Showing 18001 words to 21000 words out of 154131 words

Chapter 7 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

shigarsa ta fararen kaya masu daukar ido, dogon farin gashinsa yana kaɗawa a cikin iska...

Ransa a ɓace yake, yana tunanin meyasa wannan yaron ya ƙara ƙetare iyakar yankin da ya zaɓa don hutawa a duniyar mutane. Hannunsa ya fara miƙa wa don ƙiran takobinsa na sihiri don ya halaka shi, amma abin da ya gani ya sa shi daskarewa a wurin...

A gaban idonsa, yaga Inuwa ya cire rawanin kansa ya jefar a gefe. Sannan ya kwance ribon ɗin gashinsa, sai ga wani uban gashi, baƙi mai santsi ya zubo har gadon bayanta zuwa kunkumi...

King Diamond ya zaro ido cikin mamaki. A tunaninsa namiji ne, amma sai yaga abin ya sauya. Ya kalli yadda take fincike gashin baki da sajen da gashin girar da ta ƙara don badda kama. Sannan ta fara ɓalle rigar mazan dake jikinta ɗaya bayan ɗaya...

Idon King Diamond yana kanta, ya kasa ko kyafta idon. Ganin surar tsararriyar mace, mai fata mai sheƙi da kwarjini ya bayyana a gabansa, ya sa ya ji wani irin Shock wanda bai taɓa ji ba a duk tsawon mulkinsa na duniyar aljanu...

Ayat kuwa, tana jin daɗi ba tare da sanin cewa idon sarki aljani yana kanta ba. Ta rage saura iya short nicket da bra, gashinta a kwance a bayanta. Ta fara takawa a hankali tana shiga cikin sanyin ruwan kogin.

Tana zura kafarta, wani daɗi ya ratsa ta, ta lumshe idanunta tana murmushi.. Ta nitse a cikin ruwan tana wasa, tana iyo cikin nishaɗi kamar wata tsuntsuwar ruwa...

King Diamond yana nan a tsaye tamkar gunki, ya kasa motsawa. Kyan Ayat da irin yadda take wasa a cikin ruwan ya taɓa wani sashi na zuciyarsa da ya daɗe a bushe....

Yana tsaye a ɓoye, yana kallon ta yayin da take wasa a ruwa. Kwatsam, sai tunanin tattaunawar da suka yi a baya ya dawo masa. Ya tuna yadda ya ji wani abu game da wannan yaron amma bai ba shi muhimmanci ba..

Ya dunƙule hannunsa, ya lumshe idanuwansa, nan take siffarsa ta mutum ta ɓace, ya koma siffar aljan wadda mutum ba zai iya ganinsa ba. Ya sulale zuwa tsakiyar ruwan, ya tsaya daidai saitin inda take wasanta.

Ayat tana nishaɗi, tana nitsewa tana fitowa tana dariya ita kaɗai, ba ta san ana kallonta ba. Sautin dariyarta ya fara ratsa kwakwalwar King Diamond. Wannan dariyar ta faɗo masa da irin dariyar Ayat tana yarinya iri ɗaya ce, ba ta sauya ba...
Ya ƙura mata idanu, yana kallon kwayar idonta domin tabbatar da wacece ita. Abin da ya gani ya sanya shi tsinci kansa cikin wani sanyayyen murmushi...

"Ayat ɗina ce..."
Ya faɗa a ransa. Wannan dariyar ba za ta taba ɓace masa ba. A lokaci guda, ya ji wani irin shauƙi na son ya rungume ta..

Yanke hukunci ya yi akan ya bayyana kansa gare ta a yanzu. Ya lumshe ido, nan take ya dawo siffarsa ta mutum sanye da fararen kaya da dogon farin gashinsa yana sheƙi a saman ruwan. Ya tsaya daidai gabanta, idanunsa na kallon kyakkyawar fuskarta.

Ayat ta sa hannu ta shafe fuskarta domin ta goge ruwan da ya taru a idonta. Tana buɗewa, sai ta yi ido huɗu da wannan halitta mai ban tsoro da kwarjini a lokaci guda. Ganin dogon farin gashinsa da shekin da yake yi ya sanya ta firgita matuƙa.....kuma bata san da mutum a wurin ba kwatsam ta ganshi a ruwa tare da ita...

Ba ta san lokacin da ta saki wani irin mahaukacin ihu ba. Saboda tsananin gigita da tsoro, numfashinta ya tsaya, nan take ta sume ta faɗi cikin ruwan. Ta fara nutsewa zuwa kasan kogin, gashinta yana yawo a saman ruwan...

Ya tsaya cak a saman ruwan yana kallon inda take nitsewa, ya ji wani irin mamaki ya ziyarce shi..
Ya fara duban jikinsa yana jujjuya hannayensa da kallon fararen kayan jikinsa, a ransa yana tambayar kansa,

"Me kyakkyawar yarinyar nan ta gani a jikina da har ta kai ga yanke jiki ta suma? Shin kwarjini na ne yayi mata yawa ko kuwa muni ne dani?..."


👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```


⚠️ SANARWA⚠️

Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 7️⃣

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*



A yayin da motocin alfarma suka tsaya a harabar makarantar Alhamra International Elite School, jami'an tsaro suka zagaye motar Maayah. Tana fitowa wani irin sanyi da shiru suka ratsa ko'ina. Daliban da ke wasa suka tsaya cak, malamai da ke tafiya suka gyara tsaiwarsu..

Maayah tana takawa ne cikin ƙasaita, fuskarta babu ko ɗigon murmushi, idanunta suna kallon sama kamar babu kowa a gabanta. Wannan shi ne ainihin halinta Izza, gadara, da nuna mulki...

Tana shiga cikin ajin, duk ɗaliban suka miƙe tsaye, kowanne ya durƙusa har ƙasa yana kwasar gaisuwa.

"Barka da isowa, Gimbiya Maayah!"

Ko kallo ba su isheta ba, ta wuce kai tsaye zuwa nata Seat ɗin. Wurin zamanta ya bambanta da na kowa, domin sarki ya bayar da umarnin a yi mata ado na musamman na sarauta, kujerar tana da laushin gaske kuma an yi mata ƙawa da zane na musamman..

Malami ya shigo aji domin koyarwa, amma yana ganin Maayah ta cire wayarta ta zamani tana danne-danne, sai ya ji wani irin fargaba. Malamin ya san cewa Maayah ba ta sauraron karatun, amma ba shi da ikon buɗe baki ya ce ta ajiye wayar..
Duk da abun yana cin ransa da na sauran malamai, sun gwammace su yi shiru da su ɓata wa Gimbiya rai, domin kuskure ɗaya zai iya sa su rasa aikinsu ko ma fiye da hakan..... Maayah tana zaune cikin Miskilanci, tana ganin hoton Inuwa daga cikin zuciyarta, tana murmushin mugunta yayin da kowa ke cikin tsoro.

Koda lokacin breakfast ya yi, babu ɗalibar da ta isa ta matsa kusa da Maayah ba tare da izini ba. Tana tafiya ne tamkar tana tattaka lu'u-lu'u. Duk wanda ya gitta ta, dole ya sunkuya...

Wannan makarantar ta zama karkashin ikon Maayah, inda kowa ke fargabar idanunta.
Ita a ranta, tana ganin kanta ta fi kowa daraja, kuma duk ilimin da ake koyarwa ba wani abu ba ne a gare ta, tunda ita Gimbiya ce kuma zuciyarta ta riga ta tafi ga wani jami'in tsaro wanda take tunanin talaka ne....

Sai a wannan lokacin Hafsat ta zo makarantar, anan motarta ta tsaya bodyguards ɗinta suka buɗe mata ƙofa ta fito sanye da ƙaton baƙin glass tana tauna chewing gum...

A duk faɗin makarantar, idan ka ga Maayah to tabbas za ka ga Hafsat a gefenta. Hafsat ba wai kawai ƙawa ba ce ita ce mutum ɗaya tilo da Maayah take sauraronsa, domin matsayinta na ƴar Shugaban ƙasa ya ba ta damar da ko malamai ba su da ita.
Duk da Hafsat tana da nata girman kan, amma a gaban Maayah ita kiyashi ce....
Hafsat ce take taya Maayah rarraba idanu ga sauran ɗalibai, kuma ita ce take ba ta labaran abubuwan da ke faruwa a wajen masarautar Alhamra...

A lokacin da malami yake tsaka da koyarwa, Hafsat za ta juyo ta raɗawa Maayah wata magana, su fara yin dariyar ƙasƙanci suna kallon malamin. Malamin zai ji ransa ya ɓaci, amma ganin ɗiyar Sarki da ɗiyar Shugaban ƙasa sun haɗe, sai kawai ya sunkuyar da kansa ya ci gaba da rubutu a board...

Hafsat ta kalli Maayah ta ce,
"Bestie, kalle shi yadda yake ta zufa, wai shi malami. Idan naso yau zan sa Daddy ya dakatar da shi daga aiki."

Maayah kawai murmushin gefen baki take yi, tana jin daɗin yadda kowa ke ƙarƙashin ikon su.


A lokacin da suke zaune wanda ko wacce ta kasance kujerar zamanta daban, Hafsat ta lura Maayah ba ta hayyacinta, sai duba waya take yi. Ta matso kusa da ita ta ce,

"Maayah, tun ɗazu kanki yana cikin waya. Ko akwai wani kyakkyawan ɗan Minister ne da kike boye min? Ko kuma wani Prince kika samo?"

Maayah ta yi ajiyar zuciya, ta kalli Hafsat cikin sanyin murya wanda ba ta saba yi wa kowa ba ta ce.

"Hafsat, akwai wani yaro a masarautarmu. Ba Prince ba ne, jami'in tsaro ne kawai... amma tunaninsa ya hana ni barci. Shi ne mafarkina."

Hafsat ta zaro ido cikin mamaki, "Jami'in tsaro? Maayah, kin san matsayinki kuwa? Yaya za ki so talaka?"

Maayah ta harari Hafsat, "Kada ki sake ƙiransa talaka. Kuma wannan sirri ne tsakanina da ke. Idan wani ya ji, zan iya yanke alaƙa da ke."


Bayan an tashi, Hafsat da Maayah suka fito kowa na takun alfarma. Motocin tsaro na fadar shugaban ƙasa da na masarautar Alhamra suka cika harabar. Hafsat ta yi wa Maayah sallama ta shiga tata motar, yayin da Maayah ta shiga tata, ranta yana ƙara kishirwar ganin Inuwa yayin da take komawa gida....

✨✨✨

A bangaren Gimbiya Firdos, wacce kowa ya sani da Chingching, ana tsaka da hargagi a cikin ɗakin wanka. Uma Altine tana ƙoƙarin yi mata wanka, amma Chingching ta sa kuka tamkar dukanta akayi..

"Wayyo Daddyyyy! Kazo ka taimake ni, Uma Altine za ta cire min nonuwanaaa!"

Ta furta tana wani irin zalle-zalle a cikin ruwan ɗumi...
Uma Altine ta zaro ido, ta rasa inda zata sa kanta don kunya da mamaki, ta ce.

"Haba Auta! Ki rufa min asiri don Allah. Ta ya zan cire miki nonuwa kuma?"

Chingching ta turo baki, cikin shagwabar da ta zama jikinta ta ce...

"Yooo, ba ke kike zuba min ruwan zafi a kansu ba?"

Uma Altine ta kusan yin dariya amma ta dake, ta kalli yarinyar ta ce

"Ina suke to? Ni ba na ganinsu ai."

"Ni dai ki samu ki yi min wankan, kuma wallahi kika jiƙa min gashina sai na gaya wa Daddy!"

Chingching ta faɗa tana nuna kanta da yatsa...
Uma Altine ta yi ajiyar zuciya,
"Kiyi hakuri, ba zan jiƙa miki ba."

Ta ɗauki soso da sabulu don ta fara goge jikin ta, amma kafin soson ya taɓa fatarta, sai ta zabura ta ja numfashi tamkar ta ga dodo..

"Haaaaaa!!! Da soso zaki yi min? Cire min fatar jikina zaki yi? Saboda kinga ni ɗin mai kyau ce!"


Uma Altine ta daure ta ce..

"Ki tsaya mana, ai soson zai cire miki dattin jiki ne."

Wannan kalmar 'Datti' ita ce ta zama silar rugujewar nishaɗi.... Chingching ta zaro manyan idanunta, nan take hawaye suka fara zubo mata, muryarta ta fara fita da karfi tana maimaitawa cikin tashin hankali...

"Ni ne mai datti? Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?..."

Uma Altine ta gigice, ta san halin Chingching idan ta fara wannan kukan, duk fadar sai ta ruɗe..
"Na shiga uku! Dan Allah kiyi hakuri, ba haka nake nufi ba Auta!"


Chingching ta ki sauraronta tana nuna kanta da yatsa tana maimaita tambayar cikin kuka mai taɓa zuciya.

"Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?..."

Ta miƙe tsaye daga cikin bathtub ɗin, jikinta duk ruwa da kumfar sabulu. Tana sanye da wani gajeren short nicket da wata ƙaramar vest mai raga-raga wadda ta bayyana kyawun fatarta mai sulɓi. Gashin kanta kuwa an tukwaikwiye shi da ribbons an tura shi sama domin kar ruwa ya taɓa shi, wanda hakan ya sa kanta ya yi girma tamkar na wata baturiyar yarinya..

Ta fito daga cikin ruwan tana kuka, tana neman inda zata nufa don kai ƙarar Uma Altine wurin Sarki, yayin da Uma Altine take binta tana rarrashi cikin fargaba.

Chingching ta sauƙo stairs da gudu tana kuka, ma'aikatan da ke gyaran falo duk sun bi ta da kallo cikin mamaki, amma ba ta saurari kowa ba sai maimaita tambayarta take,

"Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?"
Ta nufi babban gate ɗin sashenta, security bakin gate suka sha gabanta don hana ta fita a wannan yanayin, sanye da gajeren wando iya cinya da riga vest ta net wadda take nuna duk jikinta, ga gashin kanta da aka tukwaikwiye shi a tsakiya. Ganin an tare mata hanya, sai ta zube a ƙasa ta fara birgima tana ihu..

"Wayyo ku bar ni na je wurin Daddy na! Za su kashe ni, wayyo Allah za su kashe niiii!"

Cikin tsoron kar a ce su ne suka taɓa ta, security suka buɗe mata gate ɗin da sauri. Ta miƙe ta fice tana gudu, yayin da Uma Altine ke biye da ita a baya tana huci...

A daidai wannan lokacin ne motocin Gimbiya Maayah suka shigo masarautar daga makaranta....
Suna tsaka da tafiya a kan dogon kwaltar masarautar, sai ga Chingching ta tsallako da gudu tana kuka,
"Ni ne mai datti?..."

Direban Maayah ya daka wani mahaukacin burki wanda ya sa motar kusan tashi sama, har sai da Maayah ta bugi kanta da kujerar gaba...

Security ɗin da ke bin Chingching duk sun daskare a wurin saboda tsoron ganin yadda motar ta kusan halaka ta. Amma ita Chingching ko a jikinta, ba ta tsaya ba kuma ba ta kalli motar ba, ta ci gaba da gudunta na neman Daddy, sanye da wannan gajeren kayan nata da jikinta duk a jiƙe...

Maayah ta fito daga motar tana dafe kanta, ta kalli ƙanwarta cikin tsananin mamaki da fargaba, tana tunanin me ya faru da Autar tasu da har ta fito a wannan yanayin a gaban jami'an masarautar...

"Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?" Muryar Chingching ta karaɗe filin, tana kuka tana gudu...

A cikin katafaren falon fadar King Nourdeen, iska ta yi tsit, sai ƙamshin turaren wuta na alfarma da yake tashi. Sarki yana zaune tare da babban aminin sa Tafida, da wasu fadawa guda biyu...

Suna tsaka da tattaunawa sai kawai aka ji ihun Auta. Tun kafin fadawa su ankara, Chingching ta faɗo cikin fadar tana kuka da ƙarfi..

"Ni ne mai datti? Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?..."

King Nourdeen ya zabura ya miƙe tsaye, zuciyarsa ta buga ganin autarsa a wannan yanayin. Jikinta duk kumfar sabulu, sanye da wannan gajeren wando da net vest ɗin da ya bayyana surar jikinta duk da tana da shekaru kusan 17..

Chingching ba ta bi ta kan kowa ba, ta nufi wurin mahaifinta tana kuka..

"Daddy! Ka ga Uma Altine ko? Wai ni ce mai datti! Kuma har ruwan zafi ta zuba min a kan nonuwana, wai wanka za ta yi min!"

Ta ci gaba da surutu cikin shagwaɓa, tana bayyana komai daki-daki ba tare da jin kunya ba, yayin da kumfar sabulun jikinta yake ɗiga a kan kafet ɗin fadar...

Sarki ya shiga rarrashinta, a lokacin da Uma Altine ta bayyano tana sakin numfashi sosai domin ba ƙaramin gudu tayi ba, ta taho mata da dogon rigar sarauta har ƙasi... Ta matso tana ƙoƙarin rufe mata jiki..

Ita kuma sai faɗin, "Daddy wallahi sai an cire Uma Altine a aiki..."....

✨✨✨


Ganin ba lokacin tunani yasa ya nitse cikin ruwan ya kamo kunkuminta, ya ɗago ta sama.... Jikinta ya yi sanyi ga gashinta yanda ya bazu a saman ruwan kamar ganyen bishiya. Ya fito da ita har gaci, ya kaita karkashin bishiyar da tsuntsuwarta take, ya kwantar da ita a hankali a kan ciyayi...

King Diamond ya durƙusa a gefenta yana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ruwan kogin ya ƙara wa kyau da sheƙi... Ya sanya dogayen yatsunsa masu sanyi a kan goshinta, ya fara karanta wasu maganganu na sirri tare da hura mata iska mai sanyaya zuciya a fuska..

A hankali, numfashin Ayat ya fara dawowa dai-dai.. Kirjinta ya fara sama da ƙasa yayin da take shirin buɗe idanunta waɗanda suka yi nauyi...

Daidai lokacin da ta fara motsa idanunta don buɗe su, King Diamond ya fahimci cewa idan ta ganshi a yanzu za ta iya sake komawa suman. Saboda haka yana ganin ta buɗe ido ɗaya, sai ya ɓace kamar hayaƙi. Babu abin da ya rage a wurin sai ƙamshin turaren sa mai daɗi da sanyi wanda ya gauraye da iskar kogin...

Ayat ta buɗe idanunta gaba ɗaya, ta miƙe zaune da sauri tana nishi sama-sama. Ta duba dama da hagun amma ba ta ga kowa ba. Sai dai tana tabbatar wa kanta cewa abin da ta gani ɗazu ba mafarki ba ne..

"Na ga wani mutum... sanye da fararen kaya da farin gashi," ta faɗa a hankali muryarta tana rawa. Ta kalli jikinta, ta ga har yanzu tana sanye da short nicket da bra, kuma tana kwance a busashen fili alhalin tana cikin ruwa lokacin da ta suma...

"Waye ya fito da ni daga ruwa?" Ta fara waige-waige cikin tsoro, tana saurin rarrafa zuwa inda kayan maza da ta cire suke. Ta fara sanya kayan tsaro da sauri-sauri tana kuka, tana jin kamar idon wani yana kanta. Ba ta sani ba, King Diamond yana nan a tsaye a siffar aljan, yana kallon kowane motsi nata cikin murmushi...

Cikin gaggawa Ayat ta fara maida kayan siffar Inuwa... Ta gyara gashin baki da sajen sannan ta naɗe uban gashinta a cikin rawanin maza..

King Diamond yana nan a tsaye a siffar aljan wadda ita ba za ta iya gani ba, yana kallon yadda take sauya kanta zuwa namiji cikin ƙwarewa. Ya ji mamaki da kuma sha'awar yadda kyakkyawar yarinyar nan take badda kama. Ya gane cewa lallai akwai babban dalili da ya sa take rayuwa cikin sirri, kuma hakan ya ƙara ba shi sha'awar bibiyar rayuwarta...

Tana kammala shiri nan take ta zaro takobinta cikin zafin rai da takaicin karya mata alƙawarin da akayi na ganin fuskarta da ko mahaifinta ya kasa gani...

Cikin tsawa ta fara magana tana faɗin,

"Ko ma waye yake bibiyata nayi alƙawarin duk san da na sake haɗuwa da kai sai nayi gunduwa-gunduwa dakai, domin bazan taɓa yafe maka ba, a wancan lokacin ka zo har kayi faɗa dani kuma ban samu damar sararka ba, yanzu ma ka kuma na biyu to wallahi kada ka sake na sake ganinka na uku domin kashe ka zanyi..."

King Diamond yana kallonta bai furta uffan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login