Showing 90001 words to 93000 words out of 154131 words

Chapter 31 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

ba yanzu, nuna isa take yi da kuma nuna cewa ita ta fi kowa saninsa...

Ching Ching ta gane cewa abin da Gely take alfahari da shi, shi ne sanin sirrin Chief da kula da na'urorinsa. Ta yanke shawarar cewa yau, sai ta sanya hannunta a cikin babban sirrin Chief domin ta nuna wa Gely cewa ita ma tana da daraja.

Ta san cewa akwai wani akwati na musamman (Safe Box) a cikin ofishin Chief, inda yake ajiye manyan takardu da wasu tsofaffin abubuwan tarihinsa. Ching Ching ta lura cewa ko yaushe Gely take buɗe shi, tana amfani da lambobi ne...

A yau, lokacin da Chief ya shiga wanka, Ching Ching ta sallaɓa ta nufi ofishin..

Ta tarar da Gely a tsaye a gefe tana goge wasu kyamarori. Ching Ching ta wuce ta da wani irin takun isa, ta nufi bangon da akwatin sirrin yake..

"Me kike ƙoƙarin yi, Shugaba Ching Ching?"

Gely ta tambaya ba tare da ta kalle ta ba. "Wannan akwatin ba na wasan yara ba ne."

Ching Ching ta yi dariyar mugunta.

"Wasan yara? Lallai gwangwanin nan, baki sani ba ne? Jiya da dare, Chief ya raɗa min lambobin sirrin nan a kunne na lokacin da yake sumbata ta. Ya ce ni ce kaɗai ya aminta da ita."
tana son gani ko Gely za ta harzuƙa..

Gely ta daina goge kyamarar, ta juyo ta zuba wa Ching Ching ido...

"Chief ba zai taɓa yin hakan ba. Lissafi na ya nuna kina ƙarya."

"To ki gani!" Ching Ching ta fara danna lambobi a jikin akwatin. Ta tuna ranar da ta ga Onyx yana latsawa, ta lura da wasu lambobi guda hudu. Ta danna.. 1-9-9-5...

Tiii-tiii-tiii! Akwatin ya buɗe! Ching Ching kanta ta firgita da ganin akwatin ya buɗe, ashe dai hasashen ta ya zama gaskiya!

Gely ta matso da sauri, idanunta suna walƙiya. "Ta yaya kika san lambobin nan? Wannan lambobin ranar haihuwarsa ne ta asali!"

Ching Ching ta ga ta samu nasara, ta yi gwalo ta ce,

"Na faɗa miki, Chief ya aminta da ni. Kuma ma... dubi abin da yake ciki."..

Ta sanya hannu ta ɗauko wani tsohon hoto na Chief Onyx sa'ilin da yake matashi, tare da wata mata kyakkyawa... Ching Ching ta zaro ido, ta kalli hoton, sannan ta kalli Gely...

"Wace ce wannan? Kuma kamar Aunty Yumna, kodai kamanni ne? A'a kama ne ashe..."

Gely ta matso kusa, ta zare hoton daga hannun Ching Ching...

"Wannan sirrin Chief ne. Kuma tunda kika buɗe wannan akwatin, kin janyo wa kanki babban hukunci."

Daidai nan, Chief Onyx ya shigo ofishin, yana sanye da rigar sanyi, ruwa yana ɗiga daga gashinsa. Ya ga akwatin a buɗe, ya ga hoton a hannun Gely, ya kuma ga Ching Ching a tsaye tana rawa...

"Meye kuke yi a nan?" Onyx ya daka wata uwar tsawa wadda ta sanya duka ofishin ya yi tsit...

Ching Ching ta tsorata ta ɓoya a bayan Gely, ta ce cikin muryar kuka..

"Uncle! Wannan gwangwanin ce ta ce na buɗe mata akwatin, wai tana son ganin abin da yake ciki!"

Gely ta juyo ta kalli Ching Ching, ta yi shiru na dakiku biyu, sannan ta kalli Chief...

"Boss, Shugaba Ching Ching tana iƙirarin cewa kai ne ka ba ta lambobin sirrin lokacin da kuke... sumbatar juna."

Onyx ya matso kusa da su, fuskarsa ta sauya kamar gajimare. Ya kalli hoton matar nan wanda kana ganin kasan mahaifiyarsa ce, sannan ya kalli Ching Ching. Wannan karon fushin nasa ya wuce na kowane lokaci....

Falon ofishin ya yi tsit, sai numfashin Chief Onyx da yake fita cikin zafin rai...

Ya ɗaga yatsansa, ya nuna Ching Ching da shi, muryarsa tana fita a dashe saboda tsananin fushi...

"Na fahimci sake miki fuskar da nake yi da kuma ƙyale ki da nake yi kina shiga jikina, shi ne ya sanya kika manta ke WACECE a nan ko?"

Ching Ching ta fara girgiza kai tana son yin magana, amma ya dakatar da ita da wani kaifaffen kallo...

"To bari na tuna miki! Ke 'YAR AIKI ce a nan! Kada ki sake, na ce kada ki sake gigin shiga cikin rayuwata ko sirrina daga yau. Ki ci gaba da aikin da aka kawo ki yi, domin babu wata alaƙar da take tsakaninmu da za ta ba ki ikon shiga sirrin rayuwata. Fice min daga ofis yanzu!"

Ching Ching ta fashe da kuka, wannan karon kuka ne na kunya da baƙin ciki. Ta juya da gudu ta fice tana kuka mai sauti, ta gane cewa iyakarta ta zo ƙarshe...

Onyx bai tsaya a nan ba. Ya juyo ya kalli Gely, wadda take tsaye tana tunanin ta tsira...
Ya nuna ta da yatsa itama, idanunsa suna walƙiya.

"Ke ma Gely, saurara da kyau! Na san duk abin da kike ƙullawa. Daga yau, ki dakata da batun wata soyayya, ko kishi, ko wani shashanci makamancin haka.... Ke na’ura ce, kuma matsayinki na’ura ne a gare ni. Kada ki sake barin tsarin jikinki ya gaya miki kina da wani iko a kaina. Idan kika sake keta wannan layin, zan ruguza ki na mayar da ke tarkacen ƙarfe!"...

Gely ta tsaya cak, hasken idanunta ya yi sanyi, ta sunkuyar da kanta ƙasa...

"An ji, Boss...An goge dukkan tsarin da ba na aiki ba."

Onyx ya fizge hoton daga hannunta, ya mayar da shi cikin akwatin ya buga shi ya rufu. Ya rage hasken ofishin, ya bar kansa a cikin duhu, yana jin yadda amincin gidan nasa ya ruguje a cikin rana ɗaya....


😅😅😅😅
GWANGWANI VS CHING CHING...

Wato idan Allah ya yo ka a matsayin mutum to ka gode wa Allah...

Gely ta shige su a gun Ching Ching...😝😝😝

*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 2️⃣6️⃣

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Ayat ta tura ƙofar ɗakinta da ƙarfi tana shirin yin kukan haushi, amma tana sa ƙafarta ciki, sai ta tsaya cak. Ta zaro ido tana waige-waige. Ɗakin dake hargitse da barguna a ƙasa da kuma kayan da ta wargaza ɗazu lokacin neman Reems, yanzu ya koma tsaf tamkar ba a taɓa shiga ba.
Kowane abu ya koma muhallinsa; barguna an ninkasu, gadonta an gyara shi da sabon zanen gado mai sheƙi, kura ma babu ita ko kaɗan.
2. Bacewar "Warin" Kundirmo
Ta nufi inda ta ajiye kundirmon nonon nan da yake ishenta da wari, ta duba ko'ina amma ta tsinci gurbinsa wayam. Ba kundirmon kaɗai ba, hatta kwanukan azurfar da ta riƙa ba shi abinci a ciki duk sun ɓace. Ɗakin ya ɗauki wani irin daddaɗan ƙamshi na fure-fure, wanda ya fi ƙamshin kowane turaren da take amfani da shi daɗi.
"Lallai aljanin nan ba shi da dama," ta furta a fili, tana jin wani irin sanyi a ranta duk da fushin da take nuna tana yi.
3. Sakon Kan Madubi
Ta ƙarasa gaban madubinta don ta cire mayafin fuskarta, sai ta ga wani abu dake haske a inda ta ajiye gashin nan ɗazu. Wata ƙaramar sarƙa ce ta zinare mai kyan gaske, wadda take da wani jan dutse a tsakiya dake walƙiya kamar jini.
A ƙarƙashin sarƙar, akwai wani ɗan guntun takarda mai rubutu da aka yi shi da wani kalar tawada mai kyan gaske. Ta ɗauka ta karanta:
"Na kwashe 'kundirmon nonon' kamar yadda kika umarta. Wannan sarƙar kariya ce gare ki. Muddin tana wuyanki, babu wani aljani ko mutum da zai iya cutar da ke ba tare da na sani ba. Ki daina fushi da Reems ɗinki..."
4. Murmushin Sirri
Ayat ta murza takardar a hannunta tana son ta yi fushi, amma sai ta tsinci kanta da yin wani ɗan murmushi na ɓoye. Ta kalli sarƙar, ta taɓa jan dutsen nan, ta ji wani irin ɗumi dake shiga jikinta yana sanyaya mata zuciya.
"Wane irin takura ne wannan? Daga taimako sai ya zama yana bibiyar rayuwata," ta fada, amma duk da haka, ba ta jefar da sarƙar ba, sai ta sanya ta a cikin aljihun rigarta tana shirin ɓoye ta...


Kwanaki bakwai sun shuɗe cur, amma Ayat ta ji su tamkar shekaru bakwai. Tun ranar da ta kore shi a lambu, King Diamond bai sake bayyana ba, kuma Reems (kuliya) bai dawo ba. Ta tsinci kanta cikin wata irin damuwa da fargaba, ko yaushe zuciyarta tana dube-dube, tana kiran sunansa a asirce duk da cewa ta ce ya fita daga rayuwarta.
Yau ta shigo ɗakinta daga can falo ranta a ɓace, ma'aikata sun kai ta bango da wasu maganganu. Cikin fusata, ta fizge mayafin fuskarta ta wurgar da shi akan gado, sannan ta wuce banɗaki tana gunaguni.
2. Sallamar Sarki
King Diamond yana nan a cikin masarautar, domin kariya ta asiri ta hana shi fita sannan ya sake dawowa. Amma yau, ya yanke shawarar komawa fadarsa ta Power Pool. Ya bayyana a tsakiyar ɗakin Ayat domin ya yi mata kallon ƙarshe.
Ya matsa kusa da gadon, ya ga yadda mayafin fuskarta yake a murtuke. Ya ɗauka a hankali, yana jin taushin zaren mayafin a yatsunsa. Wani irin sanyi ya ziyarci ƙirjinsa, ya yi murmushin gefen baki, "Ta kore ni... amma tana nemana," ya raɗa a hankali, domin yana jin yadda zuciyarta take buga sunansa.
3. Gamuwar Ba-Zata
Yana tsaye yana kallon sashen kayayyakinta, ya furta: "Gimbiya... ba ki da ƙarfi kamar yadda kike nuna wa duniya."
A daidai nan Ayat ta fito daga bathroom. Ganin mutum tsaye a tsakiyar sirrin ɗakinta ya sa ta zabura, numfashinta ya kusa tsayawa.
“ME KAKE YI A NAN?!” ta daka masa tsawa, duk da cewa tsoro ya fara ratsa ta.
King Diamond ya juyo cikin natsuwa da kwarjininsa na sarki. Ayat tana tsaye, idanunta cike da wata irin fusata dake gauraye da kunya. Ta tsaya ƙyam kamar kowace sarauniya, amma hannunta dake rawa ya bayyana raunin zuciyarta.
4. Takun Sanya
“Na ce ka fita daga rayuwata,” ta faɗa cikin daka-tsawa. “Amma ka ƙara shigo mini ɗakina?”
King Diamond ya zuba mata idanunsa na zinare, bai kau da kai ba. “Ke ce kika ce na zo,” ya ba ta amsa cikin muryar nan tasa mai ratsa jiki. “Na zo ne domin abin da kika buƙata.”
Ya ɗaga mayafin fuskarta dake hannunsa. Ayat ta zaro ido, "Ka... ka taɓa kayana?"
“Ban taɓa ba,” ya ce cikin nutsuwa, “amma gaskiya na gani.”
Ayat ta ji kamar ƙasa ta haɗiye ta tsabar kunya. Ta ƙaraso kusa da shi tana huci, “Ba ka da kunya! Kai aljani ne mara tarbiyya!”
5. Yarjejeniyar Zuciya
Maimakon ya yi fushi, sai ya saki wani murmushi mai cike da ikon mallaka. Ya matso kusa da ita sosai yadda numfashinsa yake dukan fuskarta.
“Idan da gaske kina son in bar ki,” ya faɗa cikin wata irin murya mai sanyi dake girgiza jijiya, “kar kika sake kiran sunana... koda a cikin zuciyarki ne.”
Kalmar ta daki ƙirjin Ayat tamkar aradu. Ta so ta yi musu, ta so ta ce ba ta kiran sunansa, amma bakinta ya gaza buɗuwa. A wannan lokacin ne ta gano babban sirrin dake firgita ta: Ko tana nuna ƙiyayya a fili, zuciyarta ta riga ta kamu da shi... ta riga ta fara jin bugun zuciyar Sarkin Aljanu a nata jinin.
Haka suka tsaya suna kallon juna, babu mai cewa uffan, yayin da iskar ɗakin ta sauya zuwa wani yanayi na daban...

Dakin ya dauki shiru, sai kawai sautin numfashinsu dake fita cikin sauri-sauri. Ayat ta tsaya tana kallon cikin idanun King Diamond wadanda suke sheƙi tamkar taurari. A fuskarta, akwai sauran burbushin fushi da ƙiyayya, amma a cikin kwayar idonta, wani irin sirri ne na ƙauna dake neman mafaka. Shi kuwa Diamond, kallon da yake mata kallon mallaka ne, kallon da yake ratsa kowace jijiyar jikinta.
2. Kusa Da Juna
Tsananin kwarjinin King Diamond ya sanya Ayat jin jiri, ta fara yin baya-baya tana son nisantar dumin jikinsa dake neman ruda mata tunani. Tana gab da faduwa, sai ta ji wani kakkaran hannu ya zagayo ta kunkuminta. Cikin wani irin zafin nama da kwarewa, Diamond ya jawo ta da karfi, ya mannata da faffaden kirjin sa.
"Yarafff!" Haka kirjin Ayat ya daki nasa, wani irin shock ya ratsa dukkaninsu. A wannan lokacin, babu sauran sarari a tsakaninsu; kunkuminsu ya hade daram, kirjinsu ya manne da juna ta yadda za su iya jin yadda zukata suke bugawa a tare.
3. Tawaratsin Shauki
Ayat ta kasa kwatanta abin da take ji. Ta so ta ture shi, ta so ta kwace kanta, amma hannun Diamond dake kan kunkuminta ya zama tamkar igiyar karfe. Ya daukaka hannunsa daya, ya damko keyarta cikin wata irin kulawa mai dauke da zafi, ya sanya ta dago fuskarta don ta kalle shi.
Idanunsu suka sake sarke wa da juna a wani matsayi na karshe. A nan ne Ayat ta gane cewa dukkan kiyayyar da take nunawa, tana yi ne domin tana tsoron karfin ikon da yake da shi a zuciyarta.
4. Sumbatar Da Ta Tsayar Da Lokaci
Ba tare da wani jinkiri ba, King Diamond ya sunkuya, ya hada bakinsa da nata a cikin wata irin zazzafar sumba (kiss) mai cike da sakonni dubu. Sumba ce ta nuna mallaka, ta nuna kauna, da kuma neman gafarar dukkan yaudarar da aka yi a baya.
Ayat ta ji duniyar tana juya mata. Da farko ta daskare, amma cikin dakika kadan, sai ta tsinci kanta da mayar masa da martanin sumbatar, hannunta ya sarke a wuyansa tana mai kankame shi. A wannan dakin, a wannan lokacin, babu wata gimbiya, babu wani aljani; sai masoya biyu wadanda kaddara ta gama hada su.
5. Numfashin Ruhi
Dukkan wani fushi ya narke ya zama soyayya. Iskar dakin ta canza kalar ta, tana fitar da wani irin ni'ima. King Diamond ya kankame ta, yana jin tamkar ya samu taskar da ya dade yana nema. Sun jima a haka, suna aikawa juna sakonni ta hanyar sumbatar, yayin da zuciyar Ayat take raya mata cewa: Wannan shi ne mutumin da aka halitta domin ya mallaki dukkan abin da nake da shi...


Muddin ka taba Gimbiya Ayat, tabbas ka taba zuma! Da zarar sumbar ta lafa, Ayat ta dawo hayyacinta, fuskarta ta canza kalar zuwa wani ja saboda tsananin kunya da bacin rai. Ta fara dukan kirjin King Diamond da kananan hannayenta, hawaye na wanke mata fuska.
“ALLAH YA ISA! Macuci, ka kuma yi again? Ban yafe ba!” ta fada tana huci. Ta dora hannu a kanta cikin rudani. “Na shiga uku! Na yi gamo da bakin ALJANI!” Ta fara shawagi a cikin dakin kamar wadda aka zare wa lissafi, tana son kawar da dumin bakinsa dake yawo a nata.
2. Dokar Gimbiya
Ta tsaya cak a gabansa, tana nuna shi da yatsa, jikinta na rawa. “Ka san me? Daga yau, ka daina kusantata! Ka daina shigowa dakina, ka daina bin rayuwata!”
King Diamond ya gyara tsayuwa, ya sunkuya kadan don ya daidaita idanunsa da nata, wani kwarjini na musamman na fita daga jikinsa. “Amma ke ce kika kira ni,” ya fada cikin muryar raɗa. “Ke ce kika sa ni zama ‘Reems’. Ke ce kika dauke ni, kika ba ni wuri a zuciyarki—ko baki sani ba.”
Ayat ta hadiye yawu, ta ji maganarsa ta soke ta. “Na yi kuskure,” ta fada cikin tsauri, “kuma ba zan sake shi ba.”
3. Al'ajabin Reems
Ba zato ba tsammani, sai aka ji wani sauti: “Meow.”
Ayat ta juya da sauri, idonta ya sauka akan gadonta. Wata farar kuliya ce sol, zaune tana kallonta da wasu idanu masu taushi. Ayat ta rude, ta kalli Diamond, ta kalli kuliya. “Ku... ku nawa ne a nan?”
King Diamond ya dan murmusa, murmushin dake sanya kowa natsuwa. “Na bar miki bangare na a nan domin kada ki ji kadaici. Shi asalin kuliya ne, ba ni ba. Na san yadda kika shaku da shi, hakan ya sa na baki shi don rage kewa. Idan kika fita daga masarautar nan, zaki iya kirana ta zuciyarki zan bayyana, amma a nan tarkon masarauta zai hana ni shigowa.”
4. Sallamar Guguwa
Duk da cewa Ayat ta ji wani daci a ranta na cewa zai tafi, sai ta saki murmushin keta. “Allah na gode maka da tarko ya kasance! Na gaji da kai, bana son kara ganinka!” Ta dauki kuliyar ta nufi kirjinsa da ita tana tura masa. “Ku duka biyun ku fita daga dakina yanzu! Idan kuka sake kusantata, wallahi sai na sa an binne ku da rayunku!”
King Diamond ya saki wata dariya marar sauti, dariyar dake nuna sha'awar karfin zuciyarta. “Kin fi karfin da nake tsammani, Gimbiya Ayat.” Nan take, ya bace tamkar hayaki, ya bar dakin da kamshinsa kadai.
5. Saƙon Iska
Ayat ta zauna a kan gadon tana sauke numfashi, ta rungume sabon kuliyarta. “Na maida maka sunanka Reems,” ta fada tana shafa kansa. “Kiyaye ni daga irin wannan mai farin gashi, wai shi King ko?...” Kuliyar ta lumshe ido cikin natsuwa.
Amma tana cikin wannan tunanin, sai ta ji muryar King Diamond ta ratsa iskar dakin: “Ko kin so ko ki ki... zan dawo.”
Ayat ta shafa sumar gashinta, ta turo baki tana gunaguni: “Wannan aljani fa, ba ya jin magana!”....



A harabar fadar, limousine baƙaƙe mai tsawo ya tsaya jiran Gimbiya. Motar tana sheƙi kamar madubi. Driver ɗinta ya tsaya cikin tsabta, uniform dinsa yana nuna tsoron aiki fiye da alfahari.
Maayah ta shiga motar ba tare da ta kalli kowa ba. Bodyguards guda biyu suka bi a baya cikin babban jeep.
Driver ya shiga, ya gyara rawaninsa.
“Gimbiya, ina roƙon albarka.”
Ta ɗora ƙafarta kan kujerar gaba—alamar raini da iko.
“Ka saurare ni da kyau,” ta ce cikin murya mai sanyi.
“Idan muka makara ko da minti ɗaya, zan kore ka. Ba wai daga aiki kaɗai ba—daga cikin fadar nan ma. Ina son na shiga aji kafin mai kula da aji.”
Zufa ya keto wa driver. Bai ce uffan ba. Ya taka gas da gudun sarauta.
Mulkin Aji
Makarantar tana daga cikin mafi tsada a birnin. Da zarar motar Maayah ta tsaya, yara masu gata suka taru suna kallon shigowarta—kamar yadda ake kallon wata sarauniya a titi.
Da ta shiga aji, shiru ya mamaye wurin. Wannan aji na ƙarshe (Final Year) ne, amma ikon Maayah ya fi na shekarunsu.
Ta zauna a kujerarta—kujerar da babu wanda ya taɓa kusantar ta.
Malami ya fara darasi, amma Maayah ba ta saurare shi. Ta buɗe littafi, amma tana zane-zane—tana zanen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login