Showing 27001 words to 30000 words out of 154131 words
Chapter 10 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
nema, Gimbiya. Kwarjininki ne ya tafi da ni.”
Zayana ta ja tsaki, ta yi murmushin mugunta..
“Kwarjini ko tsoro? Ki sani, idan na sake ganin idonki a nawa ba tare da izini ba, to ranar za ki daina ganin hasken rana. Ɓace min da gani!”
Ladi da gudu tana karkarwa tabar wurin, Zayana kuma ta ci gaba da tafiya tana gyara yatsun hannunta, zuciyarta tana wasi-wasi kan dakarun Pavilion dake tsaye a waje..
A can cikin fadar, Sarki Nourdeen yana zaune a kan kujerarsa, gumi na keto masa. Ganin yadda rundunar Pavilion ta cika harabar fadar ya fahimci cewa idan ya bari Chief Onyx ya tako ƙafarsa zuwa Alhamra, to mulkinsa da mutuncinsa za su iya girgiza..
Cikin sauri ya ƙira babban sakatarensa, ya umurce shi da ya ɗauki alkalami da takarda..
"Rubuta masa saƙo yanzu," Sarki ya faɗa cikin murya mai nauyi.
" *Ka ce masa*.. Ba sai ka zo ba. Ni da kaina zan zo har inda kake."..
Sarki ya yi hakan ne domin kiyaye kansa. Ya san cewa idan Chief Onyx ya shigo fadar, sirrin dake tsakaninsu zai iya bayyana a idon gimbiyoyi da talakawan gari. Ya fi so ya tafi can yankin Pavilion ya fuskanci kaddararsa shi kaɗai, maimakon ya jawo bala'i cikin gidansa..
Duk da cewa zuciyarta ta ɗan buga ganin zafafan makaman da suke riƙe da su, sai ta dake. Ta ƙura wa babban jami'in dake jagorantarsu ido, wani gardi mai ƙaton jiki, sanye da baƙaƙen kaya da gilashi.
Jami'in Pavilion ya ɗago kai ya kalli Zayana. Ko kifta ido bai yi ba, kuma bai nuna alamun rurrusunawa ga matsayinta na Gimbiya ba. Wannan rashin girmamawa ya kusa sa Zayana ta fusata, amma kwarjinin da dakarun suke da shi ya sa ta haɗiye fushin. Ta lura cewa kowace mota tana ɗauke da tambarin Pavilion Kingdom, tambarin da take gani a matsayin kalubale ga mulkin mahaifinta..
"Ina yake?" Zayana ta furta a fili, muryarta na ratsa sanyin iskar wurin. Tana nufin Sarkin Pavilion.
Babban jami'in bai amsa ba...domin ko kallo bai isheta ba.
Sarki ya fito da kansa har bakin fadar, ya miƙa wasiƙar ga jami'in Pavilion dake jagorantar rundunar.. Jami'in ya karɓi wasiƙar ba tare da ya rurrusuna ba, ya buɗe ta ya karanta.
Zayana tana gefe guda tana kallon wannan dambarwar, tana mamakin me ya sa mahaifinta yake ƙasƙantar da kansa haka. Jami'in Pavilion ya jinjina kai, ya yi wa mutanensa nuni da hannu. Lokaci guda suka buɗe motocin su suka shiga, hayaƙin dake tashi ta rufe sararin samaniya yayin da suka fara ficewa daga fadar...
Zayana ta tsaya tana kallon yadda suka fara fita daga fadar cikin tsari da iko. Zuciyarta ta cigaba da wasi-wasi...
"Waye wannan Sarkin Pavilion ɗin? Me yasa kowa ke tsoronsa? Kuma me yasa kamanin mutanensa suke nuna cewa sun fi mu komai?"
Ta ƙaraso kusa da mahaifinta, tana kallon bayan motocinsu dake ɓacewa..
"Daddy, me ya sa za ka ce za ka je wurinsa? Shi wane ne da har zai sa ka bar masarautarka ka nufi tashi? Shin Alhamra ta zama ƙarƙashin ikon Pavilion ne ba tare da mun sani ba?"
Sarki Nourdeen bai ko kalle ta ba, ya juya cikin fada yana cewa, "Akwai abubuwan da kika fi ƙarfin sani Zayana..."
Bayan motocinsu sun ɓace wa gani, Sarki ya koma cikin ƙuryar ɗakinsa na dake yanzu baya tare da ko wace mata...
Bai so Chief Onyx ya zo nan domin idan ya zo, gidan sarautar zai iya zama tamkar gidan kallo, kowa zai so ya ga kwarjinin sarkin Pavilion, wanda hakan zai jawo tambayoyi marasa iyaka...
"Ba zan bari su ganshi a nan ba," Sarki ya raɗa wa kansa yana goge gumin goshinsa. "Idan ya zo nan, asirina zai ruguje a gaban ƴaƴana."...
An bar Gimbiya Zayana a tsaye, jikinta ya yi sanyi. Ta rasa gane dalilin da ya sa mahaifinta yake nuna wata irin fargaba a fili game da mutanen nan. ta juyo, tana takawa a hankali zuwa sashenta, kanta cike da tambayoyin da babu mai ba ta amsarsu.
Tana tafiya tana nazarin wasiƙar da ta ga an bayar, me ya sa sarki ya rubuta masa cewa ba sai ya zo ba? Shin me sarki yake tsoron zai faru idan kowa ya ga fuskar sarkin Pavilion?...
A can ɓangaren Gimbiya Chingching, labarin dake girgiza masarautar bai ma shigo cikin kunnenta ba. Tana zaune a kan lallausar sofa, idanunta sun ƙafe a kan TV tana kallon katun (ƴan gwaigwai), tana ta dariya tana turo baki idan aka daki ɗaya...
Wata ma'aikaciya dake gyaran falon, tana goge wani tebur kusa da ita, ta kasa jurewa sai da ta yi magana..
"Gimbiya Chingching, shin ba ki da labarin rundunar Pavilion Kingdom sun zo wannan masarautar ne?"
Chingching ba ta ko juyo ba, idonta yana kan TV, ta ce cikin shagwaɓa..
"Su waye kuma pabiliyooo...?"
Ma'aikaciyar ta ja numfashi, ganin cewa wannan yarinyar ba ta ma san me duniya take ciki ba. Ga kowa Pavilion tsoro ne da fargaba, amma ga Chingching, suna ne kawai mai wahalar faɗi. Ma'aikaciyar ta girgiza kai kawai ta ci gaba da aikinta, ta ga gara ma ta yi shiru...
Ganin ma'aikaciyar ta yi shiru, Chingching ta ɗan harare ta tana turo baki..
"Kumaaaa za ki dame ni! Yooo ni ina ruwana da wani wani wani mene sunan? Uhmmm ni ki ƙyale ni. Ni yunwa ma nake ji... Dubi ma yadda kike goge nan, kin tare min TV."
Chingching ta koma ta kwanta tana rungume da toy🧸 ɗinta.. tana jira a gama shirinta na abincin rana, yayin da duk gimbiyoyin gidan suke cikin zulumi, ita nata damuwar ba ta wuce abinci da ƴan gwaigwai ba....
Aayat tana can a nata sashen, tana ta zirga-zirga tamkar wadda aka yi wa bushara da saƙon mutuwa. Yau ta kasance rana ta musamman, domin kwata-kwata ba ta yi shigar Inuwa ba. Tana sanye da doguwar riga ta sarauta, gashinta da fuska a rufe ga farin glass akan dara-daran idanuwanta, tana jiran jin ko sarki zai ƙira duk gimbiyoyin don yi musu bayanin abin da yake faruwa...
Duk sanda ta ji motsin takun tafiya a waje, sai gabanta ya faɗi, tana tsammanin bafade ne aka turo ya ƙira su. Amma shiru, har dare ya raba sarki bai nemi kowa ba. Wannan shirun ya fi kowane hayaniya ban tsoro a wurinta, domin tana jin cewa mahaifinta yana ƙoƙarin rufe wani babban rami ne kafin kowa ya gani...
A ɗayan ɓangaren kuwa, Gimbiya Maayah tana can kwance a kan katafaren gadonta, fuskarta a murtuke ba wai don zafin ciwo kaɗai ba, har da takaicin rashin samun damar fita ta ga abin da idonta yake son gani... Faɗuwar da ta yi a kan treadmill ta bar mata raɗaɗi a ƙunkuminta da bayanta wanda ya sanya koda juyawa ta kasa yi..
Mama Liyatu tana zaune a gefenta, tana dunduma mata baya da tsumman da aka tsoma a ruwan zafi tana lallashi...
"Yi haƙuri gimbiyata,"
Mama Liyatu ta faɗa cikin sanyin murya..
"Gobe idan Allah ya kai mu likita zai zo ya duba ki, zai baki maganin da zai sa ki miƙe nan take."..
Maayah ta cije laɓe, tana kife da kanta akan gadon domin kibda ciki tayi...
Duk wani motsi ya tsaya a masarautar.... Ma'aikata suna tafiya ne a cikin sanɗa gudun kada su tayar da fushin sarki...
Domin a wannan ranar har zuwa gobe komai zai iya faru idan wani ya kuskura ya aiwatar da laifi wa sarki, domin a kansa za'a huce takaici...
Iskar daren tana kaɗawa da wani irin sanyi daban, mai ɗauke da ƙamshin dawakan Pavilion da wani irin ƙamshin hayaƙin motocinsu waɗanda suka riga suka bar birnin, amma kwarjinin motocin yana nan maƙale a zukatan mutane..
Kowa yana jiran gobe....
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
⚠️ SANARWA⚠️
Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 1️⃣0️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Ayat ta tashi da safe tana jin wani irin nauyi a zuciyarta. Ganin ba za ta iya zama a matsayin gimbiya tana jiran abin da ba ta sani ba, ta koma asalin shigarta ta Inuwa. Ta ɗaura damararta, ta sanya kayan sojan masarauta, sannan ta fito don ganin abin da yake faruwa a tsakar gari...
Tana isa tsakiyar masarautar sai ta ci karo da Master Ibrahim. Ibrahim mutum ne mai zafi da kishin aiki, kuma shi ne yake lura da yawancin motsin ma'aikatan tsaron fada.
Ibrahim ya tsaya cak, ya zuba wa Inuwa idanu, yana nazarinsa kafin ya nisa ya ce
"Inuwa! Ina ka shiga ne kwana biyu? Ba na ganinka a wuraren aikinka, sannan ba ka bin tsarin yadda aka tsara maka hidima. Ko ka manta dokar masarautar nan ne?"
Inuwa yana sosa wuya cikin nuna alamar ba ya jin daɗi, ko da yake a ransa takaici ne ya cika shi
"Gafara nake nema Master. Kwana biyu bana jin daɗin jikina ne, shi ya sa ban fito ba."
Ibrahim ya jinjina kai, fuskarsa ba alamun wasa ya ce,
"Toh, Allah ya ƙara sauƙi. Amma yanzu tunda Allah ya haɗa mu, akwai inda nake son fita a gari. Za mu tafi tare ne don ka taya ni wasu ayyuka."
Inuwa bai yi gardama ba domin ya san idan ya ƙi, Ibrahim zai iya bincika dalilinsa wanda zai iya janyo masa matsala.
"Ba damuwa Master, mu tafi," ya faɗa a takaice...
Maimakon su ɗauki dawakai ko ababen hawa, Ibrahim ya yanke shawarar su taka da ƙafa. Suna tafiya suna ratsa lungu da saƙo na birnin Alhamra. Wannan tafiyar ta bawa Inuwa damar ganin yadda talakawan gari suke magana ƙasa-ƙasa game da motocin Pavilion da suka gani jiya...
Ibrahim ma ya yi shiru yana kallon gari, shima kansa kwanan nan bai fito ba, don haka yake son shaƙar iskar gari don jin abin da mutane ke faɗa...
Suna tafiya gefen titi, Ibrahim yana ta jansa da hira yana bashi labarai, amma hankalin Inuwa yana can nesa. Tana tunanin halin da mahaifinta yake ciki da kuma tsoron da Pavilion ya galla wa masarautarsu...
Saboda zurfin tunani, Ayat ba ta san lokacin da kafafunta suka soma raba ta da gefen titin ba, ta haura har tsakiyar titi ba tare da ta sani ba. Kwatsam! Sai wata mota kirar Jeep ta taho da gudu tana kokarin ritsa ta.
Ibrahim ya zaro ido ganin motar zata banke Inuwa. Cikin zafin nama da kwarewa irin ta jarumai, ya sa hannu ya janyo Inuwa da karfin gaske don ceton ransa. Ibrahim ya zata zai ji nauyin jikin namiji amma abin mamaki sai ya ji kamar iska ya janyo.
Hakan ya sa Ibrahim yin baya saboda karfin janyon da ya yi, shi kuma Inuwa ya faɗa kai tsaye kan faffadan kirjinsa. Suka tafi tare suka faɗi a kasa a tsakiyar titin, yayin da sauran mutane suka daskare suna kallonsu...
A nan ne duniyar Ayat ta tsaya cak. Ta faɗa daidai kan fuskar Ibrahim, wanda hakan ya sanya lebbansu suka haɗe wuri ɗaya. Wani irin numfashi ne yake fita daga juna, bugun zuciyar Ayat ya tsananta har tana jin sautin na Ibrahim a jikinta.
Sun ɗauki wasu dakikoki a haka, kowa ya kasa motsi. Ibrahim ya zuba mata ido, yana jin wani irin sanyi da laushin da bai taba ji ba a jikin namiji. Ayat kuwa, manyan idanunta sun cika da firgici tana kallon kwayar idon Ibrahim wanda shima ya ruɗe...
Da sauri Ayat ta dawo cikin hayyacinta, ta zabura ta tashi daga kansa tana sakin numfashi a hargitse...
Abu na farko da ta yi shi ne sa hannu ta taɓa lebbanta, sannan ta riƙa taɓa fuskarta tana duba ko gemun da sajen dake fuskarta sun cire saboda gogayyar da suka yi...
Taji su nan normal, sai ta sauƙe wani nauyayyen ajiyar zuciya, duk da cewa jikinta har yanzu ɓari yake yi...
Ibrahim shima ya miƙe a hankali yana kakkabe kayansa, amma hannunsa ɗaya yana kan lebbansa. Ya kura wa Inuwa ido cikin wani irin mamaki da shakku. A ransa yana faɗin
"Ta ya namiji zai kasance da leɓe mai laushi haka? Me ya sa zuciyata ta buga da karfi lokacin da jikinmu ya hade?"
Ya so ya yi magana, amma makogwaronsa ya bushe... Shi kuma Inuwa ya ƙi yarda su haɗa ido, ya juya baya yana nishin kuncin abin da ya faru.
Sun ci gaba da tafiya ɗaf-ɗaf da juna, amma babu wanda ya iya kallon ɗan uwansa, ballantana a yi magana. Ibrahim ya lura cewa tun daga wannan faɗuwar Inuwa ya ƙara nuna wata irin natsuwa da nauyin jiki.... Don ya kawar da tunanin da yake addabarsa, sai ya riƙa kallon gefe da gefe yana son ya tabbatar wa kansa cewa Inuwa namiji ne kamar kowa...
Suna shiga tsakiyar babban kasuwar birnin, nan take yanayin wurin ya canja.. Fitowar Inuwa a fili ba tare da kowace kariya ba ya janyo hankalin kowa. Duk inda suka ɗora ƙafa, sai an dakata ana kallonsu..
Kyawun fuskar Inuwa duk da gemun da ya sanya, ya kasance wani irin kyan dake fitar da haske mai ban tsoro.
'Yan mata dake gefen shaguna da waɗanda suke ciniki duk suka saki baki suna kallo. Maganganu suka fara tashi ta kowane sashe..
"Wow! Dubi wani handsome guy! Gaskiya ya haɗu," wata yarinya ta faɗa tana dafe ƙirji..
"Ya Allah! Wani irin kyau ne haka? Anya wannan mutum ne na duniya?"
Wata kuma ta tambayi ƙawarta cikin mamaki...
Wata tsohuwa dake sayar da kayan marmari ta gyara gilasinta,
"Wannan kam aljani ne! Domin kaf birnin nan da gefenta, ban taɓa ganin wanda yake da kyan wannan yaron ba. Dubi fatarsa tamkar madara."
Duk waɗannan yabo da kirari suna shiga kunnen Inuwa, maimakon ta ji daɗi sai ta ƙara jin haushi da matsuwa... Tana jin tamkar kowa yana leƙen asirinta ne ta cikin fatarta. Ta ƙara saurin taku, tana son ta ɓace wa idanun mutane..
Ibrahim kuwa ganin yadda Inuwa yake cin magani yana harara, sai abin ya ba shi dariya. Ya fara ƙunshe dariyar dake neman ƙwace masa, ganin yadda kowa ya rikice a kan ma'aikacinsa...
"Inuwa, ka ga yadda ka kusa janyo mana gobara a kasuwa? Ko mazan ma kallonka suke,"
Ibrahim ya faɗa ƙasa-ƙasa yana ɗan taɓa kafaɗarsa cikin sigar tsokana...
Inuwa ya juyo ya harare shi da manyan idanunsa..
"Master, don Allah mu koma masarauta. Na gaji, sannan ban son wannan kallon da ake mana."
Ibrahim ya yi murmushi, ya fahimci Inuwa baya son hayaniya. "To shikenan, mu zagaya ta wannan lungun mu koma fada, kafin wata ta zo ta sace ka ta gudu da kai."
Ibrahim ya dube shi, ganin yadda Inuwa yake faman basarwa kamar ba shi ne ya kusan cinye zuciyarsa ɗazu ba. Ibrahim ya kasa jurewa, ya ce..
"Wai Inuwa, me ya sa ba ka yi min magana ba tun bayan faɗuwar nan? Ko dai har yanzu kana jin tsoron motar ne?"
Inuwa ya ɗan tsaya, ya gyara rawaninsa da ya ɗan karkace ba tare da ta kalle shi ba ta ce...
"Ba komai Master. Kawai dai ina tunanin yanda Sarki yaƙi fitowa yau tin jiya, kuma kasuwar nan akwai hayaniya da yawa."..
Haka suka ƙaraso ƙofar masarauta, kowa na riƙe da abin da yake ji a ransa...
Suna isowa tsakiyar fada, sai wani bafade ya tarye su da sauri...
"Master Ibrahim! Sarki yana neman ka a yanzu haka a babban ɗakin taro."
Ibrahim ya kalli Inuwa, ya gyara tsayuwar takobinsa.
"Ka ga ko? Abin da kake fargaba ya zo. Mu je mu ji me Zaki yake tafe da shi."..
Inuwa cikin tsoro ya ja da baya yana zaro ido ya ce,
"A'a a'ahh iya kai kaɗai ake nema, kuma kumaa cikina ciwo yake..."
Wani jami'in da ke gefe yana dariya ya ce,
"Kodai period zaka yi ne Ɗan ƙwaƙur?..."
Ibrahim ya kalle shi tare da faɗin
"Kai, bana son iskanci faa..."
Sannan ya kalli Inuwa ya ce, "shi ke nan, ka je ka huta kawai..."
Inuwa ya gallawa wanda yayi mishi maganar nan harara haɗe da gatsine....
✨✨✨
Tun lokacin da Ayat ta taka kafarta a wajen masarauta a matsayin Inuwa, wani daddaɗen ƙamshi ya tashi ya ratsa sararin samaniya har zuwa can zurfin duniyar aljanu ta Power Pool. King Diamond dake zaune a kan karagar mulkinsa, ya ji wani irin bugawa a zuciyarsa. Bai buƙaci a faɗa masa ba, ya san Ayat ɗinsa ce take yawo a cikin gari...
Ta hanyar idonsa na tsari, ya riƙa kallon kowane takun da Ayat take yi tare da Ibrahim. Lokacin da motar ta kusan bugan Ayat, Ibrahim ya janyo ta suka faɗi har lebbansu suka haɗe, King Diamond ya daka wani uban tsalle idanunsa suka canza launi zuwa jawur tamkar wuta...
Wani azababben kishi ne ya turnuke shi...
"Aayat ɗina ce!" ya furta cikin murya mai rawar gaske dake ɗauke da fushi..
"Babu wani ɗan Adam da ya isa ya taɓa ta, balle ya ji yanayin daɗin da aka tanada domina."
Cikin kiftawar ido, King Diamond ya bayyana a kofar masarautar Alhamra ta waje. Farin dogon gashinsa dake tafe har kugu yana kaɗawa a cikin iska, idanunsa kuma suna fitar da wani irin kwarjini na ban tsoro. Ya nufo kofar masarautar cikin tafiyar izza da nuna iko, yana kallon Inuwa da Ibrahim dake kokarin bacewa cikin gida...
Abin al'ajabi, duk da tsayuwar sa a fili, babu wani soja ko mai gadi da yake iya ganinsa. Suna ta faman zirga-zirgarsu tamkar iska ce kawai take wucewa.
King Diamond ya yunkura zai ratsa ta tsakiyar gate din masarautar don ya biyo Ayat. Kwatsam! Sai wani irin haske mai launin gwal ya fito daga jikin bangon masarautar ya bugi kirjinsa da wani irin ƙarfi...
Sarkin aljanun ya tafi sama tamkar an harba kibiya, ya yi ta jujjuyawa a cikin iska yana neman hanyar daidaitawa. Sai da ya dage sannan ya tsaya daram a cikin iska yana kallon masarautar daga sama, fuskarsa ɗauke da mamaki...
A nan ne ya fahimci cewa masarautar Alhamra ba masarauta bace kawai ta mutane. Akwai wani tsari na musamman da aka yi mata, shinge ne na ruhaniya wanda yake toshe hanyar kowane aljani ko shaidanin abu. Wannan hasken da ya buge shi, wani irin makami ne dake iya ƙona