Showing 108001 words to 111000 words out of 154131 words

Chapter 37 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

kuwa, rayuwar Ching Ching tana rataye ne tsakanin rai da mutuwa.
A wannan ranar an shawo kan Ching Ching dake kwararrun likitoci ne a asibitin...nan danan suka gama..

✨✨

*Washegari*
Haske na safiya yana ratsawa ta tagar ɗakin a hankali. Na’urorin asibiti suna fitar da ƙananan ƙara masu natsuwa. Chief Onyx yana zaune a kujerar gefen gadon, idanunsa sun nuna alamun gajiya, domin bai ko motsa ba, hannunsa yana riƙe da na Ching Ching kamar zai ɓace idan ya sake ta...

Ching Ching ta motsa kaɗan, sai ta buɗe idanunta a hankali. Da farko duhu ta gani, sai fuskar Chief Onyx ta bayyana a gabanta. Ta ɗan lumshe ido, sannan ta yi murmushi mai cike da rauni...

“Uncle…”

ta ce da muryar da ke fita da ƙyar, “yanzu na zama jaruma ko? Ba ‘yar aiki kaɗai ba?”

Onyx ya sauƙe ajiyar zuciya, ya matse hannunta a cikin nashi, yana kokarin yin murmushi. Ya sunkuya ya sumbaci goshinta a hankali..

“Fiye da hakan, Ching Ching,” ya ce cikin tausayi.
“Ke ce zuciyar fadar Chief Onyx.”

Ta turo baki kamar yarinya ƙarama, idonta fari sol cike da barkwanci duk da rauninta..

“To… to kai ɗin mijina ne?”

Chief Onyx ya zaro ido da sauri..

“Eh? A’a! A’a!” ya ce cikin hanzari. “Ke yarinya ce, baki girma ba.”

Ta ɗan ɗaga gira, ta ce,
“To wacece zata zamo matarka ta haifa maka yara?”

Ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, sai kuma murmushi ya zauna a fuskarsa..

“Ke zaki zaɓa min da kanki.”

Nan take ta tintsire da dariya, duk da ƙirjinta yana ɗan mata zafi...

“Idan ka fita dani yawo, zan nema maka kyakkyawa… amma fa sai mai kirki!”

Onyx ya shafa kanta a hankali, ya gyara mata gashin kanta..

“Shikenan,” ya ce cikin murmushi mai cike da ƙauna..

A wannan lokacin, likita ya leƙo ta ƙofa yana kallon su da mamaki..

“Sannu patient,” ya ce yana girgiza kai, “an samu sauƙi kenam.”

Ching Ching ta juya kai ta ce,
“Likita, ka gani ko? Ni ba mara lafiya ba ce… ni special guest ce!”

Chief Onyx ya yi murmushin gefen baki kamar yadda ya saba idan yana tare da ita...

Bayan kwana 5 da kwanciya a asibiti, jikin Ching Ching ya murmure sosai. Likitoci sun sallame ta. Wannan ne karon farko da ta fito daga cikin fadar pavilion...

Bayan barinsu Hospital kai tsaye super shop suka nufa, zasu yi siyayya kafin su wuce gida..

Motar Chief Onyx mai tsaron kansa ta tsaya a harabar Super market.. Ƙofar ta buɗe a hankali, Gely ta fara sauka, idonta na scanning ko’ina kamar yadda aka saba.. Bayan ta tabbatar da komai lafiya, ta buɗe ƙofar baya...

Ching Ching ta sauko cikin fara’a, tana kallon ginin birnin kamar yarinya da aka kai ta sabuwar duniya...

“Wow…” ta furta, “ashe Pavilion City ba kawai labari ba ne...”

Chief Onyx ya tsaya gefe ɗaya, cikin baƙaƙen suits ɗinsa ta shugabanci, fuskar nan tasa tana nan cikin tsauri da natsuwa...

Mutane na wucewa suna gaishe shi cikin girmamawa, wasu ma na sunkuyar da kai. Mata da dama suna ɓoye kallonsa, amma shi ko ɗago ido bai yi ba...

Shugaban Pavilion City gaba ɗaya, matashi mai jiji da kai, kwarjini da girman kai. Kyawunsa ba abin jayayya ba ne, kuma shiru da sanyi da halayensa sun hana kowace mace kusantarsa. Ba ya kallon mata, balle ya bari zuciyarsa ta yi tunani a kansu...

Ta juya ta kalli Chief, ta ce,

“Uncle, mutane suna kallonka kamar ana kallon zinare a kasuwa.”

Ba tare da ya kalleta ba, ya ce a taƙaice,
“Ki yi tafiya a hankali.”

Ta murmusa, ta ce,
“Uh uh… ka ji yadda yake magana kamar robot, amma robot ɗin ma ya fi ka jin tausayi.”

Gely ta ɗan juya kanta, ta ce cikin murya ta robot,

“Correction... Boss yana da tausayi… amma ga ke kaɗai.”

Chief ya tsaya cak, ya kalli Gely...

“Gely.”

“Noted, Boss.” ta furta tare da yin gaba..

Ching Ching ta fashe da dariya..
“Kin gani ko? Yana abu kamar duniya aka ɗora masa a kai..!”

Ya ci gaba da tafiya, amma a karon farko, wani ƙaramin murmushi ya bayyana a gefen bakinsa, murmushin da bai ma lura da shi ba...

Sun shiga wani tsararren super shop mai ɗaukar ido, gilashi masu sheƙi suna sarrafa kansu ga kuma fitilu masu walƙiya da kaloli mabanbanta, ga kayan alatu da ba kowa ke iya saya ba...

Ƙofar ta buɗe kai tsaye da na’ura, jama’a suka juyo a lokaci guda.
Bodyguards masu baƙaƙen kaya suka zagaye su, suna tafiya cikin tsari. Gely tana gaba, idonta na scanning kowane motsi. Duk wanda ke shop ɗin ya san Chief Onyx ya shigo...

Matan dake cikin shop ɗin suka tsaya cak. Wasu na masa kallon sha'awa da burge wa, wasu kuma na gyara tsayuwarsu, wasu kuma suka fara kallon Ching Ching cike da hassada...

“Wacece ita?”
“Me yasa ita ce kusa da shi?”
“Me ye matsayinta a wurinsa?”

Ching Ching kuwa idonta na kan kayayyaki..
Ta ga kayan ado masu sheƙi idonta suka haskaka..

“Uncleee! Ka ga wannan?”
Ta ɗauki abin wuya..
“Da wannan?”
Ta ɗauki zobe..
“Wannan kuma fa?!”
Ba ta jira amsa ba ta ci gaba da ɗauka tana ajiyewa a cikin trolley kamar yarinya a kasuwar kayan zaƙi...

Chief Onyx yana tafiya a bayanta cikin shiru, fuska a ɗaure. Bai ce komai ba, amma kowa da ya san shi, ya san wannan shiru ba alheri ba ne...

Matan shop ɗin suna kallon Ching Ching suna harararta duk da sun ji tana ƙiransa da Uncle..

“Ta ɗauka kamar komai nata ne anan wurin.” wata ta furta tana harararta domin ba'a san iya adadin matan da suke ƙaunar Onyx ba..

“Da shi take magana wai? Na ga ko ta kanta baya bi...”

Wata ta ba da amsa, "ta ya zai kula ta, kalan a raina shi, wannan kucakar yarinya ƴar hau..."

“Ai ba ta kai ya kula ta ba wallahi....”

A gefe guda kuma,
Ching Ching ta ɗauki wata rigar zinariya, ta ɗaga ta sama ta ce da ƙarfi,

“Uncle, wannan zata yi min kyau ko?”

Chief ya tsaya tare da wurga mata kallo ta gefen ido...
“Ki ajiye.”

Ta turo baki, ta ce,
“Me ya sa? Kana da kuɗi fa.”

Nan take iska ta canza.
Ya matso kusa da ita, yana zaro mata ido...

“Ba batun kuɗi ba ne.”

Ganin tana shirin zubar masa da girma yasa ya barta ta ɗauka...

Haka ta nufi wurin ciye-ciye taita jidan cake da sweet da abubuwan zaƙi...

Shiru ya lullube shop ɗin.
Sai kuma kuskuren da Ching Ching ta yi...
Ta juya, ta kalli wata mace dake tsaye gefe, sannan ta ce cikin ɗaga murya..

“Kin ga wannan? Shi ɗin mijina ne, Shi ne yake biya min komai... Wallahi kuwa...”

Tsit wurin yayi ana sauraronta..
Kamar an danna maballin tsayar da lokaci..
Chief Onyx ya ɗaure fuska gaba ɗaya.
Idonsa ya sauya, jijiyoyin wuyansa suka fito. Ya kamo hannunta da ƙarfi, cikin tsaurin iko ya furta...

“Na ce miki meye? Ni za ki kalla kice mijinki? Kina nan kwaila dake, me ya sa kike son zubar mun da kima ne? To ki kama kan ki, ni ba abokin wasan ki bane...”

Ta ɗan tsorata, ta ce,
“Uncle… wasa nake fa.”

Ya sunkuya kaɗan, ya kalleta kai tsaye cikin ido...

“Ni bana wasa da sunana.”

Ya juya ya kalli Gely.
“Gely. Mu tafi....Yanzu.”

Gely ta amsa nan take,
“Yes, Boss.”

Bodyguards suka matsa gaba, jama’a suka rarrabe gefe-gefe kamar ruwa..

Ching Ching ta tsaya cak, murmushin ya ɓace daga fuskarta. A karo na farko, ta gane cewa ta taka layin da bai kamata ba..

Sauran ƴanmatan kuwa dariya su ka shiga yi bayan fitar Chief,
"Waii miji....Su miji manya.."

Ching Ching bata ko kula su ba, itama ta fice..sauran kayayyakin da ta ɗauka duk an biya, wani bodyguard ne ya ji do su...

A cikin motar, Chief bai ce kalma ɗaya ba.
Ching Ching ta kalli gefensa, zuciyarta na bugawa...
“Na ɓata masa rai…”
Ta furta a cikin ranta...

A cikin motar alfarma, shiru ya mamaye ko'ina, Chief yana zaune gefen Ching Ching, fuska a daure, idanu na kallon gaba kamar ba kowa a gefensa..

Motar ta ratsa wani tsararren titi mai yalwa. A gefe, wani babban private school ya bayyana, ginshiƙai masu sheƙi, ƙofar zamani, fitilu masu launi..

A nan ne ɗalibai suka fara fitowa, sanye da uniform masu tsabta, suna wasa da dariya, ko wacce na magana da ƙawarta, wasu suna tafe da jakunkuna a bayansu... Bus ɗin makaranta na jiran su, ƙofar a buɗe..

Idanun Ching Ching suka manne a wajen ba tare da wani motsi ba..

Murmushi ya fara tsiro a fuskarta, murmushin da ba na wasa ba, sai na tsantsar buri...
Ta matso kusa da gilashin motar, tana kallon yadda ɗaliban ke hawa bus ɗin cikin farin ciki..

Ta ɗan ɗora hannunta a kan gilashin, kamar tana so ta taɓa abin da take gani..

“Uncle…” ta fara cikin murya mai sanyi...

“Ka gan su ko?”

Chief Onyx bai ko juyo ba, bai kuma amsa mata ba...

Ta ci gaba, kamar tana magana da kanta...

“Wallahi suna da sa’a sosai.”
Ta yi dariya kaɗan, mai ɗauke da wani irin baƙin ciki..

“Ni fa… ban taɓa shiga irin wannan bus ɗin ba.”

Ta waiwaya ta kalle shi, tana sa ran zai kalle ta.
Amma yana nan yadda yake, cikin shiru da ƙasaita, fuska na kallon gaba...

Ta sake murmushi, ta fara magana a hankali kamar yarinya da ta samu abin da ke faranta mata rai..

“Idan na shiga makaranta fa, zan zauna a gaba. Zan ɗaga hannu kullum. Zan yi rubutu sosai. Zan samu abokai da yawa…”

Ta yi tsallen tunani, ta ce cikin dariya..
“Watakila ma zan zama mai hayaniya a aji!”

Ta yi shiru na ɗan lokaci.
Sannan ta ƙara da murya mai rauni..

“Amma ban taɓa zuwa ba.”

Motar ta ci gaba da tafiya.
Suka bar Bus ɗin makarantar a baya..

Chief Onyx har yanzu bai kalle ta ba.
Amma a cikin zuciyarsa wani abu ya motsa.
Hannunsa ya matse a hankali a kan cinyarsa.

Ching Ching ta koma ta jingina da kujerar, murmushin yana nan, amma idanunta sun ɗan yi ruwa.
Ta ce cikin raha, tana ƙoƙarin ɓoye abin da take ji..

“Da ace ina makaranta, da na zama shahararriyar ɗaliba. Kai ma da zaka zo Parents’ Day ka zauna ka yi shiru kamar yadda kake yi yanzu.”

Ta juya ta kalle shi..

“Kai kuwa ka je makaranta a lokacin da kake yaro ko? Kana son abin da nake nufi ko? Playground, library, school uniform mai kyau… duk abin da ke cikin movies na ke so in gani a gaske...”

Ta yi murmushi, ta kuma cewa..

“Ni ma na so in sami classmates da za su zama abokaina, in yi exams da su, in sami certificate… ba wai kawai ilimin gida ba...”

Haka ta rinƙa surutu ita kaɗai..

Motar ta nufi gida.
Amma tunanin makarantar…
ya riga ya shiga zuciyar Chief Onyx..



Bayan kwana biyu, yanayi ya sake sauyawa...

Chief Onyx yana cikin wurin wankansa na sirri, yana ta ninkaya cikin ruwan private pool ɗin da ke kewaye da furanni da shuke-shuke masu tsada..

Jikinsa babu komai sai gajeren wando, wanda ya bayyana ƙarfinsa da jarumtarsa. Ruwan yana rufe faffadan kirjinsa yayin da yake shawagi a ciki cikin natsuwa..

Bayan ya ɗau mintuna a nutse cikin ruwan, da ga bisani ya ɗago ya sa hannu yana matse ruwan gashinsa da ya jiƙe, yana tsaka da wasansa sai ga Chingching ta bayyana ɗauke da tsintsiya da bokiti... Ta shigo tana rera wata waƙa da ƙarfi, kamar ba ta san inda take ba, wai ita a dole shara ta zo yi a daidai wannan lokaci!..

_“Sharar da ke da kyau, sai a yi shi a lokaci mai kyau…_
_Idan lokaci ya zo, sai a yi shi ba tare da jawa ba!”_

Waƙar da take rerawa kenan 😅

Onyx ya tsaya cak, ruwa na saukowa daga jikinsa. Ya kalleta cikin mamaki, sannan ya haɗe rai kaɗan, duk da cewa akwai murmushi da ya ɓoye a fuskar sa...

“Ke kuma,” ya faɗa cikin sanyin murya,
“sharar me kika zo yi a nan? Kin san sarai wannan lokacin nawa ne na shakatawa.”

Chingching ta ɗage kai, ta fara share ƙasa alhalin babu ko ƙura. Ta turo baki tana cewa..

“Aiki na ne ai, Uncle.... Gani nayi wurin nan ya fara datti. Ni ban son ganin datti. Ka ci gaba da wankanka, ni sharata zan yi na wuce.”

Sai dai duk da maganganunta, idonta na satar kallon jikinsa, zuciyarta na buga mata wani irin bugun da ba ta saba ji ba..

A hankali, ya fito daga cikin ruwan sharkaf, ya tsaya da ɗan takaitaccen taku a gabanta. Faffadan kirjinsa yana kyalli, ruwa na digowa a hankali. Ya sunkuya kaɗan, ya kalleta kai tsaye cikin ido, muryarsa ta sauya ta zama ƙasa-ƙasa..

“To tunda sharar kika zo yi, kuma baki son datti…
ki share jikina.”

Nan take Chingching ta ruɗe.
Ta tsaya tana nuku-nuku, hannayenta na wasa da juna, idonta a ƙasa...

Fuskarta ta fara canja launi saboda kunya da fargaba. Ta kasa motsawa, balle ta miƙa hannu ta taɓa shi.
Onyx ya lura da rikicewarta. Wani gajeren murmushi ya leƙo a gefen leɓɓansa.
Cikin ƙiftawar ido, kafin ta ankara, sai kawai ya sa hannu ya damko kunkuminta, ya ɗaga ta sama kamar yar tsana ya cilla ta tsakiyar pool ɗin...

Ruwa ya tashi sama, ya yayyafa ko’ina. Sai da ta nitse gabaɗayanta kafin ta ɗago tana faman fyace ruwa. Onyx kuwa tuni ya ɗauki tawul, ya rataye shi a wuya, yana kallonta cikin murmushi...

“Wannan ne ladan sharar da kika zo yi,” ya faɗa yana dariya a hankali..

Ya juya zai tafi.
Da ta ga hakan, ta zauna a cikin ruwan, ta fara kukan shagwaba, tana buga ƙafafunta a cikin ruwan...

“Haba Uncle! Don Allah ka dawo! Ka taimaka min! Ka duba yadda ka jiƙa ni, ni ba zan iya fitowa ba!”

Ta yi tsammanin zai tausaya ya dawo kamar yadda take gani a fina-finai...

Amma ina!
Onyx ko waiwaya bai yi ba. Ya ci gaba da tafiyarsa cikin natsuwa, har ya ɗaga mata hannu alamar ban-kwana, sannan ya ɓace daga wurin..

Nan take ta gane wasan ya zama gaske.
Ta tsagaita kukan, ta share idonta, tana kallon hanyar da ya bi. Ta murguɗa baki tana gunaguni..

“Lallai mutumin nan mugu ne ashe… ya bar ni a nan ni kaɗai, alhalin ya san ban iya ninkaya sosai ba.”

Ta fara jan jikinta a hankali, tana lallabawa har ta fito daga ruwan. Rigarta na ɗigar da ruwa, gashinta manne da fuskarta...fuskarta cike da ɓacin rai...
Ta zauna a gefen ruwan, tana huci...

“Wallahi sai ya ji irin abun da na ji… ba bashi a tsakanin mu saina rama....”

“Amma dai,” ta faɗa tana tsuke baki,
“sai na rama.”

A wannan lokaci…
Chief Onyx ya riga ya bar wurin pool ɗin tun da dadewa.
Ya shiga sashensa na kwana...
Wurin ya kasance shiru, tsabta, babu komai face kamshin turare mai sanyaya rai..

Ya cire tawul ɗin jikinsa.
Ya tsaya gaban madubi na ɗan lokaci, fuskar nan tasa, ba murmushi ba kuma fushi a fili..

Ya fara shiryawa cikin kaya masu tsada da tsari..
Ya lanƙaya agogon da kowa ke tsoro idan ya gani, da kuma takalmin da ke sa kowa ya san mai iko ya zo..

Gely ta bayyana a gefensa.
“Boss, motoci sun shirya.”

“Mu tafi.” ya furta a daidai lokacin da ya gama shirinsa...

Yana tafe, Gely na biye da shi a baya..

Bayan mintuna akan tsararren kwalta, motocin suka tsaya gaban babbar makaranta mai katanga ta alfarma..ga tambarin makarantar da tutoci na ƙasashe daban-daban suna kaɗawa a iska...

SUNAN MAKARANTAR... AURELIUS CROWN INTERNATIONAL ACADEMY
(Elite Boarding School for Global Leaders)

Makarantar da ba a biya da nairori sai tsantsar zunzurutun daloli kaɗai..

Makarantar sai ‘ya’yan shugabanni, sarakuna, attajirai, da ‘ya’yan jakadu ne kaɗai ke nan..

Bayan aka ga tambarin Chief Onyx, jami’an tsaro suka miƙe tsaye..
Ba tare da tambaya ko bincike ba.... Suka buɗe ƙofa kai tsaye..

Shugaban makarantar da kansa ya fito, tsoho ne mai farin gashi, fuska cike da annuri da ladabi ya furta..

“Your Excellency, Chief Onyx.”

Ya sunkuyar da kai.
“Abin alfahari ne samun zuwanka.”

Onyx ba tare da ɓata lokaci ba ya sanar da shi cewa,
“Na zo ne domin registration.”

Idanun shugaban makarantar suka buɗe..
“Cikakke?”

Domin ba kowa ke biyan full a lokaci guda ba, wani duk da kuɗinsa sai ya raba sau biyu, wani uku...

“Cikakke,” Onyx ya amsa a taƙaice..

Suka shiga babban ofishin makarantar.... Aka buɗe computer da ake tura kuɗi ta cikinta daga nan ya wuce babban bankin duniya...

Adadin ya bayyana a allon kwamfuta, ga daloli masu nauyi.
Adadin da zai sa yawancin iyaye su faɗi daga kan kujerun su...

Ba tare da tambaya ko jinkiri ba ya furta..

“Done,”
Cikin mintuna kaɗan, an kammala biyan kuɗin makaranta, uniform, litattafai da komai da komai da sunan Ching Ching...wato Firdousee Muhammad Nourdeen...

Shugaban makarantar ya yi murmushi cike da girmamawa...

“Dalibar za ta fara nan da nan. Makarantarmu tana alfahari da wannan suna.”

Onyx ya miƙe tsaye yana furta.
“Ba don suna na ba, sai don makomarta...”


✨✨✨✨

Bayan dogon lokaci, Sarki ya dawo masarauta cikin kwarjini da izzah. Nan take ya bayar da umarnin taron gaggawa na duk gimbiyoyinsa. A cikin fadar, an jera kujeru na alfarma, kowacce da kalar da ta dace da asalin gimbiyar da za ta zauna akai...

(Kamar yadda muka ce a last Page)

Kuma a lokacin Ayat a matsayin Inuwa tana wurin Master suna tattauna wani batu..
Jin sanarwar sarki yana son ganin GIMBIYOYINSA yasa ƙirjinta bugawa, tasan dole za'a je duba ta...

Shin ya zatayi ga master ya riƙe ta?..

Ta saddaƙar yau kam asirinta zai tonu domin za'a sanar cewa babu Gimbiya Aayat...
Tana ta jira taji wannan sanarwa..
Ta saddaƙar sosai..domin tana tsaka da aiki da master Ibrahim..
Sai addu'o'i take ta jerowa..

Daga can nesa, sautin motocin alfarma ya fara tashi... Masu shelar masarauta suka gyara muryoyinsu a lasifika..

Motar gimbiya Zayana ce ta tsaya fara sol, ta fito..

Mai shela ya fara ƙirari..

_"Haske uwar haske! Kyakkyawa ba gajiyawa. Sarauniyar sanyi, farar mace mai kyan hali da kyan jinsi. Jinin turawa, asalin Turai, wadda kyanta ya haska fadar Alhamra. Barka da isowa, Gimbiyar Alfarma, Zayana!"_

Mota kalar ruwan gwal ta bayyana, wato gimbiya Maayah..
Mai shela ya barke da cewa,
_"Zinariyar fada, asalin Indiya! Kyakyawa mai gashin kwance, wadda idanunta suka fi taurari haske. Ɗiyar Taj Mahal, mai tafiyar kyan gani. Maayah, tauraruwar dake haska duhun fada, barka da isowa!"_

Can sai ga
Gimbiya Yumna, motarta kalar silk ta tsaya... Itama aka fara mata ƙirari..

_"Bishiyar inuwa, Gimbiyar Fulani! Kyakyawa doguwa, mai hancin siffa. Farar fulani, uwar dangi, wadda kwarjininta ya cika fada. Yumna, bishiyar da kowa ke son ya huta a inuwarta, barka da isowa!"_


A ofishin Master Ibrahim, Ayat wato Inuwa tana tsaye, ƙafafunta suna rawa... zuciyarta na bugawa domin a yanzu ko wace gimbiya an kawo ta fadar sarki da mota, duk sun kammala amma babu gimbiya Ayat...

Lokaci guda ta ji an fara ƙiran sunan Gimbiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login