Showing 57001 words to 60000 words out of 154131 words
Chapter 20 - Masarautar Alhamra Complete Hausa Novels By Asmeetah Writer.txt
da kansa. “Kawai na tsaya ne don in tabbatar ba ka samu matsala ba...Inuwa, me ya sa kake da wata irin siffa daban da sauran maza? Ko fata dake jikinka, ta fi ta maza taushi.”
Inuwa ta ji gabanta ya faɗi. Ta san asirinta yana shirin tonu muddin Ibrahim ya ci gaba da bincike.
“Master, kawai dai ina kula da kaina ne. Amma yanzu ina bukatar in tafi, ina buƙatar yin sallah...”
Ta tashi da sauri za ta fice, sai Ibrahim ya damƙi hannunta. Wani irin shock ne ya ratsa su duka biyun..
Ibrahim ya ji hannun Inuwa yana da santsi da kyan gani, ba hannun soja da ya saba riƙe takobi ba..
“Akwai sirri a tare da kai, Inuwa,” Ibrahim ya furta yana ƙara matse hannun..
“Kuma ba zan bar kowa ya taɓa ka ba, sai ni. Daga yau, duk inda zaka, ina tare da kai. Na riga na nemi izinin Sarki cewa za ka kasance mataimakina na musamman (Personal Assistant).”
Inuwa ta zare ido. “PA na musamman? Wannan ai yana nufin zan rinka kwana da tashi ne a karkashin idonsa!”
“Amma Master...”
“Babu amma! Wannan umarni ne.” Ibrahim ya miƙe, ya matso kusa da ita har tana iya jin bugun zuciyarsa.
“Idan wani ya taɓa ka, tamkar ya taɓa ni ne. Kuma na lura, tun lokacin da aka tafi da Gimbiya Ching Ching, kake cikin damuwa. Me ya haɗa ka da ita?”
Inuwa ta haɗiye miyau. “Ita... ƙanwata ce a wurin aiki. Ina sonta kamar yadda kowa yake sonta.”
Ibrahim ya ji wani kishi ya turnuƙe shi, duk da cewa Inuwa ya ce ƙanwarsa ce...
“To ka sani, yanzu ni ne gaba da ita a wurinka. Muje, ka je kayi sallah ..”
Suka fito daga sashen, Inuwa tana taku cikin sanyi tana ƙoƙarin ɓoye asalin mace da take da shi, yayin da Ibrahim yake tafiya a gefenta kamar zaki dake kare abincinsa...
A can kuryar fada kuwa, Sarki Nourdeen yana zaune shi kaɗai, yana kallon hoton Ching Ching dake hannunsa. Zuciyarsa tana tunanin yarjejeniyar da ya kulla da Chief Onyx.
“Ina fatan wannan sakalcin na Ching Ching ba zai sa Chief Onyx ya kashe ta ba,”
Sarki ya yi ajiyar zuciya.
✨✨
Bayan Kwanaki Biyu
A yau ne wa’adin hutu da kyan-kkyasan da aka yi wa Ching Ching ya cika. Chief Onyx ya ba da umarnin a kawo ta babban falonsa inda yake gudanar da ayyukansa...
Ching Ching ta shigo tana turo baki, sanye da wata riga mai ruwan hoda wadda ta yi mata kyau matuƙa, amma fuskarta babu annuri...
Ta iske Chief zaune a kan wata kujera ta alfarma, Gely tana gefensa tana duba wasu hotuna a hologram..
“Daga yau, ke ce zaki rinƙa kula da wannan ɓangaren,"
Chief ya faɗa ba tare da ya ɗago ya kalleta ba. “Zaki share, ki goge komai, sannan ki tabbatar babu ƙura ko ɗaya a kan teburina.”..
Ching Ching ta zaro ido, ta kalli hannayenta masu taushi.
“Aiki? Ni Gimbiya Ching Ching ce zan yi share-share? To wallahi ba zan yi ba! Ko a gidanmu Daddy bai taɓa ce min in ɗaga tsintsiyar ba. Sai dai in kalli tattai in yi wasa!”
Ta zauna a tsakiyar falon ta fasa kuka. “Ni yunwa nake ji! Kuma bana son robots, zuma nake so!”
Gely ta matso kusa da ita,
“Wannan shi ne umarnin Boss. Idan ba ki yi ba, ba za ki ci abinci ba.”
“Ke dakata min!”
Ching Ching ta miƙe tsaye tana nuna Gely da yatsa..
“Kinyi tsammanin tsoronki nake ji? Ke dake baki da jini? Kije ki ba ni waje tun kafin in ɓata muku wannan gidan da ihu..!”.
Ta nufi teburin Chief, ta ɗauki wata na’ura mai sheƙi tana jujjuya ta. “Wannan meye? Abun wasa ne?”
Chief Onyx ya damƙe hannunta cikin fushi...
“Stop it! Wannan na’urar tana iya tayar da boma-bomai a duk inda nake so. Leave it!”
Ching Ching ta harareshi, ta matso kusa da fuskarsa har tana shaƙar ƙamshinsa..
“Ba zan bari ba! Sai ka fara ba ni zuma ta musamman, sannan ka ba ni izinin in ƙira Daddy a waya. In ba haka ba, wallahi sai na lallata maka wannan ƙarfen dake fuskarka!”
Maimakon ya ji tsoro, Chief ya ji wani irin takaici ya ziyarce shi. Yarinyar nan mai shekara 16 amma halinta na ƴar shekara 3 ne...
Ya janye hannunsa ya nuna mata ƙofa. “Gely, ba ta aikin da ya fi ƙarfinta. In ba ta gama ba, kada ta fita.”
Ya tashi ya bar falon gaba ɗaya..
Daga nan Ching Ching ta fara nata wasan..
Maimakon ta yi sharan, sai ta ɗauki ruwan goge-goge ta rinka fesa wa Gely a jiki tana cewa,
“Kema sai na miki wanka, tunda baki da aiki sai goyon bayan Boss ɗin ki ko?!”..
Gely ta fara samun matsala (malfunctioning)
Sakamakon ruwan da ya shiga jikinta, tana ta rurruwa. Ching Ching ta tintsire da dariya, ta hau kan kujerar Chief ta fara tsalle-tsalle tana rera waƙar ta...
Daƙyar Gely ta samu ta kuɓuce, ta je ta gyara kanta..
Ching Ching ta fara wasan ƴar gala-gala a falon..
Ba ta sani ba, Chief Onyx yana can wani ɗakin yana kallon komai ta allo, yana dafe da kai...
“Wace irin bala’i ce wannan Sarki Nourdeen ya bani?”
Ya tambayi kansa cikin muryar da ke cike da nuna cewa shagwaɓar Ching Ching ta fara ratsa katangar da ya gina a zuciyarsa...
Ching Ching ta ja wani uban ajiyar zuciya, tana kallon babban falon Chief Onyx wanda ya ke kamar filin ƙwallo saboda girma...
Sai ga Gely ta shigo, ta ba ta wani mopper mai sulɓi da wani ruwa a gwalba ta ce ta goge teburin cin abinci (dining area) da babban bango na gilashi...
“Wannan aikin ai na robots ne, me ya sa za a sa ni?”
Ta ɗaka ƙafa tana kukan shagwaɓa, amma Gely ko kallo ba ta ishe ta ba ta fice daga falon...
Ching Ching ta fara goge teburin tana tafe tana rera waƙar "Daddy na, Abul na...Ni gimbiya Ching Ching...".
Tana kaiwa kusa da wani ƙaton Plasma TV wanda ke manne a jikin bango, wanda girmansa ya ninka nata sau biyar. Allon na musamman ne, domin ta nan ne Chief yake sarrafa dukkan tsaron birnin Pavilion.
“Wannan madubin meye a ciki yake ta walƙiya? Ya cika ƙura wallahi!”
Ta furta tana turo baki. Ta fesa wannan ruwan goge-gogen har sau biyar a tsakiyar allon. Ta fara gogewa da ƙarfi, tana tura allon da dukkan nauyinta wai ita a dole sai ta fito da kyali...
Tana cikin danna allon, sai ta ji ya yi wani ƙara “Ƙararasss!”...
Ashe screws ɗin da suka riƙe allon a jikin bangon fasahar zamani ne, kuma sun samu matsala saboda ruwan da ta fesa ya shiga jikinsu.
Kafin ta ankara, allon ya fara sillo wa ƙasa...
“Wayyo Allah! Zai faɗo!”
Ching Ching ta fasa ihu, maimakon ta matsa, sai ta tsaya tana kallon yadda ƙaton allon ya silalo ƙasa
“BAMMM!!!”...
Falon ya ɗauki wata irin ƙara, hasken lantarki ya fara walƙiya a wurin yana sparks... Nan take duk wani haske na falon ya ɗauke, ya koma jajir, muryar na’ura ta fara ƙiran
“Security Breach! System Failure!”
Ching Ching ta fice da gudu ta nufi bayan kujerar Chief ta maƙale, tana kuka sosai...
“Ba ni bace! Wallahi madubin ne ya gaji da zama a jikin bango ya faɗo da kansa! Daddy na!”
Chief Onyx ya shigo falon a guje, ransa ya kai maƙura wajen ɓaci. Ya kalli tarkacen allon da ya watse, ya kalli Ching Ching dake leƙowa ta bayan kujera, idanunta sunyi zuru-zuru...
“Do you have any idea what you just did?!”
Ya daka mata wata uban tsawa wadda ta sanya ta kusan sakin fitsari a wando...
“Kin kashe dukkan na’urorin tsaro na Pavilion! Wannan ba madubi ba ne, wannan shi ne zuciyar birnin nan!”
Ching Ching ta fashe da kukan gaske, ta tunkaro shi tana shure-shure.
“To meye nawa? Me ya sa ka sanya shi a inda hannuna zai kai? Kuma ma ai datti ne da shi shi yasa na goge shi. Wallahi sai na faɗa wa Daddy ka mare ni!”
“Ban mare ki ba!” Chief ya faɗa yana ƙoƙarin danne fushinsa, domin idan ya biye wa yarinyar nan zai iya hauka...
“Kuma ma ni yunwa nake ji! Ka ba ni abinci mai daɗi, sannan ka share wannan dattin da kanka, tunda kai ne ka ajiye shi a nan!”
Ta ƙarasa maganar tana gyara zamanta a kan kujerar tasa ta mulki, ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kuka tana kallon gefe.
Chief Onyx ya tsaya yana kallonta, ya rasa ko kuka zai yi ko dariya. Yarinyar tana komai kamar jaririya...
Ya juya ya kalli Gely wadda ta shigo tana ƙoƙarin gyara allon.
“Gely, share wurin nan. Sannan ki ba ta zuma da duk abin da take so kafin ta rusa gidan nan baki ɗaya.”
Yana fita, Ching Ching ta leƙo ta kalli bayan sa, ta galla masa harara. “Mai fuskar ƙarfe! Ka dai ji tsorona ne shi yasa ka ce a ba ni zuma.”...
✨
Bayan kwana biyu da farfasa babban allon Pavilion, Chief Onyx ya fahimci cewa idan ya bar Ching Ching da aikin ruwan goge-goge, to lallai za ta ruguza masa fada baki ɗaya. Don haka, ya yanke shawarar sanya ta a gaba ya koya mata yadda ake sarrafa computer, ko koda akalla ta rinƙa taɓa ƙananan ayyuka na ofis.
Chief yana zaune a kan babban teburinsa, ya sanya aka kawo wa Ching Ching wata computer ta zamani mai nuna Holographic Tablet...
"Zauna a nan," ya faɗa cikin muryarsa dake nuna gajiya da rigimarta...
"Zan nuna miki yadda ake lissafa yawan energy da Pavilion take amfani da shi. Karki taɓa komai sai abin da na faɗa miki."
Ching Ching ta turo baki, tana wasa da yatsun ƙafarta.
"Ni fa Daddyna ya ce in tafi makarantar sarakuna ne, ba makarantar kafintan kwamfuta ba. Wannan abin gashi nan kamar madubin aljanu."
"Just listen!" Chief ya daka mata tsawa kaɗan.
Ya fara bayani..
"Wannan lambar ita ce X-40, idan kika taɓa ta..."
Ching Ching ta kalle shi, maimakon ta kalli abin da yake nunawa, sai ta ƙura wa fuskar sa ta karfe ido...
"Wai kai bakinka baya ciwo idan kana magana ne? Kuma idan za ka yi hamma ya kake yi? Ko har yanzu baka taɓa yin hamma ba?"
Chief ya rufe idonsa, ya ƙirga ɗaya zuwa goma a ransa don kada ya shaƙe ta.
"Ching Ching, kalli screen ɗin!"
"To na kalla!" Ta fada tana kumbura kunci.
Ya juya kansa don ya amsa ƙiran Gely, ashe tuni Ching Ching ta karkata akalar kwamfutar. Maimakon ta yi lissafin makamashi, sai ta fara zana hoton wata katuwar ƴar tsana mai babban kai da kananan ƙafafu. Ta sanya wa yar tsanar dogon gashi mai ruwan hoda, sannan ta rubuta "MUGUN BOKA" a ƙasan hoton, tana nuna kibiya zuwa wurin da Chief yake zaune...
"Kaga yadda nayi kyau?" Ta tura masa screen ɗin gaban fuskarsa.
Chief Onyx ya kalli hoton, ya kalli rubutun "MUGUN BOKA", sannan ya kalli Ching Ching wadda take faman washe masa haƙora tana jiran yabo...
"Kin share dukkan bayanan tsaron da na dauki shekara biyar ina tsarawa... kin mayar da su hoton yar tsana?" Muryarsa ta fara rawa saboda fushi...
"To ai ƴar tsanar tafi wannan lambobin naka kyau. Duba fa kaga, har hanci na sanya mata mai tsayi, ba irin naka na ƙarfe ba." Ta tintsire da dariya tana tafa hannu...
Chief ya tashi tsaye, ya fizge kwamfutar...
"Gely! Kwashe ta! Kai ta ɗakin girki, ta rinƙa peeling ɗin dankali da karas. Tunda ba ta da hankalin yin aikin ofis, bari ta yi aikin masu abinci!"
Ching Ching ta zabura ta dire daga kan kujera...
"Pelling? Ni Gimbiya Ching Ching zan yi yanka? To wallahi ko danyen dankalin sai na cinye shi duka na barku da yunwa!!..."
Tana fita tana kunkuni, Chief ya koma ya zauna, ya dafe kansa. Ya rasa me ya sa duk rashin kunyar da take masa, baya iya sanya sojoji su yi mata horo mai tsanani. Akwai wani abu game da shagwaɓar tata da yake sanya shi jin kamar fushinsa bashi da tasiri...
A can kicin kuwa, Ching Ching ta samu dankali guda dari a gaba. Ta kalli babban robot din kicin ɗin, ta harare shi.
"Kai ma kallo na kake yi ne? To maza ka fara yankan nan, ni zan zauna in rinƙa kallon yadda kake yi, tunda Daddy na ya ce kowa ya bauta min!"..
Ta jawo kujera ta zauna, ta ɗauki dankali ɗaya ta fara wasan kwallon ƙafa da shi a cikin kicin ɗin, tana ihu...
"Gool!!! Na ci bokan Pavilion gool!!!"....
✨
Bayan kwana ɗaya...
A cikin babban ɗakin bincike na Pavilion (The Science Lab), Gely tana tsaye a jikin wata na’ura tana loda bayanai...
Wannan shi ne lokacin da Gely take tsit, ba ta motsi kamar gunki...
Ching Ching ta shigo ɗakin sanda-sanda, hannunta riƙe da wata ƙatuwar waya screwdriver wadda ta sato a wurin bincike tana gyara, da kuma wata ’yar ƙaramar na’urar wasa da aka aiko mata daga Alhamra mai kukan dabbobi...
"Yau dai kin shigo hannu, ke wannan robot mai baƙar siffa,"
Ching Ching ta raɗa a hankali tana turo baki...
"Kin cika takura min, kowace asuba sai kin zo kin tada ni da wannan muryar taki kamar na tsuntsun karfe. Yau kuma muryar kaza zan sanya miki, don ki rinƙa kukan kakarakaaa idan gari ya waye...!"
Ching Ching ta zagaya bayan wuyan Gely, inda ta ga wasu ƙananan ƙofofin lantarki. Ta fara kici-kicin buɗewa da wayar hannunta. Cikin sa’a, ta latsa wani wurin da aka rubuta “Voice Output Module”...
"Ina kike ne? Eh, ga ta nan!" Ta ciro wasu wayoyi guda biyu ta haɗa su da na’urar wasan tata mai kukan kaza.
A dai-dai wannan lokacin, Chief Onyx yana can ofis ɗinsa tare da wasu manyan baƙi daga ƙasashen Turai waɗanda suka zo tattaunawa kan tsaron duniya...
"Chief, muna buƙatar jin bayanan tsaro daga bakin Gely," in ji ɗaya daga cikin baƙin.
Chief ya latsa agogonsa,
"Gely, zo ofis yanzu, kuma ki ba mu rahoto kan matakin tsaron Pavilion."
A can ɗakin bincike, idanun Gely suka kawo hasken ja, alamar ta tashi daga bacci. Amma Ching Ching ba ta gama haɗa wayoyin ba!
"Wayyo! Ta tashi!" Ching Ching ta tura wayoyin da ƙarfi ta danna su da gam, sannan ta gudu ta ɓuya a bayan labule.
Gely ta nufi ofishin Chief da takunta na ƙarfe tak-tak-tak. Ta shiga ofishin, ta tsaya a gaban Chief da baƙin nasa..
"Yes, Boss. Gely is ready," Gely ta buɗe baki za ta yi bayani...
Maimakon muryar na'ura mai sanyi, sai aka ji..
"Kakarakaaaaaa! Ƙuƙuruƙuuuuuu!"
Baƙin Turawan suka zabura suka miƙe tsaye. Chief Onyx ya zaro ido, ya kalli Gely cikin mamaki...
"Gely, me kike yi? I said give us the security report!"
Gely ta sake buɗe baki tana ƙoƙarin cewa "Status Secure," amma sai aka ji..
"Kaza-kaza-kaza! Ƙuƙu-ƙuƙu-ƙuƙu!"
Ɗaya daga cikin baƙin ya fashe da dariya...
"Chief, shin wannan sabon salon tsaro ne? Ko kuma robot ɗinka ta koma gidan gona?"
Chief Onyx ya ji fuskarsa ta yi zafi, jijiyoyin kansa suka tashi. Ya san ba kowa ya yi wannan aikin ba sai bala'in da yazo da ita daga Alhamra...
"Gely! Shut down immediately!" ya daka mata tsawa...
Gely ta yi shiru, amma kafin ta mutu baki ɗaya, sai na'urar ta buga..
"Meeeee-meeee! Baaaaa-baaaa!" kukan akuya...
Chief ya fice daga ofis ɗin ransa a ɓace, ya nufi inda ya san Ching Ching take ɓuye. Ya tarar da ita a bayan labule, tana ta murna tana tafa hannu...
Tana faɗin
"Kin ga yadda ta zama kaza? Gobe idan ta zo tada ni kukan asuba, sai in yanka ta in sanya a miya!" Ta tintsire da dariya...
Sai ga Chief ya ɗaga labulen...
Chief Onyx ya matso kusa da ita, ya daka mata wata uban tsawa...
"CHING CHING! Kin san kuɗin da na kashe wajen ƙera Gely? Kin sanya ta zama abin dariya a gaban baƙina!"...
Ching Ching ta turo baki, ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka....
"To ni meye nawa? Ai dama cewa kake yi ita mace ce, ni kuma na ga ba ta iya kukan mata ba shi ya sa na koya mata kukan kaza, ai duk kukan mata ne!"
Chief ya dafe kai, ya zauna a ƙasan carpet, abun da bai taɓa yi a rayuwarsa ba, zama a ƙasa....
"Wace irin yarinya ce ke? Ba kya jin magana? Ba kya jin tsoro? Ba kya jin kunya?"
Ching Ching ta matso ta zauna a kusa da shi, ta kalli fuskarsa...
"Bana jin komai sai yunwa. Kuma ka sani, idan ba ka gyara mata murya ta rinƙa waƙar Alhamra ba, gobe kukan kare zan sanya mata, ta rinka cizon mutane!"...
Chief ya kalle ta, ya ga yadda idanunta suke walƙiya da yarinta da rashin sanin ciwon kai. A karon farko, maimakon ya mare ta ko ya daka mata tsawa, sai ya tsinci kansa da yin murmushi a ɓoye a ƙarƙashin fuskarsa ta ƙarfe...
"Zan ba ki zuma gora guda, amma da sharaɗi ɗaya..."
"Meye?" ta tambaya tana washe haƙora.
"Kada ki sake taɓa kowace na'ura a Pavilion ba tare da izini na ba."
Ching Ching ta yi saurin jinjina kai, tana tunanin “Ai ban ce ba zan taɓa motar ka ba, na’ura kawai ka faɗa!” 😂....
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 1️⃣9️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
A ko wace rana, Ayat ta sai tayi kukan da ba ta san lokacin gamawarsa ba...
Zuciyarta tana mata zafi tamkar an watsa mata garwashin wuta...
Ta ci gaba da maganar zuci tana kuka..
"Ta yaya Abul zai yi haka? Me Chingching ta sani a rayuwa? Za ta je ta zama baiwar wani a matsayinta