Showing 132001 words to 135000 words out of 154131 words
Chapter 45 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
da kishin kai haka..
"Ban yarda ba! Soja ba shi da al'ada idan umarni ya zo. Oyaa, cire rawanin nan yanzu ka miƙo min shi, sannan ka sake nitsawa ba tare da komai a kanka ba! Maza kai nake jira...!"
Inuwa ya fara zuru-zuru da idanu. Zuciyarsa ta fara dukan uku-uku.... Idan ya cire rawanin nan, sumar gashinta mai tsawo zai zubo, kuma vest ɗin dake jikinta zai iya bayyana siffarta ga kuma wandon jikinta tyt ne, surar hips ɗinta zai bayyana idan ta fito...
Master Ibrahim ya daka wa Inuwa tsawa, muryarsa tana sake ruri a sararin tafkin...
“Maza cire rawanin nan yanzu! Idan har ba ka da abin da kake boyewa, me ya sa kake gudun umarni na?”
Hannun Ayat ya fara rawa, ta kai shi saman rawaninta, tana jin kamar rayuwarta za ta kare a wannan lokacin. Ruwan sanyi ya ratsa ta, amma gumi ne yake keto mata a goshi. A ranta take furta,
“Ya King Diamond… ka ce za ka kare ni, ga shi asirina yana shirin tonuwa.”
A daidai lokacin da yatsun Ayat suka fara kwance rawanin, sai aka ji sautin takun takalman soja, taku ne mai nauyi da kwarjini...
Wani jami’i ne sanye da kakin masarauta, ya bayyana a cikin kamannin wani babban jami'i dake kusa da sarki, wanda ya fi master miƙami..
Kwarjininsa ya sa Master Ibrahim dakatawa da abin da yake yi...
“Master Ibrahim!” Muryar jami’in ta dake wajen, muryar da take cike da izza...
Master Ibrahim ya firgita, ya juyo da sauri ya ga babban jami’in tsaye. Nan take ya gyara tsaiwarsa ya sara masa...
“Yallabai! Ban yi tsammanin ganinka a nan ba.”
Jami’in wanda ya kasance King Diamond ne a wannan suffar bai ko kalli inda Ayat take ba, amma iskar da take kewaye da shi ta zama mai ɗumi, tana ba Ayat wani irin kwarin gwiwa...
“Sarki yana bukatar ka a fada yanzu! Akwai baƙi daga Masarautar Arewa da suka iso, kuma kai ne aka zaɓa ka jagoranci tsaron taron sirrin da za a yi.”
Master Ibrahim ya yamutsa fuska, ransa ya ɓaci domin yana tsaka da koyar da horo ne....
“Amma Yallabai, ina tsaka da horar da wannan yaron ne, akwai wani abu da nake so in tabbatar...”
Jami’in ya daka masa tsawa, idanunsa suka yi wani irin walƙiya da ta sa Master Ibrahim jin tsoro a karon farko...
“Umarnin Sarki ya fi son ranka mahimmanci, ko kuwa kana son ka sabawa masarautar ne?”
Master Ibrahim ya sadda kansa ƙasa. “Ayi hakuri Yallabai. Zan tafi yanzu.”
Ya juyo ya kalli Ayat wadda take raɓe a cikin ruwa... “Inuwa, ka tashi ka fito! Ka gode wa Allah da aka ƙira ni, amma horar gaba na nan tafe... Gobe za mu dora daga inda muka tsaya.”
Master Ibrahim ya ruga da gudu ya bar wajen...
Jami’in ya tsaya na wasu daƙiƙu, ya kalli tafkin. Ko da yake bai ce komai ba, Ayat ta ji wata murya a cikin kanta tana cewa..
“Kiyi maza ki fito ki shirya kanki, masoyiyata. Ba zan bar wani ya taɓa sirrin da yake nawa ba.”
Kafin ta farga, jami’in ya ɓace kamar hayaƙi a cikin iska. Ayat ta saki wani babban ajiyar zuciya, ta jawo jikinta ta fito daga ruwan, tana hawayen farin ciki da kuma fargabar abin da zai biyo baya gobe...
Ko da Master ya je, Sarki ya sanar masa cewa, akwai wani binciken da zasu gudanar...
Duk da ƙiran da King Diamond yayi masa duk na ƙarya ne...
✨✨✨
Gimbiya Zayana tana zaune a takure a kusurwar dakin kurkukun, wanda babu komai a cikinsa sai zafi. Iskar dakin tana da wani irin wari na danshi... Ga wasu ƙattai da miagun sauraye waɗanda suka addabi jikinta, duk inda ta shafa sai ta ji sun mata tabo...
Yau kwana uku ke nan, amma a wajenta kamar shekara guda ne. Babu waya a hannunta da za ta ƙira kowa, babu wata ƙawarta ko hadima da aka bari ta matso kusa da sashen. Shirun wurin yana mata nauyi a kwakwalwa, har ta fara magana ita kadai...
Muryarta a dashe saboda kuka, "Abul... ashe haka kake? Don kawai na nuna bacin raina akan cin fuskar da kake mun a cikin mutane, shi ne ka yardar da ni a nan? Ko duba ni ba za ka yi ba?"
Sau ɗaya kacal a rana ake turo mata da abinci, wanda ko karnukan masarautar ba su taɓa ci ba. Ruwan sha kuma a gora ake ɗuro mata a ajiye shi sai ya daɗe bai isa gare ta ba...
Zayana ta kalli abincin dake gabanta, ta tura kwanon gefe tana kuka...
"Ba zan ci ba! Gara na mutu a nan kowa ya huta. Yanzu haka Maayah tana can tana cin abinci mai daɗi cikin kwanciyar hankali, ga Ayat da Yumna kuma su ma suna can suna shawagi a fada... ni kuma an mance da ni."
Damuwar ta kai matakin da Zayana ta fara ganin jiri. Ta dora kanta a gwiwoyinta, tana tunanin mahaifiyarta dake can Sydney...
"Mommy... da kin san abin da ke faruwa dani da wannan masarautar ya gama amfani... Yanzu babu wanda zai sanar miki halin da nake ciki?...."
Bayan kwana ɗaya...
Master Ibrahim ya kasa zaune, ya kasa tsaye. Duk da shi ne ya rufe Zayana, amma zuciyarsa tana gaya masa cewa kwana huɗu a cikin cell ga gimbiya irin Zayana ya isa tarbiyya. Ya san Sarki ya fusata ne saboda rashin kunyar da ta yi masa a gaban kowa, kuma hakan ya taɓa kwarjinin sa na uba kuma sarki...
Master ya nufi sashen Sarki, ya same shi zaune yana duba wasu taswirorin ƙasa, fuskarsa a murtuke kamar babu sauran rahama a cikinta.
Master Ibrahim ya duƙa har ƙasa, ya gaishe da Sarki cikin girmamawa.
"Ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka tsawon rai da lafiya. Na zo ne domin in gabatar da wata magana akan Gimbiya Zayana."
Sarki bai ɗago kai ba, ya ci gaba da abin da yake yi. "Idan maganar fito da ita ce, to ka adana baki ka fita daga nan, Ibrahim."
Master Ibrahim ya ce,
"Ranka ya daɗe, na sani cewa ta yi babban kuskure na rashin kunya gare ka. Na san hakan ya yi maka zafi, kuma horon da take ciki ya dace da abin da ta aikata. Amma na duba yanayin lafiyarta, na ga damuwa da rashin abinci sun fara canza mata kamanni. Ina tsoron kada wani abu ya same ta kafin ta gane kuskurenta."
Sarki ya ɗago, idanunsa sun yi ƙuri akan Master Ibrahim...
"Ibrahim, ka san ni sarai. Bana taɓa jure raini daga kowa, ballantana daga jini na. Rashin kunyar da Zayana ta yi min a gaban mutane, ya nuna cewa ban yi nasarar ba ta tarbiyya ba. Idan na fito da ita yanzu, na nuna mata cewa za ta iya yi min duk abin da ta ga dama ne."
Ya ja numfashi, sannan ya ci gaba..
"Zan bar ta ta ci gaba da zama a can, har sai ta koyi yadda ake magana da uba, kuma har sai ta roƙi gafarar mutuncin da ta tattaka."
Master Ibrahim ya ga Sarki bai nuna alamar sassauci ba, sai ya yi dabarar kawo maganar mahaifiyarta dake can..
"Ranka ya daɗe, idan mahaifiyarta ta ji labarin cewa gimbiyar tana cell, na tabbata za'a samu babban matsala sosai. Amma idan ka ba ni izini, zan riƙa duba ta, kuma zan matsa mata har sai ta amince za ta ba ka haƙuri."
Sarki cikin fusata ya ce, "inason labarin ya je kunnenta, duk abinda suka ta ka ita da ƴar zan magance shi...bana tsoronta don haka kabar maganar nan kawai tin kafin ranka ya ɓaci kaima..."
Master bai ƙara cewa uffan ba, ya miƙe ya ja jikinsa ya tafi...
Yau ranar da ake ta shirye-shiryen gudanar da walimar sauƙar al'kur'ani...
Masarautar Alhamra ta cika da baƙi daga sassa daban-daban na duniya domin halartar taron sauƙar Alkur'ani na Gimbiya Ayat da Gimbiya Yumna. An tsara taron yadda duniya za ta ba da misali, inda manyan malamai za su shaidi tilawar gimbiyoyin...
Ayat tana zaune a ɗakinta, kanta cike da sarƙaƙƙiya. Zuciyarta tana gaya mata cewa wannan ranar ita ce mafi haɗari a gare ta.
Dole ta bayyana a matsayin Gimbiya Ayat don yin tilawa a gaban malamai..
Amma kuma, matsayinta na Inuwa yana nufin dole tana filin taron tana tsaro, musamman yadda Master Ibrahim ya matsa kaimi akan tsaro...
Tana cikin wannan raɗaɗin tunanin, tana kiran King Diamond a ranta, sai ta ji sanyin kamshinsa ya cika ɗakin..
King Diamond ya bayyana a gabanta, tsaye daram cikin kwarjininsa. Ayat ba ta san lokacin da ta tashi da gudu ta rungume shi ba saboda tsananin kewar da take masa. Ta ɗago kanta da sauri tana shirin bayyana masa matsalarta, amma sai ya ɗora yatsansa akan laɓɓanta...
"Ba sai kin yi magana ba. Na riga na saurari maganar zuciyarki, kuma na san damuwarki."
Ya kalli cikin idanunta, muryarsa mai ratsa jiki ta ci gaba
"Ke za ki kasance Gimbiya Ayat, ki fita taron ki yi tilawar Alkur'ani kamar yadda kika yi buri. Ni kuma, zan rikkiɗa in koma Inuwa, zan tsaya a matsayinki na soja mai tsaro. Babu wanda zai gane bambancin."
Ayat ta sake rungume shi a karo na biyu, tana jin wani irin sanyi a ranta...
Ta ɗago tana kallonsa cikin mamaki...
"Ta yaya kake iya shigo wa cikin fadar nan cikin sauƙi? Masarautar nan tana da shingen tsaro na aljanu masu ƙarfi, amma kake ratsa su?"
Cikin gajeriyar magana da murmushin isa ya ce,
"Ta ƙasan ƙasa nake shigo wa... babu shingen da zai iya dakatar da ni daga isowa gare ki."
Suka fara tattaunawa cikin wani salo mai cike da ƙauna. Ayat tana jin yadda zuciyarta take narkewa a duk lokacin da yake kusa da ita. Ta manta da duk tsanar da take masa a baya, yanzu soyayyarsa ta zama jinin jikinta.
Amma duk da haka, saboda izza ta sarauta da kuma nuna kada ya raina ta, sai ta fara janyewa tana yatsine fuska...
Ta furta "Kada ka zata don na rungume ka shikenan na daina jin haushinka. Na yi hakan ne kawai don ina buƙatar taimakonka a gobe.... Amma idan ka gama, kowa ya san inda yake."
King Diamond ya saki wani ƙasaitaccen murmushi, ya matso kusa da ita har tana jin ɗumin numfashinsa..
"Kin fi kowa sanin cewa zuciyarki ba haka take faɗa ba. Amma zan bi ki a yadda kike so... Gimbiya ta."
Ayat ta kawar da kanta gefe, tana murmushin jin daɗi a ɓoye wanda ba ta son ya gani...
*Likes ɗinku shine albashin marubuci*
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 3️⃣6️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Tun daga ranar yau, fadar ta rikkiɗa ta koma kamar wata duniya ta daban...
Wurin zaman baƙi an shimfiɗa taguwar darduma mai kalar sarauta wadda aka kawo ta musamman daga ƙasar Iran... An jera kujeru na zinare ga manyan sarakuna da malaman da aka gayyato daga ƙasashen Larabawa da Afirka...
An ƙawata fandis da furanni na gaske waɗanda ƙamshinsu ke ratsa ko'ina. A tsakiyar fandis ɗin, an ajiye wasu ƙasaitattun kujerun karatu guda biyu, waɗanda aka ƙera su da itacen Sandalwood da aka yi wa ado da azurfa...
Da daddare, an kunna dubban fitilu masu launin ruwan zinare da azurfa, waɗanda suka sanya daukacin fadar yin haske kamar rana....
Gari ya waye, baƙi sun cika masarauta maƙil. Kowa yana son ganin wannan rana ta musamman..
A sashen Gimbiya Yumna, fara'a ce ta gauraye da ibada. Ba ta da ko ɗigon baƙin ciki a ranta, zuciyarta fari ƙal take kamar kalar shigarta. Bayinta waɗanda ta ɗauke su kamar ƙawayenta, suna ta hidima a kanta..
Ta saka wata doguwar rigar gown na alfarma mai kalar Cream da aka lulluɓe ta da duwatsu masu sheƙi na Swarovski...
An rataya mata wani farin Sash mai ɗauke da rubutun...
(HAFEEDHAH: GRADUATE OF THE HOLY QUR'AN)
Ta saka takalmi High Heels masu sheƙi waɗanda ke ƙara mata tsayi da ƙasaita...
✨✨
🖤 GIMBIYA AYAT
A can nata sashen, Ayat tana shirya kanta cikin natsuwa. Ko da yake ita ma tana cikin farin ciki, amma sirrinta yana nan a ɓoye. Babu wanda ta bari ya taɓa fuskarta duk da cewa yau ce ranar da duniya take son ganinta...
Ta saka wata doguwar riga golden gown mai matuƙar tsada, wadda aka yi mata ado da zaren siliki. Ta yi wa kanta ƙayataccen Rolling na mayafi wanda ya rufe mata kyakkyawar fuskarta wato Niqab style, sai dai idanunta kawai dake sheƙi kamar lu'ulu'u...
Ta sanya wasu dogayen takalmi white Diamond Heels waɗanda suka daidaita takunta na jinin sarauta...
Ta maƙala nata lambar yabon mai rubutun..
(AL-QARI'AH: THE QUEEN OF TILAWAT)...
Bayan Ayat ta gama tsara kanta cikin kwarewa, sai masu kula da ita suka shigo ɗakin cikin girmamawa. Sun zata za su taimaka mata wurin kwalliya, sai suka ga ta riga ta gama komai, tana tsaye kamar wata tauraruwar da aka sauko da ita daga sama, fuska a rufe amma kwarjininta ya cika ɗakin...
"Gimbiya, kowa yana jiran ki a filin taro." in ji ɗaya daga cikin hadiman..
Ayat ta jinjina kai, zuciyarta na bugawa. Ta san cewa yayin da take tafiya zuwa filin taron a matsayin Gimbiya, masoyinta King Diamond yana can tsaye a matsayinta na Inuwa, yana kallonta ta bayan rawaninsa....
Ta ce dasu "ku je, gani nan sauƙo wa.."
Haka duk suka juya, ita kuwa kafin ta gama duka kanta sai ga King Diamond ya bayyana, ganinsa yasa ta firgita domin har ta tsora saboda zuwan ba zata...
Ta ɗago tana kallonsa cike da mamaki ta ce, "ina shigar da kace zakayi a matsayin Inuwa?..."
King yayi murmushin gefen baki sannan ya furta, "Ina so na zama mutum na farko da zai baki kyauta a wannan rana ta farin ciki..."
Daga nan ya ware tafin hannunsa sai ga wani tsararren sarƙa mai sheƙi da rubutun sunanta a ɗan ƙasin sarƙar....shi da kansa ya ɗaura mata a wuya, sannan ya sanya mata zoben sarƙar tare da sumbatar ta akan goshi...
Daga nan ya ɓace..
Murmushi tasau ita kaɗau tasan irin shauƙin da take ciki yau..
✨
Kamar yadda aka tsara, taron ya kankama. Filin fadar ya cika makil da sarakuna, manyan malamai, da jakadu. Lokacin da kiɗan sarauta na musamman (Trumpets) ya kaɗa, sai daukacin taron suka mike tsaye...
Gimbiya Yumna ce ta fara fitowa, tana murmushi mai cike da annuri. Takunta cikin hills ɗinta yana bayar da sauti a hankali tak.. tak.. tak.., sannan aka biyo bayanta da Gimbiya Ayat...
Ayat tana tafiya ne kamar tana shawagi a iska. Duk da fuskarta a rufe take da mayafin gown dinta da ta yi masa Rolling na musamman, amma kwarjinin idanunta kadai ya isa ya sanya mutane faɗuwan gaba. Waccan Sash dake jikinta mai rubutun AL-QARI'AH tana ta sheki karkashin hasken fitilu.
A gefen fandis inda ɗaukacin tsaro yake, Master Ibrahim yana tsaye da babban mukaminsa. A kusa da shi, King Diamond ne a matsayin Inuwa, sanye da kakin soja mai muƙami, fuskarsa sanye da rawani yadda babu mai gane shi.
Master Ibrahim ya daɗe yana lura da yaron nasa na yau...
Cikin raɗa ya ce "Inuwa, yau kuma wane irin shiru ne haka? Tun da safe baka ce uffan ba, baka ma motsi. Kwarjinin taron ne ya firgita ka ko kuwa me?"
King Diamond bai ko kalle shi ba, bai kuma ba shi amsa ba. Ya tsaya ne kamar gunki, idanunsa na kyam akan Ayat dake takowa... Wani irin kallo yake mata, kallon kariya da kuma tsananin shauki..
Master Ibrahim A ransa ya furta "Wannan yaron yau kam ya sauya min, kwarjininsa ya ninka na kullum sau ɗari. Kamar ma ba mutum ne tsaye a kusa da ni ba!"
Bayan an zauna, aka sa karatun Kur'ani mai ratsa zuciya da jiki, sannan akayi wa'azi akan masu karatun Alkur'ani...
Bayan nan ne aka buƙaci sauraron karatun masu sauƙa..Aka ba Gimbiya Yumna dama ta fara tilawa...
Ta karanta surori cikin daɗi da natsuwa, kowa ya jinjina mata. Amma lokacin da aka ƙira Gimbiya Ayat, filin taron ya yi tsit kamar babu rai a cikinsa...
Ayat ta matso gaban babban makirufo. Ta gyara zamanta, sannan ta fara sakin muryarta cikin Suratur-Rahman..
_"Ar-Rahman... 'Allamal Qur'an..."_
Muryar Ayat ta fito cikin wani irin sauti mai daɗi, mai sanyi, kuma mai ratsa jiki. Ba muryar ɗan adam bace kaɗai, domin King Diamond yana can tsaye yana tura mata wani irin taimako na spiritual aura wanda ya sa muryar ta riƙa amsa a cikin zukatan mutane...
Manyan Malaman dake zaune a sahun gaba suka fara zubar da hawaye. Wasu sarakunan suka sauƙe kawunansu ƙasa saboda tsananin tasirin ayoyin. Muryar tana tashi tana faɗuwa cikin kwarewa ta musamman...
A daidai lokacin da Ayat take kaiwa kololuwar karatunta, ta ɗago idanunta ta kalli inda Inuwa yake tsaye. Idanunsu suka sarƙe da na King Diamond. A wannan lokacin, Ayat ta ji wani irin karfi ya shigeta, ta sani cewa masoyinta yana nan kusa da ita, yana kare mata sirri da kuma kwarjini...
Shi kuma King Diamond, duk da siffar Inuwa dake jikinsa, murmushin nan nasa na gefen baki ya bayyana a ɓoye. Yana jin alfahari da wannan gimbiyar tasa wadda duniya take kuka saboda dadin muryarta...
Master Ibrahim ya lura da wannan kallon na Ayat, ya sake kallon Inuwa...
Zuciyarsa ta buga
"Me yake faruwa tsakanin Gimbiya da wannan Guard ɗin nawa? Wannan kallon ya wuce na soja da gimbiyarsa!"
Duk da cewa Maayah ba ta cikin masu saukar Alkur’ani saboda waccan matsala ta karatun, hakan bai hana ta nuna cewa ita ma gimbiyar masarautar Alhamra ba ce. Ta fito cikin shigar alfarma, sanye da doguwar riga mai kalar maroon da aka yi wa ado da duwatsu zinare... Bayinta na take mata baya, tana taku cikin isa har ta isa mazauninta ta zauna, tana kallon kowa da kallon ko oho...
Ita a ganinta, taron ma ya isheta, domin babu ita a ciki. Tana nan zaune tana kallon jama'a, sai kwatsam idonta ya sauƙa akan kofar shigowa...
A daidai lokacin ne Uncle Jalal ya shigo harabar fadar. Ya zo ne a kan wani babban Superbike mai launin baki da ja, irin wanda ake tseren gudu da su... Ya cire babban