Showing 126001 words to 129000 words out of 154131 words
Chapter 43 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
ƙasa, sannan Ya ce masa Kasance, sai ya kasance. .”
Ajin ya yi shiru..
Malami ya ce, “Excellent.”
Malami ya ci gaba..
Tambaya ta biyu
“Wace aya ce ta yi magana akan cewa Annabi Isa bai mutu ba, Allah Ya ɗaukaka shi?”
Ching-Ching ta sake miƙe wa..
Ta ƙara da cewa
وَمَا قَتَلُوهُ وَمَا صَلَبُوهُ وَلَٰكِن شُبِّهَ لَهُمْ
“Sun kashe shi ba, sun gicciye shi amma sai aka rikita musu tunani...”
Malamin ya tsaya yana dogon tunani akan fassarar amsar, amma ayar dai-dai ne...
Nan malamin yayi murmushi sannan ya ce,
"...Ba su kashe shi ba, kuma ba su kafa shi a kan cross ba wato giciye, amma dai an nuna musu kamanninsa ne..."
Malamin ya ci gaba da darasin..
Allah ya kare shi daga mutuwa a hannunsu...
Wannan yana karyata imanin da wasu suke da shi na cewa an gicciye shi a Crucifixion...
Mafi yawan malamai kamar su Ibn Abbas sun fada cewa, lokacin da sojoji suka shiga gidan da Annabi 'Isa yake, Allah ya canza fuskar wani mutum daban, wasu sun ce maci amanar nan ne Judas, wasu kuma sun ce ɗaya daga cikin almajiransa ne ya bada kansa ta koma daidai da ta Annabi 'Isa... Sai suka dauki wannan mutumin suka kashe shi, suna tunanin Annabi Isa ne...
Aya ta gaba ta ci gaba da cewa, "A'a, Allah ya ɗaukaka shi ne zuwa gare Shi..."
Wannan ayar tana cikin Suran An-Nisa (Sura ta 4), aya ta 157. Tana daya daga cikin ayoyi mafi muhimmanci da suke bayyana gaskiyar abin da ya faru da Annabi Isa (AS) lokacin da Yahudawa suka yi ƙoƙarin kashe shi...
Ching Ching ƙare shi da kallo, duk tasan wannan domin Malam Musa akwai ranakun da yake ware wa don bayyana tarihi da ayoyin da suke cikin Alqur'ani...
Bayan ajin yayi shiru sai kawai ta yi wani kwafa mai ƙarfi tana faɗin
"Allah yasa Arna su ji ka...don kashe ka zasu yi.."
Ƴan ajin ne suka yi dariya daga bisani
Malamin ba tare da ya ce komai ba, ya sake jefa wata tambaya
“Wace aya ce ta nuna cewa Annabi Isa bawa ne na Allah?”
Wannan karon wata ce ta miƙe ta amsa
إِنْ هُوَ إِلَّا عَبْدٌ أَنْعَمْنَا عَلَيْهِ
(Suratuz-Zukhruf: 59)
Malami ya girgiza kai yana murmushi..
“Alhamdulillah…”
Sai malami ya ce...
“Yanzu tilawa zamu yi.”
Kowace ɗaliba da surar da take...
Malamin ya tambayi Ching-Ching surar da take..
Ta ce cikin tana juya ido.
“Suratul Aal-Imran.”
Ta fara karatun tajwidi har ta zo yadda ta tsaya domin ba ta gama surar ba...
Bayan an tashi..
Malami ya ce...
“Miss Ching-Ching, who taught you all this?”
Ta turo baki tana murmushi..
“Malam Musa… but sometimes I argue with him.” 😌
Malamin ya ce
"Ma sha ALLAH, duk Allah ya haɗa miki, boko da Arabic, ina ma ace ke ƴata ce..."
Ching-Ching ta turo baki ta ce,
"Hu uhmmmmm! Ni fa ƴar sarki ce, ƙanwar sarki kuma amma kai na ga ba ka da wani sarauta..."
Haka malamin ya biye mata suka riƙa hira har aka zo ɗaukanta itama..
Iya bodyguards ne suka zo..
Tare da Gely...
Ganinsu ya sa Ching Ching ta fara murguɗa baki, ita tayi tunanin da jirgi xa'a zo ɗaukanta....
Kamar sauran...
*Likes ɗinku shine albashin marubuci*
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 3️⃣4️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Washegari gari ya waye da wata irin sanyayyar ni'ima. Master Ibrahim ya tare Inuwa a hanyar fita daga sashen tsaro..
"Inuwa, ka shirya. Zuwa gobe akwai wani katafaren training da nake so ka gudanar a wajen masarauta. Ina son ganin sabon salo a tare da kai."
Muryar a shake Inuwa ya ce, "An gama Master. Zan ɗan fita ne yanzu akwai abin da zan dubo."
Master ya ce, "Duk yadda za ka je, kada ka daɗe. Ka sani kaine kashin bayan tsaron nan a yanzu."
Ayat ta fito sanye da kakin sojan tsaron masarauta, takunta cike da isa da ƙasaita na babban jami'i mai muƙami... Tana tafiya ne tana sauri, rataye da wata jaka wadda yake ɗauke da tulin gwala-gwalai da zinarai waɗanda ta kwaso daga taskarta da kuma wadda Zayana ta ba ta, burinta ta je kasuwa ta canza su ta raba wa talakawan da ke shan wuya...
Tana isa wani fili mai nisa da fadar, inda bishiyoyi suka yi inuwa, ba zato ba tsammani sai ga wata mahaukaciyar guguwa ta tashi! Ƙura ta turnuƙe wajen, bishiyoyi suka fara rawa.
Cikin tsakiyar guguwar, wani haske ya bayyana, nan take King Diamond ya bayyana a gabanta, tsaye daram kamar bishiyar kuka, kwarjininsa ya cika wajen..
Inuwa ta firgita, ta fara waige-waige cikin tashin hankali..
"Me ya kawo ka a wannan lokacin?! Idan wani ya gan ka fa? Kana son tona min asiri ne?"
King Diamond cikin muryarsa mai amo kamar rugun tsumi ya ce,
"Kada ki damu, babu wanda zai gan ni. Na riga na dakatar da idon kowa a wannan yankin. Mu biyu ne kawai a nan."
Idanunsa suka sauka akan jakar da ta ƙanƙame. "Wannan jakar fa? Me kike ɓoyewa?"
Inuwa ya ce, "Gwala-gwalai ne da zinarai. Ina son in kai kasuwa in canza su zuwa kuɗi domin in rabar wa talakawa su samu abin dogaro."
King Diamond ya matso kusa, ƙasaitaccen murmushi ya bayyana a fuskarsa.
"Inuwa, bakya tsoron a fara zargin ki? A matsayinki na guard, ta yaya za ki mallaki waɗannan dukiyar? Ko babban Commander ko Master ba su isa su mallaki ko kashi ɗaya cikin goma na abin da ke cikin jakar nan ba. Idan kika nuna waɗannan a kasuwa, asirinki zai tonu, za a ce sata kika yi."
Inuwa ta daske, maganar ta doke ta. "Haka ne... ban yi tunanin hakan ba."
King Diamond ya ce, "Kada ki damu. Riƙe jakarki da kyau."
Kafin Inuwa ta ankara, King ya ɗaga hannunsa ɗaya, wani irin haske mai launin zinare ya ratsa cikin jakar. Inuwa ta ji jakar ta fara yin nauyi, tana ƙaruwa tana kumbura. Cikin ƙiftawar ido, zinarun da ba su kai rabin jakar ba, suka rikkiɗa suka koma tulin takardun kuɗaɗe sababbi ƙal, har jakar ta kasa rufuwa saboda cika!..
"Yanzu za ki iya tafiya. Waɗannan kuɗaɗen ba za su taɓa karewa ba har sai kin gama biyan buƙatar kowa. Kuma babu wanda zai yi zargin kuɗi a hannun jarumi."
Inuwa ta kalli jakar, ta kalli King Diamond cikin mamaki da godiya.
"Nagode... ka cece ni daga babban tarkon da zan faɗa."
Kafin ta rufe baki ta ji ya ce, "zan iya raka ki?..."
Ayat ta tsaya tana kallon kanta, ranta ya baci da shawarar King Diamond na raka ta...
"Tabb! So kake a akawo min farmaki? Idan aka ganni soja da kai, tambayar duniya za a rika yi, har magana ta kai kunnen Abul. Ko ka manta ni ma a boye nake?"
Cikin muryarsa mai natsuwa ya ce, "Idan wannan ne damuwarki, ai maganinta mai sauki ne."
Cikin dan lokaci, King Diamond ya nuna ta da yatsa, nan take kakin sojan jikin Ayat ya rikida ya koma doguwar bakar abaya mai santsi, tare da mayafi da nikab wanda ya boye fuskarta..
Ta dubi kanta ta ce, "To, shikenan ni na koma mace. Amma kai fa? Da wannan dogon farin gashin naka? A garin nan babu mai irin sa sai tsohon da ya haura shekara dari, ko kuma... Aljani! Dole ka canza..."
King Diamond ya gyara tsayuwa, nan take farin gashin kansa ya juye ya koma bakikirin, mai santsi da tsawo, wanda ya kara fito da kwarjininsa na matashi ɗan gayu mai jini a jika. Ayat ta saki baki tana kallo, sannan suka nufi kasuwa.
Suna isa cikin kasuwar Alhamra, sai kace an tsayar da lokaci. Hayaniyar ciniki ta tsaya, kowa ya daskare. King Diamond ne yake taku cikin kasuwar, kwarjininsa kamar rana, kyawunsa ya zarce duk wani tunani na dan adam.
Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un! 🥺
Ba mutuwa akayi ba, illar kyau ce! 'Yan matan kasuwa sun yi matuƙar ruɗe wa, kowa ya saki abinda yake tallatawa..
Wata budurwa dake siyan kayan miya, tana kallon King Diamond, nan take ta ji jikinta ya sake, wandonta na ciki ne ya jiƙe jagaf kamar wacce tayi fitsari saboda tsananin gigita da kwarjini... Da wani irin matsanancin sha'awarsa...!
Wasu kuma suka fara sumbatu..
"Wannan mutum ne ko mala'ika?",
"Wallahi idan na aure shi na gama rayuwa!"
King Diamond kuwa yana tafiya ne kamar baya taku a ƙasa, Ayat tana gefensa a cikin nikab ɗinta, tana jin duk kalaman banza da 'yan matan ke jefawa masoyinta...
Wata kyakkyawar budurwa, ganin su King Diamond sun kusa isowa kusa da ita, sai ta shirya tarkon so..
Ta matsa gaba kaɗan, daidai zasu wuce, sai ta sake jiki da gangan ta lula zata faɗi a jikin King Diamond don ta ji dumin jikinsa.
Amma King, kamar mai idanu a ko'ina, a slow motion ya yi wani irin taku na kwarewa wanda ake ƙira da Sidestep, ya goce mata tare da yin baya, ba tare da ya bari ko rigarsa ta goga tata ba..
Gippp! Yarinyar ta faɗi a kasa, Ta ɗago tana lumshe ido cikin kissa, ta mika hannu ɗaya tana kallon King Diamond da irin nuna soyayya, tana rokon ya kama hannunta ya tada ita.
Ayat dake cikin nikab, ranta ya kai babban matsayi na tafasa. Ta kasa jure ganin yadda matan nan ke hauka akan naman ta...
Cikin zafin nama da kishi, Ayat ma ta yi baya yadda King ya yi, ta watsa wa yarinyar dake kasa wani kallon kiyayya ta cikin nikab. Sannan, ta mika hannunta ta makala a cikin na King Diamond, ta rungume damtsen hannunsa da kyau irin na mata da miji, ta manne a jikinsa..
A ranta ta ce, "Kuji dashi! Nawa ne ni daya!"
Suka bi ta gefen yarinyar dake zaune a kasa cikin kunya, suka tafi suna taku daya-bayan-daya. Yarinyar ta daskare a kasa, idonta na bin bayan King Diamond da kishi da sha'awa, tana mamakin wace sa'ar ce wannan dake kumshe a cikin nikab dake rungume da wannan sarkin Kyawun"....
Bayan sun ɗan yi nisa da taron matan da suka ruɗe, Ayat ta zame hannunta daga na King cikin fushi da yatsine fuska duk da nikab ɗin ya ɓoye hakan, sautin muryarta ya bayyana komai...
"Tafi can daga nan! Ni fa gaskiya banga wani kyau a tare da kai ba da har mata za su riƙa hauka a kanka haka. Dubi yadda kake wani mumu da kai... uhmmm, wai wannan ne kyan? Ko kaɗan ma!"
King Diamond bai ce uffan ba, ya dai saki wani ƙasaitaccen murmushin gefen baki wanda ake ƙira da side smirk... Ya san sarai cewa kishi ne ke sanya ta wannan surutun, kuma kasancewarsa mutum mai kwarjini da rashin son yawan magana a cikin taro, sai ya kyale ta ya ci gaba da takunsa na isa...
Daga nan Ayat ta nufi lungu-lungu na kasuwar inda talakawa da gajiyayyu suke. Ta buɗe wannan jaka mai mu'ujiza wadda King Diamond ya cika mata da maƙudan kuɗaɗe..
Ga Makafi da Kutarai, Ayat ta shiga raba tulin kuɗaɗe, duk wanda ta ba wa sai ya ji kamar mafarki yake yi. Makafi suka sa albarka, kutarai suka ɗaga hannu sama suna kuka..
Sai Nakasassu da Masu Ƙananan Jari da matan da ke soya awara ko sayar da ganye, Ayat ta riƙa zazzaga musu kuɗin da ya ninka jarin su sau ɗari.
Ga Matasa Marasa Sana'a.. Ta kira su ta ba su maƙudan kuɗaɗe a matsayin tallafin fara rayuwa..
Duk inda suka ratsa, mutane sai kallon King Diamond suke yi, suna zaton shi ne babban mai kuɗin.. Kwarjininsa ya sa mutane ma sun kasa tambayar ko su waye, sai dai kawai godiya da addu'a..
Ayat tana cikin rabon kuɗin nan cikin sauri, tana jin daɗin yadda mutane ke farin ciki, amma lokaci guda tana lura da King Diamond wanda ke tsaye kamar dutse, yana kiyaye duk wani motsi da zai zama barazana gare ta.
Tana tsaka da raba kuɗin nan, sai ta hango wasu jami'an tsaron masarauta guda uku suna tahowa ta sashen da take. Sun ga taron mutane sun kewaye wasu baƙi, kuma sun fara zargin akwai wani abu da ke faruwa..
Daya daga cikin sojojin ya daka wa mutane tsawa..
"Ku matsa! Waye wannan yake raba kuɗi ba tare da izinin mu ba?!"
Ayat ta daskare. Ta san idan waɗannan sojojin suka matso kusa, za su iya gano asirin jakar, ko kuma su gane cewa King Diamond ba ɗan garin ba ne...
Sojojin da suka taho da zafi da nufin yin bincike, sai suka daskare a inda suke na wasu daƙiƙo'i. King Diamond ya yi amfani da sihirinsa ya shafe dukkan abin da ke cikin tunaninsu game da raba kuɗin ko ganin wasu baƙi..
Daya daga cikin sojojin ya sosa ƙezo, ya kalli ɗan uwansa cikin rashin fahimta.
"Wai me ya kawo mu nan ne?"
Ɗayan ya murza idonsa, ya duba hagu da dama, ya ga mutane na harkokinsu na yau da kullum domin su ma sun daina hayaniyar...
"Oho! Ni kaina na manta. Kamar akwai abin da zan duba, amma yanzu komai ya fice min a kai."
Suka juya baya, suna tafiya suna nuna wa juna hanyar da za ta mayar da su fada, kamar ba su ne suka taho cikin jarumta ba..
Ayat ta sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya, ta kalli jakar ta ga sauran kuɗaɗen sun ƙara yawa ma. Cikin gaggawa ta ƙarasa zazzaga wa wasu tsofaffi da ke zaune a gefen kasuwa, sannan ta rufe jakar..
Ta ɗago ta kalli King sannan ta ce, "Nagode King. Da ba don kai ba, da yanzu asirina ya tonu a hannun waɗancan mutanen."
King Diamond ya gyara tsayuwa, ya kalle ta cikin natsuwa. "Wajibi ne in kiyaye ki. Amma yanzu lokaci ya ƙure, dole ki koma kafin a fara nemanki a masarauta."
Haka suka bar dandalin kasuwar, inda Ayat ke tafiya tana waige-waige, shi kuma King Diamond yana biye da ita kamar inuwarta, kwarjininsa na ci gaba da sace zukatan duk macen da ta kuskura ta kalle shi...
Bayan sun bar kasuwa sun isa wani lungu kusa da fadar, King ya tsaya ya kalli Ayat. Da wani sassanyan haske na sihirinsa, ya mayar da ita yadda take a farko sanye da kakin sojan tsaro mai muƙami, fuskarta sanye da gashin baki da gemu na boki...
Kafin King ya ɓace, su biyun sun tsaya suna kallon juna. Wani kallo ne mai zurfi, cike da wata irin soyayya da babu kalmomin da za su iya fassara ta. Kallo ne na amana da kaunar da ta ratsa zuciya. Cikin ƙiftawar ido, King Diamond ya ɓace kamar bai taɓa kasancewa ba.
Inuwa tana tafe tana murmushi, tunanin kallon da King ya mata ne yake sake mata daɗi a zuciya. Bata ankara ba, sai ta yi kuciɓis da Master Ibrahim..
Ganin yadda Inuwa yake ta faman murmushi shi kaɗai, Master ya tsaya ya zura masa ido cikin mamaki da zargi.
Ya ce, "Lafiya Inuwa? Da wa kake wannan murmushin haka kamar wanda ya sami dukiya ko ya haɗu da masoyiya?"
Inuwa ya firgita, ya fara in-ina domin ya rasa abin da zai ce wa Master..
"Eh... dama... Master, kawai tunanin wani abu ne na daban..."
Daidai lokacin da Master yake ƙoƙarin ƙara bincikar Inuwa, sai idonsa ya sauƙa akan wata zurariyar budurwa wadda ta shawo kwana, tana taku cikin takama ta juya musu baya tana tafiya..
Master ya jinjina kai, ya saki wani murmushi na takaici, yana zaton Inuwa ita yake kalla shiyasa yake murmushi.
Master ya ce, "Lallai Inuwa... ashe abin da ya tsayar da kai kenan? Na tambaye ka ka ƙi faɗa min, ashe kallon wannan yarinyar kake? Ban hana ka bin mata ba a cikin aiki?"
Inuwa ya rasa yadda zai bayyana wa Master cewa sam babu ma maganar wata mace, kawai saɓani ne aka samu a lokacin da ya shigo ita kuma ta shawo kwana. Amma don ya wanke kansa, Inuwa ya sunkuyar da kai kawai..
"Yi haƙuri Master, ba haka ba ne yadda kake tunani..."
Master Ibrahim ya taɓa kafaɗarsa, fuskarsa ta koma ta soja mai tsanani, ya ce.
"Kada ka bari ra'ayin zuciya ya rage maka kaifin basirarka ta soja. Na dakatar da kai ne domin in tunatar da kai. Gobe da asubanci za mu fara gudanar da training ɗinmu na musamman. Ina son ka shirya tsaf, domin horon gobe ba na wasa ba ne."
Inuwa ya ce, "An gama Master. Zan kasance a can kan lokaci."
Inuwa ya wuce zuwa sashensa yana ajiyar zuciya, yana mamakin yadda Master ya yi masa mummunar fassara, amma kuma zuciyarsa tana can kan King Diamond...
✨✨✨
Lokacin tafiya makaranta, kamar yadda Uncle Jalal ya sanar, yau ya zo ɗaukanta..
Maayah ta tsaya turus a bakin motar Uncle Jalal, tana kallon tsohuwar katuwar motar tasa mai tauri da kwarji amma ba irin wadda ta saba hawa ba...Domin motar karɓa yayi a wurin wani malami don ya zo ɗaukanta, a yayinda ya bar mashin ɗinsa da helmet acan makarantar...
Ta fashe da wani irin kuka na shagwaba, tana buga kafafunta a kasa..
"Wallahi ba zan taɓa hawa wannan kaskantacciyar motar ba! Ina bodyguards dina? Ina motoci na masu sanyin AC? Abul! Abul!! Ka fito ka ga abinda malamin nan yake shirin yi min!"
Hadiman gidan duk sun taru suna kallon ikon Allah, amma babu wanda ya isa ya tari Uncle Jalal, domin kowa ya san yana da cikakken ikon Sarki.
Uncle Jalal ya ɗaure fuska, tare da matso kusa da ita, muryarsa ta daka wani irin amo da ya sa Maayah ta tsagaita kukan dole..
"Ke! Idan ba ki mun shiru ba, zan miki dukan da baki taɓa jin labarin irin sa a rayuwarki ba. Daga yau kishin ki da daularki sun kare a kofar gidan nan. Shiga mota yanzu!"
Maayah ta yi tsuru, ganin babu wani bodyguard da zai zo ya tunkuɗe shi. Cikin kunkuni da kukan kissa, ta bude kofar baya ta zauna tare da turo baki..
Uncle Jalal ya ce, "Fito ki dawo gaba! Ni ba direbanki ba ne, ni malamin ki ne. Kuma anan gaba za ki koyi yadda ake mutunta na gaba da ke."
Dole Maayah ta fito ta dawo gaban motar, tana kakkabe kujerar kamar tana taba kashi...
Uncle Jalal ya tada motar, suka bar fadar masarautar Alhamra. Iska na bugun fuskarta domin bai kunna AC ba, ya bar tagogin a