Showing 54001 words to 57000 words out of 154131 words
Chapter 19 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
ya yi tsit. Ching Ching ta tsaya cak, kukan ya dauke, sannan ta zare ido tana kallon Chief Onyx cikin tsananin tsoron da ba ta taɓa ji ba...
Bayan ƙatuwar tsawar nan da Chief Onyx ya daka wa Ching Ching, daƙin ya dauki wani irin sanyi..
Sarki Nourdeen ya ji wani zafi ya ziyarci zuciyarsa na yadda aka tsorata masa ɗiyar da yake taƙama da ita, amma sanin cewa mutumin dake gabansa zai iya goge Alhamra a taswirar duniya da yatsa daya, ya sa ya danne zuciyarsa...
"Chief... yarinya ce fa..."
Sarki ya faɗa cikin muryar lallashi..
Ching Ching kuwa tinin ta ɓuya a bayan kujerar sarki..
Maimakon Ching Ching ta nutsu, sai ƙiran yarinya da sarki ya yi ya ƙara bata ƙwarin gwiwa...
Ta leƙo ta bayan kafaɗar mahaifinta, idanunta suka sarke da na Chief Onyx...
Ta fara galla masa harara, tana wani irin jujjuya kwayar idanu cikin raini..
"Kai wanene? Kuma me ya kawo ka gidanmu kake yi min tsawa? To wallahi ba zan yi shiru ba! Mugun mutum kawai, mai fuskar karfe! Daddy ka kore shi, yana min kallo kamar zai cinye ni!"...
Chief Onyx ya ƙara tamƙe fuskarsa, jijiyoyin wuyansa suka fito radau. Bai taɓa tsammanin akwai wata halitta a doron ƙasa da zata iya kallon kwayar idonsa ta faɗa masa maganganu ba tare da tsoro ba.
Ya kalli Sarki Nourdeen da idanuwan da suka fara sauya launi...
"Nourdeen, tarbiyyar ƴaƴanka tana buƙatar gyara," ya faɗa cikin muryar sanyi dake cike da barazana. Ya kawar da kansa gefe guda cikin nuna kyama, kamar ma numfashin yarinyar dake cikin falon na damun sa...
"Na ga alama kakkaɓe datti a gidana zai yi wahala idan wannan ita ce kuyangar da zan tafi da ita."
Jin kalmar mai kakkaɓe datti, ya sa Ching Ching ta harzuka fiye da kowane lokaci...
Ta fito fili tazo har gaban Chief Onyx, ta sunkuyo da fuskarta tana kallon cikin kwayar idanunsa dake walkiya...
Ta turo bakinta gaba kamar zata masa kiss, ta kumbura kunci kamar mai shirin amai tana masa gatsine da wasu irin kallo, tana jujjuya ƙwayar idon ta...
Sannan ta furta..
"Ai ba zan yi shiru ba! Don ka ga kana da ƙarfe a fuska sai ka ɗauka kowa tsoronka yake ji? To wallahi ko datti ne a gidanka, kai ne zaka share shi da kanka!..."
Ta ɗago tana kallon Sarki ta ce,
"Daddy ka ga yadda yake kallo na ko? Kamar bashi na ci? Ko kuma ya taɓa ganina a mafarkinsa ne yake ta faman kallona haka?"
Sauran fadawa dake tsaye suka duƙa ƙasa, jikinsu na rawa, suna rokon Gimbiya..
"Don Allah Gimbiya kiyi shiru! Don Allah ranta ya dade!"
Amma ina, Ching Ching sai ma ƙara sautin murya ta yi, tana tafa hannunta..
"Ba zan yi shiru ba! Shi wanene? Ko sarkin aljanu ne shi da ba zai iya magana ba? Sai dai ya yi ta kallon mutane da wadannan idanunsa kamar mujiya?"
Chief Onyx ya zauna shiru kamar gunki. Idanunsa sun canza launi zuwa wani irin duhu mai tsoratarwa. Ya zura mata ido, yana nazarin wannan yarinyar dake hargitse fuskarta tana masa rashin kunya...
A cikin ransa, wani shiri yake tsarawa..
"Zan ga yadda zaki yi wannan surutun a cikin kagarata inda ko iska ba ta motsi ba tare da izinina ba. Zan koya miki ladabi ta yadda ko muryarki ba zaki sake so ki ji ta ba."...
Sarki Nourdeen ya janyo Ching Ching ya rufe mata baki da tafin hannunsa, yana rawar jiki..
"Chief, kayi haƙuri... shagwaɓa ce ta yi mata yawa."
Onyx ya miƙe tsaye, tsayin sa ya cika falon da wata inuwa mai nauyi, ya nufi hanyar fita ba tare da ya sake tankawa ba...
Ganin haka yasa Ching Ching ta ruga da gudu ta sha gabansa. Ganin yadda yake datsa laɓɓansa cikin fushi, sai ta tintsire da dariya...
"Wai kai ba ka iya dariya ba ne?"
Kafin Gely ko Sarki su ankara, Ching Ching tayi ɗigalgal ta sanya hannayenta biyu ta damƙi laɓɓansa, tana ƙoƙarin shimfiɗa masa su da ƙarfi wai tana koya masa dariya...
Mutanen dake falon suka daskare, sun zaro idanu waje...
Chief Onyx ya ji wani zafi ya turnuƙe shi, ya doke mata hannu... Amma yarinyar nan, cikin tsananin rashin sanin ciwon kai, ta sake kai hannu tana ƙoƙarin cire masa ƙarfen azurfar dake fuskarsa...
Wannan ne ya kai Chief maƙura. Ya damƙi siririn hannunta cikin nasa ƙaton hannun, ya yi wani irin fisga ya fara jan ta da ƙarfi kamar ya kama ɓarauniya.
Ching Ching ta fara ja da baya tana kurma ihu...
"Ina za ka kai ni? Ka bar ni a wurin Daddy na! Wallahi ba zan bi ka ba! Mugun mutum mai fuskar ƙarfe! Daddy ka ce ya sake ni!"
Sarki Nourdeen ya miƙe jikinsa na ɓari ya yo wajen fada tare da faɗin..
"Chief, mun yi yarjejeniyar zan ba ka ɗaya daga cikin gimbiyoyi, amma ba a ce kai za ka zaɓa ba!"
Chief Onyx ya yi murmushin raini, yana ƙara damƙe hannunta...
"Na zaɓe ta ne a bisa zaɓin raina, ba jiran wacce za a ba ni nake yi ba."
Duk da tirjiyar da Ching Ching take yi, Chief Onyx ko kallo ba ta ishe shi ba...
Ya ja ta yana ratsa filin gidan masarautar har zuwa inda helicopter ɗinsa take jiransa...
Iskar injin jirgin tana karkaɗa gashinta dake hargitse, hawaye suna wanke fuskarta amma haka ya loda ta a ciki kamar kayan aiki...
Ya watsa mata wani kallo mai nuna cewa..
"Yanzu ne wasan zai fara."
Sarki Nourdeen ya tsaya daga nesa, idanunsa suna kallon yadda jirgin ke ɗagawa da Gwal ɗinsa...
Zuciyarsa tana suya, ga dukkan alamu ya san ya jefa autarsa a cikin ramin da ba shi da tabbas....
✨
Tun lokacin da Inuwa ya faɗi a filin fada sakamakon harbin doki, numfashinsa ya fita, ya suma a nan take...
Master Ibrahim, wanda zuciyarsa ta buga ganin halin da Inuwa yake ciki, bai jira kowa ba ya ɗaga shi ya nufi sashensa da shi...
Ya shimfiɗa shi a kan tsararren gadonsa mai laushi, inda ya shiga yi masa treatment cikin gaggawa da kulawa ta musamman...
Hankalin Ibrahim ya tashi matuƙa. Yana matuƙar ƙaunar Inuwa, ƙauna ce dake rikita masa tunani. Duk da cewa a idonsa namiji ne, amma duk lokacin da yake kusa da shi, yana jin wani irin shauƙi da ya fi karfin abota. Wani irin kishi ne yake ji a ransa..
Baya son ganin Inuwa tare da kowa, mace ko namiji. Idan yana tare da Inuwa, ji yake yi kamar yana tare da mace, amma sai ya kawar da tunanin yana ganin kamar sharrin zuciya ne...
Bayan ya gama gyara wa Inuwa goshinsa da ya fasa, Ibrahim ya kasa barin ɗakin. Ya kwanta a gefen Inuwa a kan gadon, yana kallon fuskarsa dake cikin bacci. Nan take wani zazzafen ƙamshi ya daki hancinsa, ƙamshi ne mai daɗi, ƙamshin mace mai matsayi da muƙami...
Ibrahim ya lumshe ido, ya shafi kansa a ransa ya ce,
"Tabbas Inuwa yana da tsafta, wannan ƙamshin na musamman ne."
Bai kawo komai a ransa ba game da asalin Inuwa, domin tsantsar tsafta ce kawai ya sani...
Ba a daɗe ba, baccin gajiya da fargabar abin da ya faru ya kwashe Master Ibrahim a gefen Inuwa. Su biyun suka lula duniyar bacci...
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 1️⃣8️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
A can can nesa da duniyar mutane, a cikin kogon sirri na Power Pool, inda kyan kyan-kkyasan ruwan zinari yake gudana, King Diamond yana zaune a kan karagar sa ta duwatsun lu’u-lu’u. Duk da cewa shi sarkin aljanu ne mai izzah da kwarjini, a yau fuskarsa tana nuna wani irin yanayi da ba a taba ganinsa ba.
Farat ɗaya, King Diamond ya dafe ƙirjinsa, zuciyarsa ta buga da wani irin ƙarfi “Duh-duh! Duh-duh!”. A lokacin ne ya ji wani zazzafan ciwo ya raba goshinsa gida biyu, daidai inda Ayat ta ji rauni a filin fada sakamakon harbin doki...
Wani irin gumi ne ya lakafo masa. Tun lokacin da suka yi haɗin jini da musanyar rayuwa a bakin kogi, duk wani raɗaɗi da zai taɓa jikin Ayat, tamkar jikinsa aka taɓa.
Yana cikin wannan halin, sai wani matashin saurayi mai sanye da fararen kaya na sirri ya bayyano. Shi ne amintaccen abokinsa a duniyar aljanu, Prince Zarith...
King Diamond ya ɗaga jajayen idanunsa waɗanda ke walƙiya kamar taurari, ya kalli abokin nasa cikin izzah. “Me ya kawo ka?” ya furta muryarsa tana amo a cikin kogon.
Prince Zarith ya matso kusa, idanunsa suna kallon yadda King Diamond yake dafe da goshinsa. “Me kake tunani ne, King? Na ji alamun fargaba a cikin ikonka...”
King Diamond ya runtse idonsa, raɗaɗin goshin Ayat yana ƙara ratsa shi. “Uhm...” kawai abin da ya iya faɗa kenan.
Zarith ya yi ajiyar zuciya, fuskarsa cike da damuwa..
“Guguwar jarabawa ta uku tana tafe, amma ba ka amfani da ikonka a cikin wannan tafkin don ka ƙarfafa kanka. I’m worried... shi ya sa nake nan.”
King Diamond ya buɗe idanunsa, wani irin kwarjini ya bayyana dake sanya kowace halitta durƙusawa...
“Why are you worried about me?” ya tambaya cikin sanyi mai cike da mulki.
Zarith ya yi murmushin yaƙe, ya san kafiyar abokin nasa. “Ok, all right... So King Diamond, did you try to grab the ancient golden armor? How is it, did you get it?”
Wani irin shiru ne ya biyo baya, sai kawai ƙarar ruwan Power Pool dake bugun duwatsu. King Diamond ya kalli nesa, inda yake iya hango duniyar mutane ta cikin ruwan. Ya tuna fuskar Ayat lokacin da ta fito daga ruwan kogi, gashinta a jike, tana masa kallon abokin gaba.
“No,” ya amsa a taƙaice.
Zarith ya zura masa ido. Ya san ba rashin ƙarfi ne ya sa King Diamond bai ɗauko sulken ba, amma tunanin wata halitta ta daban ne ya shagaltar da shi.
“Zuciyarka tana can bakin kogin Alhamra, ko?” Zarith ya yi raɗa, amma King Diamond bai sake furta komai ba.
Ya tashi tsaye, doguwar rigarsa tana jan ƙasa. Duk da ciwon da yake ji a goshinsa, izzarsa ba ta ragu ba. A cikin ransa, addu’a yake yi wa Ayat, yana fatan raunin nata bai kai ga inda zai gurgunta masa rayuwar da ya danka a hannunta ba...
“Zan tafi,” King Diamond ya furta kafin ya ɓace kamar hayaƙi, ya bar Prince Zarith yana girgiza kai...
Tafiyar awanni biyu a cikin jirgin Pavilion ta kasance mafi muni a rayuwar Gimbiya Ching Ching. Tana takure a kusurwar kujera, tana kuka ƙasa-ƙasa yayin da take kallon Chief Onyx wanda ko kallo ba ta ishe shi ba. Shi dai yana latsa na’urorin gabansa, fuskarsa sanye da wannan ƙarfen azurfar da ke ƙara masa ban tsoro...
Maimakon ta zauna a mazauninta, Ching Ching ta kwance bel ɗin kujerarta, ta lallaba har bayan kujerar Chief Onyx. Ta maƙale kanta a jikin wuyansa saitin kunnensa, ta fara tura masa harshe tana kuka tana sambatu..
"Mugun mutum! Ka mayar da ni gida! Wallahi zan sa kunnenka ya yi ciwo, kuma Daddy na ba zai yafe maka ba!"
Ta rinka jan hancinta tana busa masa numfashi a kunne, tana kuka mai taɓa zuciya da kuma tada hankali...
Duk lokacin da Chief Onyx ya yi ƙoƙarin kawar da kansa, Ching Ching sai ta zagayo ta ɗayan ɓangaren ta cigaba.
Ta fara shure-shure da ƙafafunta tana dukan kujerar Chief.
Ta kai hannu ta fara latsa wasu madannai na fasahar jirgin tana cewa,
"Ina ne gidan wanka anan? Na ce maka na yi datti Daddy ya ce za a yi min wanka!"
Chief Onyx ya runtse idanunsa, hannunsa ya dunƙule har jijiyoyinsa suka fito. Wannan ne karon farko da ya ji yana son ya jefa mutum daga jirgi domin ya huta. Gely ta matso kusa, muryarta na na'ura ta ce..
"Boss, bugun zuciyarka ya ƙaru da kashi 15%. Ka bani umarni in yi mata allurar bacci"..
Kafin Chief ya ba da amsa, Ching Ching ta juyo kan Gely, ta harare ta..
"Ke kuma wacece kike wata muryar kwalba? Ki yi min shiru! Kai kuma bokan ƙarfe, ka duba min takalmina ya tsinke!" Ta mika wa Chief Onyx karyayyen takalminta har saitin fuskarsa...
Chief Onyx ya buɗe idanunsa, ya kalli takalmin, sannan ya kalli fuskar Ching Ching dake cike da hawaye da kuma shagwaba. Ya ga yadda take tura baki kamar mai shirin yin amai.
A maimakon ya daka mata tsawa, sai ya ja wani dogon numfashi. Ya gane cewa wannan yarinyar ba tsoro ba ne da ita, kawai tana rayuwa ne a wata duniyar ta daban...
"Gely," Chief ya ƙira cikin murya mai ƙarfi da ta sa Ching Ching ta ɗan tsagaita da rigimar.
"Binciko min sa'ar da za mu isa. Kuma ki tabbatar an shirya mata ɗakin da babu abin da ke cikinsa sai kayan wasa da ruwan wanka, domin wannan rigimar ba za ta ƙare ba har sai mun sauƙa."
Yayin da jirgin ya fara rage gudu yana shawagi a sararin saman Pavilion City, hasken lantarki da manyan allunan dijital na birnin suka fara haskowa ta tagogin jirgin. Ching Ching, wadda take ta faman tura baki tana kukan shagwaɓa a kunnen Chief Onyx, ta tsagaita lokaci guda...
Ta saki wuyan Chief, ta matsa kusa da tagar jirgin, ta zaro idanu tana kallon dogayen benaye dake tafe da haske da kuma motoci masu shawagi..
"Wau! Daddy ka gani... Oh, na manta ba Daddy," ta faɗa cikin murya mai rauni, sannan ta juyo ta kalli Chief Onyx,
"Wannan gidan wasan naku ne? Me ya sa akwai fitilu da yawa haka?"
Chief Onyx bai ko kalle ta ba, ya ci gaba da kallon na'urar dake gabansa, amma a ransa ya sauƙe ajiyar zuciya ganin kukan nata ya tsaya...
Bayan jirgin ya sauƙa a babban dandalin fadar Pavilion, ƙofar ta buɗe. Gely ta matsa kusa da Ching Ching..
"Gimbiya, mun iso. Da fatan za ki sauƙo cikin lumana."
Ching Ching ta kalli ƙasa, ta ga yadda filin yake sheƙi kamar madubi, sannan ta kalli Chief Onyx wanda ya miƙe tsaye yana shirin fita. Ta koma ta zaune daram a kan kujera, ta naɗe hannayenta a ƙirji, ta turo baki gaba tana girgiza kai...
"Ba zan sauƙa ba! Na gaya maka takalmina ya tsinke, kuma ƙafata ciwo take yi. Sannan wurin nan akwai ƙura, ba zan ɓata ƙafata ba!"
Chief Onyx ya tsaya cak, ya juyo ya kalleta da waɗancan idanunsa masu kwarjini. Ya ga alamar idan ya biye mata, za su iya kwashe sa'o'i a nan. Ba tare da ya ce uffan ba, ya tako har inda take...
Kafin Ching Ching ta ankara, Chief ya damƙi kunkuminta ya ɗaga ta sama tamkar ƴar tsana, ya ɗora ta a kan faffaɗan kafaɗarsa...
"Wayyo! Ka sauƙe ni!
Daddy ka gani ko, sace ni zai yi!"
Ching Ching ta fara dukan bayansa da ƙananan hannayenta, tana ihu, yayin da gashinta yake ta karkaɗawa a iska...
Chief Onyx bai ko saurari ihun da take yi ba, yana taku cikin izza da gadara..
Dakarun Pavilion dake tsaye layin gaisuwa suka sunkuyar da kai, suna mamakin ganin babban Boss ɗinsu dake kyamar hayaniya ɗauke da wata yarinya dake ta faman buga masa baya tana ihu...
Gely tana biye da su a baya, tana lura da yadda bugun zuciyar Boss ɗinta yake, amma abin mamaki, maimakon fushi, sai ta ga yanayin jikinsa yana nuna natsuwa kamar dai wannan rigimar ta Ching Ching tana rage masa nauyin damuwar dake ransa...
Anan suka shige mota mai tafiya da kansa ba tare da direba ba, suka nufi can babban site ɗinsa..
Robots ne ke ta kai da komowa, wasu suna shawagi a babban falo..
Yana shirin sauƙe ta, ta ƙanƙame wuyansa, ta ƙame.
“Ni ba zan sauƙa ba! Daddy na ya ce in zauna a gidajen sarauta masu kyau, ba gidan aljanu ba!” Tana nan ƙanƙame wuyansa...
Chief Onyx bai ko saurareta ba ya jefa ta akan kujera...
Cikin muryarsa mai kauri ya ce, “Gely, kwashe wannan abin hayaniyar ki kai ta sashenta. Idan ta ƙara magana, ki sa mata na’urar toshe baki.”
Gely ta matso da sauri, ta ɗaga Ching Ching kamar jaririya...
“A’a! Ke wacece? Mace ko na’ura? Sakeni! Mugayen mutane, maciya amana!”
Ching Ching ta fara dukan ƙirjin Gely, amma kamar tana dukan dutse ne..
Haka aka kaita wani katafaren ɗaki wanda komai na cikinsa fari ne tas. Robots guda biyu suka nufota don su canja mata kaya...
“Wayyo Allah! Daddy aljanun sun zo cinye ni!”
Ta kwashe da gudu ta shige ƙarƙashin gado, tana kuka...
“Wallahi sai na gaya wa Abul! Sai na gaya wa Inuwa ya fasa muku kai!”
✨✨
Washegari da safe
Cikin sanyin asuba, hasken rana ya fara kutsa kai ta tagogin sashen Master Ibrahim...
Inuwa ta fara motsa yatsun hannunta, goshinta da aka yi wa ɗaurin bandej ya ɗanyi mata zafi.
Cikin nauyin idanu ta buɗe su, sai ta tsinci kanta a cikin wani ƙaton gado mai lallausan bargon siliki.
Ta juya kanta a hankali, sai idanunta suka sauƙa a kan Master Ibrahim. Yana nan kwance a gefenta, fuskarsa tana kallon tata. Yana bacci cikin kwanciyar hankali, numfashinsa yana fita a hankali.
Inuwa ta firgita. “Me ya kawo ni nan? Kuma me ya sa Master Ibrahim yake kwance a kusa da ni?” Ta tambayi kanta cikin fargaba...
Ta yi ƙoƙarin tashi..
Ibrahim ya fara motsawa ya buɗe idanunsa waɗanda suka yi jawur saboda rashin bacci. Ganin Inuwa ta tashi, sai ya yi saurin zama, kwayar idonsa tana yawo a kan fuskarta...
“Ka tashi?” Ibrahim ya tambaya, muryarsa tana da wani irin sanyi da bai saba ba. “Goshinka ya fashe jiya... na yi maka treatment.”
Inuwa ta jinjina kai, tana ƙoƙarin gyara rawaninta da ya ɗan zame...
“Na gode, Master. Amma me ya sa ka kwanta a nan? Ai ɗakin dakarunmu daban yake.”
Ibrahim ya yi shiru, ya kasa cewa komai. Zai iya gaya mata cewa ya kasa barin ɗakin ne saboda wani irin kishi da yake ji? Zai iya gaya mata cewa ƙamshin jikinta ne ya ruɗa shi?
“Babu komai,” ya faɗa tare da kawar