Showing 147001 words to 150000 words out of 154131 words

Chapter 50 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

a wurina tunda baki san bambancin umarni da wasan yara ba."

Chief ya juyo kan Ching-Ching, wadda yanzu jikinta ya fara rawa domin ta ga cewa yau Uncle ba wasa yake ba. Ya matso kusa da ita, har tana iya jin huci da ƙanshin turarensa..

"Ke kuma, ki saurara da kyau. Wannan wasan Juna-biyu da kike yi, na sa muku ido ne kawai don in ga iyakar haukanku. Daga yau, muddin na sake jin wannan kalmar daga bakinki, zan sa a mayar da ke dabba na saka ki a keji.."

Yana mata wani kallo dake nuna raini da wulaƙanci..

"Kuma ki daina mafarkin soyayya. Har yanzu ke yarinya ce da ba ta san inda kanta yake ba. Babu kowa a zuciyata, kuma babu wanda zai shiga. Sophia ma tana hauka ne kawai, ban taɓa son ta na aure ba, kulawar da take ba ni ce kawai ta sa na ƙyale ta, ita kuma ta ɗauka abin da zafi. Saboda haka, ki cire batun kishi ko soyayya a kaina, ke ba komai ba ce illa 'yar aikin da aka kawo ta koya hali a gidana."

Ba tare da ya ƙara sauraronsu ba, ya juya ya nufi motarsa ta alfarma dake jiransa. Bodyguards suka buɗe masa ƙofa, ya shiga ya zauna daram, bai sake kallon inda suke ba..

Ya furta wa Driver cewa,

"Drive. Back to the Palace. Leave them here."

Motar ta yi kugi, ta bar wurin... Ching-Ching ta tsaya cirko-cirko, tana riƙe da locket ɗin dake zafi, yayin da GELY take tsaye kamar gunki saboda an soke mata Access....

*Likes ɗinku shine albashin marubuci*

👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 4️⃣0️⃣

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*


Chief onyx ya bar Ching-Ching da Gely da tafiyar wahala, domin daga asibiti zuwa masarautar Pavilion Palace ba kusa ba ne.
​Ga yadda dambarwar tafiyar tasu ta kasance...

​A babban titin Pavilion City ​rana ta fara zafi, Ching-Ching tana gaba tana kuka, tana fyace majina, yayin da take jan kafafunta cikin tafiyar agwagwa, amma wannan karon ba ta shagwaba ba ce, ta gajiya ce....

​GELY tana biye da ita a baya, amma tafiyarta ta yi nauyi saboda Chief ya soke mata damar yin amfani da gudun lantarki. Tana tafiya ne kamar tsohon ƙarfe dake buƙatar mai..

​Cikin kuka mai sauti Ching-ching take faɗin
"Wayyo Allah na! Gely kalle mu, yau Uncle ya yaudare mu. Ya bar mu a titi kamar kaji. Dama na sani, hoton mahaifiyarsa ne ya sanya shi wannan fushin. Ko kema kin ga yadda ta fito a hoton ko? Ta yi kwarjini, shiyasa shima Uncle ya zama zaki yau!"

​tana cikin magana kuma sai ta tsaya ta kalli GELY, wadda take ta faman ƙarar Krrr... Krrr... saboda tafiyar ƙasan...

​"Ke kuma GELY, me ya sa kika biye min? Yanzu gashi an soke miki baturin access. Ke robot ce marar amfani! Da yanzu kina da ikonki, da kin goya ni mun isa gida tun ɗazu....Amma yanzu kalle ki, tafiyarki ma ta fi tawa muni..."

​Muryar Gely wanda yake ta yanyanke wa ta ce,

"Warning... Battery at 15%... Chief Onyx access denied... Please... charge... me..."

​Ching-Ching tana turo baki ta ce,
"Charge kanki mana! Ni ma kaina caji yake bukata... Idan na isa gida, wallahi ko ƙofa Uncle ya rufe min, sai na bi ta ramin ɓera na shiga, in je in nemi gafararsa. Ba zan iya barin Uncle na ba, koda zai mayar da ni ɓera a gidan..."

​Bayan sa'o'i biyu na tafiya cikin gajiya da yunwa da ƙishi, suka isa kofar katon fadar Chief...
Ching-Ching ta faɗi a ƙasa kusa da Guards... Gashinta ya hargitse, fuskarta yayi duhu tsabar wahala..

​Masu gadin suka kalle ta cikin mamaki, amma saboda umarnin Chief, ba su buɗe ƙofa ba...

​Ching-Ching tana buga ƙofar fada da sauran karfinta tare da faɗin

"Uncle! Ka buɗe min... Na daina juna-biyun! Na zama tsohuwa yanzu. Uncle wallahi ko ƙafa ta ba zan sake haɗewa da ta kowa ba, koda kuwa Yarima Leonardo ne.. Ka gafarta wa Gely, laifina ne.."

​B bodyguards kuwa sun yi ƙyammm ko kallonsu basu yi ba, domin an sanar da su akan kada su buɗe musu ƙofar..

​A cikin falonsa kuwa, Chief Onyx yana tsaye a bakin taga, yana kallon yadda Ching-Ching take kuka a waje ta cikin kyamarorin tsaro CCTV... Fuskarsa ba ta nuna alamar tausayi ba, amma ya ƙura mata ido yana so ya ga ko da gaske take yi na son gyara halinta....

GELY yanzu ta daina tafiya ma, sai jujjuyawa take yi a wuri ɗaya. Idanunta dake hasken ja sun fara lumshewa, suna yin blinking... Muryarta ta koma ƙasa-ƙasa, kamar tsohon rediyo mai neman baturi...
Muryar tana katsewa...

"Ching... Ching... Sys-tem... fail-ure. Battery... at... 5 percent. Help... me... to... the... charging... port... please..."

Ching-Ching ta ɗago kai tana kallon GELY cikin haushi..

"Ke dalla rufe min baki! Taimakon me zan baki? Kalli yadda na zama, gashina ya koma kalar dambun shinkafa saboda ƙura, ƙafata tana ciwo kamar an cire min ƙashi, ke kuma kina maganar caji?"

Ching-Ching ta tashi zaune tana share hawaye da bayan hannunta, tana sake daka wa GELY tsawa...

"Meye amfaninki ma yanzu? Da kike da caji ai kin biye min mun yi ta binciken locket, yanzu da Uncle ya yi fushi kin koma kukan caji! Da na sani ma da ban zo da ke ba. Yanzu idan na suma a nan, wa zai ɗauke ni ya kai ni ciki? Tunda ke ko hannunki baki iya ɗagawa!"

GELY ta ce,
"Ching... Ching... I... followed... your... logic... error. If... I... shut... down... Chief... will... recycle... me... into... a... frying... pan..."
(Idan na mutu, Chief zai mayar da ni kaskon suya)...

Ching-Ching ta ce,

"Aii gara ma ya mayar da ke kaskon suyan, kika sani ko idan kin zama kasko ya riƙa soya naman kaza a jikinki ya ba ni in ci! Gashi nan ma kowa ya ƙi buɗe mana ƙofa. Dubi guards ɗin nan, duk sun zama kurame, sun ƙi buɗe min ƙofa gashi cikina yana ƙugi kamar an kunna injin niƙa..."

GELY ta ƙara yin ƙasa, kafafunta suka fara rawa, can sai aka ji Peeeeeep

Wannan alamar battery ya koma 2% kenan..

"I... see... darkness... Goodbye... Ching... Ching..."

Ta daskare a tsaye, hannunta ɗaya a sama, ɗaya a kasa, tana kallon sama kamar wadda take neman taimakon hadari..

Ching-Ching ta tsorata, ta rarrafa kusa da GELY
"Ke Gely! Karki mutu! Don Allah karki mutu ki bar ni a nan ni kaɗai! Idan kika mutu wa zan riƙa sa yana min Laser ɗin abu mai ƙarfi? Gely! Tashi mu yi damben karshe!"

Ta fara girgiza GELY, amma GELY ta zama dutse...
Ching-Ching ta kara fashewa da kuka, ta rungume kafar GELY wadda take da sanyi da tauri...

"WAYYOOO UNCLE! Kazo ka ga robot ɗinka ta mutu! Nima gani nan zan bi bayanta idan baka buɗe kofar nan ba! Wallahi zan daina cewa ina da ciki, zan daina taɓa hannun kowa, zan koma cin ganyaye kamar akuya amma don Allah ka buɗe mana!"

Ba zato ba tsammani, sai aka ji ƙofar gate ɗin ta buɗe a hankali. Chief Onyx ne ya fito, sanye da ƙananun kaya na shan iska, fuskarsa tana sanye da bakin gilashi duk da yamma ta yi. Ya tsaya yana kallon wannan hoton na ban-tausayi.. Yarinya duk ƙura tana rungume da gawar robot...

Chief cikin sanyin murya ta furta "Wai har yanzu ba ku daina wannan wasan kwaikwayon ba?"

Ya matso kusa da su, yana kallon yadda Ching-Ching ta ƙanƙame ƙafar GELY tana kuka. Ya miƙa hannu don ya ɗaga ta ya kai ta ciki, amma sai ta goce, ta koma ta manne wa GELY dake daskarewa...

Ya ce, "Ching-Ching, tashi mu shiga ciki. Kin riga kin galabaita, kina buƙatar abinci da barci."

Ching-Ching tana shashshekar kuka ta ce,

"A'a Uncle! Ba zan shiga ba! Ka duba GELY, ta riga ta zama dutse. Tana tsoron kar ka mayar da ita kaskon suya shiyasa ma ta daina numfashi.... Idan ba za a shigar da ita a ba ta caji ba, to nima a nan zan daskare in zama kaskon tuwo.."

Chief ya yi wani dogon nishi, ya kalli GELY dake tsaye hannu ɗaya a sama kamar tana rawar Michael Jackson. Ya san cewa idan bai biye wa Ching-Ching ba, to a nan za su kwana...

Ya furta "GELY ta gaza yin biyayya Ching-Ching.... Dole ne ta fuskanci hukunci."

Ching-Ching ta zabura ta miƙe, ta fara dukan ƙirjin Chief da ƙananan hannayenta..

"Mugun Uncle! Azalumi! Saboda mu ne ba mu da jini a jikinmu? GELY ta biyewa logic error ɗina ne saboda tana so na. Idan baka caji ta ba, nima zan sa Laser in fasa kaina in ga me ke ciki! Wallahi yanzun nan zan daina numfashi ni ma..."

Ta riƙe numfashinta, ta kumbura kumatunta har sai da fuskarta ta yi jawur tana hararar Chief...

Ganin Ching-Ching tana shirin suma da gaske don taurin kai, Chief ya ɗaga hannu ya yi wa masu gadin sa guda huɗu alama..

Cikin muryar gajiya ya ce,
"Ku ɗauki wannan ragowar ƙarfen ku kai ta babban ɗakin bincike, a haɗa ta da High-Voltage Charger.. Sannan a sake mata formatting na ɓacin ran da aka sa ta."

Nan take Chingching ta saki numfashin, ta washe haƙora..
"Yauwa Uncle! Amma karka bar su su goge mata tunanin da muke da shi na naman kaza, kaga nima ina buƙatar ta riƙa tuna min lokacin da nake da juna-biyu kafin ka ce na zama tsohuwa."

Chief Onyx bai sake cewa uffan ba, ya sunkuyo ya fizge ta ya ɗora ta a kafaɗarsa kamar buhun gishiri..

"Ayya Uncle! Karka matsa min ciki, kasan har yanzu akwai ghost ɗin jaririn a ciki..."

Ya ce, "Ching-Ching, muddin kika sake yin maganar ciki, zan sa a haɗa ki caji tare da GELY!"

Nan take ta yi shiru, ta laɓe a kafaɗarsa tana kallon yadda ake jan GELY zuwa ciki. A ranta tana cewa,

"Gely, maza ki tashi, akwai sauran dambarwa a gaba!"

✨✨✨

​Bayan kwanaki uku na fargaba da ɗar-ɗar, gari ya waye da wani mummunan labari wanda ya girgiza harsashin fadar Alhamra..

An tsinci wasu gawarwaki guda goma 10 shimfiɗe a harabar fadar, waɗanda duk jami'an tsaron fadar ne. Ba a san ta yaya aka sace su ba, kuma ba a san ta ina aka shigo da gawarwakin nasu ba..

​An same su cikin jini, sanye da kakin su, amma rayuka sun yi halinta. A gefen gawarwakin, an tsinci wata wasiƙa mai ɗauke da tambarin fadar Sydney....

_​"Mulki ba na rarrashi ba ne. Idan kuna da ƙwarin gwiwar zuwa karɓo mutanenku da muka tsare a can Yankin Hamshara. (Wani yanki mai nisan gaske), to ku shirya zuwa da shirin yaƙi. Amma ku sani, kowace gaɓa ɗaya takun da kuka yi, tana iya zama silar mutuwar mutum ɗaya a hannunmu. Gawarwakin nan goma, somin-taɓi ne kawai."_

​Ganin wannan barazanar, Sarki ya ba da umarnin rufe dukkan asibitoci, makarantu, da kasuwanni. Alhamra ta zama kamar garin kurwa, kowa ya laɓe a gida, tsoron dakarun Turawan ya mamaye kowa...

​Sarki Nourdeen ya fito cikin fushi da ɓacin rai, idanunsa sun yi ja. Ya tara dukkan jami'an tsaron sa, ciki har da Inuwa wanda yake tsaye cikin kakin sa, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa...

​Sarki ya sanar da cewa
"Ba zan zuba ido ana kashe min mutane ba! Ruma ta wuce gona da iri. Ina neman mazajen da za su sadaukar da rayuwarsu su tafi Yankin Hamshara domin ceto mutanenmu. Wannan yaƙi ne, kuma jini zai zubar!"

​Sarki ya ba wa Master Ibrahim umarnin ware zaratan jami'ai guda hamsin da za su jagoranci wannan hari na ba-zata...

​Bayan an gama taron, Master Ibrahim ya fara kiran sunaye, amma ya ƙi ƙiran sunan Inuwa.... Inuwa ya bi Master har zuwa can gefe, muryarsa a dashe yana roƙonsa..

​"Master, me ya sa sunana ba ya ciki? Ka sani cewa nima na san dabarun yaƙi, kuma zan iya shiga inda kowa ba zai iya shiga ba!"

​Master Ibrahim ya juyo cikin tsawa muryarsa na rawa ya ce,
"Ba zan saka ka ba! Wannan ba wasan yara ba ne, yaƙi ne na haƙiƙa. Ina tsoron kada a je a raunana ka, ko kuma ka rasa ranka. Idan wani abu ya same ka, ta ya zaka cika burikan ka...?"

​Inuwa ya duƙufa yana roƙon Master "Don Allah Master, kada ka bar ni a baya. Idan ban je ba, ba zan taɓa yafe wa kaina ba. Ina da kariya, kuma zan iya taimaka muku. Idan har ka yarda da ƙwazona, to ka saka ni a cikin rundunar nan."

​Ganin yadda Inuwa ya nuna taurin kai da kuma zubar da hawayen jarumtaka, Master Ibrahim ya sauke numfashi, ya ɗauki alkalami ya rubuta sunan Inuwa a ƙarshen jerin sunayen, amma jikinsa yana rawa...

Bayan an gama danbarwar ne Inuwa ya koma sashensa..
Ta shiga ɗakinta ta boyayyar hanyar sirri, tana sanye da kayan jami'an tsaron jikinta... Tana shiga ta hango wani haske mai launin shuɗi yana walwali a kan gadonta... King Diamond ne zaune, dogon sumar gashinsa na kwance a kafadarsa, idanunsa na kallon ta cikin natsuwa..

​Cikin ajiyar zuciya ta furta..

"Daman ina son ganinka... Akwai babban aiki a gaba na."

​Ta ƙarasa kusa da shi, fuskarta ɗauke da damuwar da ta daɗe tana addabarta...

​ "Idan na tafi wannan yaƙi a matsayin Inuwa, wa zai zauna a nan a matsayin Gimbiya Ayat? Idan aka nemi gimbiya ba a ganta ba, asirina zai tonu, kuma sarki zai shiga ruɗani. Ta yaya zan kasance a wurare biyu lokaci guda?"

​King Diamond ya miƙe tsaye, tsayinsa da kwarjininsa suka cika ɗakin. Ya matso kusa da ita, muryarsa kamar busar iska..

​"Na san yadda zan yi, kada ki damu da wannan. Zan samar da wata Ayat da za ta zauna a maimakonki, babu wanda zai gano bambancin. Kuma yanzu ba tare da ɓata kwanaki ba zaku ta fi, kuma kina bukatar horo na musamman domin dakarun turawa ba mutane ba ne kawai..."

​Kafin Ayat ta samu damar tambayarsa wani abu, King Diamond ya sa hannu ya yi mata ɗaukan luɗa. Nan take wani irin jiri ya kwashe ta, ɗakin ya juya, komai ya ɓace cikin kiftawar ido.

​🌸

​A lokacin da Ayat ta buɗe idanunta, ta tsinci kanta a wata duniyar daban. Wuri ne mai cike da furanni masu sheƙi da fitar da haske kalar taurari, iskar wajen tana ƙamshin da ba a taɓa ji a duniyar mutane ba...

​Wata lallausar waka, mai sanyaya rai da kwantar da hankali ta fara tashi daga ko'ina. Ba a ganin masu kiɗan, amma sautin yana ratsa ƙashi...

​King Diamond ba tare da ya sake ta ba. Ya sanya hannunsa ɗaya akan kunkuminta, ɗaya kuma ya riƙe hannunta... Ayat kuma, kamar yadda rawar turawa take, ta ɗora ɗaya hannun nata a kafadarsa itama..
​Suka fara taku ɗaya-bayan-ɗaya, suna juyawa cikin natsuwa a tsakiyar lambun furannin...

Suna bin sauti da gangar wakar...
Idanunsu suka sarke cikin na juna. Ya sauya mata kayan jikinta daga na jami'i zuwa na gimbiya haɗaɗɗiya, tsabar shauƙi na lokaci guda har ta mance da batun yaƙi...

A wannan lokacin, Ayat ta ji wani irin kariya dake tattare da King Diamond. Kwarjininsa ya mamaye daukacin hankalinta..

Yana mata raɗa yayin da suke rawar..
"Wannan rawar ba ta nishaɗi bace kaɗai Ayat... Tana koyar da ke yadda zaki riƙa sarrafa jikinki cikin sauri da natsuwa a lokacin yaƙi. Dole ne ki kasance kamar iska, ana jinki amma ba a ganinki."

Ta lumshe idanu, tana jin ɗumin jikinsa, tana fatan wannan daren kada ya ƙare. Ta gane cewa King Diamond ba aljanin kariya bane kawai, shi ne masoyin da zuciyarta ta daɗe tana nema...duk da akwai wanda take kewa kafin shi...

Waƙar da suke rawa da ita a hankali ta fara sauya sauti, daga lallausan sauti zuwa wani kiɗa mai ɗauke da sautin ƙarfe da kwarin gwiwa... King Diamond ya sakar mata kunkumi, sannan ya ɗaga hannunsa sama. Nan take, wani haske mai launin shuɗi ya ɓarke a tafin hannunsa, ya rikiɗe ya zama wani tsararren takobi mai matukar kyau da kaifi...
​Ya miƙa mata ɗaya, sannan shi ma ya zaro tasa.

​Ya tsaya takara, idanunsa sun canza launi zuwa wani irin shuɗi mai zurfi wanda yake nuna cewa yanzu lokacin horo ne, ba na wasa ba...

​"Ayat," ya ƙira sunanta cikin muryar dake amsa a cikin lambun...

"Takobi ba makami ba ne kawai, ɓangare ne na jikinki. Idan zuciyarki tana rawa, takobinki zai yi nauyi. Idan zuciyarki tana da tauri, takobinki zai zama kamar fure."

​Ya nuna mata yadda zata riƙe takobin...

​Ya daidaita yatsun hannunta akan marikin takobin, yana tabbatar da cewa ta riƙe shi da duk kwarin gwiwarta...

Ya gyara mata ƙafafu yadda zata samu natsuwa a ƙasa...

​Ya fara kai mata farmaki na farko, ba da nufin raunata ta ba, sai dai don ya gwada saurin motsinta..

​ Sautin ƙarfe ya tashi a lokacin da takobinsu ya haɗu...

​"Kada ki jira in kawo hari, ki riƙa hango inda zan sa ƙafa kafin in ɗaga ta," ya faɗa yayin da yake juyawa kamar iska...

Ayat ta fara bin sa, tana lura da yadda jikinsa yake motsawa. Cikin kankanin lokaci, ta fara koyon yadda zata kaucewa hari ta hanyar juyi da kuma yadda zata kare kanta...

​Ya koya mata wani salo na musamman inda jiki zai kasance yana rawa irin ta motsa jiki, amma takobi yana saran kowane bangare...

Ta riƙa yin tsalle tana kai hari daga sama..

Ya koya mata yadda zata riƙe numfashinta yadda ba zata yi saurin gajiya ba...

​Ayat ta ji wani irin ƙarfi yana gudu a cikin jininta. Duk wani tsoro na dakarun turawa ya ɓace, ya koma wani irin zafi da kishin ganin ta ceci mutanen Alhamra. Gumi ya fara keto mata, fuskarta ta yi jawur, idanunta suna kyallin jarumtaka...

​King ya tsaya, yana kallon kyakkyawar jarumar dake gabansa ya ce,

"Madalla. Yanzu kin shirya. Zuciyarki ta zama ɗaya da takobinki. Yanzu babu wani soja na Turawan da zai iya tsayawa a gabanki ya yi nasara."

​Ya matso kusa da ita, ya sanya hannunsa a kanta...

"Inuwar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login