina kina yiwa Aunty shagwab'a ko kuma kina surutunki ko kuka da tsalle_tsallenki, sai in ji ina son na kuma ganinki, a lokacin ban gane ma'anar hakan ba sai daga baya na fahimta. Duk yanda zan miki bayanin yanda soyayyiyar ki ta azabtar dani baza ki gane ba Miemerh, amma dai na sha wahala. Bayan Allah ya yiwa su Abba rasuwa kin dawo hannunsu Mum da zama bazan iya kwatanta miki farin cikin da na ji ba a wannan lokacin, na tabbata ko Mum bata kai ni farin ciki da hakan ba, tunda ko ba komai idan na zo gida duk weekend zan gan ki in ji daɗi a raina. Dalilin da yasa ban bayyana miki soyayyata a gare ki ba a lokacin da ya dace, da na yiwa Daddy maganar ina sonki sai ya nuna mun in bar maganar dan bazai bani ke ba, ban kuma san dalilinsa na faɗar hakan ba har yau. Na haqura da maganar ko Mum ban faɗawa ba, ba kuma wai dan na daina son ki ba ne, ko kaɗan soyayyar ki bata ragu ba a cikin zuciyata sai ma ƙaruwa da take yi, saboda in yiwa Dad biyayya ne kawai na haqura." Ya yi shiru na wasu sakanni yana goga mata sajen fuskarsa a kuncinta sannan ya cigaba da magana. "FATEEMAH....! I LOVE YOU WITH ALL MY HEART, I LOVE YOU MORE THAN WORD CAN EXPLAIN, I LOVE YOU MORE AND MORE NEEHAL." Ta lumshe idonta tana jin ta kamar a cikin gajimare saboda wani irin shauk'i from no where da yake mamaye dukkan zuciyarta, an sha faɗa mata kalaman soyayya babu adadi a rayuwarta, an furta kalmar *i love You* babu adadi, amma bata taɓa jin waɗanda