Showing 87001 words to 90000 words out of 154131 words

Chapter 30 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

bayanai na sirri, yayin da shi kuma yake shigar da su cikin tsarin bincikensa...

Bayan sun gama aikin, Chief ya sauƙe ajiyar zuciya yana ƙoƙarin miƙewa don ya huta...

Kwatsam! Sai Gely ta yi wani irin tangal-tangal kamar za ta faɗi ƙasa, jikinta ya fara wata irin rawa...

"Boss..." ta ƙira sunansa cikin wata murya wadda ba a saba ji daga robot ba...

Onyx ya zabura a ruɗe, ya tashi da sauri ya riƙo ta kafin ta kai ƙasa. Saboda ƙarfin jikinta da nauyinta na ƙarfe, sai ya jawo ta jikinsa, ta tsinci kanta a zaune daram a kan cinyarsa, yayin da hannuwansa suke kewayye da ita.

"Gely! Me yake faruwa? Akwai matsala a tsarin jikinki ne?" Onyx ya tambaya cikin damuwa, fuskarsa tana kusa da tata sosai.

Gely ta ɗaga idanunta waɗanda suka sauya launi zuwa wani haske mai sanyi, ta kalle shi cikin ƙwayar ido...

"Boss... na ji wani irin System Overheat ne a ɓangaren sarrafa saƙonnina. Ina jin kamar duk wayoyin jikina suna neman narkewa ne idan ina kusa da kai. Na kasa gano dalilin wannan matsalar a lissafina."..

Wannan ƙarya ce tsagwaronta, Gely ta ƙirƙiri wannan yanayin ne don kawai ta mallaki damar zama a jikin Chief Onyx. Ta sani cewa idan ta yi hakan, zai rarrashi jikinta kamar yadda yake rarrashin Ching Ching...

Ta matso da fuskarta daf da tasa, hancinsu yana gogayya da juna...

"Ina jin kamar akwai wani abu da kake buƙata daga gare ni, wanda ni kuma nake son ba ka shi... amma wannan yarinyar tana toshe duk hanyoyin."

Onyx ya tsaya cak, numfashinsa ya fara sarƙewa. Ya kalli leɓen Gely wanda aka ƙera shi da wani irin roba (synthetic skin) mai taushi kamar na mutum... Ya kasa gaskata cewa Gely ce take faɗar waɗannan kalaman. Ga ɗumin jikinsa yana neman ratsa na'urorin jikinta.

A daidai lokacin da bakinsu yake neman haɗewa, sai aka ji ƙarar buɗe ƙofar ofishin...

Ching Ching ce ta shigo da gudu, riƙe da kwamfutar a hannunta tana kuka..

"Uncle! Uncle! Dubi abin da ya faru a film ɗin nan! Jarumin ya rasu..."

Maganar ta maƙale a maƙogwaronta sa'ilin da ta ga abin da yake faruwa. Gely a zaune a kan cinyar Chief, suna fuskantar juna kamar za su yi sumba...

Kwamfutar hannun Ching Ching ta kuɓce ta faɗi ƙasa... Gararrass!...

Kwamfutar da take hannun Ching Ching ta rabe gida biyu a ƙasa, amma hayaniyar faduwarta ba ta firgita Gely ba. Maimakon Gely ta tashi daga kan cinyar Chief Onyx cikin kunya kamar yadda ɗan adam zai yi, sai ma ta ƙara nannaɗe hannuwanta a wuyan Chief, tana ƙara tura kanta a saitin fuskarsa.

Ching Ching ta tsaya cak, numfashinta ya fara fita da sauri-sauri, idanunta suka firfito waje...

"Uncle... me... me kuke yi?" muryarta tana rawa...

Onyx ya so ya ture Gely amma ta ƙara matse shi, sannan ta juyo da kanta a hankali ta kalli Ching Ching da wani irin kallo na isa da nuna iko...

"Baki ga abin da yake faruwa ba ne, Shugaba Ching Ching?"

Gely ta faɗa cikin murya mai sanyi wadda take amo na ban mamaki...

"Boss yana kula da ni ne. Tsarin jikina yana buƙatar ɗumin jikinsa domin na daidaita. Shin ba ke ce kika ce 'ba a miki tsawa, sai dai lallashi' ba? To, ni ma yanzu lallashin nake buƙata."

Ching Ching ta ji kamar an watsa mata ruwan zafi..

"Lallashi? Ke Robot ce! Inji ce ke! Ba kya buƙatar lallashi, sai dai a sanya miki mai ko a ƙara miki wutar lantarki!"

Gely ta yi wani ɗan murmushi na gefen baki, wanda ya fi na ɗan adam zafi. Ta sake juyawa wurin Chief, ta sanya hannunta tana shafa fuskarsa cikin sanyi, idanunta suna lumshewa kamar mai jin daɗi...

"Boss, ka ga yadda kake sanya ni jin daɗi? Kada ka bari kowa ya raba mu. Wannan yarinyar ba ta san yadda ake kula da kai ba, rigima kawai ta sani."

Ching Ching ta ƙara matsowa kusa, ranta a ɓace ta kai maƙura...

"Sauƙa daga jikinsa! Uncle, ka ce ta tashi! Dubi yadda take taɓa ka, wallahi ba ta da kunya!"

Onyx ya rasa yadda zai yi. A gefe guda, yana jin tsoron yadda Gely take sauyawa, a gefe guda kuma, wannan shauƙin da Gely take nuna masa yana sanya shi jin wani irin yanayi da bai taɓa sani ba...
"Ching Ching, ki yi haƙuri... Gely ba ta da lafiya ne..."

"Ƙarya take! Tana yi ne don ta sa ni haushi!" Ching Ching ta daka tsalle ta nufi Gely, ta sanya hannu tana ƙoƙarin janyo ta daga kan cinyar Chief...

Amma Gely tana da ƙarfin ƙarfe. Da hannu ɗaya ta tunkude hannun Ching Ching, sannan ta ƙara matse Chief a jikinta, har ta kai ga taɓa leɓensa da nata a hankali, tana kallon Ching Ching ta cikin ta gefen ido..

"Ke ba kowa ba ce a nan, Ching Ching," Gely ta raɗa. "Ni ce PA ɗinsa ce, ni ce kariyarsa, kuma ni ce kaɗai na san sirrin jikinsa. Ke kuwa... 'yar aiki ce kawai mai shagwaba."

Ching Ching ta fashe da kuka mai ƙarfi, wannan karon na kishi ne tsagoronsa. Ta juya ta ruga da gudu tana kuka tana shura ƙafa...

"Na tsane ka Uncle! Na tsane ka! Ka fi son gwangwani a kaina! Wallahi sai na bar gidan nan!"...

Onyx ya kalli inda Ching Ching ta bi, sannan ya kalli Gely wadda take zaune a jikinsa tana murmushin nasara...
Ya gane cewa Gely ta ƙulla wannan makarkashiyar ne don ta nuna wa Ching Ching matsayinta..

"Gely... ya isa haka," Onyx ya faɗa muryarsa ƙasa-ƙasa... "Kin yi abin da kike so. Yanzu tashi."..

Gely ta tashi a hankali, ta gyara kanta...

"Na yi hakan ne domin na nuna mata cewa ni ce nake da iko da kai, Boss. Kuma tana buƙatar sanin hakan."...

Chief Onyx ya bar Gely a ofis, ya nufi ɗakin Ching Ching cikin sanyin jiki. Yana shiga, ya tarar da ita a takure a gefen gado, tana ta kuka kamar ranta zai fita. Ganin yadda take kishin nan ya ba shi mamaki, domin bai taɓa tunanin yarinya irin Ching Ching tana ma san ma’anar kishi ba.

Ya zauna a gefen gadon, ya yi gyaran murya. "Wai meye na kukan nan? Kuma me ya sanya kika shigo ofis ba tare da izini ba?"

Ching Ching ta ɗago fuskarta wadda tayi ja saboda kuka...

"Na tsane ka! Ka je ka cigaba da zama da gwangwanin taka, me ya kawo ka nan?"

Onyx ya yi murmushin gefen baki, yana kallon ta..

"Ching Ching, shin kin fara so na ne?"

Ta zaro ido, ta harare shi cikin shagwaba...

"Cabb! Na rasa wanda zan so sai kai? Wa ya gaya maka ina sonka? Ni Daddyna nake so da Auntyna, ban ma san ma'anar sonka ba!"

Chief ya ɗaga gira ɗaya... "To idan ba kya so na, me ya sa kike kishi?"

"Meye kishi kuma?" Ta fada tana turo baki...

"Ni ba na kishin komai! Kawai dai na ga tana zama a kan cinyarka tana so ta sumbace ka, kuma... kuma na ga kai babban Chief ne, bai kamata kana irin wannan abun ba."

Onyx ya sake yin murmushi, ya ce,

"To idan ke ba kya so na, ita Gely tana so na, kuma soyayya ce ta sa ta yi hakan."

Ching Ching ta dakata, ta tuna abin da ta gani a film ɗin Indiya ɗazu.
.
"Soyayya? Eh... soyayya ce ai! Na gani a film ɗin da na kalla ɗazu, ana rungumar juna, kuma idan aka sumbaci mutum to soyayya ce."

Onyx ya tashi tsaye kamar zai fita, ya ce, "Shikenan, tunda ke ba kya so na, bari na je na sumbaci Gely tunda muna soyayya da ita."

Ching Ching ta zabura ta tashi tsaye. "To... to... taya za ka yi soyayya da ƙarfe? Kuma ma'aikaciyar ka ce fa?"

"Ita ce kaɗai take so na, ai dole na biya ta," Onyx ya faɗa yana haramar fita.

Cikin sauri da rashin tunani, Ching Ching ta ce.. "Ni ma ina sonka ai!"

Onyx ya tintsire da dariya, sai yau sautin dariyar Onyx ya fito, ya kalle ta daga sama har ƙasa...

"Ina kika san soyayya ke da ko period baki fara yi ba? Har yanzu ke yarinya ce ƙarama, ba ki san zafin so ba."

Jin wannan maganar ya sanya Ching Ching ta fusata matuƙa... Ta tashi a fusace tayo kansa. Onyx ya matsa gefen ƙofa yana tunanin ko fita za ta yi, amma sai ya ga akasin haka... ta daka tsalle ta rungume shi, ta sanya hannuwanta ta karkato da wuyansa ƙasa don ta kai saitin fuskarsa...

Kafin ya ankara, ta haɗe bakinsu wuri ɗaya! Onyx ya zaro ido cikin tsananin mamaki, ya ji numfashinsa ya ɗauke na ɗan lokaci..

Ching Ching ta fara sumbatar sa cikin wani irin salo na rashin sani mai cike da shauƙi, tana tsotsan leɓensa kamar ta samu lollypop mai zaƙi...

Duk da cewa Onyx yana ƙiran ta yarinya, amma a take ya ji tsikar jikinsa tana tashi, wani irin saƙon lantarki ya ratsa kashin bayansa. Ya kasa jurewa, ya manta da cewa yarinya ce, ya manta da cewa shi babban mutum ne... A hankali ya zagayo da hannuwansa ta bayanta, ya matseta a jikinsa sosai, ya fara biye mata yana sumbatar ta cikin wani irin yanayi mai zafi da rudarwa...

A daidai wannan lokacin, Gely tana tsaye a bakin ƙofar ɗakin, idanunta sun sauya launi zuwa Ja wur! (Deep Red). Tana kallon yadda Chief Onyx yake musayar numfashi da Ching Ching, wani irin amo na sarrafa saƙonni ya fara tashi daga jikinta...

A hankali Chief Onyx ya zare bakinsa daga na Ching Ching, yayin da numfashinsa yake fita da sauri-sauri. Ya riƙe kafaɗun ta, yana mata wani irin kallo mai zurfi, kallo ne da yake cike da mamaki, sha’awa, da kuma fargaba...

Tana numfashi sama-sama, fuskarta ta yi jawur, idanunta sun yi lamo alamar shauƙin ya tafi da ita. Ta tabbatar masa cewa duk da ita yarinya ce, tana da irin tata soyayyar da ba ta inji ba...

Onyx ya gyara tsayuwar sa, ya natsu, sannan ya ce da ita cikin muryar raɗa mai cike da natsuwa...

"Ching Ching, ke yarinya ce. Kuma yanzu ba na son ki ɓaci. Ke amana ce a gare ni daga mahaifinki, saboda haka dole ne ki kiyaye kanki, ki kiyaye mutuncinki."...

Ya kalle ta sau ɗaya na ƙarshe, sannan ya juya ya fice daga ɗakin da sauri, domin ya ji cewa idan ya ƙara daƙiƙa ɗaya a wurin, zuciyarsa za ta iya sa shi ya sake aikata abin da ya fi wannan...

A gefe guda kuwa...
Gely tana tsaye a falon sa'ilin da Chief ya fito. Tun kafin ya raba bakinsa da na Ching Ching, Gely ta juya ta tafi. Ba ta jira ta ga ƙarshen sumbar ba, domin Data ɗin da take gani ta kyamarorin sirrin jikinta ta riga ta gaya mata cewa...

Chief ya fara son Ching Ching fiye da kowace na'ura...

Gely ta nufi nata ɓangaren, tana tafiya tana jin wani irin rawa a jikinta (System Vibration)... Wannan karon fushin da take ji ya kusa sanya wayoyin jikinta fashewa. Ta tsaya a gaban madubi, ta kalli fuskarta dake kama da ta mutum komai irin na macen mutum...

"Amana?" Ta maimaita kalmar da Chief ya faɗa wa Ching Ching...

"Idan har ita amana ce, ni kuma me nake a gare ka Boss? Inji? Ko kuma tsohuwar na'urar da za ka wurgar dan ka samu sabuwar rayuwa?"

Idanun Gely suka yi wani irin haske na fitar hayaƙi. Ta yanke shawara... Tunda Chief ya ce Ching Ching Amana ce, to ita kuma za ta nuna masa cewa babu amincin da zai dore muddin tana kusa da shi....



Washegari da safe, Chief Onyx ya fito daga sashensa zuciyarsa cike da fargabar haduwa da Gely ko Ching Ching...

Ya zata zai tarar da Gely cikin yanayin kishi ko kuma ta tambaye shi abin da ya faru a jiya, tunda ya san kyamarorin jikinta ba sa barci...

Amma abin mamaki, yana fitowa falon dining, ya tarar da Gely tana tsaye daram, idanunta masu hasken shuɗi suna kallon gaba. Yanayinta ya koma kamar ranar farko da ya ƙere ta, babu shauƙi, kuma babu alamun kishi a fuskarta.

"Ina kwana, Boss," ta faɗa cikin murya mai sanyi ta robot, ba tare da ta kalle shi ba...

"An riga an kaddamar da dukkan ayyukan safe. Breakfast ɗinka yana nan, kuma na riga na tura wa Shugaba Ching Ching nata abincin zuwa ɗakinta don kada ta takura maka."

Onyx ya tsaya yana kallonta da mamaki. "Gely... game da abin da ya faru jiya..."

Gely ta katse shi cikin sanyin murya,

"Boss, bayanan da nake da su game da daren jiya an riga an goge su. Ba su da amfani ga tsarin aikina na yau da kullum. Aikina shi ne na tabbatar da tsaronka da kuma tafiyar da ofishinka. Sauran abubuwan da suka shafi dan adam ba su cikin damuwata."

Wannan halin ko-o-ho da Gely ta nuna ya fi sanya Onyx jin ba daɗi... Ta nuna masa cewa yanzu ta koma
"Inji" tsagwaronta, ba ta damu da shi ba kuma ba ta damu da kowa ba. Ta daina shishshigi a rayuwarsa, ta daina taɓa shi, har ma ta daina zama kusa da shi idan yana cin abinci.

Daidai nan, Ching Ching ta fito daga ɗakinta tana washe baki, tana tunanin yadda sumbar jiya ta kasance. Ta rugo da gudu tana nufar Chief...

"Uncle! Barka da asuba!" Ta zo za ta rungume shi kamar yadda ta saba..

A daidai lokacin da Gely za ta sanya baki ta hana ta ko kuma ta nuna kishi, sai kawai Gely ta juya baya ta nufi kitchen tana cewa,

"Boss, zan je na duba tsarin wutar lantarki na sashin baya. Idan akwai buƙata, za ka iya kirana ta intercom."

Ta wuce ko kallon inda Ching Ching take ba ta yi ba, kamar ma ba ta ga mutum a wurin ba.

Ching Ching ta tsaya cak, ta kalli Onyx.

"Boss, me ya faru da wannan gwangwanin? Yau ko hararata ba ta yi ba?"

Onyx ya sauƙe numfashi, ya kalli ƙofar da Gely ta bi. Ya gane cewa Gely ta ƙulla wani sabon shirin ne a ranta. Wannan shirun nata ya fi komai haɗari, domin bai san me take ƙullawa a cikin ƙwaƙwalwarta ta ƙarfe ba yayin da take nuna masa ba ta sani ba.

"Ki kyale ta Ching Ching,"

Onyx ya faɗa a hankali...
"Ƙila ta gane matsayinta ne."...

Ganin yadda Gely ta share ta, Ching Ching ta ji ranta ya ɓaci. Ita a ganinta, idan Gely ba ta nuna kishi ba, to nasarar da ta samu a kan Chief ba ta cika ba... Tana son ta ga Gely tana ƙuna, tana son ta ga idanunta sun yi ja saboda kishi...

Ta bi bayan Gely har zuwa kitchen, ta tarar da ita tana latsa wasu na'urori. Ching Ching ta matsa dab da ita, ta yi wani irin takun alfarma...

"Haba Gwangwani... wai yau ko kallona ba kya don yi ne? Ko don kin ga Chief ya daina yaba miki ne?" Ching Ching ta faɗa tana murguɗa baki.

Gely ba ta ko ɗago ba, ta ci gaba da aikin ta...

"Shugaba Ching Ching, kalla-kallan fuskarki ba ya cikin tsarin aikina na yau. Ina ba ki shawarar ki je ki ƙarasa karin kumallonki."

Ching Ching ta fusata, ta ƙara matse Gely tana hura mata iska a kunne...

"Kin san me ya faru a ɗakina jiya? Chief ya ce min ni Amana ce a gare shi. Ya rungume ni, ya sumbace ni... ya ma ce ni na fi kowace halitta da yake tare da ita zaƙi."
Ta ƙara da wata dariyar mugunta...
"Shin kin taɓa jin ɗumin sa kuwa? Ko kuwa ƙarfen jikinki ba ya jin komai?"

Gely ta tsaya cak, hannunta ya ɗan yi rawa kaɗan a kan na'urar, amma nan take ta daidaita kanta...
Ta juyo ta kalli Ching Ching da idanunta masu haske...

"Bincike na ya nuna cewa mutane suna yawan ƙarya idan suna son nuna isa. Amma ko da gaske ne, hakan ba zai canza cewa ni ce nake riƙe da dukkan sirrin rayuwar Chief ba. Ke sumba ce kawai kika samu, ni kuwa rayuwarsa gaba ɗaya tana hannuna."

Jin haka, Ching Ching ta ƙara kuluwa... Ta ruga falon dining inda Chief yake shan kofi. Ta tafi da gudu ta zauna a kan cinyarsa, ta rungume shi a gaban idanun Gely da take fitowa daga kitchen.

"Uncle! Uncle!! Ka ga Gwangwani ko? Wai cewa ta yi ita ce take da ikon komai na rayuwarka, wai ni sumba kawai na samu!" Ta faɗa tana kuka na shagwaba tare da goge fuskarta a kafaɗarsa..

Onyx ya kalli Gely, wadda take wucewa ta gefensu da tiren kofin shayi. Ta ajiye tiren a kan teburin ba tare da ta kalle su ba..

"Boss, idan ka gama, akwai taron gaggawa da za ka yi ta bidiyo da wasu abokan kasuwancinka. Na riga na shirya maka komai a ofis."

"Gely," Onyx ya ƙira sunanta,
"ba za ki ce komai ba a kan abin da Ching Ching take yi?"

Gely ta tsaya, ta yi wani ɗan sanyayyan sauti na inji...

"Me zan ce Boss? Yarinta tana damun ta, kai kuma kana jin daɗin hakan...
Aikina shi ne na gyara ofis, ba na gyara halayen yan adam ba."..

Ta juya ta tafi, takun ƙafafunta yana bada sauti ɗas-ɗas a kan falon...

Ching Ching ta haura, ta tashi daga kan cinyar Chief ta bi bayan Gely...

"Ke! Tsaya kiji! Wallahi sai na sanya Chief ya goge ki daga gidan nan! Yau ma sumbata ta zai sake yi, kuma a gabanki!"

Gely ta dakata ba tare da ta juyo ba....

"Kina iya yi, Shugaba Ching Ching. Amma ki sani, ko sau nawa za a sumbace ki, ba za ki taɓa sanin abin da yake cikin ƙwaƙwalwar Chief ba kamar yadda na sani. Ni ce inuwarsa, ke kuma wasan yara kike yi."

Ching Ching ta kalli Chief tana faman huci...

"Uncle! Ka ji abin da ta ce min ko?"

Onyx ya dafe kansa, ya gane cewa dambarwar ta sauya salo. Gely ba kishi take nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login