Showing 63001 words to 66000 words out of 154131 words

Chapter 22 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

da wuyar sha'ani...

Malami Mr. Collins ya fito daga ajin yana huci, ya nufi ofishin Shugaban Makarantar. Ya shiga ba ko sallama, yana korafi..

"Wannan wane irin iskanci ne? Wata ɗaliba ta kora ni daga aji, kuma tana barazana gare ni!"

Principal ɗin, wanda yake karanta wasu takardu, ya ɗago kai da sauri. Lokacin da ya ji bayanin abin da ya faru, sai fuskarsa ta koma kalar tsoro maimakon fushi. Ya mike tsaye da sauri, gumi ya fara keto masa.

"Mr. Collins, ashe ba a gaya maka ba? Waccan ba kowa ba ce illa Gimbiya Maayah, 'yar gidan Sarkin masarautar nan. Yarjejeniyar fitowarta makaranta ta musamman ce. Ko ni ban isa na nuna mata iko ba!"..

"Amma ai ni malami ne..." Mr. Collins ya yi kokarin kare kansa...

"Ba wani amma! Idan har tace ba ta son ganinka, to ka kwashe kayanka ka tafi. Idan Sarki ya ji cewa an ci mutuncin diyarsa, wannan makarantar tana iya rugujewa a yau."

Principal ya ɗauki waya nan take, ya ƙira Maayah cikin muryar lallashi...

"Ranki ya daɗe Gimbiniya, muna ba ki hakuri. An riga an dakatar da malamin nan, kuma za a turo muku da wanda ya fi shi kwarewa da sanin ya kamata yanzu-yanzu."

Maayah dake zaune a class ba tare da ta furta komai ba ta sauƙe wayar daga kunnenta ta katsar...

Bayan an gama darasi, Maayah tana zaune a wani waje na musamman a cikin garden din makarantar, inda babu dalibin da ya isa ya tunkaro wajen. Tana shan wani tsadadden juice wanda aka kawo mata daga gida...

Hafsat ta ƙariso kusa da ita, tana tafiya cikin ladabi duk da ita ma 'yar President ce. Ta zauna a kujerar dake kallon ta Maayah...

"Maayah, gaskiya kin tsorata ni yau,"

Hafsat ta faɗa tana murmushin damuwa...

"Malamin nan fa baƙo ne, bai sani ba. Ko ba za ki ɗan rage zafi ba? Karatu fa ya kawo shi."

Maayah ta ajiye glass ɗin juice, ta kalli Hafsat da idanuwanta masu cike da izzah.

"Hafsat, ki sani, ni ban zo nan don na koyi ladabi daga wurin wani malami ba. Na zo ne don na cika alkawarin da aka yi wa mahaifiyata. Duk wanda ya manta matsayina, to aikina ne na tuna masa."

Hafsat ta gyaɗa kai,

"Na sani, amma kowa a makarantar nan yana tsoronki. Ko ni ɗin nan ma wani lokacin sai na ji tsoron kulla magana dake."

Maayah ta gyara zamanta, ta ɗan dube ta da wani kallo na alfarma.

"Tsoro shi ne mutuncin shugaba, Hafsat....Idan ba su tsoronki, ba za su girmama ki ba. Ke ma ya kamata ki fara nuna matsayinki na 'yar President, ba wai ki bar kowa yana sakar miki fuska ba."

Hafsat ta yi shiru, domin ta san halin Maayah ba na canzawa ba ne. A daidai wannan lokacin, ɗaya daga cikin bodyguards din ya kariso, ya sunkuya ya ce..

"Gimbiniya, lokacin tashi ya yi. Motoci suna jiran ki a waje."

Maayah ta miƙe ba tare da ta sake cewa Hafsat uffan ba, ta fara tafiya cikin takunta na alfarma, yayin da Hafsat ta bi bayanta tana mamakin wannan dabi'a ta Maayah...



A sashen Gimbiya Ayat kuwa...

A yau ta sulale ta fito a matsayin Inuwa, domin ta kwan biyu bata leƙo waje ba, kuma tasan dole Master ya tuntuɓe ta...

Cikin Sa'a ta samu master Ibrahim baya nan...ta yi amfani da damar rashin Master ta sulale daga masarautar. Bayan ta yi sa hannu a babban littafin fita na jami'ai, ta zura wa dokinta linzami, kai tsaye ta nufi bakin kogin da ya zama tamkar maɓoyar sirrinta...

Iskar wajen mai sanyi ta daki fuskarta, amma zuciyarta cike take da tunanin Mai Farin Gashin nan, mutumin da har yanzu ba ta san asalin ko shi wanene ba, amma kewarsa ya addabeta.

Ta sauƙa daga kan dokinta, ta zauna a bakin ruwan tana kallon kwarararsa. "Ina kake ne?" ta faɗa a hankali, tana mamakin yadda abokin gaba ya zama abin kewa a gare ta.

Can ba zato ba tsammani, wani abu mai nauyi ya faɗo daga sama, ya sauƙa a tsakiyar faɗin filawowin da ke haskaka wajen...

King Diamond ne. Jikinsa duk jini, yana aman jini ta baki da hanci sakamakon raunukan da ya samu na rushewar kogon. Cikin zafi da raɗaɗi, ya ji motsin mutum. Ko da yake ya yi nisa a cikin mawuyacin hali, hankalinsa na sarki ya gaya masa cewa ba zai iya barin kowa ya ga rauninsa a matsayin mutum ba...

Cikin sauri yayi amfani da ikon tsafinsa, ya jirkita ya zama Ƙaramar Kuliya...

Farin gashin kuliyar ya ɓaci da jinin da ke fita daga jikinsa, yana nishi sama-sama...

Inuwa ta miƙe a zabure, ta zaro takobinta tana raba idanu, tana tunanin ko wani makiyi ne ya biyo bayanta. Amma tana isa wurin, maimakon katon jarumi, sai ta ga wata kyakkyawar kuliya mai farin gashi tana nishi cikin azaba, jini na malala daga jikinta...

Zuciyar Ayat ta buga. Duk dake ita jaruma ce da ba ta tsoron jini, amma tausayin dabba ya kasance rauninta tun tana yarinya. Ta maƙale takobinta, ta nufi kuliyar da gudu...

"Haba! Waye ya yi miki wannan aika-aikar?" ta faɗa cikin muryar tausayi, yayin da ta tsugunna kusa da Diamond wanda ke cikin siffar kuliya...

Ta sa hannuwanta biyu ta ɗauke shi cikin kulawa, ba ta damu da yadda jinin jikinsa ya ɓata kayan jami'in da ke jikinta ba...

King Diamond, yana cikin siffar kuliya, ya kalli idanun Ayat. Duk da duhun da ya fara rufewa idanunsa saboda suma, ya ji wani irin ɗumi da aminci a tattare da ita wanda bai taba ji ba....


👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 2️⃣0️⃣

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*



Bayan Ayat ta ɗauki kyakkyawar farar kuliyar nan mai rauni, ba tare da ɓata lokaci ba ta haye dokinta da sauri. Iskar dake kaɗawa tana busota yayin da take ƙara matse kuliyar a jikinta, tana gudun kada raunukan jikin kuliyar su ƙara tsananta...

Tana isa ƙofar masarautar, ta yi sa hannu a littafin jami'ai cikin hanzari, sannan ta jefa kuliyar cikin wata leda ta musamman domin ɓoye ta daga idanun masu gadi. Ta san idan aka ga kuliya a hannun jami’i irin Inuwa, zai iya tada shakku...

Bayan ta ajiye dokinta a rugar dawakai, tana ƙoƙarin sulalewa zuwa cikin masarauta, sai ta hango Master Ibrahim daga nesa. Cikin sani, ta san cewa muddin idonsa ya faɗa kanta, tambayoyi ne zasu biyo baya. Ta duƙa a hankali, ta laɓe bayan dogayen ginshiƙan masarautar, tana jin wasu jami'ai suna bi ta gefenta suna wasa da dariya..

Tafiya mai nisan gaske tayi a ƙafa kafin ta bi ta wata ɓoyayyen hanya, hanyar da ta kai ta kai tsaye zuwa cikin ɓangarenta na alfarma...

Tana shiga ɗakin baccinta, wanda ke ƙamshi da turaren oud, ta ciro kuliyar da ke lumshe ido cikin galala, ta kwantar da ita a tsakiyar gadonta mai laushin gaske.

A gaban babban madubi, Ayat ta fara cire kayan jami'an nan. Ta cire rawani, ta cire saje da gemun da take amfani da su wajen ɓoye siffarta. Nan take, dogon gashinta baƙi wul, ya bazu har zuwa gadon bayanta. Ta zama asalin kyakkyawar mace, mai kwarjini da izzah...

King Diamond, wanda ke kwance cikin siffar kuliya, yana kallon kowane motsi nata. Duk da ciwon da yake ji, zuciyarsa ta buga ganin wannan canjin. Daga jarumin jami'i zuwa mace mafi kyau da ya taɓa gani a duniyar bil'adama.

Abin da ya ƙara ruɗa Diamond shi ne lokacin da Ayat ta cire kayan jamin'an gaba ɗaya, ta ɗaura farin tawul kawai wanda ya bar fatarta mai santsi a bayyane. Ta nufi gadon, ta ɗauki kuliyar a hankali ta nufi banɗaki da shi...

Yayin da take haɗa ruwan ɗumi a cikin bahon wanka, Diamond yana ta maganar zuci..

"Wannan me take shirin aikatawa ne? Shiga banɗaki tare da ni? Lallai wannan yarinyar ba ta san ko ni wane ne ba!"..

Duk da haka, wani sashe na zuciyarsa yana cike da farin ciki. Masarautar nan tana kewaye da hasken garkuwa wanda ke hana aljanu da kowane irin tsafe-tsafe shiga, amma saboda canjin da ya yi zuwa dabba, kuma ta sanadin Ayat, ya samu damar shigowa har cikin zuciyar gidan...

Ya ƙura mata ido yana mamakin yadda kyakkyawar mace irin wannan take rayuwa a matsayin soja. Wani irin sirri ne yake tattare da ita?

Kuma wane irin ɗumi ne hannuwanta suke bayarwa yayin da take shirin fara yi masa wanka?..

Ayat ta gama gyara wa kuliyar jikinta tsaf, ta naɗe ta cikin tawul mai laushi sannan ta fito bedroom ta ajiye ta a kan gado...

"Minti goma kacal zan yi," ta faɗa cikin murya mai sanyi, "amma kinsan wanka na akwai delay."

Ta shige banɗakin, ta fara haɗa ruwan ɗumi da turaruka masu ƙanshi, tana shirin wanke gajiyar ta...

Tana zaune a cikin bahon wankan, tana goga lallausar fatarta da sabulu, kanta na jingine da gefen bahon. Idanunta a lumshe, amma tunaninta yana can bakin kogi...

"Me yasa nake kewar sa?" ta tambayi kanta. "Duk da abubuwan da ya yi min, musayar jikin nan da ya kusan haukata ni, da kuma kallon tsiraicina da ya yi a kogi, me yasa har yanzu nake jin tamkar akwai wani abu da yake haɗa mu?" Ta ji wani irin ɗumi a ranta, tana fatan da ace maimakon wannan kuliyar, 'Mai Farin Gashin' ne ta gani a yau... A cewar ta..


Tana shiga wankan, Diamond ya ji jikinsa ya fara wani irin zafi...

Kasancewar Ayat tana cikin jin daɗin ruwan ɗumi, shi ma King Diamond ya fara jin wannan ɗumin ta sanadin haɗin jinin da ke tsakaninsu. Ikon tsafinsa ya dawo masa da ƙarfi saboda natsuwar da ya samu a ɗakinta..

Cikin kifawar ido, ƙaramar kuliyar nan ta zama haske, sai ga King Diamond zaune a tsakiyar gadon Gimbiya Ayat. Doguwar farar rigarsa ta masarautar aljanu ta bayyana, sumar kansa fara sol ta bazu har gadon bayansa...

Ya zura wa ƙofar banɗakin ido, yana jin sautin ruwan da yake kwarara. Zuciyarsa tana bugawa. Ya tuna daren nan a bakin kogi lokacin da sukayi musayar jiki, sannan sumbatar da ya haɗa su ya fara dawo masa ƙwaƙwalwa...ya tuna yadda ya kalli kyakkyawar surarta tana wanka ba tare da ta sani ba...
Wannan haɗin jinin da sukayi ya sa yanzu duk abinda take ji, shi ma yana ji. Yana iya jin dumin ruwan da yake taba fatarta, yana iya jin kamshin sabulun da take shafawa...

"Ayat..." ya faɗa a hankali cikin ransa. "Kin zamo wata sirri a rayuwata!.. Kuma me yasa kika zama sanadin da zan ji tausayin bil'adama?"...

Diamond ya miƙe a hankali daga kan gadon, ƙafafunsa tamkar baya taka ƙasi yayin da ya nufi hanyar banɗakin. Ya tsaya a jikin ƙofar, yana sauraron numfashinta....

Ya san cewa idan ta fito ta ganshi a matsayin mutum, babban tashin hankali zai faru, amma wani sashi na ransa yana son ta san cewa yana kusa da ita...

A cikin banɗaki kuwa, Ayat ta fara jin wani irin yanayi na daban. Ta ji tamkar ba ita kaɗai ba ce a ɗakin...

Zuciyarta ta fara bugawa da sauri,
Ta miƙe da sauri daga cikin ruwan, ta ɗauki babban tawul ta ɗaura, tana sauraro da kyau...

"Kamar akwai mutum a ɗakin nan..." ta raya a ranta...

Ta fito daga banɗaki, sanyin ruwan ya sa fatarta yin luwai-luwai..

Tana ganin kuliyar nan a yadda ta bar ta a kan gado, sai ta saki wani irin murmushi mai ban sha'awa irin murmushin da babu wanda ya taɓa gani a masarautar nan sai ita kaɗai...

Ta zauna a gaban madubi, ɗaure da gajeren tawul ɗin da ya tsaya dai-dai cinyoyinta...

Ta fara shafa mayuka masu ƙamshi na alfarma, waɗanda ake yi wa gimbiyoyi oda na musamman daga ƙasashen waje. Kowane shafa mai da take yi, ƙamshinsa yana ratsa hancin King Diamond...

King Diamond, wanda ya riga ya koma siffar kuliya kafin ta fito, ya kwanta lamo yana kallonta ta cikin ƙwayar idonsa. A ransa yana jin wani irin takaici da daɗi lokaci guda...

"Ayat..." ya furta a zuciyarsa...

"Idan kika san cewa ni ne abokin wasanki na ƙuruciya, mutumin da kika yi wa rantsuwar kiyaye fuskarki dominsa, shin zaki kashe ni ne ko kuwa zaki rungume ni?"

Ya kalli yadda take shafa man a wuyanta da kafaɗunta.... Ya tuna lokacin da suke yara, lokacin da komai yake da sauƙi kafin ƙaddara ta mayar da shi sarki a duniyar aljanu..

Ganin yadda ta girma ta zama kyakkyawa haka, kuma jaruma mai faɗa a matsayin Inuwa, ya sa ya ƙara jin kwarjininta a ransa.

Ayat ta juyo ta kalli kuliyar, ta miƙa hannu ta ɗaukota ta ɗora a cinyarta. Ta fara shafa kanta a hankali, tana wasa da farin gashinta..

"Kinsan me? Ke kaɗai ce kika ga fuskata a yau bayan shi," ta faɗa cikin muryar raɗa, tana nufin Mai Farin Gashin da ya ganta a kogi...

"Shi ya ruguza min alƙawarina, amma ke... ke kyakkyawa ce. Zan kula da ke kamar jariri har sai kin warke."...

Diamond ya lumshe ido, yana jin ɗumin jikinta da laushin hannunta. Haɗin jinin da ke tsakaninsu ya sa kowane shafa da take yi masa, yana jin sa har cikin ransa tamkar ita ma tana jin abinda yake ji...

A wannan lokacin, Diamond ya manta da sarautarsa, ya manta da mulkinsa na aljanu, kawai yana son ya dawwama a haka, a jikin Ayat, yana kallon kyawun da kowa yake mafarkin gani amma shi kaɗai ya samu nasarar gani...

Yayin da take cikin wannan yanayin na natsuwa, ba zato ba tsammani sai ta ji takun tafiya a babban falon ɓangarenta...ana haurowa saman bedroom...

Zuciyarta ta buga. Babu wanda yake shigowa ɓangaren Gimbiya Ayat ba tare da izini ba, sai mutum ɗaya...
Wato Saratu, nan ma bata shigowa sai da izini..

"Gimbiya Ayat? Kina ciki ne?" Saratu ce ta daki ƙofar ɗakin...

Ayat ta zaro ido, ta kalli kuliya, sannan ta kalli kayan jami'an nan da ke warwatse a ƙasa waɗanda ba ta gama ɓoyewa ba...

Idan Saratu ta shigo ta ga kayan jami'ai a ɗakin, asirinta zai tonu!...

"Menene Saratu?..."
Ta furta tana shafa jikin kuliya...

Saratu daga bakin ƙofa ta ce,
"Daman an kammala shirya dining ne..."

Ta ce, "ok ki je ina zuwa, na fito a wanka ban kuma sa kaya ba..."

Daga nan Saratu ta juya...


Ayat ta miƙe ta ɗauko akwatin magunguna (First Aid Box) na musamman...

Ta dawo kusa da kuliyar, ta fara goge mata ragowar jinin da ya bushe a wasu sassan jikin, sannan ta shafa mata magani mai sanyi da kuma turaruka masu ƙamshi don rage radadin raunin...

Yayin da take gyara masa gashinsa, Ayat ta kalli cikin idanun kuliyar, wani irin tausayi da shauƙi suka mamaye zuciyarta. Ta ji tamkar kuliyar tana fahimtar kowane sauti da yake fita daga bakinta...

"To ni ban sani ba, mace ko namiji?..."

Tana kallon kuliyar ta kasa gane wa amma ita mace take bata...

Sai kuma ta ce, "idan mace ce ke, ina son ki mun wani alama da zan gane..."

Kuliyar tayi tsumu ko motsin bata yi ba..

Ayat ta kuma cewa "to idan namiji ne yi mun alama.."

Nan kuliyar ta ɗago hannu tana shafa kanta..

Murmushi Ayat tayi tare da ƙara ringumarsa..

Ta ce da shi... "Ka zamo abokina ɗan amana...
Daga yau, ke ba kuliya bace," ta faɗa cikin murya mai cike da shauƙi...

"Zan sanya miki suna Reems... sunan mutumin da ya fi kowa daraja a zuciyata."...

King Diamond, wanda ke cikin siffar kuliya, ya ji wani irin shock ya ziyarci zuciyarsa. Sunansa na asali! Sunan da ya binne shi tun ranar da ya zama sarki a duniyar aljanu. Wani daci da dariya suka taso masa a ransa, ya ce a ransa...

"Ayat... ki rasa a wa zaki sanya sunana sai a dabba? Ni ne Reems dinki, asalin mutumin da kike jira, amma yau gashi kina kira na a matsayin kuliya!"

Duk da haka, ya ji daɗin yadda sunan yake fita daga bakinta, ya tabbatar masa da cewa har yanzu yana raye a zuciyarta.

Ayat ta miƙe ta nufi wurin tufafinta na sarauta. Ta saka riga ta alfarma mai ratsin zinare, sannan ta ɗauko ɗankwalin fuskarta ta rufe kyakkyawar fuskarta kamar yadda ta saba, ta bar idanunta kawai masu Golden Eyes a bayyane.

Ta dawo bakin gadon, ta sunkuya ta manna wa kuliyar sumba a goshi...

Wani irin sanyi Diamond ya ji ya ratsa shi har cikin bargonsa...

"My Reems, zan sauƙa ƙasa domin yunwa nake ji. Zan taho maka da abinci kai ma ka ci, ka huta a lallausar gadona," ta faɗa a hankali sannan ta juya ta fice daga ɗakin cikin takun isa da izza.

Tana fita, kofarta na rufewa, sai ga wani farin hayaƙi ya mamaye tsakiyar gadon. Nan take King Diamond ya dawo asalin siffarsa ta mutum. Ya zauna a tsakiyar lallausan gadon, sumar kansa fara sol ta bazu a kan zanen gadon Ayat...

Ya ɗan gyara zama, ya taɓa goshinsa inda ta sumbace shi, sannan ya saki wani murmushin gefen baki...

"Ayat... idan kika san cewa Reems ɗinki yana zaune a kan gadonki a matsayin sarki, shin zaki iya kawo min abincin kuwa?"

Ya kalli ƙofar da ta fita, idanunsa suna shining da wani irin kwarjini da nuna cewa har yanzu shi ne mai iko, ko da kuwa yana cikin gidan masoyiyarsa ne a asirce....

✨✨

Washe gari a safiyar yau, Gimbiya Maayah tana zaune a kan kujerarta ta musamman a wurin dining area na sarauta, tana cin French Toast mai kwai da zuma wanda aka kawo mata a cikin wani faranti na azurfa mai sheƙi...

Gefenta tsaye masu aiki biyar sanye da fararen uniform, ɗaya na shara, ɗaya na gyaran teburi, ɗaya na kawo abinci, da sauransu...

Acan bakin ƙofa Bodyguards guda biyu ne masu jikin dambe, sanye da baƙaƙen kaya..

Maayah ta ɗaga hannu, ba tare da ta kalle su ba..

“Where is my orange juice?”

Muryarta a sanyaye cike da izgilanci..

Wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login