Showing 228001 words to 231000 words out of 262509 words

Chapter 77 - NEEHAL Book Complete 1 To end by Zeey Kumurya.txt

Advertisement

20 Jan 2025

21388

wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._












..........A safiyar ranar Hafsat tana zaune a ɗakinta na gidansu abun duniya duk ya ishe ta, tunda ta zo gidan bata da aiki sai kuka, duk ta rame ta lalace ko abinci sai uwar ta yi yaƙi da ita take tsakura ta ɗan ci. Tana son Ameen kuma baza ta so su rabu ba, amma kuma baza ta iya jure kallon sa da wata macen ba. Gashi kuma Mom ta k'wace duk wayoyinta wai saboda kar ta kira Ameen ta zubar musu da kima a wajensa dan ta san halinta, shi kuma ya ƙi kiran ta balle ya zo, gashi Dad ɗinta baya nan yana London. Abin da yake ƙara d'aga mata hankali idan ta tuna Ameen yana can yana shirin bikinsa da wata ita ya banzatar da ita, ita yanzu burinta ɗaya a duniya ta san wa Ameen zai aura, ta ga me matar ta fita da yasa Ameen ɗin zai aure ta, ƴar waye a ina kuma take? Kamar amsar tambayarta ta ji an turo ƙofar ɗakin, ta d'aga kanta da sauri tana share hawayen fuskarta. Wata ƙawarta ce mai suna Jalilah ta shigo Mom na biye da ita a baya. Ba tare da ƙawarta_ta ta damu da yanayin da ta gan ta a ciki ba ta ce. "Hafsy wannan ba mijinki ba ne Ameen?" Tana miƙa mata wayar hannunta ta yi maganar. Hafsah ta karɓa tare da ƙurawa screen ɗin wayar ido. Katin d'aurin Auren Ameen da Neehal ne irin wanda ake yi a yanzu a waya a saka wak'a, amma ita ba wannan ne damuwarta ba, sunan wadda ta gani a matsayin amaryar shi yasa zuciyarta bugawa da ƙarfi. FATEEMAH MUHAMMAD TAFIDA (NEEHAL). Ta murza idonta a tunaninta idon ne ya ganar mata ba dai-dai ba, amma still dai abun da ta gani shi ta ƙara gani. Wata uwar ƙara ta saki tare da sakin wayar, Jalilah ta yi saurin tare abarta cikin tsoron kar ta faɗi ta fashe. Hafsat ta miƙe tsaye jikinta na bari cikin tashin hankali ta ce. "Mom, kin ga abun da na gani kuwa? Neehal Ameen zai aura, yarinyar da Mamansa take riƙo." Mom ta ce. "Na gani nima Daughter, auran cin amana zai yi." Cikin ƙaraji Hafsat ta ce. "Ameen why? Me na yi maka? Ka rasa dawa zaka haɗa ni kishi sai da wannan aljanar yarinyar, yarinyar dana tsana." Sai ta fashe da kuka ta ce. "Munafuki, komai ya ce Neehal Neehal ashe son ta yake yi, yarinyar ta ƙi auruwa shine shi zai aure ta, in ma wani mugun abun ne da ita ya shafe mu kenan? (Hafsah bata san me ya faru ba akan case ɗin Daddy da Neehal, da yake an ɓoye abun ne babu wanda ya ji sai wanda ƴan'uwa na jiki.) Jalilah ta ce. "Na daɗe da ganin wannan videon tun last week, ina ta kiran wayarki bata shiga, a online ma bana ganin ki kwata_kwata. Shine na ce bari dai na je gidanki na tabbatar da gaske mijin naki ne zai yi aure, na je kuma na tarar bakya nan sai masu aiki, suka ce mun kina gida." Hafsah ta haɗa kanta da jikin wardrobe tana kuka sosai, tashin hankalinta ya ninku akan na da, Neehal fa, yarinyar data tsana a duniya tun kafin ta gan ta, ita Ameen zai aura, ashe dama son ta yake? Ko kuma ta ce soyayya suke? Da ƙyar Mom da Jalilah suka rarrashe ta. Mom ta kira ƙanwarta Safiya suka haɗu suka zauna suna zagin Ameen da Neehal har Mama ba su ƙyale ba suka dinga cewa ita ce munafuka ita ta haɗa komai. Aunty Safiya ta kwantarwa da Hafsat hankali ta ce ta bar komai a hannunta, ta yi mata alƙawarin Ameen sai ya zo har inda take yana kuka da idonsa tare da begging ɗinta, wannan aure da zai yi kuma sunansa matacce.












Da daddare Neehal tana zaune a cikin ƴan'mata suna ta tsokanarta, wannan ta ce mata daga jibi shikenan zata shiga daga ciki. Su Haneefah ne sakaran sharri, harda cewa yanda ta sha gyaran jikin nan ta yi kyau Allah yasa kar ta zautar musu da Yaya. Ita dai idanunta a lumshe tana tunanin abun da ya dame ta bata su take ba. Damuwarta yanda rayuwar Auranta zata kasance, tana yawan jin ana cewa kowanne Aure yana da tasa matsalar da kuma k'alubale, to ita ko wacce matsalar zata je ta tarar sai Allah? Ta sauke numfashi tana tuna yanayin mijin da zata aura da yanda Auran nasu ya kasance, zuciyarta ta kasa hasaso mata yanda rayuwar auren nasu zata kasance, ga kuma wani ƙarin matsalar kishiya, ta riga ta san Hafsat bata son ta tun a da ballantana kuma yanzu. Ta sauke ajiyar zuciya tana jin zuciyarta babu daɗi ga tarin fargaba a cikinta. Muryar Aunty A'isha ta ji a kanta tana kiran sunanta. Ta buɗe ido tare da amsawa. Aunty ta ce. "Tunanin me kike yi haka inata magana baki ji ba? Ga hayaniya ta cika ɗakin amma ke baki ma san ana yi ba." Cikin sanyin murya ta ce. "Babu komai Aunty." Aunty ta ce. "Koma da akwai ki yi addu'a, addu'a makamin mumuni ce, ba wai ki zauna ki yi ta tunani ba." Ta ce. "Insha Allah Aunty." Aunty ta ce. "Yawwa, tashi mu je part ɗin Daddy Umma na son ganin ki." Ta miƙe ba tare da yi magana ba suka fice. A falo suka yi kicibus da Hajiya, ta dubi Neehal ta ce. "Ke wai ya kike abu da sanyin jiki ne kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki? Ko baki da lafiya ne?" Neehal ta turo baki bata ce komai ba. Aunty ta yi murmushi ta ce. "Mood ɗin amarci ne kawai." Hajiya ta ce. "Mudun amarcin me? Ki zage jiki ki dinga abu cikin kazar_kazar da annashuwa mana, kin wani cukele fuska kamar waccan uwar taki Saratu da bata k'aunar fara'a. Wai ina Aminun ne? Tunda na zo ban gan shi ba, ko ɗan zancen nan ma shi ba ya zuwa ne?" Aunty ta yi murmushi ta ce. "Hajiya gida fal da baƙi ina zaki gan shi?" Hajiya ta tab'e baki ta ce. "Bai ga damar zuwan ba ne, amma Aminu ai ba wata kunya ya cika ba." Aunty ta kama hannun Neehal suka yi gaba. Umma kaɗai suka tarar a Extra room ɗin dake part ɗin Abba. Neehal ta zauna a ƙasan gado Aunty ta juya ta fita. Faɗa da nasiha sosai Umma ta yiwa Neehal akan zamantakewar aure, ta nusar da ita abubuwan da ba'a so a zaman aure da kuma wanda ake so, ta nuna mata mahimmancin tsafta, addu'a, iya sarrafa girki, ladabi da biyayya da iya kula da miji a rayuwar aure. Sai kuma uwa uba haquri, wanda mutane da dama tun kafin Umman suke ta faɗa mata aure ɗan haquri ne, sai ta yi haquri. Mama ma ta zo ta ɗora mata da nata faɗan. Washegari aka yi Kamu kamar yadda su Aunty Sadiya suka shirya, a harabar gidan Maman aka yi decoration mai kyau na gurin zaman amarya, aka jera fararen kujerun roba na zaman baƙi. K'wararrun masu kiɗan ƙwarya suka zo suka buga kiɗa manyan mata suka cashe, an ci an sha an yi bidiri, kuɗi kamar tsinto shi ake yanda family da k'awayen Mama suka dinga zuba lik'i, Mama ta yi kyau sosai, ta sha kiɗan uwar amarya uwar ango a gurin masu kiɗan ƙwarya. Neehal ma ta yi kyau sosai ta sha make up, tsoffi suka feshe ta da turaruka aka kamata (Kamun amarya). Gidan ya cika ya yi mak'il da jama'a. Amarya dai dauriya kawai take amma k'iris take jira ta fashe da kuka, halin da zuciyarta take ciki ba zai misaltu ba, ita kaɗai ta san me take ji. Ga jama'a sun hana ta sakat da ɗaukar hotuna.














Bayan Sallar isha'i Mama suna falon Daddy ita da su Aunty, cikin ɓacin rai da takaici ta dube su ta ce. "Wai ashe Hafsah bata gidan Ameen ta yi yaji?" Aunty A'isha ta ce. "Yaji kuma kamar ya?" Mama ta ce. "D'azu Doctor Rahina wadda muka yi aiki da ita a asibiti take faɗa mun, ashe ƙanwarta ƙawar ƙanwar mahaifiyar Hafsat ɗin ce." Aunty Sadiya ta ce. "To akan me ta yi yajin? Ko dan zai ƙara Aure ne?" Mama ta ce. "Hmm, ina zan sani, amma Ameen bai taɓa faɗa mun, a yanda Rahinan take faɗa mun zata yi sati uku fa a gida." Aunty Sadiya ta ce. "Subhallahi, wannan abu bai yi daɗi ba, amma bari na kira Ameen ɗin na ji asalin maganar." Ta kira shi bai d'aga ba. Mama ta ce. "Gaskiya Ameen bai kyauta mun ba, akan me zai bar yarinya ta daɗe a gida haka? Shi yasa shekaran jiya da nake tambayar sa zata yi taro ya ce mun ta ce baza ta yi ba, ashe yasan tsiyar da ya shuka kenan." Aunty A'isha ta ce. "Baki san me ta yi masa ba Yaya, kar ki ga laifinsa." Mama ta ce. "Koma me ta yi masa dai ai haquri ake tunda a da bata taɓa yi masa ba, yanzun ma da dalili ai, duk matar da za'a yi mata kishiya ai sai an yi haquri da ita." Ta miƙe tana faɗin. "Zai zo ya same ni ne." Ta shiga ɗakin Daddy ta tarar da Neehal ta zubawa hannunta da ya sha ƙunshi ido tana kalla. A zahiri zaka yi tunanin hannun take kallo, amma a badini tunani take, tunani take daga gobe fa shikenan ta zama matar Ameen, wataƙila ma i yanzu an kaita gidansa. Mama ta ce. "Kina nan ashe inata neman ki ki ci abinci." Ta sauke numfashi tare yin ƙasa da kanta hawaye ya zubo daga idonta. Mama ta ce. "Kukan ne dai Neehal? Allah ya nuna mun ranar da zaki daina wannan kukan naki." Kamar zuga ta Maman ta yi sai hawaye sharr kamar an buɗe fanfo. Mama ta ƙarasa ta zauna a gefenta tare da janyo ta jikinta ta ce. "To ya isa haka kukan, ki yi shiru kar kanki ya yi ciwo." Maimakon ta yi shirun sai ta ƙara fashewa da kuka tana shigewa jikin Maman. Mama ta shiga bubbuga bayanta cikin danne zuciyarta, dan itama idan ta tuno few days idan ta tashi baza ta ga gilmawarta a gidan ba sai ta ji babu daɗi a ranta. Ganin ta ƙi yin shiru ta d'ago fuskarta ta ce. "Haba Neehal ki yi shiru haka mana, ko a akwai wani abun da yake damunki?" Ta girgiza kai cikin kuka ta ce. "Ni bana son barin ki Mama." Mama ta ce. "Oh Neehal rigima, sau nawa zan faɗa miki dan kin yi aure hakan ba yana nufin kin barni ba ne, kuma ai haka rayuwar take tunda aure ya zama dole, kowa da haka yake sabawa, ki yi haquri kin ji." Ta ƙarashe zancen tana share mata hawaye. Mama ta ce. "Ina nan ina murna na kusa samun ƴan jikoki daga gurin autata, ita kuma tana damun kanta." Neehal ta rufe fuskarta da hannunta tare da juyawa Mama baya. Mama ta yi murmushi ta miƙe ta kama hannunta ta ce. "Mu je ki ci abinci, na san baki ci ba."........ Yau kam bacci rabi da rabi Neehal ta yi, ƙarshe ma sai tashi ta yi ta ɗauro alwala ta shiga yin nafilfili tana roƙon Allah ya kawo musu komai cikin sauƙi a rayuwar Auransu.










Washegari ranar D'aurin Aure, gida ya ƙara ɗinkewa da jama'a maza da mata. Sai ƙarfe biyu za'a d'aura auren a babban masallacin juma'a na unguwar. Da safe su Ummi suka zo harda matar Ahmad Khadijah da Ahmad ɗin. Neehal bata taɓa tunanin shi kanshi zai zo ba balle matarsa, Khadijan kuwa mai kirki da faran_faran ba ruwanta ta shiga cikin su Haneefah ana ta hira da ita. Batul ƙanwar Sadik ma wajen sha biyu na rana ta zo, ta ce su Maamah ma suna hanya. Sai da Neehal ta gan ta sannan ta tuna da kuɗin da Sadik ya turo mata ta account a matsayin gudunmawa ta manta bata faɗawa Mama ba, sai a lokacin ta faɗa mata, Mama ta ce zata kira shi bayan biki ta yi masa godiya. Tsoro da fargabar Neehal yau ya fi na kullum, dan da mutum zai yi close da ita sosai zai iya jin yanda zuciyarta take bugawa da sauri da sauri. Ta dai daure tunda garin Allah ya waye yau bata yi kuka ba, amma ta kasa cin komai dak'yar ta iya shan ruwan tea kaɗan. Ita da Haneefah da wata Freind ɗinta Zee suka je aka yi mata make up. Ta yi kyau sosai ta fito tsaf a amaryata sai baza k'amshi take. Ƙarfe biyu na rana kamar yadda aka tsara Ubangiji ya nufa aka ɗaura Auren AL'AMEEN MUHAMMAD TAFIDA da FATEEMAH MUHAMMAD GABASAWA. A lokacin Neehal ba su jima da dawowa daga gurin kwalliya ba, ta ji Aunty Sadiya tana an ɗaura, yanzu Uncle Ahmad ya kira ta ya faɗa mata. Bugun zuciyarta ne ya ƙaru ta ji ta a cikin wani irin yanayi da bazai misaltu ba, shikenan ta zama matar Aure matar Ameen. Ta lumshe idonta tana sauraren yanda zuciyarta take bugawa. "Finally an ɗaura, yarinya ta zama matar Aure..." Ta ji muryar Haneefah cikin dariya a kanta tana faɗar haka. Duk yanda taso mayar da hawayen idonta kasawa ta yi sai da suka zubo.








Wajen ƙarfe uku na rana suna part ɗin Ameen na gidan da yake anan ƴan'mata da k'awayen Amarya suka tare tunda aka fara bikin. Afrah ta zo da murnarta ta ɗane jikin Neehal da fara'arta ta ce. "Aunty Uncle ya zo, ya yi kyau sosai." Amrah ta ce. "Aunty wai shine Ango ke kuma Amarya?" Wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarci Neehal, ta san yanzu za'a ce ta zo su je a yi musu hoto tare da shi, ita kuma gaskiya bata san da idon da zata kalle shi a matsayin Mijinta ba, wani irin feeling na daman take ji a kansa, kunyarsa da tsoronsa sun ƙara cika zuciyarta. Ta janye Afrah daga jikinta da sauri ta miƙe ta shige toilet duk da bata da abun yi a toilet ɗin. Tana ji Aunty Sadiya ta shigo tana neman ta amma ta ƙi fitowa har ta gaji ta fice. Mutun sama da biyar sun shigo neman ta sai a ce musu tana toilet, ita kuma ta ƙi fitowa dan ta san dalilin kiran nata, sai haqura aka yi aka ƙyale ta. Aka cigaba da shagalin biki cikin nishad'i da farin ciki. Hada_hadar mutane yasa Neehal ta ɗan saki ranta, dan da biki ya yi biki ko lokacin Kaɗaita bata samu ba, daga a gaisa da wannan sai a gaisa da wancan. Ga k'awayenta da ƴan gurin aikinsu sun zo mata sosai. Sai can yamma da Aunty A'isha ta zo ta jata part ɗin Daddy zata yi wanka a kaita gidanta ta fara kuka sosai, tana kukan ta yi wanka aka taimaka mata ta shirya. Zuwa lokacin har an fara ɗibar mutane ƴan kai Amarya. Ta zauna a gefen gadon Daddy tana ta kuka a cikin mayafi. Daddy ne da kansa zai kai ta gidanta, ya shigo ya tarar da ita tana kuka su Aunty suna aikin ban baki da ƙara yi mata ƴan nasihohi. Mama kuwa dama ko ɗakin bata tunkara ba, dan ta san idan Neehal ta gan ta kukan da zata yi sai Allah. Shi ma Daddy zama ya yi ya ƙara ɗora mata da nasiha akan zaman aure. Sai bayan ya gama yi mata faɗan za'a fita da ita Mama ta shigo ɗakin. Neehal ta tashi da sauri ta rungume ta tare da ƙara volume ɗin kukanta, duk dauriyar Mama sai da zuciyarta ta karye ta yi hawaye. Da ƙyar Daddy ya janye Neehal daga jikinta ya kama hannunta suka fice tana gunjin kuka.








Gidan Neehal babu nisa sosai, anan cikin Nasarawan ne unguwar badawa. Kafin a ƙarasa da ita wasu har sun fara dawowa. Har ɗakinta har kan gadonta Daddy ya kai ta bayan ya ce ta shiga da ƙafar dama tare da yin Bismillah. Gidanta ya yi kyau ya tsaru sosai, madaidaici ne ba ƙato sosai ba, amma an ƙawata shi da kayan ado da alatu dan har ya fi gidan Hafsat kyau da tsaruwa. Mama da Daddy kuma sun zuba mata kaya na alfarma, kowa sai Masha Allah da sam barka yake. Daddy ya kama hannunta a cikin nasa ya shiga yi musu addu'ar fatan Alkhairi da zaman lafiya a zaman auransu. Mutanen ɗakin na amsawa da Ameen, abun gwanin burgewa. Bayan ya gama ya ɗan bubbuga bayanta ya ce. "Kukan ya isa haka Daughter, ki yi haquri kin ji." Ta zame daga kan gadon ta durk'usa a ƙasa ta rungume ƙafafunsa tana kuka sosai ta ce. "Na gode, na gode, na gode sosai Daddy, Allah ya biya ku da Aljannah maɗaukakiya, Allah ya saka muku da Alkhairi kai da Mama, bani da bakin godiya a gare ku." Cikin karayar zuci Daddy ya ce. "Amin Daughter, Allah ya sanya miki albarka ya baki ƴaƴa masu albarka." Ya ƙarashe zancen tare da d'ago ta ya mayar da ita kan gadon ya zaunar. Ta riƙe hannunshi gam tana hawaye, da ƙyar ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login