Showing 78001 words to 81000 words out of 154131 words

Chapter 27 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

17 Mar 2026

108

cika kicin..
Masu tsara taruka kuma suna ta kai-komo, suna duba kowane lungu da saƙo don tabbatar da komai ya dace da bukatar gimbiya...

A gefe guda kuma, Gimbiya Maayah tana zaune a cikin ɗakin gyaran jikinta na musamman, wanda aka gina a gefen tafkin wanka mai sheƙi...

Masu aiki uku ne ke zagaye da ita ɗaya na gyara ƙafafunta, ɗaya na kula da farcen hannuwanta, yayin da na uku ke tsara gashinta bisa umarninta..
A daidai wannan lokaci ne Mama Liyatu ta shigo da sauri, tana riƙe da jerin sunayen baƙi, fuskarta cike da damuwa..

“Gimbiya,” ta faɗa cikin ladabi, “an kammala duk shirye-shirye. Mun kawar da tsofaffin ma’aikata da kan iya yin kuskure. Abinci na alfarma an tanada, kuma zauren taro an ƙawata shi da fitilun sarauta na musamman.”

Maayah ta lumshe idonta, tana jin daɗin yadda ake shafa mata ƙafa. Ta amsa cikin sanyin murya mai cike da girman kai..

“Mama Liyatu… wa aka saka a cikin wannan jerin sunaye? Ina fata babu wani marar tsafta ko talaka da ya kutsa ciki. Kin san ƙura na min allergy...”

Mama Liyatu ta gyara muryarta da sauri..

“Na tabbatar miki, Gimbiya. Duk baƙin ’ya’yan manyan jami’ai ne, ’ya’yan ministoci, da ’yan kasuwa masu dukiya.”

Maayah ta buɗe idonta a hankali, ta watsa mata kallo...

“Ki tuna,” ta ce, “wannan taro don nuna aji ne, ba wurin ciyar da jama’a ba.”

Mama Liyatu ta sunkuyar da kai...
“Na fahimta, Gimbiya. Sai dai… Hafsat, ’yar shugaban ƙasa ta nemi izinin zuwa da makwabciyarta wadda ba ta da wani matsayi a birnin.”

Nan take Maayah ta ɗaga hannu, alamar tsayawa, fuskar ta na nuna izgilanci...

“Mama Liyatu! Wannan gidan sarauta ne, ba wurin sadaka ba. Ki ƙira Hafsat ki gaya mata ko dai ta zo ita kaɗai, ko ta zauna a gida. Ba zan yarda mutane marasa aji su ƙazantar min gida ba.”

Mama Liyatu ta fitar da ajiyar zuciya a hankali. Ta san dokar gimbiya ba ta sauyawa. Ba tare da jinkiri ba, ta juya don aiwatar da umarnin...

A lokacin da ake cikin zauren taron, wani ma’aikacin gyaran haske ya yi kuskure wajen haɗa wutar lantarki. Wutar ta ɗauke na daƙiƙu kaɗan kafin a tada generator..

Cikin hanzari, Maayah ta tashi daga kujerarta, fushi ya turnuƙe fuskarta..

“Wane ne ya aikata wannan?! Wa ya yi wannan kuskuren?!” ta daka tsawa...

“Mama Liyatu, ina so a sallame shi nan take! Yana ɓata kyan gidana!”

Ma’aikacin ya durƙusa, jikinsa na rawa.
“Gimbiya, don Allah ki yi haƙuri, ba zai sake faruwa ba.”

Maayah ta watsa masa kallo mai tsauri, babu alamar tausayi a cikinsa...

“Zan ba ka dama guda ɗaya ka gyara kuskurenka. Amma idan wutar ta sake ɗauke yayin taro, zan ɗau hukunci akan ka...”

Ta koma ta zauna cikin natsuwa, kamar sarauniya mai cikakken iko. Ta ɗaga hannu tana umartar mai gyaran farce..

“Ci gaba. Ina so farcen ya yi sheƙi kamar lu’u-lu’u.”

A zuciyarta, Gimbiya Maayah na jin cewa ikon ta ya fi na kowa, kuma a wannan masarauta babu wanda ya isa ya ƙalubalanci umarninta....

Domin tasa a ranta yanzu ta fara gasa da Zayana..

*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 2️⃣3️⃣

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*



Fadar Gimbiya Maayah ta zama Majalisar Ƙasaita a wannan ranar Party ɗin...

Kowane lungu da saƙo an yi masa ado da fitilun zinare masu haske, ƙamshin furanni masu tsada da aka shigo da su daga ƙasashen waje ya cika wurin.. Waƙar Classic Jazz mai ratsa zuciya tana tashi a hankali a cikin babban zauren taro...

Gimbiya Maayah ta fito cikin wata Doguwar Rigar Sarauta mai ƙyalli, wadda ta fi kowane abu a wurin tsada. Da kyar ake iya jure kyawun ta da ajiinta. Tana tafiya a hankali, kamar tana taka gilashi, fuskarta a ɗaure, babu murmushi, ba fara'a...

A lokacin da Maayah ta fara tafiya cikin babban falonta da aka ƙawatar, duk waɗanda suke wurin sun tsaya cak. Aƙalla mutane 50 ne suka duƙar da kai, suna girmama Girman Kan Gimbiya... Ta kalle su, ba tare da ta nuna ko ɗan tausayi ba..

Ta hango wani saurayi wanda shi ne kawai bai duƙar da kai ba, wani Ɗan Gidan Babban Minista mai suna Zaidu.... Zaid ya miƙe tsaye, yana murmushi cike da sha'awar ta...

Maayah ta wurga masa wani irin kallo, tana nuna shi ta ce,

“Kai! Tashi ka bar wurin nan! Na gaya wa Mama Liyatu cewa ban buƙatar ganin talakawa a cikin fadata. Kuma kai, ba ka da gata da za ka tsaya ka kalle ni kai tsaye! Ka fita yanzu, kafin in umarci Bodyguards su kore ka da ƙarfin tsiya.”

Zaid ya firgita. Ya duƙar da kai cikin gaggawa, fuskarsa cike da kunya, sannan ya fita daga wurin taron da sauri, ba tare da ya yi magana ba. Kowa ya ga wannan al’amari ya yi shiru, saboda sun san dole ne a bi dokokin Gimbiya tinda har masarautar ta aka zo..

Ta juya, tana gyara rigarta da hannu ɗaya...

“Mama Liyatu! Meye wannan? Ina nufin an tace jerin sunayen mutane ne kawai don ganin waɗanda suka dace su shigo fadata!”

Mama Liyatu ta matso da sauri, tace,

“Kiyi haƙuri, Gimbiya. Wataƙila an shigo da shi a cikin rukuni ne. Zan tabbatar an ƙara tsananta tsaro!”

A daidai lokacin da Gimbiya Maayah ke cikin kololuwar kasaitarta, cike da girman kai da jin ikon sarauta, Mama Liyatu ta sulale zuwa ɗakin kula da tsaro, domin duba faifan bidiyon Security (CCTV) na ƙofar shiga fadar..

Manufarta ɗaya ce ta tabbatar cewa babu wani talaka ko wanda bai cancanta ba da ya samu damar shiga cikin Fadar Sarauta.
Cikin faifan bidiyon, wani abu mai firgitarwa ya bayyana a idonta.
Ta ga wani mai gadi, sanye da uniform na tsaro, ya shiga wani ɗaki na sirri a bayan kitchen. Bayan ƴan daƙiƙu, ya fito da ƙaramin kwalba mai ɗauke da ruwa. Da sauri ya nufi cikin kitchen, inda aka tanadar da kayan sha na musamman na Gimbiya, ya zuba ruwan cikin gilashin lemun tsami da aka shirya domin Maayah.
Idanun Mama Liyatu suka kaɗa da tsoro. Jikinta ya yi sanyi...

"Guba!?..."

Ba shakka, wannan yunƙuri ne na kashe Gimbiya Maayah.

A dai-dai lokacin nan ne aka ɗauki kayan sha aka nufi inda Gimbiya ke zaune.
Mama Liyatu ta tashi da gudu, tana huci, gumi na tsatstsafowa a goshinta. Ta manta da komai, rayuwar Gimbiya ce kawai a ranta...

Ta kutsa cikin zauren taron a guje, tana rawar jiki. Ta tarar da Gimbiya Maayah ta ɗaga gilashin lemun tsami zuwa bakinta...

“GIMBIYA! Don Allah ki tsaya!!”

Mama Liyatu ta ƙwala ƙira, muryarta na rawa saboda tsananin tsoro..

Maayah ta tsaya cak. Ta ɗauka Mama Liyatu ta zo ne don ta bata mata rai. Ta sauke gilashin a hankali, fuska cike da ɓacin rai...

“Mama Liyatu, me wannan hayaniya take nufi? Kin san ɗaga murya na lalata min walwala!”

Mama Liyatu ta durƙusa a gabanta, hawaye na zuba ba tare da shiri ba..

“Gimbiya ta, don Allah ki yi haƙuri. Wannan lemun guba ne! Wani ya saka miki guba a ciki! Rayuwarki tana cikin mummunan haɗari!”

Nan take hayaniya ta tashi a falon...

Maayah ta yi shiru na ƴan daƙiƙu…
Sai kawai ta tintsire da dariya, dariya mai cike da izgilanci da ɓacin rai...

“Security!” ta ɗaga murya da ikon Sarauta,

“Ku gano wanda ya kawo wannan gilashin. Yanzu nan take!”

Babban Bodyguard ya karɓi gilashin cikin gaggawa, aka kai shi ɗakin bincike. Mama Liyatu ta bayyana abin da ta gani a faifan bidiyo, mai gadi ne ya saka guba...

Ba a jima ba, aka kama mutumin yayin da yake ƙoƙarin tserewa ta ƙofar baya. An dawo da shi cikin falon taron, sanye da uniform na jabu, wanda ya nuna ba ɗan tsaron Fadar Sarauta ba ne..

An daure hannayensa ta baya, yana durƙushe a gaban Gimbiya Maayah..

Maayah tana zaune kan kujerarta cikin cikakkiyar kasaita...

“Ku fita mun daga nan!” ta umarci duk baƙin Party ɗin...

“Wannan ba nishaɗi ba ne hukunci ne na Sarauta!”

Kowa ya fita cikin fargaban kashen gimbiya da ake shirin yi...

An bar Gimbiya Maayah, Mama Liyatu, da Bodyguards guda uku kaɗai a zauren..

Maayah ta ɗaga ƙafarta a hankali. Takalmin mai tsini wanda farashinsa ya kai na motoci da dama ta ɗora shi a kan kafaɗar mutumin da ke durƙushe...

“Yanzu ka gane inda ka shigo ko?” muryarta cike da izgilanci...

“Ka zo Fadar Sarkin Alhamra domin ka kashe Gimbiya? Wa ya turo ka? Wa ya ba ka izinin saka uniform ɗin mu?”

Mutumin ya kasa magana, yana haki saboda tsoro.
Maayah ta danna ƙafarta a kafaɗarsa da ƙarfi...

“Kin ga ko, Mama Liyatu? Rashin ladabi har ya kai wannan matsayi.”

Ta ɗaga ƙafarta, ta kalli Bodyguards ɗinta da tsauri...

“Wannan hukunci na! Ba zan zubar da jininsa a nan ba, saboda kada ya ɓata min wannan falon mai tsarki. Amma rayuwarsa ta ƙare tun yanzu!”

Ta juya zuwa Mama Liyatum..

“Ki kira Masu Gadi na Musamman.Ku tafi da wannan ƙazamin mutumin zuwa Fourth Chamber!
Ku rufe shi a can. Ku tabbatar cewa kafin faɗuwar rana babu wani alamar rayuwarsa a duniya!”

Mama Liyatu ta runtse ido. Ta san Ɗakin Huɗu wuri ne da ba wanda ya taɓa fita da rai...

“An gama, Gimbiya. Za a yi kamar yadda kika ce.”

Maayah ta tashi ba tare da ta nuna ko ɗigon tausayi ba. Ta kalli gilashin guba, ta girgiza kanta...

“A kawo min sabon lemun tsami mai sanyi. A tsabtace wannan falon kamar ba'a taɓa taka shi ba. Party ɗin nan zai ci gaba!”

Ta juya zuwa ɗakin gyaranta...

A bayanta Bodyguards suka ɗauki mutumin, suka nufi Ɗakin Huɗu....

Can Gimbiya Maayah ta sake mamaye falon da kasaitarta...
kamar babu abin da ya taɓa faruwa..
Kudi, iko, da gata sun gama lalata zuciyarta…


A tsakiyar falon, inda aka gyara shi da labulen alharini, wasu Masu Rawa daga Indiya da aka ɗauko na musamman sun fito...

Mata guda uku da maza biyu, sanye da kayan rawa na gargajiya..
Sun fara rawa mai ban sha’awa (Indian Dance) cike da tsari da fasaha, inda suke juyawa da yin motsin kai da ido na musamman....Anan Maayah take zaune a kan Kujerar alfarma mai ƙasaita, tana kallo ba tare da ta nuna ko ɗan sha'awa ba...

Waƙar Indiya mai daɗi ta cika wurin, kuma Masu Rawa na ƙoƙarin nishaɗantar da Gimbiya ta kowace hanya. Sauran baƙin Party ɗin sun yi shiru, suna kallon rawar da kuma Gimbiya, wadda ta fi kowa muhimmanci a wurin...

Ana cikin wannan nishaɗi na ƙasaita sai aka ji wata ɗan hayaniya a babban ƙofar fadar... Hayaniyar ta kasance muryar mutum ɗaya wanda ke masifa da ƙarfi..

Nan take, wani Bodyguard ya shigo da girmamawa ya durƙusa a gaban Maayah...

“Gimbiya, Babban Minista Alhaji Bello yana waje. Ya zo da zafi yana masifa. Yana neman ganin ki a kan dalilin da ya sa kika wulaƙanta ɗansa, Zaid... Muna ƙoƙarin hana shi shiga saboda yanayin zafin ransa.”..

Maayah ta yi murmushi wanda ya nuna cewa ta shirya domin faɗa... Ta ɗaga hannu, ta yi nuni ga Masu Rawar Indiya da su tsaya...

“Ku barshi ya shigo. Idan har Babban Ministan ƙasa zai zo ya yi min faɗa a gidana, to zan nuna masa matakin sarauta da ikon Gimbiya Maayah! Ku barshi ya shigo. Kuma ku kawo Zaid tare da shi.”

Bodyguards suka buɗe ƙofar. Minista Bello ya shigo, fuskar sa cike da ɓacin rai... A bayansa kuma Zaid ne wanda yake duƙar da kansa saboda kunya...

“Gimbiya! Me kika yi haka?! Wa ya ba ki izinin kore min ɗa daga Party?! Na san cewa Sarki baya nan ne, amma wannan bai ba ki ikon wulaƙanta Babban Minista ba! Ni ba talaka ba ne! Ina da kuɗi! Ina da gata!”

Ministan ya fara masifa, muryarsa cike da zafi.
Nan da nan, Bodyguards guda biyu suka matso kusa da Ministan...

“Mai Girma Minista, don Allah ka sassauta muryarka. Kana cikin Fadar Sarauta ne!”

Amma Maayah ta ɗaga hannu....
“Ku kyale shi. Ina son in ji duk abinda yake da shi. Bari Minista ya yi speech.”

Minista Bello ya ci gaba da masifa, har ya kai ga zagin rashin ladabin Gimbiya... Ya rufe da cewa...

“A tunani na, za ki yi hankali. Amma a’a! Kuɗi da gata sun lalata ki!”

Bayan ya kammala, Maayah ta gyara zamanta a kan kujera. Ta lumshe idanunta tana kallon Minista da ɗansa, kamar tana kallon kashi. Ta fara magana da murya mai sanyi mai shiga jiki!...

“Minista, ka kammala? Zan fara da kai, Zaid.... Ka san dalilin da ya sa na kore ka, ko ba haka ba? Bari in tuna maka!”....

Maayah ta kalli Ministan...

“Minista Bello, ɗanka bai san matsayinsa ba! Yana da fitsara! Yana abu irin na ƙazaman mutane!”

Ta sake juyawa ga Zaid...

“Ka zo Party na, sannan ka aiko min da letter na soyayya a cikin makaranta! Letter! Wai kai har kasan soyayya? Ni Gimbiya ce! Ni ba ƴar makaranta ba ce da za a aiko mata letter na soyayya! Wannan wulaƙanci ne!”

Ta kalli Minista Bello, idonta cike da ƙasaita...

“Minista, ka ce kana da kuɗi da gata? To, ikon sarautata ya fi kuɗin da gatanka! Kuma a cikin wannan fadar, ni ce Sarauniya! Kana gani? Ka raina ni ne saboda mahaifina baya nan? To, ka sani, babu wanda Gimbiya Maayah take jin tsoro a duniya! Ko Shugaban Ƙasa ne! Idan har ɗanka ya sake min kallo na soyayya, ko kuma ya sake zuwa kusa da ni, to zan kore ka Minista! Zan cire maka mukaminka har abada!”

Ta ɗaga hannu...

“Bodyguards! Ku fitar da waɗannan mutanen marasa aji daga nan! Kuma ku tabbatar ban sake ganinsu ba a cikin Fadar masarautar Alhamra har abada!”...

Minista Bello da ɗansa Zaid sun ji matukar kunya da kuma tsoro! An ja su da ƙarfin tsiya daga cikin taron...

Maayah ta jingina a kujerar ta, fuskar ta cike da nasara...

★★★

Bayan korar Minista Bello, Fadar Maayah ta koma shiru, amma tashin hankali ya mamaye zukatan baƙin da ke wurin, sam babu wanda ya ji daɗin wukaƙancin da Maayah tayi wa minista....

A kan kujerar ta, ta jingina, fuskarta cike da baƙin ciki da gajiya....

​“Mama Liyatu, raina fa ya sosu,”

Maayah ta yi magana da murya mai sanyi...

“Wannan Party ya zama cikin kasala! Ba ni da farin ciki! Komai a gidan nan yana da tsari, amma babu nishaɗi.”

​Mama Liyatu ta durƙusa, hannunta a ƙirji...

“Allah ya taimaki Gimbiya, ya huci zuciyarki mai jiran gado. Komai zai daidaita.”

​Maayah ta juya kai...

“Ba wannan nake so ba! Ina so a nemo mun wasu mutane masu barkwanci! Waɗanda za su iya sanya raina nishaɗi! Ina so in manta da wannan ƙazantar mutanen da suka fita..!”

​Mama Liyatu ta yi saurin miƙewa...

“An gama, Gimbiya! Za a nemo miki ƙwararru! Allah ya taimaki Gimbiya mai jiran gado!”

​“Duk wanda ya sanya ni farin ciki,”

Maayah ta ƙara,

“yana da kyauta mai tsoka! Har da mota da gida! Amma idan ka ƙara ɓata min rai… za ka ga tashin hankali!”

​Nan take, aka sanar a birnin cewa Gimbiya Maayah tana neman masu barkwanci don sanya ta farin ciki, kuma kyauta mai tsoka na jiransu....

Cikin ɗan gajeren lokaci, mutane kusan talatin masu neman kyauta suka cika ƙofar Fadar..

​Maayah ta kalle su ta faifan bidiyo (CCTV)...

“Mama Liyatu, ina buƙatar nishaɗi, ba tattara datti ba! Ba na buƙatar yawan wannan ƙazanta! A zaɓi mutum biyar kawai masu ɗan tsabta a ciki. A korar sauran da bulala don su san cewa Fadata ba gidan wasan kwaikwayo ba ce!”

​Hakan kuwa aka yi. Bayan minti talatin, an kawo masu barkwanci guda biyar a gaban Gimbiya Maayah, dukansu sanye da sabbin tufafi kuma suna cikin tsoro...

​Maayah ta zuba musu ido ɗaya bayan ɗaya...

“Shin zaku iya sanya ni farin ciki? Ni ba kamar sauran bane, ni Gimbiya Maayah ce. Ku san cewa ina da wuya wajen dariya.”

​Ta sake ɓata rai...

“Duk wanda bai sanya ni nishaɗi ba, zai sha bulala 50 a gaban kowa! Kowa zai fito, cikin minti ɗaya ya yi barkwancinsa. Idan kuma duk ku ka sanya ni farin ciki, zan baku kyauta mai tsoka gaba ɗaya!”

​Dukansu mutum biyar ɗin suka hadɗiye yawu cikin tsoro...

​Na Ɗaya:

Wani saurayi mai ɗan lukuti ya fito.... Ya fara rawa ta barkwanci yana lanƙwasa jiki, ya fara wata baƙon sauti kamar kukan akuya...

​Maayah ta sauƙe kai, ta toshe kunnenta da hannu...

“Mama Liyatu! Wane ne wannan? Meye wannan sautin na dabba? Ya ɓata min rai! Ku janye shi! Kuma ku tabbatar ya sha bulala 50 kafin ya fita daga gate ɗin mu!”

​Nan take, Bodyguards suka ja shi da ƙarfi, ya fara neman gafarar su...

​Na Biyu:

Wani dattijo ya shigo, ya fara salon sa na tsohuwar barkwanci ta hanyar ƙoƙarin yin yabon Maayah ta ƙarya...
​Maayah ta zuba masa ido. Hawaye suka fara zuba mata, na baƙin ciki da bacin rai...

“Ku! Meye wannan? Kuna nufin baƙin ciki yake so ya sanya ni? Wannan ya fi mai yunkurin kisa ɗin nan ɓata min rai! Ku koreshi! Bulala 50!”

​Na Uku:

Wani mai tumbi ya shigo, ya sanya wani abu a baya da ya ƙara masa girman ɗuwawu. Ya fara lanƙwasa jiki yana motsa tumbin sa da duwawun sa a salon wasa...

​Maayah ta fara ƙoƙarin amai! Ta rufe bakinta da hannu....

“Wai ku! Meye wannan ƙazantar banza! Wannan datti ne! Wannan cin zarafin Sarauta ne! Ku cire min shi daga nan! Bulala 60 saboda ya sanya ni amai...!”

​Na Huɗu:

Wani saurayi mai ƙarfi ya shigo. Ya fara ƙirari da yabon Sarauta da gata...

“ƴar Sarki jikar Sarki! Taka lafiyarki, ƴar gata! Hasken birnin Alhamra!” Haka ya ci gaba da yi da girmamawa mai yawa...

​Maayah ta kawar da kai cikin gajiya...

“Wannan kirari a kowace rana ana min! Idan ma ba a yi min ba, sai an ga tashin hankali! Don haka, kaima ka ban wuri! Ka tafi! Babu wani abu na musamman a cikin kirari! Bulala 50!”

​Na Biyar:

Shi ne mafi tsoro a cikin su. Ya ga yadda Gimbiya Maayah take ba da hukunci. Ya shigo, duk jikinsa na rawa, ya durƙusa a gaban Gimbiya. Yana kuka cike da tsoro!

​“Dan Allah ki yi haƙuri! Na san ba zan iya sanya ki farin ciki ba! Wallahi inada Basir! Zai iya motsa wa saboda wannan tsoron! Ga tamowar da ke damuna! Wayyo Gimbiya! A gafurce ni...bulala hamsin zan iya rasa rayuwata ga iyalai..."

​Nan take, Gimbiya Maayah ta fara dariya! Dariya ta gaske,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login