Showing 48001 words to 51000 words out of 154131 words

Chapter 17 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt

17 Mar 2026

107

mutu da haushina."

Tana gama faɗar haka, ta karkade rigarta ta fice cikin takama...

Maayah ta bi ta da wani uban tsaki, ranta yana ƙuna..

Ayat itama ba tare da ta furta uffan ba. Ta wurga wa Maayah wata zafaffiyar harara dake nuna cewa tana sane da duk abin da yake faruwa, sannan ta juya ta fice tare da Saratu...

Maayah ta saki baki tana huci, "Can muku dai munafukai kawai! Kuma aniyarku ta biku. Ni na fi ƙarfinku, na zama muku ciwon ido, sai dai a ganni a barni!"...

Yumna ta kalli Maayah cikin rashin fahimta..

"Amma ina jin mamaki Aunty Maayah, ganin ba kya wani shiri da Aunty Ayat. Kuma naga mahaifiyar Ayat kafin ta rasu ita ta ci gaba da riƙe ki. A ɗaki ɗaya kuka tashi bayan tafiyar mahaifiyarki, me ya sa kuke haka?"

Maayah ta kawar da kai, tana jin ɗacin tunowa da baya.

"Yumna, Ayat ta canja. Ta ɗauki ƙanwarta Chingching kawai a matsayin iya ƙanwarta ta jini, shi ya sa wannan fifikon ya wargaza haɗin kanmu. Idan mutum ya nuna maka kai ba jininsa ba ne, me za ka yi masa in ba ka ja girmanka ba?"..

Bayan sun kammala, Yumna ma ta tashi cikin sanyin jiki ta nufi nata sashen..

Tana shiga, sai ga ma'aikatanta sun rugo da gudu, fuskokinsu cike da tsananin farin ciki...

"Aunty Yumna! Barka da dawowa!"
Wasu suka rungume ta, wasu suna kukan murna domin sun yi kewarta sosai a tsawon kwanakin da ta yi a ƙasar waje...

Yayin da Yumna take tsaka da karɓar gaisuwar ma'aikatanta, sai ga wani babban hadimi daga ɓangaren sarki ya bayyana a ƙofar...

"Gimbiya Yumna," ya faɗa yana mai sunkuyar da kai..

"Sarki yana nemanki a cikin ɗakin taron sirri yanzu-yanzu. Kuma ya ba da umarnin kada ki zo da kowa."..

Ma'aikatan suka yi shiru, farin cikin ya koma fargaba. Yumna ta gyara mayafinta, zuciyarta ta fara bugawa da sauri.

"Yanzu zan zo," ta amsa, sannan ta bi bayan hadimin ba tare da ɓata lokaci ba...

✨✨✨

Yumna ta shiga babban ɗakin taron sarki, inda ta tarar da shi zaune shi kaɗai, babu ko fitilun da aka saba kunnawa na alfarma, sai dai wasu 'yan kaɗan dake bada haske dishi-dishi...

Yanayin fuskar sarki a murtuke yake, amma da ya hango Yumna, sai ya ɗan saki fuska...

"Yumna," Sarki ya ƙira sunanta cikin muryar kulawa.
.
"Na'am barka da dare Abul,"
ta amsa cikin ladabi tare da tsugunawa har ƙasa..

Sarki Nourdeen ya ja numfashi, ya kalli 'yar tasa wacce ko kaɗan ba ta taɓa ja masa magana ba..

"Na ƙira ki ne domin in sanar da ke cewa, gobe idan Allah ya kaimu asubanci, muna da tafiya tare da ke. Ina son ki shirya da zarar kin idar da sallar asuba, ki fito ki same ni a babban filin saukar jirage na fada."

Yumna ta ɗan yi shiru, zuciyarta ta cika da mamaki. A rayuwarta ba ta taɓa yin tafiya ta musamman da sarki shi kaɗai ba, yawanci idan za a fita kowa yana tafiya ne tare da ma'aikatansa... Amma duk da haka, bai taɓa ranta har ta tambayi sarki "ina za mu?" ko "me za mu je yi?" Ba...

"To Abba, Allah ya kaimu. Zan kasance a can kamar yadda ka bayar da umarni," ta amsa cikin sanyin murya..

Sarki ya ji wani daɗi ya ziyarci zuciyarsa. Ya jinjina kai yana kallon Yumna har ta fice daga ɗakin. A ransa ya ce,
"Tabbas Yumna ta bambanta. Da ace Ayat ce ko Maayah ko Zayana da yanzu sun sani a gaba da tambayoyi na diddigi, ina za mu? Me za mu yi? Me ya sa yanzu? Amma ita Yumna, sanyin ranta da hakurinta sun kai matsayin da ba zan taba iya mantawa da su ba."..

Wannan halin nata ya ƙara sa sarki yake son ta, amma kuma raɗaɗin zuciyarsa ya ƙaru domin ya san yana gab da miƙa wannan taskar ga mutumin da bai san darajar mace ba..

Yumna ta koma dakinta, ta ƙi faɗawa ma'aikatanta komai domin sarki ya nuna tafiyar ta sirri ce...

Ta kwanta amma barci ya ƙi daukarta. Tana ta tunanin wace irin tafiya ce sarki zai fita da ita shi kaɗai? Ta saka a ranta cewa ƙila wani babban alheri ne mahaifinta yake son yi mata..



Ƙarfe huɗu da rabi na asuba, Yumna ta tashi ta yi sallah, ta shirya cikin wasu milk kaya masu kyan gaske dake rufe jikinta sosai...

Already wani bafade ya zo ɗaukanta wanda dashi za'ayi tafiyar.. suka nufi filin saukar jirage na fada, inda ta tarar da sarki cikin riga da wando na dakarun yaƙi, ya shirya tsaf, yana jiranta a kusa da wani karamin helicopter na sirri...

Jirgin ya kutsa cikin gajimare, babu abin da ke tashi sai ƙarar injin jirgin..

Yumna tana kallon mahaifinta wanda idanunsa ke kallon gaba amma hankalinsa yana wani gun..

Bayan awanni, sai ga wani ƙaton birni ya bayyana wanda gine-ginensa duk na gilashi ne da karafa, jirage na yawo a tsakanin dogayen bene. Yumna ta zaro ido tana kallon abubuwan al'ajabi,
manyan allon tallace-tallace dake shawagi a iska da kuma hasken lantarki dake walkiya duk da hasken rana...

Bayan jirgin ya sauƙa a babban filin Pavilion, ba a ba su damar takawa ba sai da wasu na'urori lasers suka ratsa jikinsu baki ɗaya. Wata na'ura ta bada sautin....

"Scan Complete. No weapons detected."

Daga nan wasu motoci masu tafiya ba tare da direba ba suka dauke su zuwa babban fadar Chief Onyx...

Suka shiga wani babban falo wanda girman sa ya kusan ninkin fadar Alhamra. Komai na ciki fari ne sol kuma na zamani...

Robot Gely tana tsaye a tsakiyar falon, idanunta na jan haske suna bin sarki da Yumna daga sama har kasa, tana tantance kwayoyin halittarsu..

Yumna ta ji wani irin tsoro ya ziyarce ta, ganin yadda Robot din ke kallonsu ba tare da kyaftawa ba. Ta kamo hannun sarki ta matse da karfi, jikinta na rawa..

"Abul, ina ne nan? Me ya sa mutanen nan suke kallonmu haka?" ta tambaya cikin muryar kuka..

Sarki Nourdeen ya daure ya dafa kafadar ta, "Kada ki ji tsoro Yumna, nan ne inda za ki zauna na ɗan lokaci. Ina nan tare da ke."



A can saman bene, Gely ta isa ƙofar ɗakin Chief Onyx..
Ta latsa jan kati (key card), kofar ta bude ba tare da karar komai ba. Chief Onyx yana kwance a babban gadonsa, jikinsa babu komai sai gajeren wando. Kwantattun gashin kirjinsa suna sheki, yayin da dogon gashin kansa ya bazu a kan pillow kamar gashin zaki..

Yana baccin sa ne cikin natsuwa, kirjin sa na dagawa da sauƙa a hankali..

Gely ta tsaya a kansa, tana nazarin yanayin bugun zuciyarsa da kwakwalwarsa. Ta yanke shawarar tashe shi domin biya masa bukatarsa..

Gely ta matsa kusa, ta sanya yatsanta mai sanyi ta taɓa wuyansa a hankali, sannan ta yi wata yar muryar ba tare da tada hankali ba,

"Boss... Boss... lokaci ya yi."

Chief Onyx ya ɗan motsa, ya buɗe idanunsa a hankali waɗanda suka yi dumu-dumu da barci...

Ya yi addu'o'in tashi daga barci a zuciyarsa, sannan ya tashi zaune yana shafa fuskarsa..

"Gely, me ye?..."
ya furta cikin muryarsa dake daukeda kwarjini...

Gely ta yi ƙasa da murya,

"Sarki Nourdeen ne ya zo, yana jiran ka a falon ƙasa. Ya taho da ɗaya daga cikin 'ya'yansa. Ya cika alkawari yau, ganin cewa shirun da muka yi masa ya nuna masa karshen Alhamra ya kusa idan bai yi biyayya ba."

Chief Onyx ya yi wani murmushin gefen baki, murmushin nasara da nuna isa. Ya ɗaga wa Gely hannu alamar ta bar ɗakin, ya ji abin da take nufi..



A can ƙasa, ma'aikata waɗanda rabi mutum ne rabi na'ura suka fito da wasu tebura na gilashi..

Suka jera abinci kala-kala waɗanda ba a taɓa ganin irinsu a Alhamra ba, da wasu abubuwan sha masu launuka daban-daban dake fitar da hayaƙi mai daɗi...
Amma Yumna ko kallon abincin ba ta yi ba, idonta yana kan kofar da take sa ran ganin wannan mutumin da ya sanya mahaifinta cikin damuwa har ya kawo ta wannan duniyar...

Chief Onyx ya sauƙo ƙasa cikin takunsa na isa, sanye da wata baƙar riga ta alfarma wadda aka buɗe maballan saman, inda faffaden ƙirjinsa dake cike da gashi yake bayyane, yana ɗaukar idon kowa. Ya zauna a kan kujerarsa ta sarauta, yana gyara agogon hannunsa na zamani ba tare da ya kalli kowa ba...

Sarki Nourdeen ya ja numfashi, muryarsa tana ɗan rawa ya ce,

"Chief, yau alƙawari ya cika. Ga yarjejeniyar nan na kawo ta kamar yadda muka tsara."..

Yumna wadda take jin tamkar ana tura ta cikin wuta, ta kalli sarki cikin lallashin murya..

"Abul... me yake faruwa ne? Me ya sa kake maganar yarjejeniya?"

Jin muryarta mai zaƙi da sanyi ya sa Chief Onyx ɗago kansa a hankali. Bai kalli fuskarsu kai tsaye ba, amma ya kalli gabansa yana nazarin sautin muryarta wanda ya taɓa wani sashi na zuciyarsa da ya daɗe a rufe...

Sarki ya kalli ƙasa, ya kasa haɗa ido da Yumna.

"Ki yi haƙuri ƴata. Na kawo ki ne domin ki yi masa aiki a nan. Ke ce za ki zama mataimakiyarsa."..

Yumna ta saki hannun sarki, idanunta suka cika da hawaye. Ta kasa yarda cewa mahaifinta wanda take gani a matsayin garkuwarta, shi ne zai sayar da ita a matsayin baiwa ba...

Chief Onyx ya yi wani murmushin gefen baki, murmushi mai cike da rainin wayo. Ya kalli sarki Nourdeen, sannan ya kalli Yumna. A matsayinsa na wanda yake da fasahar da ta san abin da ke ɓoye, ya ji cewa sarki yana ƙoƙarin yaudararsa ne....

"Gely"

Chief ya ƙira sunan Robot ɗinsa cikin sanyi.

"Babu wanda zai iya shigo wa har duniyar fadata sannan ya yaudare ni. Mutane suna tsammanin ni wawa ne. Ki duba jininta... Idan ƴarsa ce ki sanar da ni. Idan kuma akasin hakan ne, ki gaya min ko ita wacece ta hanyar asalin jinin jikinta."

Gely ba tare da ɓata lokaci ba. Wasu koren haske wato scanners suka fito daga idanunta suka ratsa jikin Yumna....

Cikin sanyi Gely ta juya ta kalli Chief Onyx..

"Boss... an kammala tantancewa. Wannan yarinyar ba ɗiyar Sarki Nourdeen ba ce ta jini."

Falon ya ɗauki shiru na wasu daƙiƙoƙi. Sarki Nourdeen ya fara gumi, yayin da Yumna ta daskare a inda take...

Gely ta ci gaba,
"Abin mamaki shi ne, jinin jikinta yana da alaƙa ta kusa da naka da kashi 99.9%...."

Chief Onyx ya miƙe tsaye da sauri, kofin dake hannunsa ya faɗi ya fashe. Idanunsa suka yi jawur yayin da yake kallon Yumna, wadda ita ma take kallonsa cikin tsananin mamaki da tsoro...

Sarki Nourdeen ya riga ya san asirin zai fito, amma bai yi tsammanin Gely za ta gano hakan cikin sakan biyar ba. Ya san cewa daga yau, rayuwar Alhamra da Pavilion za ta sauya zuwa wani abu daban..

Gely ta tsaya kyam, tana zazzago bayanan da na'urarta ta bankaɗo..

"Binciken jini ya nuna kamar haka...
Blood Group, O Positive.
Genotype, AA.
Blood Pressure, 110/70 domin Akwai alamun fargaba da saurin bugun zuciya...
Hemoglobin Level, Normal.
Amma babban abin lura a nan shi ne.....Tsarin kwayoyin halittarta na Chromosomes da DNA Markers sun yi daidai da naka, Boss...
Wannan jinin ba na Sarki nourdeen ba ne. Jinin ya fito ne daga asalin tsatson King HAMSHAK...domin inada file na jinin jikinsa a ƙwaƙwalwata tare da naka Boss..."

Yumna ta ji kanta ya fara juyawa. Ta kalli sarki Nourdeen wanda kansa yake sunkuye a ƙasa, ya kasa cewa uffan..

"Abul... me take faɗa? Wacece ita da zata ce ni ba jininka bace? Kuma wane ne wannan mutumin da take cewa dan uwana ne?"

Hawaye suka fara wanke fuskarta. Duk wani buri da take da shi na cewa tana da uba mai kariya ya ruguje a cikin sakanni kalilan...
Ta ji kanta ya yi nauyi, duniya ta fara juya mata...


Sarki nourdeen ya dubi Gely da kyau sannan ya ce,
"Amma taya zaki tantance ta lokaci guda kuma ki bada sakamako a take?..."

Gely ta ce, idonta a ƙyafe ana Sarki nourdeen..

"Malam Nourdeen, tin farkon ganinka da nayi na gama tattarar duk bayananka da jinin jikinka, yanda a duk lokacin da na ga jininka zan san taka ce..."

Daga nan Sarki bai ƙara furta uffan ba..

Chief Onyx ya matsa kusa da Yumna, takunsa yana bada sautin
"thud, thud" a kan benen falon. Ya tsaya daf da ita, kwarjininsa da kamshinsa suka gauraye da iskar dake kewaye da ita. Ya miƙa hannunsa, ya kamo habarta ya dago fuskarta don su hada ido...

A karon farko, Chief Onyx ya ji wani irin ɗumi a ransa..

Idanun Yumna masu ɗauke da rauni da gaskiya, sun tunatar da shi idanun mahaifiyarsu... Ya juya cikin zafi ya kalli Sarki Nourdeen...

"Nourdeen!" Chief ya ƙira sunansa cikin muryar dake razana kowa...

"Ka kwashe shekaru ashirin kana ɓoye min jinin jikina...Ka sace kanwata, ka mayar da ita 'yarka, sannan yau ka taho da ita a matsayin 'yar aiki domin ka kare kanka da 'ya'yanka na gaske?"...


Sarki Nourdeen ya ɗago kai, fuskarsa cike da gumi duk da sanyin AC dake ɗakin..

"Chief... ba sace ta na yi ba. Cetonta na yi a lokacin da aka kai muku hari aka tarwatsa gidan ku. Na riƙe ta tamkar 'yata ta cikina, na ba ta duk soyayyar da uba yake ba wa ƴarsa. Ban taɓa barin ta san ita wacece ba domin in kare rayuwarta daga maƙiya!"

Chief Onyx ya shaƙe wuyan sarki da hannu ɗaya, ya ɗaga shi sama har kafafun sarki suka daina taɓa ƙasa...

"Ka kare ta? Ko ka mayar da ita 'yar garkuwa domin ranar da bashi ya matsa maka ka mika min ita?"

Yumna wadda hawayen farin ciki suka wanke mata fuska, ba ta tsaya tsoron kwarjinin Chief Onyx ba. Da sauri ta faɗa jikinsa, ta rungume shi sosai a daidai lokacin da yake ƙoƙarin wurgar da sarki...

Chief Onyx ya saki sarki Nourdeen nan take, ya ji wani sanyi ya ratsa shi wanda bai taɓa ji ba a rayuwarsa ta sarauta da fasaha..

Ya rungume ta, yana shafa sumar kanta cikin wani irin yanayi na kariya. Yumna ta ɗago tana kuka, muryarta na rawa..

"Yayana, kun tafi kun bar ni... Shin wane ne kai a cikin twins ɗinmu? Kai ne Yaya Ra'ees ko kuwa Yaya Reems? Shi ɗayan yana ina?"

Tambayar Yumna ta soki zuciyar Chief Onyx tamkar mashi. Tunawa da ɗan uwansa tagwaye, wanda aka hallaka ta hanyar sauya masa halitta tun suna yara, ya sanya shi jin wani raɗaɗi...

Don kar ya tayar mata da hankali, ya jure ya ce.

"Ni ne yayanki, Ra'ees."

Amma lokacin da ta tambayi inda Reems yake, Chief ya rufe idanunsa na ɗan lokaci kafin ya ce,

"Baya raye."

Ya faɗi hakan ne domin bai san inda zai fara neman Reems ba a cikin wannan sabuwar siffar da aka ba shi..

Sarki Nourdeen, wanda yake gefe yana gyara numfashinsa, ya san gaskiyar magana... Ya san cewa Reems yana raye, kuma ya san cewa wannan canjin halittar da aka yi masa ya mayar da shi wani abu daban wanda ya ɓace daga idon duniyar mutane. Amma ganin yanayin da ake ciki, sarki ya gwammace ya yi shiru don kada ya ƙara tunzura Chief...domin yasan shima ya sani kawai ya ɓoye wa ƙanwarsa ce...

Chief Onyx ya rarrashe ta, ya share mata hawaye sannan ya kamo hannunta suka nufi babban mazauninsa na musamman. Ya zaunar da ita a gefensa a kan kujera ta alfarma, sannan ya kalli sarki Nourdeen da wani kallo na daban..

"Zauna, U. Nourdeen,"

Chief ya faɗa cikin muryar izzah.

"Ka yi min abin da dakaruna da fasahata suka kasa yi min shekaru ashirin. Ka riƙe min ƙanwata, ka kare ta, kuma ka kawo min ita."

Gely tana tsaye, tana ɗaukar dukkan hotunan wannan taron domin adana su a cikin babban kundinta na ƙwaƙwalwa...

Yumna tana kallon yayanta Ra'ees wato Chief, tana jin cewa yau ne karon farko da ta sake samun asalin rayuwarta..


👍 Like
🔁 Share
💬 Comment


*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*

_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_

✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

```JARUMAI WRITERS TEAM```

▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43

📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter

📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter

📲 Contact:
09065443871

📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥

📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```

CHAPTER 1️⃣7️⃣

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*



Bayan ma'aikata robots sun fita da Yumna zuwa sashen hutu, falon ya koma shiru..

Chief Onyx ya gyara zama, yana kallon Sarki Nourdeen kamar zai cinye shi mama ɗanye...

"Na yafe maka hukuncin yaudarata da kayi.." Chief ya faɗa cikin murya mai sanyi dake shaƙe da barazana.

"Ka riƙe Yumna ne a matsayin 'yar kallo domin ka samu mulkin Alhamra. Amma tunda ka kiyaye min lafiyarta, zan bar ka ka rayu."..

Sarki Nourdeen ya haɗiye miyau, ya san duk takunsa Chief ya sani...
Ya ce,

"Ina neman alfarmar ka bar ni in koma da ita Alhamra, idan na koma ni kaɗai, sannan bayan kwana biyu na kawo mata wata to sauran 'ya'yana da mutanen gari zasu zargi wani abu. Kuma idan asirin cewa ita ba 'yata ba ce ya fito yanzu, za a iya samun rudani a masarautar da kake so ka gada."..

Chief Onyx ya yi murmushin mugunta...

"Zaka koma da ita ne domin ka kare kanka, ba don ka damu da ita ba. Amma zan amince, domin ina bukatar ta kasance a masarautar Alhamra a matsayina. Amma ka sani, yarjejeniyar mu tana nan. Dole ka kawo min ɗaya daga cikin gimbiyoyinka,
Ina son ɗaya daga cikinsu ta zama personal maid ɗina, domin ta zauna a nan, ta gane cewa mulkin da kake taƙama da shi, ni ne mamallakinsa..."

Sarki ya jinjina kai, jikinsa na rawa.
"Na yarda. Zan shirya wacce zan kawo maka."..

"Gely!"

Chief ya ƙira.

"Yes, Boss."

"Shirya yarjejeniya Digital Contract. Sarki Nourdeen zai mayar da Yumna, amma zai dawo da ɗaya daga cikin 'ya'yansa nan da kwanaki uku. Idan ya saɓa, Pavilion zata ƙaddamar da hari akan Alhamra ba tare da sanya kowa a ciki ba...."

Gely ta fitar da wani hologram na takarda, sarki ya sanya hannu wato digital thumbprint...

Bayan sarki ya fita, Gely ta matsa kusa da Chief.

"Boss, me ya sa zaka bar ta ta koma hannun mutumin da ya sanya aka kashe iyayenku? Akwai haɗari."

Chief Onyx ya tashi tsaye, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login