Showing 39001 words to 42000 words out of 154131 words
Chapter 14 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
so, ba za ta iya tsinkewa ba...
Ta matsa kusa da madubin tana kallon kwayar idonta. Tana neman ko za ta ga inuwar King Diamond a ciki, kamar yadda ya ce yana tare da ita..
"Karka ɗauka kayi nasara...."
Ta maimaita maganar da ta gaya masa, amma a ranta tana jin cewa ita kanta ba ta san waye ya yi nasara a tsakaninsu ba...
Tana cikin wannan tunanin sai ta ji an buga ƙofar ɗakin..
"Gimbiya! Gimbiya Ayat kina ciki?!" Muryar Saratu ce ta katse mata tunani.
Ayat ta firgita, ta goge fuskarta da sauri. Dole ne ta saita kanta, ta dawo Gimbiya Ayat mai natsuwa, ko da kuwa zuciyarta tana can bakin kogi tare da sarkin aljanu...
✨✨✨
A yau ba tare da kowa ya sani ba..
Da misalin ƙarfe huɗun asuba, lokacin da kowa yake nannaɗe cikin bargo, Sarki Nourdeen ya fito sanye da manyan kayan sarauta fuskarsa cike da damuwa..
Baya son gimbiyoyinsa su sani, don haka ya ba da umarnin a shirya babbar Helicopter ɗinsa ta alfarma a filin jirgi na sirri dake bayan fada...
Koda Master Ibrahim bai san da wannan tafiyar ba har sai da aka buga musu ƙofa. Sarki ya zaɓi dakarun tsaro guda biyar kacal, waɗanda ya amince da su, ciki har da jami’an tsaro na musamman da za su raka shi...
"Ba ma neman yaƙi," sarki ya faɗa wa shugaban masu tsaron nasa. "Zamu je ne don mu cika alƙawarin da aka daɗe da yi. Amma ku kasance a shirye da kowane irin yanayi."..
Ƙarar injin Helicopter ta mamaye sararin samaniyar fadar.
Sarki Nourdeen ya shiga ciki, ya zauna a mazauninsa na alfarma ya zuba wa masarautar Alhamra ido ta taga yayin da jirgin yake shawagi sama...
A ransa yana addu'ar wannan tafiyar ta zama silar zaman lafiya, ba silar rugujewar mulkinsa ba..
Tafiyar ba ta da tsawo sosai ta sama, amma ga sarki, kowane minti ɗaya tamkar shekara yake...
Suna isa ƙasar da suka nufa, daga sama ya fara hango wani babban birni dake kewaye da baƙaƙen ganuwa da hasken fitilu masu launin purple...
Wannan ita ce daular Pavilion...
Ganin tsarin gine-ginen wurin kaɗai ya isa ya nuna maka cewa wannan ƙasa ce dake da ƙarfin da ya zarce na kowace masarauta...
Yayin da Helicopter ɗin take neman gurbin sauƙa a katafaren filin jirgin Pavilion, sarki ya hango dakarun Pavilion sanye da baƙaƙen kaya sun jera layi tamkar bango. Babu wani rurrusunawa, babu wata gaisuwa ta girma sai kallo mai cike da kwarjini...
Sarki Nourdeen ya ja numfashi, ya gyara kambunsa...
"Lokaci ya yi," ya raɗa wa kansa yayin da matattalar jirgin ta sauƙa..
Sarki Nourdeen ya fito daga helicopter ɗin, kansa a ɗage amma zuciyarsa tana bugawa. Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un! Abin da ya gani ya wuce misali...
Girman gine-ginen Pavilion kawai ya isa ya sanyaya wa mutum jiki. Ko’ina ka kalla dakarun Pavilion ne sanye da baƙaƙen kaya, tsaye daram ba sa motsi tamkar gumaka, idanunsu ƙafe a kan kowane taku na baƙin..
Sauran jami’an tsaron sarki da suka biyo shi, suka tsaya a tsakiyar katafaren harabar fadar, fuskokinsu cike da tsoro da mamaki. Sun ji kansu ƙanana a cikin wannan makeken fili wanda aka ƙawata da dutsen marmara mai sheƙi.
Wani babban jami'in Pavilion wanda kwarjininsa ya kusan zarce na sarki kansa, ya tako a hankali ya yi wa sarki nuni da hannu...
Ya fara yi wa sarki jagora ta cikin sashe-sashe mabanbanta..
Sarki ya ga jerin motocin yaƙi da na alfarma waɗanda ba a taɓa ƙera irinsu ba a duniya..
Dawakai ne baƙaƙe, manya masu sheƙin fata, waɗanda kowane ɗaya ana masa hidima ta musamman...
Kowace kusurwa akwai jami'ai, wasu a sama wasu a ƙasa, dukansu idanunsu ba ya kiftawa.
Sarki Nourdeen yana tafiya ne kamar a mafarki. Wurin ya kasu Part part, kowane sashe da abin da ake gudanarwa a ciki, tun daga tsaro har zuwa na'urorin zamani da suke ta faman aiki...
Daga ƙarshe, jami'in ya kai sarki zuwa wani babban falo da ya fi kowane falo da sarki ya taɓa gani a rayuwarsa. Kujerun wurin an ƙera su da wani irin fata mai taushi da launin zinare..
Suka zaunar da sarki a can, aka bar shi shi kaɗai a cikin wannan faffaɗan ɗakin..
Ba a daɗe ba, wasu ma'aikata mata waɗanda kyan fuskarsu kaɗai ya isa ya saka mutum cikin damuwa, suka shigo ɗauke da tire-tire na zinare. Suka shimfiɗa masa kayan ciye-ciye da abubuwan sha na alfarma, waɗanda ƙamshinsu kaɗai ya isa ya nuna tsadar su.
Sai dai waɗannan ƴan mata ma'aikata duk ba mutane bane, su ɗin robots ne masu amfani da na'ura...
Sarki ya zauna a kan kujerar, amma ya kasa ko taɓa ruwan dake gabansa. Idanunsa suna ta kai-komo, kowane motsin labule ko ƙofa sai ya tsorata shi. Yana nan zaune yana jiran jin takun tafiyar da zata sanar da isowar mutumin da ya sanya shi barin masarautarsa a lokaci guda...
Falon ya yi shiru sai ƙarar sanyin na'urorin sanyaya ɗaki kawai ke tashi. Sarki ya duƙar da kansa, yana tambayar kansa..
"Me zai faru idan wannan mutumin ya fito? Shin yarjejeniyar da muka yi tsawon shekaru da suka wuce, yau ce ranar da zan biya ta?"..
Sarki Nourdeen yana tsaka da fargabar jiran abin da zai faru, sai ya ji iskar falon ta canza launi. Ba tare da an ji takun tafiya ba, da motsin ƙofa ba, kawai sai ga Chief Onyx ya bayyana a tsakiyar falon tamkar iska ce ta huro shi...
Tsayuwar sa kawai ta isa ta nuna cewa shi ba mutum ba ne irin na wannan zamanin, ƙirar jikinsa irin ta magabata ne, samudawan farko masu girman jiki da ƙasusuwa ƙusassu...
Tsayinsa ya zarce tunanin mai kallo, faffaɗen ƙirjinsa kuma ya nuna irin ƙarfin dake ɓoye a jikinsa...
Sanyi ya ratsa falon kamar wani abu mai rai ya shigo, fitilun suka ɗan fara rawa..
Kamar yadda iska ke bayyana ba tare da izini ba haka Chief Onyx ya bayyano a tsakiyar falon...
Dogon baƙin rigarsa tana ja har ƙasi, amma rigar ta gaba a buɗe take tana bayyana faɗaɗen farin ƙirjinsa kamar an sassaƙa shi da ƙarfe...
Farin ƙirjinsa, wanda ya yi fari ƙal tamkar madara ya fito fili, tare da wasu kwantattun gashi dake kwance a kan faffaɗen ƙirjin nasa, wanda ya ƙara fito da jarumtarsa...
Manyan nonuwansa sun tsaya daram, irin ƙirar namiji tsantsa wanda kallo ɗaya zai sa zuciya ta manta bugawa...
Wasu sarƙoƙi na musamman masu tsada na azurfa sun zubo daga wuyansa har zuwa kan faffaden ƙirjinsa, suna walkiya a ƙarƙashin hasken fitilun falon...
Dogon baƙin gashinsa mai santsi da sheƙi yana sauƙa har kafaɗunsa, yana kaɗawa a hankali cikin sanyin AC...
Gefen fuskarsa guda na rufe da wani ƙarfen azurfa mai sarƙaƙƙiyar ƙira, wanda ya ƙara wa idanunsa kwarjini..
Idan ka kalle shi, ba wai ka ga kyau kawai bane har da tsantsar barazana...
Idan ka tsinci kanka kana kallonsa tsawon daƙiƙu to jikinka zai daskare.
Zuciyarka zata buga da sauri ba tare da dalili ba..
Takalmansa baƙaƙe, masu nauyi kamar na soja suna sauƙa ƙasa da ƙasa ba tare da amo ba, amma kowane taku yana da nauyin da yake sa ƙasa ta tuna da shi...
Kana kallonsa zaka ce..
“Wannan ba musulmi bane.”
Amma shi musulmi ne cikakke mai bautar Allah cikin sirri, mai tsananin tsoronSa, kuma mai tsananin hukunci ga wanda ya karya doka...
A bayansa, tana taku cikin natsuwa da izza tamkar ɗawisu, wata zafaffiyar budurwa ce kyakkyawa dake sanye da baƙaƙen kaya matsattsu. Gashinta a kwance yake har gadon bayanta, idanunta kuwa suna fitar da wani irin haske na musamman...
Wannan budurwa ba mutum ba ce, ita ce ƙololuwar fasahar Pavilion. Robot ce ta musamman, wacce aka ƙera ta don kariya da aiwatar da ayyukan da mutum ba zai iya ba. Ita ce babban makamin Chief Onyx...
Halitta ce da aka ƙera domin yaƙi, tsaro, da aiwatar da umarni ba tare da tambaya ba.
Ita ce hannun damar Chief Onyx.
Ita ce garkuwarsa da takobinsa...
Chief Onyx ya zauna a kan kujerarsa ta alfarma, ya ɗora hannuwansa a kan madafan kujerar, idanunsa suka sarƙe da na Sarki Nourdeen. Robot ɗinsa tana tsaye a gefensa tamkar mutum, idanunta suna nazarin kowane motsi na baƙon da yake gabansu...
Sarki Nourdeen ya tsinci kansa da kasa magana. Duk wani iko da yake takama da shi a Alhamra, ya neme shi ya rasa a gaban Chief Onyx..
Muryar Chief Onyx ta fito da zurfi da amo tamkar ana hura busa..
"Barka da zuwa, Sarki Nourdeen. Na san ka daɗe kana jiran wannan ranar. Amma tambayar ita ce... shin kana shirye da farashin da za ka biya?"...
Chief Onyx ya karkata kansa gefe guda, yana kallon Sarki Nourdeen da idanunsa dake fitar da wani irin kwarjini na daban..
Robot ɗinsa dake tsaye a gefe ta lura da yadda bugun zuciyar sarki ya tsananta..
"Nourdeen," Chief Onyx ya ƙira sunansa ba tare da lakabin sarauta ba, muryarsa tana amo a cikin falon.
"Shekaru goma sha biyar sun shuɗe tun ranar da kuka kawo min yaƙi tare da taimakon dakarun turawan matar ka Ruma. Ranar da kuka so ku raba ni da gadon mahaifina. Na bar maka Alhamra ba don tsoro ba, sai don umarnin kotun duniya da kuma buƙatar kwanciyar hankali."..
Chief Onyx ya miƙe tsaye, tsayinsa ya sa sarki ya ji tamkar shi wani ƙaramin yaro ne. Ya fara takawa a hankali yana zagaye Sarki Nourdeen, yayin da takalmansa suke bada sauti a kan lallausar carpet..
"Na bar maka Alhamra a matsayin aro, amma da sharaɗi guda ɗaya. Ka amince za ka mallaka min ɗaya daga cikin 'ya'yanka don ta zama Personal Maid ɗina wato ƴar aikina. Ka yarda da hakan don kawai ka riƙe mulkin da ba naka ba. To yanzu lokaci ya yi. Na zo karɓar abin da yake nawa ne."..
Cikin Ruɗani Da Takaici
Sarki Nourdeen ya duƙar da kansa, gumi na keto masa. Ya tuna lokacin da ya yi wannan yarjejeniyar, a ransa ya ɗauka lokacin ba zai taɓa zuwa ba. Amma yau, ga Chief Onyx nan a raye cikin ƙarfi da mulki fiye da kowane lokaci...
"Ina buƙatar mace mai tarbiyya, jajirtacciya, kuma wacce za ta san darajar Pavilion,"
Chief Onyx ya ci gaba da magana yayin da ya tsaya a gaban sarki..
"Ban san ko su wane ne 'ya'yanka ba, kuma hakan bai dame ni ba. Abin da nake so shi ne ɗaya daga cikinsu ta zama ƴar aikin pavilion kingdom."..
A idon Sarki Nourdeen, fuskokin 'ya'yansa suka fara giftawa...
Zayana wacce take jinin Ruma ce, matar da ta janyo wannan yaƙin. Shin zai iya bayar da ita? Amma kuma Ruma ta kasance mata mai ƙarfin iko fiye da tunanin mutum, kuma jinin turawa wacce a yanzu take mulkan ƙasar Canberra babban birnin Australia...
Aayat wacce take amintacciyarsa kuma take kare shi?
Ya girgiza kai alamun rashin amincewa..
Maayah wacce take cikin jinya yanzu?...
Chingching wacce ba ta san zafin rayuwa ba?
Duk wadda ya bayar ya sani cewa ya tura ta ne zuwa bauta a gidan mutumin da yake ƙin jinin mahaifinsu.. Amma idan bai bayar ba, ya san Chief Onyx zai iya murƙushe Alhamra a cikin sa'o'i kalilan...
Chief Onyx ya yi wa Robot ɗinsa nuni da hannu. Robot ɗin ta matso kusa da sarki, ta miƙa masa wata na'ura mai nuna hotuna..
"Zaka ba ni sunan wadda ka zaɓa kafin rana ta faɗi..,"
Chief Onyx ya faɗa cikin murya mai sanyi...
"Idan kuma ka kasa zaɓa, to ni da kaina zan shigo Alhamra in ɗauki duk wacce idona ya nuna mun... Kuma ka sani, idan na shigo da kaina, ba zan fita hannu empty ba..."...
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
⚠️ SANARWA⚠️
Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 1️⃣4️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Sarki Nourdeen ya shiga cikin wani hali na ƙunci da matsanancin tunani. Ga shi a gaban babban maƙiyinsa, mutumin da yake bin sa bashin dake iya ruguje masa mulki da mutunci...
Chief Onyx kuma yana nan zaune, idanunsa tamkar takobi suna sassaƙa zuciyar sarki yayin da yake jiran amsa...
Sarki Nourdeen ya fara rarraba wa zuciyarsa zaɓin 'ya'yan da yake da su, amma kowace ya kalla sai ya ga cikas...
Zayana! Ko kusa, sarki ba zai taɓa iya bayar da ita ba. Tsoron mahaifiyarta Ruma yake yi fiye da yadda yake tsoron kowa. Ya san idan ya bayar da Zayana, Ruma za ta iya janyo masa yaƙin da ya fi na farko muni, domin tana da ikon da zai iya girgiza dukkan masarautar...
Ayat kuma wannan ma ba zaɓi ba ne a gare shi. Ayat tana da wani irin zafi da rashin haƙuri. Ba ta jure wulaƙanci kuma tana iya tunkarar kowa. Idan ya bayar da ita, ya san za ta iya tayar da babban rikici a cikin Pavilion wanda zai iya kai su ga halaka...
Maayah kuma halinta da na Chief Onyx ba za su taɓa haɗuwa ba. Maayah tana da tsananin girman kai, yayin da Chief Onyx yake son mutum mai sauƙin kai da biyayya. Ba zai taɓa dacewa a kai ta can ba...
Yumna kuma Shima sarki ya sani cewa Chief Onyx ba zai taɓa karɓar Yumna ba saboda dalilai na kashin kansa da suka shafi tsarin masarautar Pavilion...
Ganin sarki ya yi shiru, Chief Onyx ya ɗan yi nuni da hannunsa zuwa ga babban bangon falon. Nan take bangon ya juye ya zama babban screen wanda ya fara nuna hotunan dakarun Pavilion dubu-dubai dake atisaye a ƙasa da kuma na'urorin yaƙi masu firgitarwa...
"Uncle, kada ka ɓata lokaci kana tunanin yadda za ka yaudare ni,"
Chief Onyx ya faɗa cikin murya mai sanyi dake cike da jan kunne...
"Duniya ta canja. Idan na ba da umarni yanzu, kafin rana ta fito Alhamra za ta zama toka. Ba na neman wadda kake so, ina neman wadda za ta biya bashin da nake binka ne."...
Sarki Nourdeen ya haɗiye yawu, ya dubi Chief Onyx cikin raunin murya...
"Chief, na san na yi alkawari, kuma ban musanta ba. Amma ina neman alfarma guda ɗaya. Ka ba ni kwanaki uku kacal in koma in tsara yadda zan taho maka da ita. Ba zan iya ɗaukar ɗaya daga cikinsu a yau ba tare da wani shiri ba."..
Robot ɗin dake tsaye a gefe ta kalli Chief Onyx, tana jiran umarninsa...
Chief Onyx ya yi shiru na ɗan lokaci, yana kallon yadda sarki yake gumi..
"Kwanaki uku?" Chief Onyx ya maimaita, sannan ya yi wani murmushin gefen baki wanda ya ƙara bayyana kwarjininsa.
"To shikenan. Na ba ka kwanaki uku. Amma ka sani, idan kwanaki ukun nan suka cika baka kawo min wacce nake buƙata ba, to ni da kaina zan shigo Alhamra. Kuma a ranar ba zan karɓi 'yar aiki ba, zan karɓi duk masarautar ne baki ɗaya."....
Sarki Nourdeen ya ji wani sanyi, amma kuma ya san kwanaki ukun nan ba komai ba ne. Ya miƙe cikin sanyin jiki yayin da Robot ɗin ta fara yi masa jagora don fita daga falon zuwa inda helicopter ɗinsa take...
✨
Sarki ya jingina kansa da jikin kujerar jirgin, idanunsa a rufe. "Chingching," ya raɗa a fili...
Itace kaɗai zaɓin da sarki yake gani zai iya fitar da shi kunya. Ba ta da uwa mai iko kamar Ruma da zata tada masa hankali, hasali ma uwarta bata raye, kuma ba ta da zafin kan Ayat ko girman kan Maayah...
Amma kuma, zuciyarsa ta buga lokaci guda.... Chingching yarinya ce ƙarama, wacce ba ta san komai ba sai wasa da neman abinci...
Ta yaya zai ɗauki wannan ƴar gaban goshin tasa ya kai ta matsayin yar aiki ga mutum irin Chief Onyx?...
"Amma idan ban bayar da ita ba, Alhamra zata ruguje,"
Sarki ya faɗa cikin ransa, yana jin raɗaɗin yanke wannan danyen hukuncin...
✨
A can cikin masarautar Alhamra, kishin shaƙuwar dake tsakanin Inuwa da Master Ibrahim ya fara kai ma'aikata maƙura.. Ganin yadda Inuwa baya wani aiki na kwarai, sai dai ya fita yawonsa ya dawo ya huta, ya sa sauran dakarun fadar suka kulla masa sharri..
Sun haɗa gungunsu suka nufi wurin Master Ibrahim da nufin ɓata Inuwa..
"Master, gaskiya wannan yaron yana neman ɓata mana suna,"
ɗaya daga cikinsu ya fara magana..
"Wannan fitar da yake yi, ashe yawon neman mata yake yi a gari. Yana zuwa yana sharholiyarsa da mata, shi yasa idan ya dawo baya iya aiki saboda gajiya."..
Ibrahim ya ji wani irin ɗaci a ransa. Kalaman sun sosa masa zuciya, musamman idan ya tuna yau da safe da Inuwa ya sanar da shi cewa ya kwana da wata a asibiti... Amma a matsayinsa na jagora, bai nuna musu rauninsa ba. Ya share su, ya kuma ɗaure fuska tamkar bai damu ba..
"To, ina ruwanku?" Ibrahim ya faɗa cikin tsawa wacce ta sa suka ja baya.
"Shi Inuwa ba namiji bane? Kamar yadda kuke son mata, haka shima yake sonsu. In dai yana yin abin da na sa shi, to ku barshi yasha soyayyarsa, lokacinsa ne!"
Duk da cewa ya kare Inuwa a gaban ma'aikatan, amma bayan sun tafi, Ibrahim ya zauna shi kaɗai yana tunani. Wani irin kishi ne ya ziyarci zuciyarsa wanda shi kansa bai san dalilinsa ba..
"Mata yake nema a gari?" ya tambayi kansa.
Yana jin tamkar an yaudare shi. Ya fara jin cewa dole ne ya sanya ido sosai kan Inuwa, ba don sharrin ma'aikatan ba, sai don yana son tabbatar wa kansa cewa lallai Inuwa namiji ne cikakke mai sha'awar mata, domin har yanzu akwai wani abu game da Inuwa da ya kasa ganewa..
✨✨
Bayan kwana biyu...
Yau ma, Inuwa ya sulale ya fice daga fadar ba tare da Master Ibrahim ya sani ba, ya nufi tsakiyar kasuwar birnin Alhamra domin ɗan zagayawa ya rage wa kansa damuwa..
Kasuwar tana nan cike da hayaniya da rance-rancen ma'amaloli. Muryoyin masu talla suna tashi ta kowane gefe, musamman muryar mai sayar da abubuwan zaƙi, wanda ƙamshinsa ya cika ko'ina. Inuwa ya tsaya a gaban mai tallan, ya ji yana