Showing 51001 words to 54000 words out of 154131 words

Chapter 18 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

17 Mar 2026

104

kalli hoton birninsa na Pavilion ta tagar gilashi...

"Zan bar shi ya ji tsoron wacce zan zaɓa a cikin 'ya'yansa... zan ɗauko wacce ya fi so, in mayar da ita baiwa a nan, yadda ya so mayar da Ƙanwata..."

A can sashen hutu, Yumna tana zaune a gaban wani tebur na alfarma, amma zuciyarta tana can gun sauran gimbiyoyi, bata son tayi nisa da Alhamra..."

✨✨

Sai da suka kwana, Sarki aka bashi ɗaki na musamman duk da bazai iya kwanciya yayi bacci a wannan birnin ba saboda fargaba da tsoro...

Bai rintsa ba har asuba..
Tafiyar asubanci suka yi cikin sirri, inda jirgin sarki ya sake sauƙa a babban filin Alhamra...

Yumna ta fito, fuskarta babu annuri domin akwai wani irin kwarjini na daban da ya fara bayyana a tare da ita..

Sarki Nourdeen ya ƙira ta gefe kafin su rabu zuwa sassan su...

"Yumna," ya ƙira sunanta cikin muryar lallashi,

"Kamar yadda muka tattauna da Yayanki, wannan maganar sirri ce tsakaninmu. Kada ki kuskura ki nuna wa kowa, har ma da 'yan uwanki gimbiyoyi cewa kin san wani abu. Ke ƴar gidan nan ce, kuma haka zaki ci gaba da zama a idon duniya."

Yumna ta jinjina kai cikin sanyin jiki.
"Na ji, Abul. Amma zuciyata ba za ta taba daina tunanin Yayana ba."

Sarki ya yi ajiyar zuciya, ta wuce nata sashen yayin da shi kuma ya nufi fada, zuciyarsa tana bugawa...

Dole ne ya zaɓi ɗaya daga cikin gimbiyoyinsa ya miƙa ta ga Chief Onyx a matsayin personal maid wato baiwa....

Sarki Nourdeen ya zauna a babban falonsa, idanunsa sun yi jawur saboda rashin bacci da kuma fargabar abin da zai biyo baya. Yana nazarin matan nan guda huɗu da ya riƙe a matsayin 'ya'yansa..

Ya san cewa kowacce a cikinsu idan ya kai ta Pavilion, tamkar ya jefa kansa ne a cikin babban bala'i. Idan ya kai Zayana, Ruma za ta iya sa sojojin Turai su ƙone Alhamra...

Idan ya kai Maayah, fushinta da girman kai zai iya sa ta yi abin da Chief Onyx zai kashe ta...

Idan kuma ya kai Ayat, wacce ko shi bai san fuskarta ba, to lallai masarautar Pavilion za ta ga abin mamaki...

Duk da ya tura Yumna da fari, yanzu tunda asiri ya tonu cewa ita ƙanwar Chief ce, ya zama dole ya zaɓi ɗaya daga cikin gimbiyoyin nan...


A yau

Sarki ya ƙira babban hadiminsa, ya ce masa..

"Ina son a shirya babban taron gimbiyoyi na musamman gobe. Ba zan jira lokacin haɗuwarmu na shekara ba. Ina son kowacce ta fito daga sashinta, su hallara a fada."

Hadimin ya firgita, "Allah ya ba ka nasara, har da Gimbiya Ching Ching?"

"Har da ita!" Sarki ya daka masa tsawa.

_A washegari da safe_

Sashen Gimbiya Zayana..

Tana zaune a kan wata kujera ta zinariya, ma'aikatanta na tsugune a gabanta kamar dabbobi...

Tana ɗore da ƙafarta akan bayan wata yayinda tayi goho..ta miƙe ƙafar tana danna wayarta..

Ɗaya kuma a gefe itama tana durƙushe kamar mai yin rarrabe, Miemie tana zaune akan bayanta tana cin abinci, ita bazata zauna akan kujera ba sai a bayan baiwa ko zata ci abinci..

Kana ganinta kasan jinin Zayana ce, Zayana kuma jinin Ruma.. domin duk siffar turawa ne dasu, cat eyes da kuma galden hair...

Wata ce ta shigo ta durƙusa ta sanar cewa..

"Princess hadimi ya zo, wai sarki yana son ganinku..."

Ta daka mata tsawa da cewa,

"Wane irin taro ne Sarki zai ƙira yanzu? Shin bai san cewa fito da ni daga sashena ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba zubar da mutuncina ne?"

Ta miƙe ta kalli madubin dake manne a bangon falo kusa da plasman ya sha ado, tana gyara farin gashin kanta, zuciyarta na raya mata cewa lallai akwai wani abu da sarki yake shirin yi...



Sashen Gimbiya Maayah..
Ita kuwa ko kallon ma'aikatan ba ta yi ba. Ta kalli gefe ta ce,

"Bana son hayaniya! Idan sarki yana son ganina, ya zo nan sashena mana. Amma tun da ya ce kowa ya fito, zan je, amma kowa ya shirya wa kowane irin fushi da zai fito daga gare ni in har ba tattaunawar arziƙi bane."...



Sashen Gimbiya Ayat..

Ta tashi tsaye a hankali, mayafinta na rufe da fuskarta, sai idanunta kawai dake walƙiya. Ta yi shiru ba ta ce komai ba.. sai amsar da ta bayar da

"Shi ke nam, Allah yasa lafiya..."



Sashen Gimbiya Ching Ching..

Sanar mata hadimi yayi da cewa..

"Gimbiya Ching Ching, ki je inji sarki..."

Turo baki tayi da faɗin..

"Bana zuwa! Ni wanka za a yi min, kuma barci nake ji. Idan Daddy yana so na, ya sa a goyo ni a kai ni fadar."

Uma Altine tana lallashinta,

"Gimbiya, umarnin sarki ne, dole ne mu je."

Sai da Uma Altine ta goye ta kafin suka tafi, dake ta saba da nauyin Ching Ching yanzu goyon baya damunta...

Fadar sarki ta ɗauki tsit bayan an ƙira taron gaggawa. Gimbiyoyin sun zauna a kujerunsu na alfarma, amma dukansu suna jin wani sanyi a jikinsu..

Sarki Nourdeen ya kalli 'ya'yan nasa, musamman Yumna wacce take nuna kamar ba ta taɓa jin sunan Pavilion ba..

"Na ƙira ku ne domin in sanar da ku wani abu mai mahimmanci. Masarautar Alhamra tana da yarjejeniya da wani babban sarki, kuma an buƙaci a aika da ɗaya daga cikinku don wakiltar mu a can."

Gimbiya Zayana ta yi gyaran murya. A ranta tana tunanin cewa lallai ita ce za a aika, domin ita ce babba kuma ta fi kowa kwarewa...

Sarki Nourdeen ya cigaba da
 "Kasar da za a je itace... Pavilion."

Jin sunan Pavilion ya sa duk ma'aikatan dake tsaye suka girgiza. Wasu sun fara raɗa-raɗai a hankali,

"Pavilion? Wanda muke ji a labaran litattafai!"

Yumna kuwa ta daskare, amma ta danne fuskarta, ta nuna cewa ita ma a yanzu take jin sunan...

Sarki Nourdeen ya kuma cewa,

"Kuma wacce na zaɓa ita ce... Gimbiya Ching Ching."

Wani irin shiru ne ya biyo baya. Maayah ta kalli Sarki da mamaki, Zayana ta buɗe baki har ta manta da izzarta...

Gimbiya Ayat ta kalle shi a dimauce. Ta miƙe tsaye, mayafinta yana kaɗawa, idanunta suna nuna tsananin damuwa..

"Abul! Ta yaya? Ka san cewa Ching Ching ba ta san ciwon kanta ba. Har yanzu wanka ake mata, kuma bata damu da komai ba sai wasa da bacci! Me ya sa za ka zaɓe ta a cikinmu? Ni, ko Zayana, ko Maayah, har ma da Yumna, duk mun girme ta kuma mun fi ta sanin yakamata. Me ya sa ita?"

Gimbiya Zayana ta kalli Ayat da rainin hankali, tana mai gyara kayanta..

"Ke! Ayat! Waye ya ba ki damar kawo sunana a cikin wannan maganar? Ni dai ba ruwana! Kuma Abul, wannan yarinyar (tana nuna Ching Ching da hannu) ba ta cancanci ta je ko ina ba."

Sarki ya daka musu tsawa...

"Ya isa haka! Umarni na ne na ƙarshe!"

 "Ayat, baki fini ƙaunar Ching Ching ba. Ina jinta a raina kamar rayuwata, amma na san cewa a can ba za a cutar da ita ba, domin na san wanda zan aikata wuri. Kuma na san cewa ita ce mafi dacewa."

Sarki ya kalli Ching Ching, wacce ke zaune a gefensa a kujerar sarautarsa tana wasa da ƴan tsananta...

 "Ching Ching! Za ki shirya tafiya gobe da asuba. Za ki je wata ƙasa mai kyau, inda za ki ci abinci iri-iri kuma za a ba ki sababbin kayan wasa."...

Ching Ching ta ɗaga kai,

"Da gaske Daddy? Amma ba zan iya tafiya ba, ba na son manyan jirage masu tashi sama, goyona za'ayi a kaini wurin.."


Bayan an sallame su, kowacce ta koma sashenta cike da tunani da fargaba..

Ayat ta kasance cikin damuwa matuƙa, tana jin cewa za a aike ƙanwarta can wata duniyar da ba ta sani ba...


Sarki yana zaune a kujerarsa, sai ga Uma Altine ta shigo cikin damuwa, ta durƙusa tana gaishe shi...

Ya dube ta sannan ya ce, "me ke tafe dake?..."

Uma Altine cikin damuwa ta ce,

"Ranka ya daɗe! Na ji batun za'a aika Gimbiya Ching Ching can ƙasar, kuma na duba ita yarinya ce har yanzu bata fara jinin al'ada ba, ina tunanin idan ta fara wa zai kula da ita?
Shine na ke roƙon alfarma a tura mu tare domin na cigaba da kula da ita, tin tana jaririya nake riƙe da ita ina so na kare martabarta da mutuncinta..."

Sarki ya jinjina kai sannan ya ce,
"Kar ki damu akwai waɗanda zasu cigaba da kula da ita acan, ku kasance a sashenta, duk abinda kuke so kuyi magana..."

Uma Altine tayi godiya sannan ta fice cikin damuwa, bata so tayi nisa da Ching Ching ba duk da wahalar da take bata...

Wannan bayani da uma Altine ya sanya sarki shiga nazari, duba da babu mata a fadar Pavilion sai robots da akayi musu siffar mata.... Kaf sojojinsa maza ne...

Wannan tunanin ne yasa shi ƙara jinkiri a tafiyar...



An kwashe sati biyu cur, amma shiru babu Sarki Nourdeen, babu kuma alamar wata gimbiya da za'a kawo..

Fadar Pavilion ta shiga cikin wani irin yanayi na shiru mai cike da tashin hankali. Chief Onyx yana zaune a ɗakinsa, yana kallon wata babbar allon dijital inda hotunan gimbiyoyin Alhamra suke...ko wacce yasan bayananta..

Gely cikin muryar na'ura mai sanyi ta ce,

"Boss, wa'adin sati biyu ya cika. Sarki Nourdeen ya sake karya alƙawarinsa."

Chief Onyx ya yi murmushin rainin wayo...

"Idan shi karya alƙawari ba matsala ba ce a wurinsa, to ni babban matsala ce, komin ƙarantarsa.
Zamu shirya tafiya garin Alhamra. Ƙasar da babu wanda ya taɓa ganin kamannina har zuwa yanzu, sai dai su ji labarina. To, zuwa gobe za su ganni ido da ido."...



Bayan kwana ɗaya, sararin saman Alhamra ya shaida wani baƙon abu. Wani jirgin sama mai cike da fasaha, ba kamar namu na al'ada ba, ya sauƙa a babban filin sauƙar jirage na masarauta...

Wannan jirgin na musamman ne, domin babu kowa a cikinsa sai mutum biyu kaɗai, Chief Onyx da kuma Gely, robarsa mai taimaka masa...

Sarki Nourdeen ya fito don tarbar baƙon, fuskarsa cike da fargaba...

Babu wanda ya san fuskarsa, sai labarinsa da ake ji a litattafan fiƙira...

Chief Onyx ya fito daga jirgin, sanye da doguwar riga baƙa mai kwarjini, yayin da fuskarsa ke ɗauke da wani abin rufe fuska wato digital mask wanda ya ke ɓoye ainihin kamanninsa. Gely tana biye da shi, idanunta na bada hasken ja...

Jama'ar Alhamra suka yi tsit. Kowa yana kallon Sarkin Pavilion da ido cike da tsoro da mamaki...

A cikin taron jami'an tsaron da suka tsaya don kare lafiyar sarki, akwai Inuwa...

Sanye da kayan tsaro irin na sarakunan, Inuwa yana kallon Chief Onyx da idanu cikeda mamaki da kuma shakku...

Inuwa yana maganar zuci.

"Wannan shi ne mutumin da Abul yake son kai wa Ching Ching? Yana da kwarjini, amma kuma yana da ban tsoro. A yanzun ma babu wanda zai bada shaidar fuskarsa."

Domin rafin fuska na sanye da ƙarfen azurfa mai kyan gani da ado..sai rabin fuskar ne a bayyane ..

Chief Onyx ya matsa kusa da Sarki Nourdeen, ba tare da ya kalli kowa ba sai sarki...

Cikin murya mai kauri da izza ya furta..

"Ina fatan ba ka manta da ni ba, Sarki Nourdeen... Wa'adin ya cika, kuma na zo ne don karɓar abin da nawa ne."

Sarki Nourdeen jikinsa na rawa ya ce,

"Barkanka da zuwa, Sarkin Pavilion. Ka yi haƙuri, an samu wasu matsaloli ne."

Chief Onyx ya ce,

 "Matsalolin da wataƙila wani na cikin gidanka ne ke ƙirƙiran su?"

Ya faɗa yana kallon Inuwa wanda ke tsaye a cikin jami'an tsaro. Idanunsa na dijital sun duba kowane jami'i...

Inuwa ya ji wani sanyi ya ratsa shi. Yana tunanin ne ya sa Sarkin pavilion yake kallonsa ba, amma ganin wannan robot yasa ta tuno da yunƙurin sace ta da akaso yi, har ta faɗo saman jirgi....nan jikinta ya fara rawa...

"Kodai su ne za'a ba wa Ching Ching?..."

Sai kuma ta fara nadamar cewa,
"Da nasan hakan zata faru da tin lokacin na bisu mun tafi, na tabbata da yanzu basu zo neman ƴar uwarta ba..."

Sarki Nourdeen ya bi ta inda Chief Onyx ya kalla, ya ga Inuwa..

"Babu wanda ya isa ya kawo matsala a masarautata."

Chief Onyx ya ce,

 "To, tunda al'amarin ya zama haka, zan zauna a nan Alhamra har sai an shirya komai. Gely, nemi masauki a cikin fadar."

Sarki Nourdeen cikin damuwa ta ce,

"Za ka zauna a nan?"

Chief ya furta.

 "Eh, zan zauna, domin in tabbatar da cewa ba a sake karya alƙawari ba."

Hakan ya sa Sarki Nourdeen shiga wani sabon yanayi na damuwa, domin a yanzu Sarkin Pavilion yana cikin fadar Alhamra, kuma babu wanda ya san menene shawararsa ta gaba...


Filin masarautar ya kasance cike da tsit, yayin da Sarkin Pavilion Chief Onyx, ke shirin shiga wuce wa cikin fadar.... Kowa ya sunkuyar da kai, ba tare da ya kalli kwarjinin mutumin ba...

Gely ɗinsa ta kalli Inuwa wanda ke cikin jami'an tsaro. Ta buɗe baki kaɗan don ta yi magana, domin ta tuna cewa wannan ita ce yarinyar da ta taɓa gani a baya. Amma Chief Onyx ya ɗaga mata hannu alamar ta yi shiru. A yanzu, abin da yake gabansa shi ne bukatarsa, ba ruwansa da abin da bai shafe shi ba...


Sarki Nourdeen ya yi masa iso da su shige cikin fada. Chief yana ƙoƙarin motsawa daga inda yake tsaye...

Sai aka ji wata hayaniya daga can nesa..

 "Ku taimaka mana! Ku riƙe! Wayyo Allah! Ching Ching ki dakata dan Allah!"

Kowa ya juya kansa. Gimbiya Ching Ching ce ta fito daga ɓangaren part ɗinta da gudun gaske a kan doki. Da duk kan alamu dokin ne ya kuɓuce mata, kuma ba ta iya control ɗinsa ba, bata san yadda zata tsayar da shi ba. Dokin sai gudu yake yi, tana ihu kamar ranta zai fita, tana ƙanƙame shi da ƙarfi...

Dakarun da suke tsaronta suna bin dokin da gudu, amma duk sun kasa dakatar da shi. Hankalin sarki ya tashi matuƙa ganin autarsa na shirin hallaka...

Ayat ta zaro manya-manyan idanuwanta cikin tsoro da fargaba.

Dakarun masarautar duk sun kauce wa dokin saboda gudunsa.

Ayat, cikin shigarta ta Inuwa, ta yi ƙarfin hali. Ta ruga da gudu don ta dakatar da dokin. Amma dokin ya yi mata wani irin harbi da ƙafafunsa na baya. ta yi sama, ta faɗo ƙasan floor ɗin masarautar, har goshinta ya fashe...

Dokin bai tsaya ba, ya nufi Chief Onyx kai tsaye dake yanda dokin ya sako kai ko kwana baya sha, ba alamun dakatarwa...

Gely, ganin dokin zai afkawa Boss ɗinta, ta shige gaba don ta kare shi...

Chief Onyx, wanda fuskarsa ke ɗauke da abin rufe fuska na ƙarfen azurfa, ya fusata...
Ya riƙo kunkumin Gely ya manna ta da jikinsa ta gefe, kamar asalin macen da yake ji da ita. Sannan ya kai wani irin mari da tafin hannunsa a kan goshin dokin..

Nan take ƙwaƙwalwar dokin ta juye, ƙafafunsa na gaba suka durƙushe. Ching Ching da ke samansa ta yo gaba kamar zata kifo ƙasi ta fuska sai kuma ta faɗa kan faffaɗen ƙirjin Chief...

Ta riƙe wuyansa da hannu biyu, fuskarta a kife a kan ƙirjinsa, tana shaƙar ƙamshin jikinsa mai daɗi. Ta gama tsorata sosai...

Kowa ya sauƙe ajiyar zuciya. Sarki ya riƙe ƙirji, yana hamdala da sakin numfashi...


Bayan da Chief Onyx ya dakatar da dokin, Ching Ching ta kankame shi tana shakar kamshinsa, amma shi ko gezau bai yi ba..

Ganin yarinyar ta yi lumm a jikinsa kamar wata bishiyar randa, Chief ya janye jikinsa da karfi, ya sake ta daga samansa...

"Timmm!" Haka Ching Ching ta faɗi a ƙasa ba tare da ya kalle ta ba. Ya juya cikin takunsa na gadara, ya nufi cikin fadar Sarki Nourdeen...

Gely tana biye da shi a baya, koda yake ita na'ura ce amma tsarin Artificial Intelligence ɗinta ya nuna wani irin kishin ɓoye ganin yadda wannan yarinyar ta manne wa Boss ɗinta...

​Sarki Nourdeen, cikin tsoro ya daka wa dakarunsa tsawa..

"Ku riƙe min auta! Kada ku bari ta shigo ciki, za ta iya fusata shi. Shi ba mutum ne mai son hayaniya ba!"

​A cikin katafaren falon fadar, iska ta ɗauki shiru, sai kamshin turaren wuta na alfarma dake tashi a sanyaye. Sarki Nourdeen yana zaune tare da babban aminin sa Tafida, da wasu fadawa guda biyu, dukkaninsu jikinsu na rawa...

​A ɗayan bangaren, Chief Onyx yana zaune a kan wata lallausar kujera ta luxury. Idanunsa a kaife suke ba tare da ya kalli kowa ba, sai agogon hannunsa yake kallo cikin matukar miskilanci. Gely tana tsaye a gefensa kamar gunki, ba ta ko kifta ido.

​A waje kuwa Ching Ching tana ta kici-kicin kwacewa daga hannun dakarun da aka sa su tsare ta. Ta duba jikinta ta ga dan ƙurar da ta taɓa ta yayin da Chief ya watsar da ita, nan take ta fashe da kuka. Tana tsaka da kukan ne, sai ta kufce musu...

​Suna tsaka da tattaunawa kan yarjejeniyar da ta kawo su, sai kawai aka ji wani ihu...

"Wayyoo!". Kafin fadawa su ankara, Ching Ching ta faɗo cikin fadar tana kuka da ƙarfi, tana nuna jikinta...

​"Me ya sa ya mun datti da jikina? Ya mun datti! Me ya sa ya mun datti?!" Ta faɗa tana shashshekar kuka...

​Sarki Nourdeen ya zabura ya miƙe tsaye, zuciyarsa ta buga ganin autarsa ta shigo falon a daidai lokacin da yake son lallashin Chief Onyx...

Ching Ching ba ta bi ta kan Chief ba, ta nufi wurin mahaifinta tana kuka tana nuna Chief da yatsa..

​"Daddy! Ka ga wannan bokan ko? Ya faɗar ni ƙasi na yi datti! Kuma sai ya mun wanka!"

Nan take ta fara kici-kicin cire kayanta a gaban kowa domin a wanke mata dattin. Sarki ya yi saurin rike hannunta, fuskarsa cike da kunya da fargaba yana lallashinta...

"Yi hakuri auta, za a yi miki wankan, tsaya kiji..."


​Chief Onyx, wanda ya tsani yawan magana da surutun da ba na hankali ba, ya fara haɗe rai.
Jijiyoyin kansa sun tashi, idanunsa suka fara yin ja..

Ya zo ne don muhimmiyar yarjejeniyarsu, amma wannan yarinyar ta zo ta cika masa kunne da surutun banza da na wofi...

​Lokacin da Ching Ching ta ƙara sauti, tana nuna shi tana cewa...

"Daddy wallahi sai ka kore shi! In ba boka ba me ya sa zai rufe fuskarsa da karfe?..."

​Chief Onyx ya ɗago kansa, wani irin kallo mai firgitarwa ya watsa mata, kallon da ya sa numfashin kowa a ɗakin ya tsaya...

Sannan ya daka mata wata uban tsawa wadda ta girgiza bangon fadar..

​"SHUT UP!!!"

​Daƙin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login